Showing 117001 words to 120000 words out of 130717 words

Chapter 40 - DUHU sark'ak'iya complete hausa novel

slimzy   

23 Oct 2025

189

Allah yaseer ka rokarmun alfarma daddy ya rikeni kaji?wallahi zan zauna dasu da amana"yaseer jin abun yayi banbarakwai ta zauna dasu dama korarsu akayi?ya kalli akwatunan bece komuba yace "malam muje sashen mara lafiyar dik suna can"malam yabi bayansu....

To mutanena masuso muyi savin number juna suyimun magana sanan akwai documents hudu nawa na zafafan labarai akan 1k meso tamun magana....



*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*


08036953516
07042277401


*SLIMZY*🥱
50
muneeba hawaye ke gudu a idonta bugun zucuyarta ne ya tsananta ganinsu daddy a tsaye dukkansu sun zuba musu ido hajiya rabi ja da baya tayi kafafuwanta sun kasa daukarta ta durkushe a kasa jagwab daddy ya kasa magana gumi ne kawai yake karyo masa kawai ya fashe da kuka yana nuna hajiya rabi jikinsa na karkarwa "Allah ya isa tsakanina dake rabi?yanzun dama shirkarki da rashin tsoron Allahnki har ya kai kisa yar cikinki da kika haifa tayi zina?rabi zina fa kikasa muneeba tayi da boka"yaseer wata juwa ce ta fuzgesa jin furucun daddy yana kokarin shigowa ganinsa sukai kamar an jefosa malam yayi sallama cike da natsuwa mazurai da idanuwa yaseer keyi idanuwansa sunyi jajir yana kallon muneeba ko kifta idonsa bayayi tamkar an dasashi yake tsaye itama shi take kallo cikin kuka ta sunkuyar da kanta kasa cike da nadama da tsananin tashin hankali ta durkushe akan gwiwoyinta cikinta ya zauna akan cinyoyinta tace "yaseer ka gafarceni na aikata babban laifi na aikata mummunan laifin da nasan bazaka taba yafemunba,dikda zuciyata da gan gan jikina basason aikata hakan amma zuga da kururuwa da busar iblis hade da wanan da nake kira mahaifiyata suka hadu sukai tasiri wajen karfafamun gwiwa na aikata zina da aurena na aikata mummunan aiki da boka matsafi, yaseer am sorry to say cikin jikina ba naka bane cikin boka ne wanda a yanzun haka bokan ya mutu ya mutu ya barni da cikinsa a jikina wanda banida tabbacin shin mutum ne ko aljan ko kuwa wata cuta ce?"tuni hawaye sun balle a idon yaseer dikda dauriya irinta yaseer da jarumta kuka yaseer ya balle dashi yana ja da baya hafeez ya rukosa cikin tattausan lafazi yace"comr on my friend bansanka da raunin zucuyaba kai jarumi ne wanan mummunar kaddara ce ta sauka a gareku wanda muneeba koba yar uwarka bace ta cancanci taimako da afuwa"

