Showing 87001 words to 90000 words out of 130717 words
bayani "yana zuwa mun a mutum a siffar dana sanshi da ita watarana Dodo"ta fashe da kuka "la'anannen Allah shedani in Allah ya yarda saiya rabu dake husnah"cewar hajiya saude a fusace malam ya jinjina kai yace"ya taba kusantarki?"ta girgiza kai "Alhamdulillah tunda bai taba kusantarta ba inshaaa Allahu idan har kun dage zai iya rabuwa da ita wanan turaren da nayi mata bazai taba iya kusantar jikinta ba"momy ta jinjina kai cike da gamsuwa ya cigaba da magana "yadda kika jajirce akan ta hajiya indai kundage zai rabu da ita sanan kar mujinta ya nisanceta idan so samune kamar yadda kikace zata tare to ta tare a gidan nata sanan kar a rinka barinta ita kadai a daki tunda tana fama dasu shima zai bada gudun mawa wajen kara zamansu a tare da ita dik runtsi ya zamana tana tare da wani ko wata"ajiyar zuciya momy tayi tace "yanzun malam baka ganin zai cutar da mijinta?"ya girgiza kai yace "tunda har mijinta yayi nasarar kwanciya da ita kadarinsa ya karye akwai abinda zan baki kiba mijin nata shima ya rinka amfani dashi"momy a fusace tace "nusrah daukomin wayata in kira yaseer ja'irin yaro saboda yasan yana gudun fad'ana yasa ya gudu jin nadawo yazo kuyi magana kayi masa bayani"nusrah ta karasa dining table ta dauko jakar momy ta mika Mata ta ciro wayarta tayi dialing number yaseeer kawai sukaji ringing din wayar yaseer cikin daki,tsaki momy tayi "a d'aki yabar wayar"bakin husnah na rawa tanason tayi magana ta kasa kallon glass din window tayi fuskar Abraham ta gani ta kalli glass din dake gefe nanma shi tagani ta sunkuyar da kai "mai kikeso ki fad'a husnah?akwai abinda kikeso kice fadamun menene karki boye idan kika boye zai cigaba da cutar dake"kwalla ta cicciko a idanuwanta muryarsa takeji can nesa kamar a iska "idan kika fada musu niba yaseer bane zan kashe yaseer "damm gabanta ya Fadi "ki fada mana menene?"hajiya saude tace cikin kosawa ta girgiza kai kawai "hajiya akwai abinda takeson fad'a ina zargin akwai wani wanda yake tsoratar da ita musamman yadda take kallon gefe taki magana,yana kusa ko?"ta jinjina kai tana hawaye malam ya kada kai kawai ya ciro wani koren magani "hajiya kinada nono?"momy tayi shiru tace "banidashi amma akwai yoghourt "
"nusrah dauko yoghourt a fridge"nusrah ta tafi kitchen tana shiga tayi kicibis dashi tsaye taja da baya zatayi ihu ya bace jikinta na rawa ta dauko ta kawo yace "wanan maganin zan bata Tasha sakamakon kema kin taimakeni amma bakowa nake bamawa ba saboda wuyarsa"ya mika mata "juye a kopi"ta juye tasa yoghurt ta mikawa husnah hannunta na rawa ta karba ta soma sha tari ya turnuketa "karasa shanyewa kinji?"ta shanye yace "alhamdulillah wanan da kike gani,maganine bishiyar maganin inda take unguwar da akwaita aljanu basa zama wajen nabata ne kawai amma badan zaki iya biyana ba saboda yanada wahalah"momy ta daga hannu ta godewa Allah gumi ne ya karyowa husnah tadan jingina tana sauke numfashi ji tayi jikinta tamkar ba nata ba,"Mai kikeso ki fada dazun?"tace "dama yaya yaseer bashi bane Abraham ne"momy ta kalli malam ya kalleta "anya husnah"ta jinjina kai momy tace "malam kodai yana rikidar da fuskar yaseee ne a matsayin nasa yasa take ganin kamar shine ba yaseer ba?malam yace "zai iya yuwuwa,amma kisa ido zanbaki abinda zakiyi idan har ba yaseer bane to zaman gidan bazai yuwu masa ba"
"Tou shikenan"ta ja ajiyar zucuya,husnah ta mike yusrah ta rukota suka nufi daki malam ya bata komi yadda zatayi ta karba tayi masa godiya
