Showing 42001 words to 45000 words out of 233624 words

Chapter 15 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2528

suka sauka kan Ya Hamadi dake kwance kan gadon Mamie idanunshi a lumshe yana sanye da wata faran t-shirt na polo da wandon kayan sallanshi da alamu bacci ne yadan sace shi adakin Mamie yabar dakin sabida baki dan taji muryan maza datana shigowa.
Faduwa gabanta yayi dummm! Saita dan koma baya dasauri ta tsaya tana kallonshi the way he s sleeping peacefully, dogayen bakaken gashin idanunshi sun rufu ruff fuskanshi na sheki kaman me yin skincare, yamata wani kwarjini a idanunta kaman me, kasa koda motsi tayi sai kallon fuskanshi take kirjinta nawani irin racing kaman akwai wani abu dake kama kafafunta yana pulling nata zuwa gaban gadon, taka kafarta tashiga yi daya bayan daya tana zuwa gab da gadon ta tsaya daidai bakin gadon tana kallonshi tai shiru kaman wawiya kaman wacce is confuse akwai wani kalan abun datakeji tunda tai girma tai wayau arayuwanta kullum she s feeling tense at any moment cikin tashin hankali take da fargaba da tsoro both boko da islamiyya da gida gudun Mom tsoronta da gudun karta mata laifi, she don t know what happened yesterday was the first ever time she felt peace azuciyanta the little moment that she shared with Ya Hamadi ganinshi gives her wani internal peace, tafiyan shi, maganan shi, kallonshi, duk yana sa taji wani natsuwa acikinta da bata taba sani ba akwai kalan natsuwar, tarrr Hamad ya bude idanunshi sabida kamshin bodymist nata that s so calming, it s smell s fruity with notes na amber and slight oud, hada idanu sukayi eyes nashi looks freaking wild idan yatashi daga bacci sabida kwallin he looks like wani aljanin misira da mahaukacin tsoro tajuya zata gudu karaf yakama bakin gyalenta bawai yawani rike da karfi bane hakan yasa gyalen yazame daga kanta gashinta suka wani bayyana ta tsaya chak batare data juyoba sai tahau kame kame.  Ummm Ma& Mamie tace nazo na gyara dakin su Areef sun bata bansan kana ciki ba sorry yakai kusan 5secs yana kallon bayanta which is so unlike him dan babu wata mace dayake tsayawa ya kalla arayuwanshi banda Mamin sa sannan yasaki gyalenta yatashi daga gadon ahankali yasauka yadan gyara riganshi ya saukar kasa da kyau, yasaka slippers dinshi dake wajen sannan yazo yawuce ta gefenta yafita tabi bayansa da kallo har saida yafita tawani duka tana dafa kirjinta, wat is wrong with her? Takai kusan 5mins aduke awajen sannan ta mike tsaye tawuce wajen gadon danta gyara sannan tayi shara wayanshi tagani agadon iPhone XR yar karama size na wayan, ko ita 11 pro max take amfani dashi, gently tadauki wayan, wayan kamshi, samin kanta tayi da zama abakin gadon Mamie takai wayan ahankali zuwa hancinta tana shinshinawa wayan smells exactly like him, ijiyan zuciya ta sauke wayan smells exactly like him is so calmling, vibrating wayan yayi hakan yasa da sauri ta sauko da wayan ta kalli screen din taga whatsapp message ne from number da babu suna.  Please talk to me Hamadi saikuma wayan yasake vibrating another message na shigowa from same number  I am madly in love with you Hussain! Aneesah ce! Hakanan wani abu Asmeey taji a wuyanta why did she even carry the phone? Maisa wayanshi ba key? Maisa notification nashi aren t hidden? Vibration wayan yasake vibrating another message ya shigo  I was able to trace your house nazo ance kunzo Bauchi salla daci wuyanta yahauyi sosai tana kallon screen din kawai taga ruwa ya diga akan screen din hakan yasa da sauri takai dayan hannunta tadaura saman idanunta taji ashe kuka take daidai an bude kofan dakin dasauri ta dago kanta hada idanu sukayi da Hamad daya hade giran sama da kasa yana kallon wayansa dake hannunta da sauri ta ijiye wayan akan gado tawuce bayin Mamie da gudu ta shiga tana maida kofan tana rufewa, yadan jima tsaye awajen yana kallon kofan cus yaga hawaye kan fuskanta sannan yashigo yazo gaban gadon yadauki wayanshi yaga bata shiga wayan ba but he saw the messages shima, sake kallon bayin yayi na kusan 3secs sannan yawuce yafita yarufo kofan hakan yasa ta fito idanunta sunyi ja gadon Mamie kawai tawuce ta gyara sannan ta share dakin tass tafito da packer da broom sai sunan Aneesa ke yawo aranta kitchen ta wuce ta zubar sannan takoma daki tai sallan isha i ko ina Gwaggo take oho ita kadaice agidan su Ramla ma duk basa ta kanta toh salla ake kowa is happy wake zama adaki sai ita abincin ta dauka spoon tayi tahauci duk ranta abace yake ijiye wa tayi tadauki magungunanta dan kawai tayi bacci ta sha tarasa yanda zatayi ranta sai baci yake sai kawai taja karaman tsaki.  Aneesah sunan ma ko dadi Mtsww taja tsaki sai kawai ta kwanta har Gwaggo tashigo mutane da dama sun shigo duk taki juyowa an dauka bacci takeyi nan ko baccin bai dauketa ba sai around 12 nadare.