cikin kuka muneeba tace "ban cancanci afuwa da gafarar yaserr ba abinda yafi cancantata shine karbar hukunci daga garesa ko wani iri ne,dikda tsananin son da nakeyiwa yaseer ya zama dole in hakura dashi saboda Bai kamaceniba bai dace dani ba nidin ba macen data cancanci a zauna da ita bane,dik abinda ya sameni mahaifiyata itace sila ita ta jefa rayuwata cikin DUHU daga haske ta jefani cikin mummunan had'arin da na gwammaci mutuwa da Rayuwa"da sauri hajiya saude ta rike muneeba ta toshe mata baki tana kuka itama kukan takeyi "dik wadanan maganganun basu bane muneeba kidainayinsu ko a kalaman da mukazo muka tarar dake munsan cewar ba yin kanki bane uwace bakiyi dacen da ta gariba,tirrr da halinki rabi Allah ya wadaran halinki kin cucemu kinci amanarmu kuma sai Allah ya saka mana sanan kisan da sanin dik inda kike zamu nemoki mu mikaki hannun hukuma akan dik abinda yasamu muneeba kece "cikin kakkausar lafazi hajiya saude ta karasa maganar ummah hadiza tuni zucuya ta kawo mata wuya tana bude baki zatayi magana ta kasa kallonsu kawai tayi tw zare hijabin jikinta cikin fakon idonsu momy dake kuka a tsaitsaye sukaga ummah hadiza ta rufarwa hajiya rabi da wani irin duka ta hankada kanta jikin bango ji kake kummmm "matsiyaciya wallahi bazakicu bulus ba kafin kibar gidan nan kibar zuriar mu sai na canja miki kama"nushin hajiya rabi ummah hadiza keyi ta cukwikuye kanta cikin hijabinta ta danneta ihu hajiya rabi keyi cikin azaba "hadiza karki kasheni kada ki kasheni numfashina ki kyaleni ki rabu dani zainab kuyi mata magana kuna gani zata kasheni?"momy tana kokarin mikawa innah jinjiri daddy ya rukota "badai karbarta zakiyi ba ko?ai abinda ya kamaceta kenan dan idan nine wallahi na kamata kasheta zanyi har lahira kubarta ta canja mata kamanni kafin yan sanda suyi gaba da ita suyi mata nasu"cikin wani irin yanayi momy ta share hawayenta tana kallon yadda ummah hadiza ke kirbar hajiya rabi kamar Allah ya aikota tace"ummah hadiza ya isa haka dukan bashi bane maslaha"hafeez ya kama yaseer yana kuka ya fita dashi muneeba tabi yaseer da kallo tausayinsa ya lullubeta take taji wata tsanar kanta da tsangwamar kanta ta dira a zuciyarta cikin gyaran murya malam yayi wanda shi yasa ummah hadiza tana cafke da wuyan hajiya rabi ta dakata yace "dukan da koke koken bashi bane maslaha ki rabu da ita dukan bashi zai bawa yarinyar nan lafiya ba bashi zai goge bakin fyantin da uwarta tayi mataba dan haka kyaleta shine maslaha yanzun asan abinyi"...hankadeta ummah hadiza tayi bakin hajiya rabi ya tashi yayi zundundum yayi jajir idonta daya ya kumbura suntum fatar idon tayi baki goshinta kuwa jini ne kawai yake tsattsafowa fuskarta dikta kuje da jikin bango ummah hadiza wani bakin ciki ne ya tokare mata wuya ta fashe da kuka tace "fitar mana a gida zoki fita idan ina ganinki kasheki kawai zanyi"tsoro ne ya cika hajiya rabi dakyar ta yunkura ta mike jikinta da kafadarta dik ya sage muneeba tabi mahaifiyarta da kallo fuskarta jajir hajiya saude tace"yanzun mal muje cikin gida baban parlor ko?"malam ya jinjina kai ya fice hajiya rabi na hada hanya ta fito sadiya nayin tozali da ita ta fuzgi akwatunta ta baza aguje tayi gate cikin sassarfa itama tabi bayanta a waje suka hade "Anty lafiya?meyafaru kinga yadda fuskarki tayi kamar kinyi hatsari"cikin tsoro sadiya ke maganar tana waige waige "nidai mubar gidan nam kafin su fito su cinmana a nan natabbatar sunji abinda yasamu muneeba ko?"gumi ne ya karyowa hajiya rabi cike da nadama a karo na farko tace "na cuci rayuwar yata ma cuci rayuwata sadiya yanzun ina zamu gashi Alhaji badamasi yace idan har muneeba wani abu ya sameta sai ya daureni"jim haka sadiya taja akwatinta tayi gaba hajiya rabi na biye da ita hannu akai take rusa kuka tana waigen tamfatsetaem gidan tana fadin "nashiga uku na lalace na shiga uku shikenan ni rabi yanzun ina zani"....
****
shiru sukai dukkansu daga yaseer hafeez da husnah dake parlorn sautin kukan yaseer ne ya karade cikin parlorn tsananin bakin ciki yasa yake kuka husnah cikin tattausan lafazi tazo gabansa ta durkusa ya dago idanuwansa shabe shabe da hawaye Yana kallonta yadda yake kallonta taji wani abu ya karya mata zucuya ta fashe da kuka yayi saurin zamowa daga kujera ya tsugunna gabanta "husnah kukan mai kikeyi husbah?meyasa kike kuka?kina zargin na dauko cuta daga jikin muneeba nasa miki ko?wallahi"be karasa ba ta rufe masa baki ta kwantar da kanta a kafadarsa tace "haba yaya yaseer wanan kukan da kakeyi bakasan shi kadai tadamun da hankali zaiyi ba?bakasan bazanso ganinka cikin wanan yanayin ba?shin muneeba kake ganin laifi ko laifin ummah?"yayi saurin kallonta yana nazarinta ta girgiza kai ta share hawayenta da bayan hannunta tace"muneeba batada laifu hasalima yanzun itadin abar tausayi ce dan baasan menene a jikinta ba batada laifi ba ita tasa kanta ba idanuwan mahaifiyarta ne suka makance har tasata ta aikata abinda ta aikata Dan Allah ka tausaya mata yaya yaseer ko zakai wani hukunci kabari tasamu lafiya tukunna"zucuyarsa tamkar zata tarwatse yakeyi daya tuna furucin daddy na karshe dayaji akan muneeba ta aikata zina da boka,sanan furucin muneeba na daga masa hankali cewar cikin dake jikinta ba nasa bane cikin boka ne kuma ya mutu, yaseer ya cije bakinsa saida lebensa ya fashe jini na zuba a bakinsa yace "muneeba ta cuceni ta cutardani da danginmu ta bata mana suna da ace zanyi ido hudu da wanan bokan da saina rabashi da ransa"hafeez ya jinjina kai yace"ko baka rabasa da Ransa ba Allah kadai yasan Azabar dayake ciki tunda ya mutu yanzun yaseer dik wanan bashi bane a gabanmu ka duba furucin matarka"ya nuna husnah da tayi tsumu jiki a sanyaye tayi saman rakuma a jikin yaseer hafeez ya cigaba da magana "maganarta abun dubawa ce yanzun abinda zaayi shine tashi zakayi muje cikin gidan tunda kaga malam na ciki musan abinda ake ciki"kin magana yaseer yayi zucuyarsa cunkushe take da tsananin bakin ciki miyaun bakinsa har d'aci yakeyi masa ya kallesu kawai ya mike ya nufi hanyar bedroom dinsa saida yakai tsakiya yace "kuje amma bazan iya shigaba bazan taba iya kallon fuskar muneeba a halin yanzunba domin bakinkirin nake ganinta bazan taba jurar ganinta ba zan yanke hukunci a lokacin da be kamata ba dam haka kuje kawai"yana gama magana ta nufi bedroom dinsa da besan kalarsaba yaune ranar farko daya Shiga Yana shiga yasawa dakin key ya zube a jikin kofar ya dafe kansa wasu sababbin hawayen bakin ciki yakeyi yanaji husnah na bubbuga kofar dakin ta baya take fadin "haba masoyina haba mijina ka bude kofar nan ka saurareni nicefa matarka husnah kayimun alkawarin farantamun rai akan dik abinda nakeso"cikin sassanyar murya take maganar da tattausan lafazi zucuyarsa na azalzalarsa ya bude amma bazai iya budewa ba kasa magana yayi ya mike ya zare rigar jikinsa yana zuwa ya fada gadonsa ya kifa ciki husnah jin bayi da niyyar budewa ranta a bace ta shiga dakinta ta gyara fuskarta ta sako hijab ta fito ta samu hafeez tayi tagumi a parlor yana ganinta yace"yaki budewa ko?"ta jinjina kai tace "muje can gidansu momyn nasan yayi fushi ne zai bude zan lallashesa"hafeez ya saci kallon husnah tayi kyau ta koma normal mutum kamar ba husnahr Abraham ba tare suka fice.....

