Showing 150001 words to 153000 words out of 233624 words

Chapter 51 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2522

ya sara komawa tayi ta zauna tamika hannunta tadauki bottle water dake wajen tabude takai bakinta ta kurba maganan Baba na fado mata dazu yanada suprise for her PM menene menene ma yace? CNN? Remote na tv ta dake nan kan table tasa hannu tadauka tana ijiye bottle water ta danna power button tv ya kunnu, TV ya kunnu tadauki remote na DsTV decoder ta chanza zuwa CNN daidai ana program din CNN da ga turawa dayawa ciki harda bill gates, Elon musk, Ambani, da other top world richest people hall din an cika makil, Mom tadan yatsine fuska tace  me mutumin nan yasa nake kallo ? Daidai mai hosting wata British woman tace  Ladies and gentlemen! Let s welcome the star of night! Microsoft Talent Hunt Winner who design, create and invent the SOFT AI! Mr Hussein Hamad Abubakar! Aka fara wani irin tafi camera na hasko Hamad dake zaune kan wani kujera sanye da black suit da tie awuyansa yasaka wani earplug a kunnensa guda daya wanda kaman a wajen aka ba_a sabida speech dazai bayar, yayi bala in kyau yawani mike tsaye!
Mikewa tsaye Mom tayi tana zaro idanu tana wani kama kirjinta tana kallon Hamad na walking to the stage while presenter na bada short biography na rayuwan Hamad wani soft low plane music na tashi.  Mr Hamad is Nigerian born and brought up in Kano the northern part of Nigeria! He s 33yrs has a bachelor degree in computer science engineering and MSc in software engineering and Inovation, he s into Tech, acquired different certifications from the likes of Azure, AWS, Oracle, CSM, Sensor flow developer, Artificial Intelligence Practitioner, etc.. Daidai Hamad na karasa hayowa stage din looking handsome, charming and damn charismatic, gashinsa da coils nasa na kyalli ya tsaya elegantly ya kallo hall din, tamikamai hannu, karba yayi gently suka gaisa ta matsamata gefe ana tafi ba kakkautawa& . Dawani irin sauri Mom ta dauki wayanta har duhu duhu take gani ganin kaman karyane abinda tv ke nuna mata tashiga Google tay typing  Microsoft talent hunt winner kawai taga hoton Hamad da kudin dayaci kimanin 500 million dollars kudin Nigeria 777 billion naira kawai waya ya kufce daga hannun Mom kanta na juyawa tana ganin duhu duhu, kirjinta nawani irin bugawa na bakin ciki da azaban hassada ta tafi luuuuuuuu ta zube kasa bata sake sanin inda kanta yake ba jini ya buga.
EPISODE 7?? 2??





