Showing 129001 words to 130717 words out of 130717 words
zama yar kirki ki cire son yaseer daga zucuyarki saboda babu sauran zama a tsakaninku sanan kinga yar uwarki yake aure ko yaya zuciya batada kashi karkuzo kuna samun matsala"ta jinjina mata kai tace "yaseer ya fita daga rayuwata ummah hadiza tun mintuna arbain da suka wuce daya kirani da tsauraran kalamai wanda har yanzun zafinsu ke barazanar tarwatsa kirjina ummah na cireshi daga rayuwata ban tsanesa ba saidai ba sauran soyayyarsa ki duba kiga saki uku yayimun lokaci daya ummah"bakinta na rawa idonta suka kawo ruwa ummah hadiza taja numfashi ta girgiza kai tace"rabuwarku shine maslaha idan kina tare da yaseer bakida sauran farin ciki saboda idan miji ya kama matarsa da zina to batada sauran kima ko mutunci a idanuwansa bazai taba yarda da itaba dama ace labari yaji ba kunnuwansa suka jiye masa daga bakin da bazai masa karya ba kuma a gabanki dan haka kiyi hakuri koba komi yaseer yayanki ne"
"toh ummah hadiza ina alfahari daya kasance kudin iyayena ne da badan haka ba da bansan inda zan saka rayuwata ba sakamakon wanan halin dana tsinci kaina nasan idan inadaku bazan tabayin kuka ba"ta rungume ummah hadiza tana kuka ummah hadiza ta share mata hawaye tace "kidaina kuka a nan zan kwana tare da ke kinji yar Lelena"tadanji dadi atlis da mutum a kusa da ita ta ware Tasha kunun sosai sanan ta zauna tayi jigum tana tunanin rayuwa da yadda rayuwa tazo mata.....
*****
yaseer na rungume da husnah tace"shiyasa akace zargi babu kyau haramun ne gashi na zargeka da muneeba ashe ba hakan bane kayafemun"dariya yayi yana yawo da hannunsa cikin jikinta yace "aida irin kallon da kikaimun na tabbatar da cewar kinyi ne saboda kishi bayan da kince im zauna da ita yanzun daga ganina daga bangarenta hankalinki ya tashi to inda na barta din fa?"ta turo baki tace "amma tabani tausayi saidai nayi maka uzuri ina kuma fatan cewa kayafe mata ta koma kanwarka kamar yadda kace a gabansu daddy"ya jinjina kai yace "inshaaa Allah zanyi hakan kuma zamu dauketa muje asibiti in an kwana biyu a dubamin ke da lafiyar abinda ke cikinki sanan a duba cikinta asan lafiyar mahaifarta saboda idan ta sake aure ko? tunda tace likita yace akwai kari a gefen mahaifarta dikda tayi amfani da adduoi nasan sharrin tsafi ne amma dai asake dubawa "rungumesa sosai husnah tayi cike da jin dadin yadda ya nuna kulawa yadda ya sauko da wuri murmushi kawai yayi kasan zuciyarsa kuwa daya tuna da abinda muneeba tayi ransa ke baci yaji wata sabuwar tsanarta....
*****
*Agurguje*
bayan wata hudu da faruwar hakan abubuwa sun faru dayawa ciki kuwa harda yadda muneeba ta koma mutuniyar kirki ta cigaba da zamanta tare da momy rayuwa ta sauya itada husnah tamkar yan biyu kome yaseer zaiyiwa husnah sai yayiwa muneeba yake samun kwanciyar hankali cikin husnah yayi girma sosai ya shiga watan haihuwarta yan biyun momy shuraim da sudais sun fara koyon zama kamanninsu daya sak babu banbanci tsabanin kama sukeyi da yar uwarsu husnah wani irin shakuwa ce mai tsanani tsakanin Yaseer da husnah,
husnah na zaune a parlor cikinta yayi zungurere yaseer ya shigo tare da hafeez suna dariya "ah ah lafiya naganku kuna dariya injidai badani kukeba dan kunga nayi muni?"ta turo baki yaseer ya tsugunna a gabanta ya rausayar da kansa cike da tsananin kauna yace "waye ya isa yayi miki dariya sarauniyar mata mai mulki a fadar zuciyata?aiba wanda ya isa yayi miki dariya"tadan hararesa cike da soyayya tace "to dariyar ta me kukeyi?"yaserr ya kara kallon hafeez yayi dariya yana nunasa yace "ya zama kanina yanzun dan ni din yayansa ne ashe guy din nan jirgamu kawai yakeyi?"tadan ware ido tace"ban gabe jirgamu ba mai kake nufi hubby "
"wai ashe dik zuwa gidan nan da yakeyi a kwanakin baya ko ince watanni ashe tuni ya kulla soyayya da nusrah ni bansaniba shegen gora minti minti yake cewa azo aci abinci ashe abinda ke kawosa Kenan itama munafuka bata taba fada ba"dariya sosai husnah tayi cikin farin ciki take kokarin mikewa yaseer ya rubgumota kirjinsa "ya haka yq zaki mike ina zaki ki wahal mun da kanki da babyna?"sai lokacin hafeez yace "kaidai kaji kunya wallahi a gabanmu kake rungume rungume kamar wani bature"husnah ta turw yaseer ta hararesa yana dariya ya shiga kwalawa nusrah kira yaji shiru "ina nusrar take?"