hajiya saude na rungume da muneeba malam yana rike da kofi ya juye ruwan zamzam husnah da hafeez suka Shiga daddy na ganinsu yace"ina yaserr din?ina kuka barosa?"husnah ta sunkuyar da kai batace komiba suna hada ido da muneeba wani tausayinta ya lullube ta ta fashe da kuka tana kallon muneeba itama muneebar ita take kallo tayi murmushin karfin hali ta mika mata hannuwanta ta taho ta rukota ta durkusa a gabanta "yaya yaserr ya tsaneni ko husnah?nasan bazai sake marmarin rayuwa dani ko zama daniba na tabbatar yanzun hakan ya sakeni"shhhhhh husnah tace "be sakekiba kuma bazan taba bari ya rabu dakeba idan har zai rabu dake to tabbas saidai ya rabu damu tare saboda kedin yar uwata ce"sosai sukaba mutanen cikib parlorn tausayi muneeba ta gyara zama sosai jikin hajiya saude tana sanye da hijab amma gumi ya gama jika wuyan hijabin gyaran murya malam yayi sukayi shiru "kun tabbatar kun amince akan ayi Mata addua ta haife abinda ke cikinta ko mutum ne koba mutum ba?"dukkansu a tare suka hada baki "mun amince"malam ya jinjina kai yace"wanan addua ce nayi a ruwan zam zam gashi Wanda mafi akasari masu nakuda akeyiwa su haifi abinda ke cikinsu dan wasu ma idan sukasha lokacin haihuwa beyiba zasu haihu a lokacin da izinin Allah dan haka gashi tasha ta shafe cikinta sai musa ido mu zubawa sarautar Allah ido"momy ta girgiza kai ta kalli muneeba rike sa kofin tana kokarin sha tausayin yarinyar ya lullubeta ta kauda kanta gefe ta fashe da kuka muneeba tashanye adduar husnah ta taimaka mata suka hude cikinta aka shafe cikin da adduar