Wuraren 1 Asmeey ta tafi sama dakinta danyin salla azahar, she s extremely missing Ya Hamad, tun shekaran jiya dasukai maganan zuwa saloon bai kara kiranta ba, she guess he s busy sabida yaune akace za ayi lunching AI din, tana zaune akan dadduman akai knocking dakinta tareda sallama jin muryan Ya Mustapa dasauri tamike tsaye bude kofa tayi tadan sauke kanta kasa akunyace tace  ina yini Yaya? Gyadamata kai yayi yace  ya jikin wat are you doing inside? Dadduma ta nunamai tace  salla nazo nayi gyadamata kai yayi yace  okay muje downstairs Hamadi app lunch is in few minutes gyadama Ya Mustapa kai tayi ahankali yawuce saita biyosa abaya tana rufe kofan, muryansu duka taji a kasa itama Mamie tabude dakin nata tafito dan itama salla tazo tayi hatta Abba yadawo daga kasuwa duka suka wuce kasa harda Gwaggo dasu Munir, wajen Munir Asmeey taje ta zauna kusada shi tana kallon TV an fara program din kawai gabanta sai faduwa yake, Ya Hameed yatashi yana sassauke labulen window yakashe wuta, falon yayi duhu tv kawai ke haske duk kallon TV ake Gwaggo tace  suwa Allah su nunamin Hamadi na nagansa Faisal yace  an kusa Gwaggo, yanzu wannan dake magana shine mai Microsoft din Yana gama magana yakoma sit dints dake kusa da Billgates daidai mai hosting wata British woman dake sanye da suit mai kyau tace  Ladies and gentlemen! Let s welcome the star of night! Microsoft Talent Hunt Winner who design, create and invent the SOFT AI! Mr Hussein Hamad Abubakar! Bugawa kirjin Asmeey yashiga yi wani chills na sanyi na ratsata tundaga kan yatsun kafafunta har brain nata, aka fara wani irin tafi camera na hasko Hamad dake zaune kan wani kujera sanye da black suit da tie awuyansa yasaka wani earplug a kunnensa guda daya wanda kaman a wajen aka basa sabida speech dazai bayar, yayi bala in kyau yawani mike tsaye! Asmeey ta tsaresa da idanu kaman yau tafara ganinsa Ya Allah! Tanason mijinta! Bata tabajin tanason abu aduniya kaman Ya Hamadi ba, see tanason Ya Hamad kaman taita ihu tana screaming she loves him, butterflies taji suna tafiya acikinta bana wasaba takai hannunta ta daura saman cikin kozai rage motsi, Gwaggo tace  ku kalli jikana wlh uwa bature baida banbanci dashi, Hamadi ne haka? Yazama bature Murmushi Mamie tayi sosai ganin danta looking damn handsome hawaye na zuwan mata idanu Abba yakama hannunta yarike yana murzawa yana kada kafafu proud parent kenan! Anatse Ya Mustapa ke kallonsa shi kadai yasan yanda yake alfahari da kaninsa, Hameed yaciro wayansa yana daukan hoto daga tv yace  status status lets pepper the haters Faisal yace  look at my Hamadi! Looking classy and rich, wlh ya chanza gabaki daya Ya Abdullahi yace  jibi yanda bill gate ke kallon Hamadi karya kwacema Microsoft shi ko numfashi Asmeey bata iyayi da kyau sabida yanda take kallon Hamadi daya mike walking to the stage calmly babu wani gara gara ko garaje a tafiyan, one step at a time yake while presenter na bada short biography na rayuwan Hamad wani soft low plane music na tashi.  