Wuraren biyar ta tashi daga bacci akan dadduma taga Gwaggo data tsareta da idanu tace  sannu tashi kije kiyi salla Yayyinki Aya da Aysha duk sun kirani jiya da daddare amman kinyi bacci sunmin barka da salla sunce ki kirasu gyadama Gwaggo kai tayi tawuce bayi brush tayi ta dauro alwala tafito tazo gefen Gwaggo tai dalla data idar tai azkar sannan tajuyo ta kalli Gwaggo ahankali tace  ina kwana Gwaggo washe mata baki Gwaggo tayi tace  jibi yanda kika fara kumari dana dagaki daga gaban uwarki ohh wallahi Asama bakiyi dacen uwa ba sauke kanta kasa tayi tasa hannu ta dauki wayan Gwaggo dake wajen ta mike zatai kofa Gwaggo tace  wayan ne har sai kin fita murmushi tayi tabude kofan tafice waje tafice tana dialing number Ya Aya da ringing daya taga an katse tana kira back

Wucewa tayi parking space ta boye bayan wani mota tadauki wayan kafin tai magana Ya Aya tace  Asmeeeey wani irin Asmeey taji zuciyanta yayi she missed her sister Mom ta hanata kiransu sukuma hardly calls hawaye kawai ya sauko daga idanunta da sauri tasa hannu ta share cikin muryan dake nuna tana kuka tace  na am ina kwana shiru Aya tayi saikuma softly tace  cry cry Baby wai har yanzu bakisan kinyi girma ba shiru tasakeyi batai magana ba, dan ijiyan zuciya Aya ta sauke tace  I secretly talks to Munir and nayi magana da Mom ma tasake yin shiru sannan tace  Asmeey Mom has always been like this, Mom nada zafi and she s harsh but duk tana haka sabida mu zama wani abu ne, look at me I m a nurse today ga Ya Aysha kullum kika kunna TVC news zaki ganta, kalleki is all thanks to Mom kika gama Law at 20 yanzu sauranki Law school, look at Munir 400level Medicine Mom raised amazing kids kawai dai approach nata is harsh all of us know this gyadamata kai Asmeey tayi tana kuka mara sauti, Ya Aya tace  ke da Munir should stop feeling kaman Mom hates the two of you, besides the Mom dana sani bata dukan daya wuce saurin kai mari idan tana koya ma karatu bakayi ba ko wani abu data saka highest ta daddakeka ajiki oh tana miki sama da haka? Lumshe idanu Asmeey tayi ita kadai tasan me Mom kemata muryanta nadan cracking sabida kuka tace  a a Aya tace  kingani ya isa stop crying ai yau zanzo Aysha ne bazata iya zuwa ba sai kun dawo daga kauye sabida sunje salla a Abuja tareda family mijinta zanzo yau murya chan kasa dake cracking tace  Ya Aya please take me with you idan zaki koma dan shiru tayi tace  tom nazo i will try again kaman yanda na sabayi but Mom bata bari let s see idan this time zata yarda gyadamata kai tayi ahankali Aya tace  kije ki gaida Mom today wat you did jiya was very wrong and tell her sorry kinji gyadama Aya kai tayi tace  tom ahankali Ya Aya tace  akwai wani abu dakikeson gayamin ? Girgiza kai tayi tace  a a ijiyan zuciya Aya tasauke tace  akwai plenty clothes dana saya miki zan kawo miki yau harda very very fine abayas masu kyau murmushi tayi tace  thank you Ya Aya nakira Ya Aysha? Ahankali tace  no you don t have to I will talk to her, okay Baby Sis bye take care ahankali tace  tom bye zare wayan tayi daga kunne ta kifa kanta akan kafafunta tana kuka but mara sauti batajin dadin rayuwanta at all duk ta tashi daga bacci she feels inama bata tashi ba tai tai bacci haka kawai sabida Mom saukan abu me taushi taji asaman hannayenta dake kan knees din hakan yasa ta dago kanta ahankali wani soft handky ne mai bala in taushi dake kamshi gashi so warm dasauri ta dago kanta bayanshi ta iya gani dan yawuce yana sanye da farin jallabiya ya sanya farin hula na kwankwasa kaji hadisi kamshin hanky kawai taji tasan Ya Hamad ne rike hanky tayi ahankali da hannayenta sannan ta matse takai saman fuskanta wani lumshe idanu tayi feeling super calm and warm dan sanyin asuba dukya hura hancinta kusan 1good minutes tana ahaka sannan tace mike tsaye