"Tou Alhamdulillah yanzun ni zan tafi tunda bamusan lokacin da nakudar zata tashiba ko?saidai kar a barta ita kadai asamu wani yq zauna tare da ita"hajiya saude tayi ajiyar zuciya tace "mungode malam Allah ne kawai zai biyaka abinda kayi mana Allah ya saka maka da alheri"suka hada baki tare suka amsa da "Ameen"malam ya tashi hafeez yabi bayansa yacewa su momy "Bari in kaisa gida zan dawo zuwa yamma"suka fita tare da malam daddy ma ficewa yayi sakamakon kiransa da akayi a waya....

husnah ta yunkura ta mike muneeba ta rukota tayi saurin juyowa tace"ina zakije?"murmushi husnah tayi tace"zanje ne nidasu nusrah muyi aikin abinci duka gidan nasan yanzun bazaa samu sukunin dafa wani abuba yanzun zanje in dawo kinji?"ta jinjina mata kai shaawa sukabasu dukkansu tasa kai ta fice suka bita da kallo,

suna nan zaune ko minti goma sha biyar husnah batayiba da fita muneeba ta fara jin ciwo motsawa tayi dakyar ta ruko kasan mararta da yayi mata nauyin gaske tace"ciwo nakeji momy"tana kallon hajiya saude jikin hajiya saude ya mutu nan da nan gumi ya soma karyowa muneeba ta soma murkususu a kasa mararta na ciwo addua takeyi tana yarfa hannu tana kiran sunan Allah tana kiran sunan yaseer,

husnah ta gama hada abinci ta Shiga dakinta tayi wanka ta fito daure da towel a jikinta ta gansa zaune gefen gadonta tana ganinsa ta hada rai dan fushi takeyi ya saci kallonta suna hada ido tayi masa wata harara ya mike ya zuba hannuwansa cikin aljihunsa yace"fushi kikeyi dani saboda matata ta aikata zina?"damm gabanta ya fadi ta kallesa idonta jajir zatayi magana yace "Tou ki cigaba da fushin nima zan tafi inbarku kinga tafiyata"yasa kai ya fice kasa magana tayi sai zama datayi gefen gado tana tunanin me yaseer ke nufi shin besan kaddara bace?koko beyi imani da Allah bane?"nusrah ta shigo dakin cike da damuwa husnah tace "lafiya na ganki hakan meya faru?kin duba abincun yayi kuwa?"

"ehh yanzun nadawo daga dubawa Anty husnah,yaya muneeba nacan ta soma ciwo"kuuuuuu husnah taji cikinta na kugi cike da tashin hankali ta zaro Ido cikin sauri ta zura rigar data ajiye zatasa ta sa ta fice ko ganin gabanta batayi



*NAGODE KWARAI DA ADDUOI DA UZURIN DA KUKAIMUN ALHAMDULILLAH MUBEENA AN SALLAMEMU A ASIBITI SAIDAI JIKIN SAI A HANKALI A TAYATA DA ADDUA*



*GA MAI BUKATAR WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAI BIYA YA KARANTA*