*******
daddy ko karasa parking beyi ba ya zubawa kayan ido yana kallo daya bayan daya yayi tsaki ya fito yana kwalawa momy kira "zainab zainab"kamar a mafarki takejin kiransa tad'an kishingida ta diro daga gado ta fito da sauri taba gyara daurin zanin lashenta tace "lafiya daddy meya faru naji kana kirana?"fuskarsa a daure yace "wadanan kayan fa?"numfashi ta sauke tana kokarin basa amsa hajiya rabi ta fito kitchen da plate a hannunta tace "AI yaseer ne yazo dashi yw siyowa husnah na tarewarta,inace ya fada maka ai kasani"jinjina kai daddy yayi yace "lallai yaseer wato rashin muhimmancina har yakai yaseer yayi abu batare da neman shawarata ba?ni tabdijan dik inda yake yazo ya kwashe kayan nan tin kafin ransa ya baci"hajiya rabi tayi murmushin mugunta "yauwa Zainab ga wanan farfesun kifi ne nayi nasam zakiji dadinsa ku masu ciki"da sauri daddy ya kalli hajiya rabi yace "masu ciki?waye keda cikin?"ta nuna masa momy dake tsaye ta sunkuyar da kai tace "au bakasan da cikin ba aina dauka kasam dashi Alhaji ka boyemun ne ga ciki nan ya fito rikikis dashi?"ya kalli momy cikin tuhuma yace "ciki zainab? ciki fa?"ta jinjina Kai cike da kwarin gwiwa tace "ciki fa Alhaji ciki kuma naka ne dikda ka dade baka kusance ni ba amma wanan cikin naka ne ka lissafa daga lokacin da ka daina kusantata zuwa yanzun watanninsa kenan"ra hada rai tana kallon hajiya rabi wadda mamaki ya kasheta tace "nidai ga wanan"kici d'anmu yayi kwari tunda nasan ai dan mijina ne?"momy tasa hannu ta kabe plate din ya fadi kasa ta watse daddy ya daga hannu zai mari hajiya zainab da sauri hajiya rabi ta rikesa cike da kissa tace "ah ah kulll kasan masu ciki kila kamshin beyi mata bane yasa ta zubar"jikin daddy na rawa yace "har ta Isa ki kawo abu kibata tasa hannu tq zubar sabida batada ilimi batasan darajar abinci ba?"momy ta kalli daddy Cike da mamakin kalmar daya jefeta da ita hajiya rabi kuwa zucuyarta tazo wuya maganin data zuba shine ta zubar?ta jinjina kai zatayi maganinta ai akwai layar da boka ya bata,
daddy na faman kiran wayar yaseer baya dauka dik abinda sukeyi Abraham na tsaye Yana kallonsu,wucewa yayi muneeba na parlor zaune bata ganinsa ya shige daki motsin mutum taji ta mike ta dan gyara rigarta cikin kwarkwasa ta shiga yana kwance kan gado dagashi sai singlet tace "ai nadauka har yanzun baka fito wankan bane"ya kada kai "na fito"ta taho cikin yanga tana kokarin hawa gadon ya mike ya zauna ransa a bace yake ainun "ya naganka cikin wanan yanayin yaya yaseer?"Abraham ya juya yace "momy ce ke kirana inaso inje inji menene sam banason zuwa saboda matsalar husnah tafara isata"tabe baki muneeba tayi tace "ah tou nidai nasan koda kafara Sonta na tabbatar dama baa hayyacinka kake ba kaje kawai kafadawa momy baka Sonta ka saketa "Abraham yayi mata wani kallo ya janyo rigarsa yasa "ina zuwa bani awa daya zan dawo kinji?"ya shafa kanta ya fice murnushi tayi ta dafe kirjinta ta saki ajiyar zucuya tasamu kan yaseer ta kwanta rigingine tana murmushi.....
Abraham ya fito yayi kicibis da daddy wata harara daddy ya watsa masa ya sunkuyar da kai yace 'barka da yamma daddy"
"barkanka yaseer ai bansan cewar munkai wanan matsayin nidakai ba, wato kaida uwarka kun yanke shawara batare da nasaniba kasa kudi masu yawa ka siyo kaya ko?to yadda kazo da kayan haka zaka fitar dashi nafada maka idan kuma ba hakaba zen dauki kwakkwaran mataki akanka"gumi ya karyowa Abraham yace "tou daddy"daddy yayi tsaki ya wuce.....shiru Abraham yayi yana tunani so yakeyi yaga husnah,yana barin wajen ya fice kofar gate ya bace...