tafara tafiya ahankali tawuce flat dinsu tabude kofa ta shiga duk yaran basa falo wucewa stairs tayi tana kallon side din Mom gabanta na faduwa tawuce falon Baba tai sallama tareda bude kofan, Baba na zaune tareda Abba duk suka bita da kallo tace  ina kwanan ku Baba da Abba Abba yace  Ya jikin kin tashi lpy  Alhamdulillah ta amsa kanta na kasa ahankali Baba yace  why did u come to this side ? Kanta na kasan tace  nazo na gaisheku ne Baba shiru yayi bai kara magana ba tamike tsaye tafice side din Ammi ta wuce tabude kofa sai alokacin taga duka yaran harda su Nana da Ramla duk suna wajen tayi wajensu Ramla tace  ke baccin lafiya kike tayi jiya murmushi tayi tace  maganin da Ya Mustapa yabani ne daidai Ammi tafito daga bedroom dinta tace  Ammi ina kwana Ammi tayi murmushi tace  Asmeey yaya jikin an tashi lpy ahankali tace  lafiya lau Nana ta kalla tabata wayan Gwaggo tace  tayani kaima Gwaggo tana maganan tamike tayi kofa suka bita da kallo tana bude koda daidai itama Mom na bude kofan side nata suka hada idanu ta ganta tana fitowa daga side din Ammi ta dauke kanta sai kawai tajuya takoma dakin tarufe kofan yanda kirjin Asmeey ke bugawa kaman zai dare.
Ahankali take tafiya tai wajen kofan ta tsaya hannuwanta na rawa takasa bude kofan handky na hannunta ta matsa sannan taji karfi da jarumta yazo mata ta daga hannu tabude kofan ahankali tareda sallama chan kasa Mom na zaune afalonta kan dogon kujera tayi crossing kafa daya kan daya ga table gefenta da sliced fruits ke kai sai wani journal haka data rike a hannu da glasses a idanunta tana dubawa ko nuna alamun da tasan mutum na wajen batayiba maida kofan Asmeey tayi tarufe ta shigo dakin tana tafiya kaman wacce akama kaciya da kyar tazo tsakiyan dakin tana facing Mom tai kneeling ta zube guiwowi akasa ko Baba dasu Abba bata musu kalan gaisuwan nan muryanta na rawa tace  good morning Mom Idan banza tai motsi Mom ma tai motsi next page ma tabude na journal din datake karantawa tadauki fork na fruits taci, zuciyan Asmeey harwani girgiza yake, bakinta na rawa tace  Mom dan Allah dan Allah kiyaf& .fe& min, Mommy I am sorry sake bude next page Mom tayi tadauki slice na grape tasaka abaki saida ta cinye tass sannan ta sauke journal din ta ijiye akan kujera tajuyo da kanta tama Asmeey wani irin kallon kaman zatazo ta kasheta har lahira komawa baya Asmeey tayi ta jingina da kujeran wajen Mom tawani kada kafa tafara huci tadaga hannunta ta bugi kirjinta dake wani tense sound tace  ni zaki gani jiya ki zubar Asmeey! ? Dasauri Asmeey ta girgiza kanta arude tace  Mo& .. hannu Mom ta daga mata hakan yasa ta hadiye magananan, Mom tace  ni uwarki dana dauki cikinki wata tara na raineki kawowa yau zaki kalla ki zubar Asma u! Ina kwana, good morning bai hadani dake jiya ba rather you went and join my enemies Mom tayi wani dariya tana karkada kafa tana kallon Asmeey tasake dukan kirji da karfin gaske tace  Asam u dangin Babanki da kikasan basa sona da akwai yanda zasuyi tundaga kan makiran tsohuwar dayake kira da uwarsa da yayinsa Abubakar da shi dayan Kawu da munafukar matarsa maman doctor da tuni sun fitar da ni, mutum daya ke sona kap dangin su itace Maman su Nana amman shine kikaje cikinsu aka rikeki ana kula da ke ana baki magani an saki cikinsu ana gulma dake, opportunity da basu samu jikin yarana na amana Aya da Aysha shine yanzu ke sun samu ajikinki, ubanki ma ya jonasu yau rana na biyu bai kulani ba baikuma shigo dakina ba hmmmm tasake murmushi tana kada kafafu tace  wallahi wallahi kome zakuyi saidai kuyi kinga gidan nan zama daram banga uban daya isa ya fitar dani ba wlh nasha karfinku gabaki daya ai ba tun yau akeso a kadani ba tun kafin ahaifeki to nasha karfinku kinganni nan nan gani nan bari, dake da su kuma karo wasu su jona jam iyyan ku baku isa