Mr Hamad is Nigerian born and brought up in Kano, the northern part of Nigeria! He s 33yrs old has a bachelor degree in computer science engineering and MSc in software engineering and Inovation, he s into Tech, acquired different certifications from the likes of Azure, AWS, Oracle, CSM, Sensor flow developer, Artificial Intelligence Practitioner, etc... Daidai Hamad na karasa hayowa stage din looking handsome, poised, charming and damn charismatic, gashinsa da coils nasa na kyalli ya tsaya elegantly ya kallo hall din, tamikamai hannu, karba yayi gently suka gaisa ta matsamata gefe ana tafi ba kakkautawa saida raf1n ya tsagaita yace  good day ladies and gentlemen zokaji tafi sabida yanda voice nasa yayi a mic din, turencinsa is very sweet, rich and simple, bawani kakalen banza da wofi, speech zai fara badawa dangane da winning dayayi da dedication sai presentation na software anatse yace  I want to thank God Almighty for making my dreams come true, I wanna Microsoft team for looking beyond where I come from, rather they look at my potentials, my skills, my dedication and hardwork& .. I want to dedicate this win to my family! Yadanyi shiru ana tafi yace  My Dad Abba did everything for me if you are watching this thank you Abba! Akahau tafi saida aka tsagaita Hamad yace  you know I have a second Dad& . Yadanyi shiru kadan yana kallon audience din yace  he happens to be my brother Ya Mustapa! He s my everything! Yafadi asanyaye kafin ahankali yadan fuzar da iska yace  without his support I wouldn t have been here today yayi shiru cus baiso yayi kuka akahau tafi bana wasaba to lift his spirit, Ya Mustapa yayi shiru yana kallon Hamadi daga tv idanunsa nada ciko da kwalla kadan, haka kowama na dakin, ahankali yace  My Mom! Mamie is my comfort zone, my peace, my encouragement and my strength! I have the world best mother yafadi ahankali dayasa Mamie tashare hawaye dasauri, anatse yace  to the rest of my family, my nosy brothers, my twin they all contributed and made me who I m today I wish everyone have brothers like mine yadanyi murmushi kadan, sai akuma ahankali cikeda wani irin natsuwa ta daban yana kallon mic dake gabansa daban daban yace  and my wife! Yayi shiru hall akai tsit jin ya ambato mata yace  she s is my sunshine that made my life brighter and colorful! And she s my lucky charm, my better half! su Hameed suka kalli Asmeey sukace  awwwwwwwnnnnn Asmeeeyyyyyyy boye fuska Asmeey tayi akunyace zuciyanta na mata kaman an watsa wani sugar mai sanyi tana wani kara crushing on Hamad tanajin mahaukacin sonsa aranta hawaye na fitomata daga idanu, anatse Hamad yace  this win is not for me alone, is for my family! For my state! For my country Nigeria and for African in whole! Aka fara tafi sannan sai ya shiga bayanin soft AI yana nuna musu a screen da yanda yake aiki, ba yan hall din kadaiba harsu dasuke kallo daga tv knows Hamad was made for this! He s the definition of a talented genius, this is his thing he killed it, he ate and left no crumble, gaban Asmeey sai bugawa yake yanda ake nuno yan hall din na kallonsa, abubuwa na mata yawo a zuciya Ya Hamadi zai sota again? Idan wata ta kwacesa fa? Look at yanda maza ke sonsa ballema mata, kowafa yasan mijinta kenan ko? Tai shiru tana tunani daban daban gabanta na faduwa tsoro na shiganta, deep deep down she prefers Hamad dinta dasuke tare koda yaushe adaki daga ita sai shi, karya shagala yaga matan dasuka fita komi ya manta da ita, har aka gama ta tashi ta sulale sama ganin su Ya Hameed na tsokananta, yace  gobe yace na kaiki saloon daganan zamuje gidansu Zee Munir yace  Yaya nima zani saina dawo dakai Hameed yace  okay tom .
EPISODE 7?? 3??





