Showing 108001 words to 111000 words out of 233624 words

Chapter 37 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2545

daga daki falon sama ta zauna.




Gama kushe dakin Mom tayi sannan tayi shiru tana kallon Asmeey dake kneeling agabanta kanta akasa jikinta na rawa uppan bata ceba, jakanta Mom tabude taciro wani abu a black leather tamika mata tace  stand up and take this hide it inda babu wanda zai gani tashi Asmeey tayi jikinta na rawa ta karba tawuce wajen wardrobe tabude ta boye ledan a karkadhin kayanta sannan tadawo tasake kneeling agaban Mom, Mom takalleta ji take kaman tasa kafafunta ta murje wuyanta ta mutu amman tadaure, yanda takara kyau abin namata ciwo but ta daure da kyar tace  stand up and carry your hijab mikewa Asmeey tayi tawuce wajen wardrobe tadauko hijabinta gabanta na faduwa, Mom tace  sakashi sakawa tayi, Mom tanuna mata kofa tace  wuce mutafi auren yakare! Bugawa kirjin Asmeey yayi sosai dan kallon Mom tayi, dudda gabanta na mahaukacin faduwa amman ta daure ta dake jin Mom nacemata auren yakare tace  ina z& &  kwata kwata maganan ya makale mata awuya sabida kallon da Mom ta mata, strictly Mom tace  are you questioning me Asmeey? Koko gezo idanuna ke miki? Koko ciwon kunne yasa naji kaman kin tambayeni ina zaki? Girgizamata kai tayi tana kuka tace  Y& .a yace& ..kar& ..kar& .na& ..na& & fiii& &  Mom tadaga murya tace  ni kike gayama Yaya yace karki fita? Ni Asama u? Mamaki yawani kalan cinye Mom ganin Asmeey kaman tarage shakkan ta dan wlh ada Asmeey bata isa tace mata wane kaza ko kaza ba, Mom ta buga kirji tace  nadaukeki acikina! For 9months! Na raineki! Na haifoki! Nature you kawowa this day, Asmeey ni mahaifiyarki kike cema ina zan kaiki? That tababben yaron nan yace karki fita ? Girgizama Mom kai tayi tana kuka wani tsoro na tarwatsa mata zuciya, Mom tace  okay sabida kinyi aure kin zauna awannan wulakantaccen dakin karo karo dawani gantalallan yaro da iyayensa ke ciyarwa har yau! Tufatarwa har yau! Basa makwanci har yau shine kike kike tambayana ina zankaiki kehh! Tufiakwa! Kasa Asmeey tafarayi tana dukawa cus Mom tafara maganganun nan saitaji rayuwanta na hargitsewa Mom tazo wajen, batai wata wata ba ta daga kafanta da takalminta ke kai mai tudu tawani daki kan Asmeey tace  na kasheki na kashe banza wulakantacciya! Jikake kummm goshin Asmeey da kanta gabaki daya sun daku da katakon gadosu, gindin tundun takalmin Mom yasa goshinta ya fashe saiga jini wajen na kulu lokaci daya sai kawai Mom ta duko takalleta yanda kan Asmeey ke kasa tana kuka ta rakube da gado kaman marainiya, Mom takai yatsanta takama habanta tadago da fuskanta tace  kalleni nan! Kallonta Asmeey tayi jikinta na tsuma na kuka tana makyarkyata bamata iya kallon Mom sosai tsabagen tsoranta kaman wata doddanniya haka Asmeey ke ganin Mom, cikin wani irin murya Mom tace  tsakanina dake is biyayya Asma u sabida ke diyata ce, duk randa kikace bazakini ba bakida ragowan amfani a duniyan nan! Mom ta nuna mata wardrobe tace  kinga ledan chan maganin bera ne aciki full sachet! Idan you refuse to come with me you choose here kinyi choosing mijinki bakida ragowan amfani aduniya makesure kin dauki maganin chan kin ci inaso naji sanarwan mutuwanki da gaggawa shiyafima rayuwata alkhairi naga kin