******
momy ta fito ta rako makociyarta taji horn din mota ta waiga mai gadi ya bude kofar yaseer tagani ciki ta girgiza kai tayi tsaye har ya fito fuskarsa a daure yace "barka dai momy"momy tace "kaima barka ina kaje?daga zuwana Ka fice saboda kasan abinda kayi ko?ka haikewa yar mutane ko tafiya batayi sanan wanan laanannen aljanin yasakota gaba haka ka fice"yatsina fuska Abraham yayi ji yayi kamar zai fadi sakamakon kamshin turaren da momy ta turare gidan dashi ya daure idanuwansa sukai jajir "kai lafiyanka kake daure daure?"yayi jimm kada ta gane yace "bacci naje nayi naje gidan daddy ne na siyo kayan tariya yace bayaso a kwashe to nasa an kwashe inaga zan samu baba kabiru akan maganar"momy ta jinjina kai "da kaina zan kirasa karkaje nasan maganin badamasi muje ciki nadai barsu tare dasu yusrah zasu zauna da ita malam ya hana a Barta ita kadai"yana taka kafa dakyar hankalin momy baya kansa tafiya yake amma ba akan kafarsa ba yana shiga cikin parlorn wani tukuki ya ziyarcesa yayi baya kamar zai fita a wahale yake ji yayi kamar ana zuba masa barkono cikin sauri yabar parlorn "Bari inga husnah"
Mony ta girgiza kai "ko meke damunsa oho"tin daga kofar shiga yake fan tari idanuwansa sun koma bakinkirin ya rufe ido nan da nan yad'aga hannu saiga glass yasa "ku fito nazo inganta ne intafi yamma tayi"husnah ta fito toilet kenan da alwala,su yusrah najin muryarsa suka mike "mijinki yaxo anty husnah"suka fice basu lura da fuskarsa yadda take canjawa ba yana shiga ya sauya kamanni jikinsa sai rawa yake hayaki na fita daga jikinsa yana tozali da ita yaga haske a gabbanta ya tabbatar tayi wanan abun tayi murmushi tana kallonsa "Abraham kenan kazo ka kwanta dani ne ka tattaba jikina?"ya dago ido yw cire glass idanuwansa bakinkirin yace "au kinsan abinda kukayi ko?zaki kasheni hardake husnah?"ta jinjina kai tace "sam kai ba abokin zama bane kaiba mutum bane ina fatan in rabu dakai in daina sonka dan cutar dani kakeyi"dakin ke girgiza kamar zai fadi jikinsa kamat ana zuba masa wuta lankwashewa ya shigayi yana baya baya tana tunkarosa batare da tsoro ko furgici ba ganin wuta na tahowa zata konasa kawai hawaye yakeyi ya bace daga dakin,ajiyar zuciya tayi ta tsugunna akan gwiwarta tausayin kanta yq kamata Allah sarki yaseer tace....ta dauki hijabinta tana kwalawa su yusrah kira,
momy na parlor tagansa cikin sauri ya fito "ah ah yaseer ina zaka haka cikin sauri"kasa hada Ido da ita yayi yace "zani gida ne sai zuwa gobe"
"nakira babanku kabiru yace jibi husnah zata tare zashi gidan wajen Alhaji badamasi"ajiyar zuciya Abraham yayi burinsa husnah tabar gidan idan tana gidan nan bazai taba iya kusantar inda takeba dan zai mutu,jinjina kai kawai yayi yace "saida safe momy "ya fice momy ta bishi da kallo tana jinjina kai......