"sun fita da muneeba siyomun abu sakamakon yau dai tin safe banajim dadi kilan dai an kusa yinta ta kare"ya ware ido "to kodai nakuda ce?"ta girgiza kai ta cije lebenta da mararta data d'an mintsineta
hafeez yace "ina sukajene in tarosu?"be rufe bakiba suka shigo da sallamarsu muneeba ta rankwashi nusra "dama nasan shine zaizo yasa kika azalzaleni mutafi gida da muka biya gidan innah"
"au munee dama kinsan suna soyayya?"yaseer ya tambayeta cike da mamaki ta jinjina kai ta ware ido tace "kwarai dagaske"suka kwashe da dariya muneeba ta ciro gorar ruwa ta mikawa husnah "karbi wanan innah tace a baki addua ce da malam ya tofa miki nafada mata kin soma nakuda"
"yanzun sis yad'ani kikaje kinayi?"dariya muneeba tayi kiran wayarta akayi tace "doctor na kirana"tayi murmushi tayi daki husnah ta girgiza kai tace "Allah ya amsa"
yaseer ya kalleta da mamaki ta cigaba da magana "ai tunda mukaje asibiti da ita ya dubata yayi clearing bakomi a mahaifarta lokacin likita ya kyasa musamman dayaji auren babu so be nunaba saida ta fita iddah"yaseer farin ciki ya lullubesa husnah tasha adduar da muneeba ta bata da bismilla ta mike ta nufi daki tabar su yaseer a parlor nusrah ta kawo musu abinci....
*****
hajiya saude da momy ne zaune suna hira cikin farin ciki sukaji sallamarsu innah momy ta gyara zama "sannunku da zuwa"innah tace cikin zolaya "ina naga ta zama ancemun kishiya ta soma ciwo kadan kadan shine bayan wadanan shakiyyan yaran sun taho muka biyosu muzo mu tabbatar"
momy ta warw ido ta kalli hajiyq saude "Tou ai mu bamuma saniba muda muke gidan yanzun haka halan sunje gidanki ne da muneeba"
"Tou Allah yasa ba karya sukeyi ba"bata rufe bakiba muneeba ta shigo cikin sassarfa innah tace cike da masifa "shine kikasa na kamo hanya nataho ko?bayan ba ciwo husnah keyiba?"dakyar muneeba ta hadiyi miyau cike da fargaba tace"shi nazo fada muku ciwo ya tashi sosai sai nishi takeyi ance ta tashi a tafi asibiti har na Kira doctor gamunan zuwa taki wai yaya yaseerr ne zai karbi haihuwarta"
"kaji yar kwal uban yarinya muje gidan"dukkansu a tare suka fito suka baro momy da dik ta rude kunya da kawaici irin nata yasa ta kasa biyosu sai kaiwa da komowa da takeyi cikin dakin tanayiwa husnah addua bayan fitarsu daddy ya shigo bataji motaba ganinsa tayi rungumota yayi "kewarki tasa nadawo daga wajen aiki"ganin yanayinta yasa ya tambaya "lafiya kuwa zainab meke faruwa?"