mutu! Mom tai maganan batare data daga murya ba Asmeey tawani irin kallonta tana nishi tanaji kaman ma mutuwan na zuwan mata yanzu, Mom tace  since you are torn between Mahaifinki, ni, dakuma mijinki, idan baki bini ba nima na jaye permission na barinki kicigaba da numfashi aduniya your live belongs to me Asmeey! Menace? Bak1n Asmeey nawani kalan bari batama iya maganan da kyau sabida yanda Mom tarike mata habba tace  my life belongs to you Mom! Wani kalan kallo Mom tamata ido cikin ido tace  na tsaneki Asma u! Na tsaneki! Ke Allah ya halakaki mutuwan ma banso kiyi ta sauki! Nakawo Fawaz nace shinakeso ki aura ki zabi mahaukaci! Arayuwanki kap ni uwarki niyakamata kibi zabinta not zabin mahaifinki or this jobless boy! I made you Asmeey! You become human in my tummy, and u come to this world through my vagina so kawani yaro mahaifiya ke da iko dashi not uba saisa Annabi ya ambato uwa sau uku kafin uba! Wani irin ijiyan zuciya Asmeey take tana kallon Mom kallon wat is left again? Rayuwanta yagama yawo? Mom tasaki kumatunta tamike tawuce  tashi mutafi wlh kasa motsi Asmeey tayi maganganun Mom yasa taji kaman she s brain dead sai hawaye dake sauka daga idanunta kawai, juyowa Mom tayi ganin Asmeey batai motsi ba mamaki na kashe Mom ganin Asmeey ta chanza tace  badake nake magana ba? Wuce muje someone need to see you! Ko gezau Asmeey batayiba kaman ma bata hayyacinta, Mom batai wata wata ba tazo wajen ta duko ta daura mata mari dayasa Asmeey taji she s not just brain dead yanzu she went blind Mom tai ihu da duka gidan ya amsa.  Wuce muje nace kin gama zama da mahaukaci ma kashe auren! Daidai lokacin aka bude kofan dakin Mamie ta shigo idanunta kan Asmeey dake duke gaban gado tarakube kaman mussa ga jini nabin goshinta dayayi kululu kumatunta yayi jajir hannuwan Mom sun fito radau, dasauri Mom tai wajen Asmeey taduka tanakai hannunwanta tataba goshinta tace  Asmeey! Asmeey! Innalillahi! Asmeey! Ko motsi Asmeey batayiba, Mom azuciye tace  Hamida tashi kibar wajen nan ko ranki yabaci yanzun nan, zan miki duk abinda yazo raina wallahi, you keep coming between me and my daughter ubanwa yataba coming between ke da yaranki ? Sakin Asmeey Mamie tayi ta taso batai wata wata ba tawani kalan tura Mom Mom ta bugu da kofa azuciye Mamie tace  bar gidan nan! Get out of my house! Mom tayi wani dariyan keta ta nuna gidan tace  is this wat you call house? This useless 90s house? Yes I am going but da y ata idan kin isa kihanani Mamie nawani kalan kallon Mom tace  Salima bantaba ganin wata Uwa dana kalla naji araina cewa she don t deserve to be a mother arayuwana ba saike! Salima kin dauka abin adone yara sudingajin tsoron iyayensu haka? This is not flex halin nan da dabi an nan yasa duk na raina iliminki! Your education, qualifications is rubbish is utterly nonsense, kina part of human right activist yet you abuse this poor innocent girl kullum kullum! Koda agidan karuwanci, cikin shege, a turakan karuwai kika haifeta banjin you will be treating this poor child like a goat or jaka hakaba! What is her mistake? What is her sin? Me Asmeey tayi? Look at her! She is just an innocent little girl da all she wants is Mamanta tasota, just look at her face for once arayuwanki with love! Me Asmeey tamiki? What is her crime