ABRAHAM na fitowa ya yanke jiki ya fad'i ganinta yayi tsaye gabansa tana kallon yadda yake a wahale tace "Abraham"ya dago da sauri jin muryar narjisu ya kalleta hankakinsa yayi mugun tashi ganin yadda ta sauya iska na yawo da ita a sama cikin guguwa mai karfi tace "gani nadawo dama bana nan ne naje insamo karfin dayafi naka na kuma dawo saidai wanan karon bazam barka ba"tace tana jujjuyawa gashin kanta na yawo a sama fuskarta da idanuwanta kyarrr akansa dariya ya hau mata dikda a wahale yake sakamakon abinda ya shaka gidan momy.....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*✍🏻
38
hajiya zainab ce zaune bakin gado ta rafka tagumi bayan ta idar da sallahr magriba tayo wanka tana daure da zani a kirjinta maganganun daddy ke yawo a kunnuwanta daddy yau shi yake kiranta da jahila mara ilimi batasan darajar abincu ba?bankad'e labule daddy yayi ya shigo ya tsaya akan momyn husnah ransa a bace "ke zainab zaki fad'amun a inda kika samo cikin jikinki ko sai kin tattara kayanki kinbar gidana?wato kinyi kinyi kija hankalina kin gagara kinbi ta asiri kinyi tsafacw tsafacenki dik akan na auri hajiya rabi shine yanzun kika jajubo ciki ko?tou bari kiji kifadamun gaskiya tun kafin kisan inda dare yayi miki kinji nafada miki"Yana maganar jikinsa na rawa yana nunata da yatsa,cikin takaici momy take kallonsa idanuwanta dishi dishi ya somayi amma hakan bai hanata samun kwarin gwiwa daga zucuyarta ba "kai Alhaji badamasi ni kake kallon tsabar idanuwana kake fadamun cewar insan inda nasamo ciki? na tabbatar kafi kowa sanin ni wacece idan ni yar iskace a darwn farko zaka tantance hakan,sanan inaso kasani karka gayyato zargi ka kawo cikin aurenmu dan ina mai shaida maka zakayi aikin danasani"daddy jikinsa na rawa ya d'aga hannu ya zabgawa hajiya zainab mari da sauri ta dafe kuncinta wasu taurari suke yawo a idanuwanta ta tsaresa da ido saida taji ta dauke wuta na seconds maganganunnsa yasa ta dawo hayyacinta "harni zaki rinka fad'awa magana gatsa gatsa bakiji kunyaba da girmanki da shekarunki kin samo ciki amma kike fadamun maganar banza shashasha to ki tattara kayanki kibarmun gida na kinji na fada miki a daren nan"momy ta girgiza kai wasu hawaye masu zafi suka zubo mata ta share hawayenta tace"kafi kowa sanin ni din wacece a hakan ka auroni sakamakon tsananin kaunar da kakemun, bakada laifi Alhaji badamasi amma inaso kasani idan kanaso inbar gidanka to tabbas saida shaida maana takardar saki kai koda sakina kayi ma bazan bar gidanka ba saina cika idda don haka idan ka shirya rabuwa dani bismillah amma dik ranan daka dawo hayyacinka kada ka nemeni"daddy yayi kwafa sam ko ganin hajiya zainab baya sonyi idan ya cigaba da zama cikin dakin zai rufeta da duka zai iya shaketa ta mutu har lahira dan haka kawai juyawa yayi ya fita,
momy ta zauna dirshan ta daga hannuwanta sama tana hawaye tacev"Allah kana gani"ta runtse idanuwanta kuka mai karfi ya kwace mata,
hajiya rabi na lab'e tabajin dik abinda ya faru sautin takun sahun dady yasa tayi saurin komawa ta tsaya daga kofa ta taresa "Alhaji lafiya ya naganka haka kana faman haki?inajiyo sautin muryarka a dakin zainab meyasa kakeson ka dorawa kanka damuwa ne umm?"a fusace yace "ba dole indamuba ina zaman zamana zaayimun karuwanci a cikin gida?kina gani zainab da girmanta wai tayi ciki cikifa rabi?"tabe baki hajiya rabi tayi hade da kasa da murya cike da kissa ta ruko hannunsa "ya isa haka ya isa Alhaji kayi hakuri karka tayarwa kanka da ciwo ka jazamun kaji?"
"nace tabar gidan tace bazata bariba saida shaida zataga yadda zanyi da ita kuwa saita gwammace zaman makabarta da zaman gidan nan"yasa kai ya wuce murmushin mugunta hajiya rabi tayi ta sauke ajiyar zuciya cike da nishadi tabi bayansa zuwa sashensa tana lallaminsa da makirci da kissa.....