Saida aka gama program din tsaf a falo Baba dake kallo da Ammi da Ramla dan sauran yaran na school yayi murmushi yataso dan yazo yaga fuskan Mom, bude kofan yayi da sallama ganin Mom sandare kan kujera tarike kirjinta bata numfashi yasa yayi wajenta da gudu yace  Salimah! Salimah! Ina Mom bata motsi kokarin dagata yayi yakasa ya kwalama Ammi kira sai gata yace  tayani mu kaita mota zuwa tayi tace  Subhanallahi meya sameta ? Baba yace  I don t know kaita mota sukayi Ramla takawo hijabi da slippers na Mom, Baba yaja motan da kansa suna kaiwa asibiti aka karbi Mom Baba yasami waje yazauna yana dafa kansa saikuma yaciro wayansa yakira Yayanta ya sanar dashi ya katse wayan yayi shiru

Chan saiga Dr yace  come with me binsa Baba yayi, suna shiga Dr yace  ya akayi BP Madam yayi raising haka? And tanada Cardiomegally which happens due to hypertension Baba yace  mekenan likita? Dr yace  zuciyanta ya kumbura sabida hawan jini, yanzu I will put her on heart drugs dazata sha for a month tadawo, dudda haka I will still refer her to see a cardiologist, please please Madam tai avoiding damuwa dawani tashin hankali da sauransu, zuciya muke magana anan is dangerous is not something to be taken likely Baba yayi shiruuu yau daya ganta tabbas yaga ta rame sosai me Salima keso ne? Kin tsani yarinyar sannan kuma an aurar da ita an cireta daga gabanki kince a a baki yardaba, wani kalan concoction kalan damuwa ne wannan da fitina da bala i dahar tana samin kumburin zuciya sabida damuwan? Yadawo mata da Asmeey and watch her kill yarinyar dabata mata komi ba? Shine abinda zai kori BP da ciwon zuciyan ko me? This life is funny fa, like wani kalan irony ne wannan, baki sami daman cin zali ba damuwan hakan kuma haryakai gayasa miki hawan jini da kumburin zuciya? Ikon Allah! Yadai lallaba yace  to ya take yanzu? Dr yace  we ve given her all the necessary help we will wait ta tashi mugani Baba yasauke ijiyan zuciya yace  tom nagode yatashi yafito yazauna awajen yayi shiru yana kallon gaban dakin datake ciki saiga Alhaji Mahmoud yana zuwa suka gaisa da Baba yace  tana ina ? Baba ya nuna dakin yace  ba a ce nashigo ba tukunna ganin yanda Baba ke magana ba karfi a murya da yasa yazauna gefensa yace  meke faruwa?

Shiru Baba yayi saichan yace  enlargement of the heart sabida hawan jini, damuwa yamata yawa Baba yadanyi shiru dan son Mom Allah yasani yanayi, ahankali yace  Alhaji narasa yanda zanyi da lamarin Salima bantaba ganin mata mai bakin naci da kwallafa rai akan abu kaman Salima ba, yarinyar nan ta tsaneta bata kaunar ganin Asma u na aurar da ita nacireta agabanta shima ban huta ba, tace ba a kyauta mata ba ita bata yardaba saita dauko diyarta Baba yadanyi shiru yace  nakiraka ai na sanar dakai abinda taje tayi a kano takusan kashema yaran nan mahaifiyarsu, Asama u kuma ta barbadeta da burkono, wani kalan maita ne wannan? Sabida burinki bai cika ba kashe kanki zakiyi hawan jini haryakai ga zuciya na kumbura yazanyi Alhaji Cikeda bacinrai Alhaji Mahmoud yace  wace kalan tambaya ne wannan yazakayi? Yako zakayi? Idan mutuwa ta zaba ai shikenan Allah ya jikanta yarinyar zaka dauko kabata takashe tunda ita batada lafiya akai? Da ace haka iyayenmu suka mana danace okay gado halin mahaifiyarmu tayi amman wlh mun taso cikin kauna, iyayenmu na sonmu kafin Allah ya dauki ransu, mahaifiyarmu da mahaifinmu basuda zafin Salima bansan a ina tadauko nata ba bansani ba, tun wuri gwara ta sassautama zuciyanta tsana da ki data saka aciki ko ta mutu abanza a wofi Baba yayi shiru duk suna wajen akace zasu iya shiga suka shiga Mom ta farfado bata da karfi amann tana ganin Baba da Yaya ta hade fuska tamau duk suka kalleta suna mamakin Salima.