Salima? Metayi? Metayi? Metayi miki tell me why are you hurting Asmeey na? What did this bright young smart child did to you Salima menene gayamin? Mamie tafashe da kuka dan yau takasa rike zuciyanta abin namata ciwo, tanunama Mom dake kallonta hannunta dakeda jinin Asmeey na goshinta Mamie nawani kalan kuka tace  look at blood na yarki? Salima wanda ta sanadinki yake zuba! Look at hannunta akarye ta sanadinki! Dubi jikinta duk kene Salima me Asmeey tamiki ehhhhhhh? Menene? Why this much hate for yarki dakika haifa da kanki, why why why do you want Asmeey dead? Sai kinga gawanta zaki huta? What did this poor girl do? Ki gayamin cus azaban yayi yawa, ina gujemiki alhaki fa! Wata rana zaki nadaman abubuwan dakikama yarinyar nan ki rubuta ki ijiye, Salima kiji tsoron Allah lumshe idanu Mom tayi tabudesu takalli Mamie tace  kinga yanda kika hankadani na bugu da kofa na yafe miki sabida naga kin tsufa jikinki ya gajiya amman kika kara kuskuren tabani saina miki jina jini wallahi tallahi, y a dai nina haifa ba ke ba ko, ko sokamata wuka nake ba ruwanki! Abarmin kayana! Ninayi wahalanta tun tana yar kunzugu, tashinmini agaba nadauki y ata mubar gidan nan tsayuwa Mamie ta gyara tace  idan kin fita da yarnan daga gidan nan saidai idan nafadi anan na mutu Salima! Ijiye jaka Mom tayi akasa tace  hahaa inaga Asmeey bata gayamuku wacece mahaifiyarta ba, tashi Salima nace Mamie tace  kome zakimin kimin yanda kika tsani yarnan zan gwada miki akwai wayanda zasu iya basu ranta just to protect her, Salima kasheni shine abinda zaisa ki dauki Asmeey, do your worst wani irin yunkurowa Asmeey tayi tana layi kanta ya bugu, wani dummm yake mata but tanajin hayaniyan Mom da Mamie hakan yasa ahankali tace  Mamie karki fada da Mom sabida ni Mamie yakuri maganan da Asmeey takeyi kadan kadan yasa Mamie tajuyo tana kallonta tana kokarin dukawa tama Asmeey magana Mom tawani pushing Mamie mercilessly Mamie tayi mummunan faduwa ta bugu ta desk da chair na Hamad laptop dinsa da desktop suka fado kanta tana kokarin tashi takasa tarufe idanu kaman ta mutu.
EPISODE 4?? 3??




Asmeey tayi wani ihu tana layi zata tashi tai wajen Mamie Mom tawani ja gaban riganta tadauki jakanta ta finciki Asmeey kaman karya tafito da ita, Asmeey na ihu tana  Mamie, Mamie amman Mom janta take, yau Sunday masu gini duk basanan mai gadi ma yafita matarsa ce kawai agidan, Mom awaje tai parking motarta, jan Asmeey take sosai akasa Matar mai gadi tafito da gudu but ayanda taga fuskan Mom da yanda Asmeey tai kama da Mom saita sandare takasa magana Mom ta fito da Asmeey waje, daidai Hameed na wani wawan parking motarsa agefe gindansu yafito da gudu, saiga motansu Abba da kawai yakirasu kai tsaye yace komenene su barshi sudawo gida ba lafiya, suna duk sukai parking suka fiffito, Hamad yafito idanunshi sun rikida yashiga takowa a zuciye da saida gaban Mom yafadi ganinsa, dasauri tasaki hannun Asmeey data zube awajen tana kallon Hamad tadan rude takai hannunta tasa ajaka tafito dawani black Nylon dayayi nauyi a hannunta, Hamad yasa gudu dan sundanyi parking nesa da gidan su, kafin ya iso Mom ta jefama Asmeey ledan wani red grinded yaji na zubewa tundaga saman kan Asmeey down to jikinta kawai tabude mota tashige taja motar da mugun gudu tabar wajen.