"husnah ce zata haihu daddy gasu hajiya saude can sun tafi gidan wai taki bari aje asibiti"daddy ya rude zai fita momy ta rukosa "haba yar fari ce dai ka dawo na tabbatar su ummah hadiza na can zasuyi komi"ya dawo ya cire hularsa yana fifitawa gumi na karyo masa ta shiga kwantar masa da hankali ganin ya rude,
dik yadda hajiya saude ke jijjiga kofar husnah yaseer yaki budewa sakamakon uadda yayi mata alkawarin zai tsaya ta haihu tare dashi yana rungume da ita yana rizgar kuka tana salati hade da nishi gumi ya jikasu sharkaf ya shimfida mata under pad na siyayyar kayan haihuwar asibiti da sukayi cikin ikon Allah husnah tayi nishi mai karfi gumi ya karyo mata tace "wayyo Allah na wayyo momy"saiga baby ta fad'o santaleliya mace a kasa sai kukan jaririya su innah sukaji tace "zaka bude ko sainaci ubanka yaseer kunada lafiya"ya kalli husnah cike da tausayawa imani ya shigesa sosai yace "in bude?"ta jinjina masa kai ta durkushe tana kallon jaririyarta mai tsananin kama da yaseer kamar an tsaga kara a tare suka Shiga dakin momy ta rufe yaseee da masifa kokarin kutsa kai yake tace "ina zaka shugaban marasa kunya"ya juya cikin sauri ya nufi sashen su momy tana ganinsa ta mike ganin rigarsa jini yasa ta furgita yayi dariya tayi ajiyar zucuya yace "ta haihu Momy ta haifi mace mai kama Dani baki gantaba"tayiwa yaseer dakuwa tana murnushin farin ciki tace "daddy ka tashi kayi mata"da sauri dady ya mike daga zaman dayayi yace "dagaske"yaga yaseer ta bakin kofa daddy ya washe baki cike da farin ciki ya soma kiran wayar jamaa abokansa yasamu jikar fari....
muneeba ce mai zaman jego bata zuwa nan da can komi ita keyiwa husnah dinkuna daban daban tare sukayi tamkar yan biyu ta mance da wata rayuwa da tayi a baya zuba soyayya sukeyi da doctor Aliyu wanda ake maganar turowarsa tare da hafeez a hada aurensu da nusrah yusrah ma tasamu miji daban da suke tsananin kaunar juna,
ranan suna yarinya taci suna SAUDAT wanda husnah ce ta roki yaseer yasa mata sunan hajiya saude sakamakon jajircewa datayi akanta ta nema mata lafiya da yadda take nuna kaunarta agareta dikda yaseer sunan momyn husnah yaso yasa zainab fir husnah taki ranan suna yaseer ya gwangwaje husnah da dalleliyar mota sanan daddy ya basu kyautar sabon gidansa halak malak inda zasu koma su cigaba da rayuwa cikin wata daya da haihuwa husnah ta gyagije zuba soyayya sukeyi da yaseer tare da kulawa da jinjirarta bata fasa mata adduoi da azkar ba kullum cikin addua da sauraren alkurani take a haka aka soma hidimar bikin muneeba da docto da hafeez da nusrah sai yusrah da angonta iyalen alhaji badamasi basa sukuni dangi daya ne komi tare ake gudanarwa na amare muneeba taga gata wajen hajiya saude da momy da alhaji badamasi uban gayya babban yaya yaseer ya taka rawar gani wajen nuna bajinta husnah ba zama biki kawai akeyi basuda kawaye itada muneeba komi tare sukeyi kowa shaawarsu yakeyi musamman yadda renon Samha yar husnah yake hannun muneeba tamkar ta maidata ciki dan kauna komi ita takeyi mata baka gane waye uwar yarinyar.....
ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH NAN MUKA KAWO KARSHEN LABARIN NAN MAI SUNA DUHU....SAI KUNJINI A SABON LABARI MAI SUNA *K'UGIYA*...... INA FATAN KUNJI DADIN LITTAFIN NAN ZAN HADU DAKU CIKIN DUMBIN MASOYANA A SABON LITTAFINA MAI ZUWA NAN BADA JIMAWA BA
AKWAI LITTAFAINA GUDA HUDU MAI BUKATAR COMPLETE DOCUMENTS YA NEMENI A NUMBERTA KUMA INASO KUYI SAVING NUMBERTA DON ZUMUNCI...
MASU BUKATAR MUYI SAVING NUMBER DIN JUNA SUMIM MAGANA DIKDA WASU MUNDADE DA JONEWA.....
TAKU HAR KULLUM SLIMZY INA JIRAN SHARHI.....
07042277401