Takalli Baba kur kaman wacce ba yanzu ta farfado ba zuciyanta na radadi idan ta tuna kudin da Hamad yayi tace  ina wayata? Anatse Baba yace  bansani ba ke kawai na dauko maybe yana gida meke miki ciwo yanzu? Dan murmushi tayi tana cizan yatsa takalli Baba ko gaida wanta batayi ba tace  Ina y ata ? Shima yana kallonta yace  tana kasan waje tareda mijinta dayaci abun kampanin nan Microsoft Alhaji Mahmoud yace  ohh right rashin lafiyan Salima yasa nama manta nace maka Allah ya sanya akheri nagani a news wlh congratulations ai yaron nan kana ganinsa kasan kwanyansa fire ne, kwaro ne yaron Allah yasa albarka Mom na kallonsu tace  Yaya kagayama mutumin nan inaso ayi agabanka kasheda kada kuga banda lafiya ku dauka ko karshen kenan, Billlahillazi La ilaha illahuwa idan bai dawomin da diyata ba kome nayi nan gaba kada ya kuskure ya kuka dani ya kuka da kansa Mom ta nunasa da yatsa tace  Muhammadu Sani saina gwadamaka cewa ba Uba kadai ya haiho yarinya ba dan haka kai kadai bakada iko da ita! Me and you have equal right akan Asama u, bakada wata uwar hujja ko dalili dazaisa ka dauki y ata ka aurar batare dana sani ba dan haka I don t accept auren, kuma kome nayi ka kuka da kanka Muhammadu Sani ka kuka da kank& &  Takasa karasa maganan sabida kirjinta dataji yarike Alhaji Mahmoud yace  zaki kashe kanki abanza a wofi sabida tsana da bakar zuciya shashasha, ki mutu ayar, abin kunya ki rasa wacce zaki tsana haka sai yarki, wlh ko kishiyoyi basama junansu wannan tsannan, balle ke Uwa ki daurama yar cikinki kalansa, Allah kara sauki ni sai anjima Alhaji Alhaji Mahmood yawuce yafita yana takaicin halin sister sa.

Har dare suna asibiti sai kawai out of good will Baba yakira Aya ya sanar da ita but yace mata karta gayama sauran yaran Aya da mijinta sukazo tsaf Mom tai magana da mijin, ai dama ita tahada auren but taki kula Aya saida yabama Mom hakuri Aya sai kallon Mom take imagine tana gadon asibiti zuciya na kumbura but Mom is still holding on to grudges Baba ma abinda kawai yake kallo Kenna but sirikinsa na wajen baice komiba da kyar Mom tahakura hakan yasa yatashi yafita dan Aya tayi magana da Mamanta zama Aya tayi takama hannun Mom tarike gam tana kallonta wlh tausayin Mom take she prays to Allah ya yayema Mom koma menene ke damunta ahankali tace  Mom I m sorry dan girman Allah Mom kinji, Mom Wallahi Wallahi I will never betray you Mom dan darajan Allah kiyafemin shiru Mom tayi tana kallonta sai kawai ta gyadamata kai tace  naji yawuce dasauri Aya ta taso tadan rungumeta tureta Mom tayi but still Aya bata damuba tace  Mom I cooked for you Baba yace you refuse to eat Aya tafito da warmer tadebo rice ta dago gadon Mom ta zauna Aya tashiga bata abaki Baba na kallonsu shima tausayin Mom din yake but iya bata tausayin kanta babu komi a kumburareen zuciyan nan nata banda bala i da fitina da tsanan mutane, kowa da jarabawan sa she just pray Allah yabama mahaifiyarta ikon ci cus Mom is lost!
EPISODE 7?? 4??






Around 8 Asmeey ta shirya cikin wani black abaya after dress ne tasaka wani black inner ciki tasaka botura mai kyau da stones tai rolling gyalenta tadauki handbag tarike, Ya Hameed yace dawuri zasu sabida agama yakaita gidansu Zee, bini bini tana kallon wayanta Ya Hamad bai kiraba, wayan tasaka a jaka tafito Mamie tace  ke kadaine baki breakfast ba zokiyi sai kuje gaida Ya Hameed dake falo tayi ya amsa tawuce taci sannan ta tashi tace  nagode Mamie Ya Hameed yatashi da Munir suka fito Mamie har mota tarakasu tace  Hameed kamin gudu da yara ahankali kana jina dariya Munir yayi yashiga gaba Asmeey tashiga baya, Hameed yace  ni ba yaronki bane ? Mamie tace  ahh ka girma ai saikun dawo Allah kiyaye, kadawomin da yarinya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login