Asmeey tayi wani irin ihu da tunda aka haifota duniya bata tabajin kalansa ba.  Wayyyyoooooo Allah na namutu! Innalillahi wa Innailaihi raji un, na shiga uku na lalace, azaba na mutu, wayooooooo azaba she s screaming in excruciating pains da top na voice nata tanajin azaban da tace maybe zare ranta akeyi Ya Allah! Hamad baiyi wata wataba kawai yarungume Asmeey batare daya damu da barkonon ba, ina Asmeey bamatasan wake kanta ba sabida kololuwar azaban burkono datakeji, tana wani irin bankarewa daga jikin Hamad dake kokarin daukanta tana kokarin yin tsirara tadaga duka hannayenta tasa asaman kanta kaman wacce tasamu tabin hankali! Ina Hameed jiyayi kaman ya halaka Mom yace  Wlh saina kashe matan nan yabude mota Faisal da Ya Abdullahi suka bisa sukaja motar Abba yakasa motsi haka ma Gwaggo sunyi mutuwan tsaye, da sauri Ya Mustapa yayi wajen Hamad harya dauketa yashiga gida da ita ganin an fara taruwa awajen, garden ya ijiyeta yadauki pipe na ruwa yawani bude with full force yasamata tundaga saman kan Asmeey zuwa kirjinta da hannayenta idanunta ta runtse su, ya Mustapa yayi wajen motansa yabude yana neme neme Abba yarike Gwaggo dake wani kalan kuka suna shigowa ciki, tass saida Hamad yacire duk wani yajin kawai yasake daukanta Ya Mustapa daya kwaso magunguna yabiyosu da gudu yace  take her to bayi wash her body with soap and cold water with salt bari na dauko salt da ice a kitchen kuje .
 Zan mutu, zan mutuuuuu na shiga uku wayyooo azaba, Innalillahi wa innailaihi raji una dakinsu dayake abude Hamad yayi Mamie yagani akasa tana kokarin motsi takasa idanunta sunyi jajir, wani irin ihu Hamad  Mamie! Yana ijiye Asmeey yayi kan Mamie Abba da Ya Mustapa na tahowa dakin da gudu, hannu Hamad yakai zai daga Mamie Ya Mustapa yace don t touch her akwai yaji ajikinka just handle Asmeey Hamad yawuce da Asmeey bayi Abba yadago Mamie da sauri datake motsi da kyar tace  metama Asmeey take ihu haka? What happen to this poor innocent child ? Abba na shafa fuskanta yace  are you okay ? Gyadamai kai tayi tace  dan bugawa nayi bari naje wajen Asmeey she s screaming Abba yatayata ya dagota da kyar take tafiya tana dafa bango, bay1n tawuce Hamad dake hada ruwa yana zuba salt da ice, yace  Mamie go and sit ahankali tace  jeka Hamad ihu Asmeey take banawasa ba bamata gane komi, Mamie yacire mata kayan ta wanke mata jiki tundaga kai tana kwara mata ruwan sanyin da aka saka ice da salt Asmeey na wani irin nishi, Hamad yazo dawani gown Mamie ta karba tasamata suka fito da ita kwantar da ita sukayi tana makyarkyata kawai Ya Mustapa yamata wasu allurai na instant bacci that s the only way na calming yaji cases, Mamie dake tsaye tayi baya zata fadi dasauri Ya Mustapa yariketa bacci na fizgan Asmeey dahar wani zabura take na pepper daidai su Ya Faisal na zuwa sama ganin an rike Mamie yasa dukansu sukai kan Mamie! Mamie! Mamie! Ahankali Ya Mustapa yace  bugawa tayi I will give her injection mukaita daki Dasauri Hameed yadauki mahaifiyasa chak sukai dakin Mamie Hamad na binsu idanunsa yayi ja, allura Ya Mustapa yamata suka kwantar da ita dukansu suka zagaye mahaifiyarsu da shi kansa Abba saidai ya tsaya a gefe, Hameed yakalli Hamad dake wani kalan nishi yana kallon Mamie yace  you are burning too! Yaya akwai yaji ajikin Hamadi shima dasauri suka zagayeshi, Ya Mustapa zai tabashi Hamad yace  leave me saiga hawaye mai zafi yana wani irin huci yace  how dare she touch my Mom! ? Saiga hawaye kowa yasan Hamad loves Mamie sosai, Abba yace  ya isa tashi kaje ka cire kaya kai wanka ka chanza kaya yaji duk a hannuwanka da wuyanka sauke Kansa kasa yayi yana wani kalan huci yabala in basu tausayi, duk sukai shiru Hameed yayi tapping shoulder nashi yace  stop crying Faisal ma yace  ya isa dan sunsan shi yamafi kowa hurting his Mom and his wife, murya chan kasa yace  me Asmeey tamata that is so wrong take zuba mata yaji haka? Why did she hates her why? Why? Wat brought Mamie na into all her madness!? She thinks Mamie na yarta ne data saba duka and go scout free I will mess her up give me her number Hameed! Ya Mustapa yace  kar wanda yabasa number ta that is idanma any of you nada number kenan, go and shower Hamad you are burning Ya Hamad yadagasa yamike da kyar yafice daga dakin.