kuja dani ba, na taka inda kaf dinsu babu wanda ya take ke kin sani! Kinsan the kind of people I deal with, me suke da shi? Shi Abubakar din dayake fama da kasuwancinsa na kayan hatsi dayake surviving da kyar jari yakare? Koshi dansa Mustapa da ke aikin likita surgeon? Nawane salary nashi? Cus naga shine ai abin alfaharinsu agidan abin tunkahonsu kenan, koko shi Abdullahi dayake aiki a wani NGO yana fama ana turasu kauyuka koyama yara ABCD? Ko shi Faisal dake kirari yazama lawyer yana fama har yau baitaba cin case daya ba, ko shi Hameed dake fama da bank dinsa da ake biyansa baikai 150k salary ba, koko shi Hamad din da har yau ba aiki? Sis baida shi sai abinda Yayinsa da ubansa suka tsammai? Yana saida data online tama Asmeey dake girgiza kai tana goge hawaye da hijabinta wani kallo, Mom tace  shi Kawun naki ma ba a sashi a lissafi saisa nakeba matarsa kudi nasaka su Aya suna matarsa zakka cus she s loyal to me to tell me saisa takejin dadi, me zasu nunamin? Me sukeda shi? Waye su kap dinsu? Ke I handle case na vise president I won! Da na yarda na karbi appointment na Abuja da tuni Allah kadai yasan mena zaba but bansan Babanki na nan ni ina wani waje, bar ganina haka Babanki dakikaga ina zama dashi sabida mijinane danakeso amman ubanki baida kudin dazai nunamin Asmeey, inada mazan dasuka fisa, so fara tundaga kansa da dangin nasa Billahillazi ni Salima nafi karfinsu, nasha karfinsu, kuma babu abinda wani shege ko shegiya ya isa yamin ke kin sani! Mom tayi maganan tana dukan kujeran datake kai a zaune saida yayi kara Asmeey ta manne da kujera tana kuka Mom namata wani kallo tace  the only reason dayasa bazanci ubanki da durun uwar ubanki ba sabida mijinki zaizo yau da mamarsa ne amman wlh wlh saina gwada miki ke karaman yar iska ce Asama u, zan kuma nunamiki ke yar kiyashi ce agaban Giwa, zan takeki na wuce batare danasan nayi ba, Shegiya wulakantacciya, kaskantacciya, Allah yahanaki farin ciki arayuwanki! Dasauri Asmeey ta kalleta, Mom tace  Wlh bazaki tabajin farin ciki ba har abada yar bura uba sainaci ubanki wlh jaka kawai karuwa! ?Wani irin kuka Asmeey tafashe dashi tana kallon Mom duka zagin nan da addu o in nan babu wanda Mom bata saba mata ba, she keeps saying this prayers, goge idanunta tayi gwanin ban tausayi hawaye still na zubowa tace  dan Allah kiyakuri Momy kiyafe mini kinji Mom haukacewa Mom tayi tadauki journal na gefenta tawani wurgo mata amman bai sameta ba Mom ta zabura ta mike tana dunkulle hannu tace  ke zan kasheki fa na huta Asmeey na tsaneki, na ganki jinake kaman na halakaki, karatu yau kwana nawa bakiyi ba? Kuma bazance kiyi ba ki koma wajen yan uwan ubanki zaki sha mamakin abinda zan miki wuce kifita ki shirya karfe daya mijinki zaizo gidahuma kawai jaka kasa tashi tayi sabida yanda Mom take a tsaye rarrafe tayi tawuce saida takai wajen kofa ta iya mikewa ta tashi tabude kofan tafita tana share fuskanta tawuce dakinsu Munir daya labe abayan wani kujera awajen yataso dan yaji komi cus yazo ya gaida Mom ne shima yaji magananta.
=ث?UWA KO UKUBA?=ث?



'



EPISODE 1?? 3??
KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???

JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA=?%?

GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA=?H?

CHAT ME UP DON SHIGA
wa.me/+2347012181461

EPISODE 1?? 3??




Dakinsu Asmeey ta shiga ta kwanta akan gadosu tai shiru hawaye na gangarowa daga cikin idanunta yana sauka kan pillow, ahankali tashiga fito da hannunta daga cikin hijabin taciro handky din Ya Hamad tana kallo fashewa da kuka tayi sosai ahankali tace  I am not happy, I can t remember da last time dana wayi gari yamma tayi inajin farin ciki araina tunda nai hankali I don t have this day, I just want nayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login