07042277401
08036953516


*SLIMZY*✍🏻51
tafe yaseer yake cikin mota tuki yakeyi hankalinsa gaba daya baya tare dashi tunanin cin amanar da muneeba tayi masa yakeyi don me husnah zatace ya yafe mata yanzun inda ciwo ta dauko fa?da yanzun tasa masa shi gaba daya hankakinsa a tashe yake dole ya dauki husnah suje a gwadasu horn yakeyiwa mutanen da sukai cincirindo a bakin titi shiru basuda niyyar matsawa a fusace ya fito daga motar "dalla kunzo kun taru a gefen titi sai kace...."cakk harshensa ya tsaya kallon hajiya rabi yayi jini na zuba a goshinta gefenta sadiya ce kwance warwas babu alamar rai a tattare da ita wani jiri ne ke neman daukarsa suka hada Ido da hajiya rabi kallonsa takeyi kamar tasanshi saidai ta kasa ganesa yaseer surutan da takeyi ne ya furgitasa "kun gani ko motace ta bugeni boka ya mutu yabar muneeba da ciki a jikinta tanacan a wani kauye yanzun gashi Alhaji yq sakeni umm kungani ko ninasan sharrin matarsa ne itace ta karya asirin da nayiwa Alhaji"damm gaban yaseer ya yanke ya fadi ya karasa inda take jikinsa na rawa wani mutumi daga bayansa yace "kai bawan Allah zaka kai kanka ne wajen wacce take tare da tsinuwar Allah bakajin kalaman da take fada ai bataga komiba yanzun tafara gani daga gani asiri tayi ya dawo mata shedaniya ka dawo Baya 'jikin yaseer a sanyaye ya hadiyi wani miyau mai kauri jikinsa babu kwari ya juya hajiya rabi ta mike ta ruko yaseer "karka tafi baka bani kudiba kabani kudi kawai ninasan me zanyi dasu"wani saurayi dake tsaye ya zabga mata mari ya fincike ta daga jikin yaserr ya hankadatw "yanzun nan mota zatazo a kaiki asibitin mahaukata a cillar dake daga ganin yadda kuke dambe a titi da abokiyar tafiyarki bakuda dangi "

"dambe?"yaseer yace a sanyaye

"ehh dambe sukeyi suna surutai mota tazo ta bugesu waccen kanta ya bugu a titi dayar kuwa har yanzun bata motsi kamar ma ta mutu"goge gumi sa yayi yace "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun umm"

"kasan su ne?"da sauri yaserr ya girgiza kai 'bansanta ba"cikin sauri yabar wajen mutane na tsaitsaye ya Shiga cikin motarsa ya had'a kansa da sitiyarin mota yanajin jiniyar mota emergency na asibiti yaja motarsa yayi kwana ya koma gida dakyar yake tukin motar ya iso kofar gida kasa fitowa yayo daga ciki motar ya kunna karatun alkurani ya kwantar da kanta a jikin seat na mota

kuka husnah keyi shabe shabe rike da muneeba dake durkushe akan gwiwoyinta gabanta ke budewa wani abu na turowa sai tayi saurin hade kafa hajiya saude ta riketa da kyau ummah hadiza addua take tofa mata ta saki wata kara cikin ikon Allah saiga abu ya fado sukuf a kasa kallon juna sukeyi a razane cike da tsoro da furgici ummah hadiza ta kalla sak mutum saidai babu ido babu komi babu baki a fuskar sai hannuwa da kafafu jikinsa tamkar kifi tarwada fatar jikinsa bakinkirin kana kallon wasu jijiyoyi cikin abun baya numfashi,hajiya saude ta janye muneeba gefe da tuni ta suma tsananin masifar da take ciki da ciwo husnah ta mike ummah hadiza tace "dauko zaninta gashi can a rufe abun"da sauri husnah tayi yadda ummah hadiza tace ta rufe tana kokarin tabawa hajiya saude ta daka mata tsawa "ke husnah bakida hankaline zaki taba wanan halittar a tare dake ga juna biyu kinadashi salon ki janyo mana fitina dama dakyar muka rabu da fitinannen aljanin nan"jiki ba kwari husnah ta fito tayi gumi kaca kaca mahaifiyarta ce ta shigo parlorn dakin "yadai husnah ina muneeba?ta haihu kuwa"gyada mata kai husnah tayi tana kokarin fita hajiya zainab ta daga hannu sama cikin farin ciki tace "Alhamdulillah "ta kutsa kai cikin dakin ummah hadiza na shafawa muneeba ruwa a fuska a hankali ta bude idonta tana kallon sama wani zugi da radadi ne takeji a kasanta ta motsa a hankali tace "washhh wayyoo Allah"ta kasa hada kafafuwanta hajiya saude wani takaici taji ya tsaya mata a wuya tsananin tsanar hajiya rabi taji da haushin ita kanta muneebar tace "gaba ki sake wanan kuskuren kindaiga ishara na tabbatar mu da wani gidan ne ko wata zuriar ne saidai kibi mahaifiyarki kusan yadda zakuyi amma dayake mahaifinki jininmu ne bazamu taba barin jininsa ya wulakanta munada rayuwa ba muneeba"jikin muneeba yayi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa momy dake tsaye tace "sannu muneeba sannu kinji Allah ya baki lafiya"ta jinjina kai dakyar ta motsa bakinta tace "Ameen momy"wasu hawaye masu zafi ke zubowa daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login