*****
husnah suna zaune a parlor da yusrah sun saka sunna tv suna kallo momy da nusrah suka shigo a tare nusrah ta zubo musu abinci a tray ta ajiye momy tace "a canja Tasha akai ta karatun alkurani mana"
"momy nan ma ai waaazi akeyi shiyasa muka kai"momy ta zauna tadan kalli husnah tace "yadai husnah ya kikejin jikin naki?"murmushin karfin hali husnah tayi hankalinta baya jikinta gangar jikinta ce a wajen hankalinta na wajen yaseeer,ta cije tacev"da sauki momy jikina kamar ba nawa ba banajin komi"
"da kyau husnah ki dage kinji karji kuskura ki rinka zama ke kadai kinji?sanan ki rinka zama nan munasa karatun alkurani munayin hira tare dikda zaman naki yau ne zuwa gobe jibi zaki koma gidanki gobe zaayi komi a gyara tunda babanki ya sai miki kaya dazun yake fadamun da mukai waya"husnah ta sunkuyar dakai idanuwanta suka kawo ruwa yanzun da Abraham zata tare?aljani?ta cije lebenta tabbas sai tasan yadda tayi momy ta gamsu da cewar yaseer din da yake zuwa ba yaseer bane Abraham ne kuma aljani ne amma kuma bataso hankalin momy ya tashi d'anta kwaya d'aya tilo,"ya kikai shiru husnah?"girgixa kai husnah tayi cike da kunya ta sunkuyar da kanta kasa tace "bakomi momy"
"gobe ki shirya da wuri idan yaseer yazo sai kuje dasu nusrah a siyo kayan sawa ko?"husnah wasu hawaye ne suka cicciko idanuwanta ta tabbatar da momy na tsananin kaunarta dikda kasancewar tana tare da aljani bai hanata sonta ba besa ta kyamaceta ba nusrah ta ajiye ruwa tacev"bismillah kumuci abincin"
"yan ubanci zakuyimun ko kun kama yar uwarku zakuci ni baku samin nawa ba"sukai dariya a tare yusrah tadan kalli momy cikin sigar wasa tacev"kishi kikeyi?"momy tayi dariya ja'ira kawai"jujjuya cokali kaeai husnah keyi ta kasa cin abincin momy na lura da ita sosai "husnah meyasa kika kasa cin abincun?"kuka husnah ta fashe dashi kamar tana jira momy ta zamo daga kujera ta karaso ta rungumota jikinta tana fad'in "lafiya meyafaru husnah kodai bake bace fadamun"
"momy ki yarda dani yaya yaseer dake zuwa gidan nan bashi bane Abraham ne, Abraham ne ya sauya kamanninsa zuwa yaseer shine yakeso ya tare dani ya batar da yaya yaseer "momy ji tayi kamar husnah ta buga mata guduma gabanta ya yanke ya Fadi tayi shiru tana nazari cike da rudu take girgiza kai "yanaso ya haukataki ne kawai husnah amma yaseeer ne kila yana sauya miki fuskar yaseer din ne kawai babu siddabarun da aljanu basu iyaba kinji kiyi hakuri kidaina kuka yaseer ne yana nan babu inda yaje"husnah kasa magana tayi cike da tausayi take kallon momy share mata hawaye momy tayi "maza ci abincunki kinji ki koshi sanan kije ki kwanta kin shiga ruwan zafin danace ki gasa kanki?"ta jinjinawa momy kai ta dibo abincun ta kai bakinta tamkar tana cin mad'aci haka takecin abincin....
*******
turare mai kamshin gaske muneeba ta shasshafa a jikinta lungu da sak'o cikin tsananin farin ciki take yau kalaman da yaseer ya fad'a mata ke yawo a kanta tana daure da towel taji motsin mutum da sauri ta waiga Abraham ne tsaye ya jingina da jikin kofa bashida karfi ko kadan a tare dashi sakamakon abinda ya shaka kamar zai mutu yakejin jikinsa kamar ana tsira masa allura,shiru muneeba tayi tana kallonsa "lafiya yaya yaseer naganka cikin wanan yanayin kamar kana cikin damuwa"idanuwa jajir Abraham ke kallonta yadda idanuwansa suka rine saida tad'an tsorata ta hadiyi miyau ta mike tana kusantosa ya d'aga mata hannu da sauri ta dakata kallon tsana yakeyi mata ji yakeyi tamkar ya shaketa ya mutu dan tsananin haushin da yakeji yaso ya rabu husnah yau burinsa bai wuce ya kusancetaba ya rabata da yaseer amma hakan ya faskara bazai taba iya zaman gidan ba zai iya hallaka,"karki matso kusa dani jikina bashida kyau mtswww naje gidan momy ne wanan sarkin aljanun husnah itace suka motsa shine na tabata jikina warin maganinsu yakeyi"ajiyar zuciya muneeba tayi dan cikinta gaba daya ya d'uri ruwa ganinsa cikin wanan yanayin ta dauka ya dawo hayyacinsa ne tayi murmushi "shine kake fushi?to kayi hakuri bari na taimaka maka kayi wanka ko?"cije lebe Abraham yayi sam bayaso ta gano shidun ba mijinta bane gashi