EPISODE 4?? 4??




Ahankali take bude idanunta da kyar kanta yayi mata nauyi, jikinta tabi da kallo an lullubeta da bargo, komi daya faru jiya nadawo mata dasauri tabi dakin da kallo especially wurin desktop din Ya Hamad datasan anan Mamie tafadi saitaga an maida komi daidai, dawani kalan sauri tamike ta tashi zaune tana dafa goshinta dataji yana mata ciwo tace  Mamie dudda babu karfi ajikinta saukowa tayi daga gadon tana tafiya ahankali, Mamie kawai takeso taje tagani, bude kofan dakinsu tayi ahankali baiyi making sound ba tafito, tundaga wajen take jiyo muryan Gwaggo adakin Mamie na zubawa Mom ashar, cigaba da tafiya tayi daidai gaban dakin zatasa hannu tabude kofa kenan taji muryan Hameed yace  haba dan Allah just look at bakin cikin da Hamadi ya kwana dashi! This is what I said lokacin nan, what is the point na auro yar matan nan da lafiya ta da tunanina? This is the same reason yasa su Ya Musty basu taba kwadayin auren su Aya da Aysha ba, waye ita? What gives her the right ta taba mahaifiyar mu? Wlh wlh I said it jiya, Hamadi ma yafadi if anything happens to Mamie mu that woman will pay for it na rantse da Allah! Faisal yace  kawai dai dan laifin wani baya shafan wani ne but mata irin Salima baka fatan wani abu nasu ma yashigo hannunka I am so angry God! Ya Abdullahi yace  jikina har tsuma yake da ace damuka ganta awaje munsan ta taba Mamie da wlh sai na mata jina jini, saina fasa munafukin gilashin idanun nan nata, very stupid useless woman Gwaggo dake kuka tace  wlh, wlh dan kawai Asama jikata ce babu yanda zanyi amman da wata ce da sainayi nadaman aurota da Hamadi yayi anatse Ya Mustapa yace  duk ku yakuri Mamie is fine bagashi nan tana bacci ba Ya Mustapa yace  Hamadi stand up kaje dakinku Mamie is fine ahankali Asmeey taji Ya Hamad yace  I want to stay with Mamie Yaya! Wani iri zuciyan Asmeey yayi sai kawai tashiga komawa baya zuciyanta na radadi tajuya da dauri takoma dakinta maida kofa tayi ta rufe ta jingina da kofan tana wani irin kuka feeling extremely bad because of ita Mom tayi hurting mahaifiyarsu, Mom tayi hurting Mamie all of them are angry with her, tip na hancinta da bakinta har wani rawa rawa yake tsabaragen yanda zuciyanta ke radadi, dago idanunta tayi ta kalli wardrobe nata tai shiru saikuma ta kalli karyayyen hannunta,  What is special about rayuwanta? Is all because of her zuciyan kowa ke lalacewa tundaga kan Mom, Baba, yayyinta Ya Aysha tace Mom bata magana da Ya Aya all sabida ita, Munir kullum jin haushin Mom yake all sabida ita, itama Mom haushin Munir takeji all because of her, Baba yasaki Mom

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login