Showing 12001 words to 15000 words out of 233624 words

Chapter 5 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2509

yajiki?  I m not sick Hamad yafada ciki ciki, hararanshi Hameed yayi yace  kaida ke kuka jiya pretender kawai hade fuska Hamadi yayi, cikeda tsokana dan kawai yasashi yayi magana yace  ohh bakasan sanda kayi kuka ba ko wen u were having pains saiga hawaye sharrr a idanun yaron Mamie tashi daga dadduman Hamadi ya yunkura zaiyi da sauri Hameed yarikeshi yace  yakuri yakuri toh! Zauna lemme go and make coffee for you dauke kai yayi yay banza dashi Hameed yawuce yafita yasauka kasa ya shiga kitchen yasa ruwa a heater yadauko musu cups guda biyu ya zuzxuba instant coffeee ruwan na yafasa ya tsayaya yasamusu sugar da spoon yadauko yahayo sama yashigo dakin ya ijiye agabansa shima ya zauna, gently Hamad yasa hannu yadauki coffee yakai bakinshi ya kurbi kadan Hameed ma haka ahankali yace  an biyamu jiya nasama kudi a account dasauri yakalleshi hade fuska yayi sosai bana wasaba, Hameed yayi murmushi yace  ni wlh bantaba ganin mutum abaibai irinka ba Allah idan da nine bana aiki kai kana aiki I swear ATM card dinka ma dani zai dinga zama tsabagen yanda zanci kudinka kaiko u hate nabaka kudi, you hate kaci kudina why eh Hamadi? Am I not your twin? Why do you hate taking money from me ?Kaman bazaiyi magana ba saikuma murya chan kasa yace  save your money kayi aure da Zainab wani irin zaro idanu Hameed yayi, wlh, wlh Hamad baitabamai magana hakaba sai yau, dauke kai Hamad yayi kaman bashi yayi magana ba yakai tea bakinshi, Hameed yawani kwashe da dariya yace  Hamadi daman kasan ina soyayya da Zee? Duk wayan damukeyi kana pretending kaman bakasan komiba dama kasani? Iyye ikon Allah har wani so kake nayi saving kudi for aurenmu dariya Hameed yahauyi sosai yana kallon Hamad da kaman bashi yayi maganan ba coffee yake kurba abinsa kuma yaki kallonsa, dan tsagaita dariya Hameed yayi yace  jiya I don t know what got over me I almost kissed her ijiye mug na coffeee Hamad yayi kawai ya yunkura zai mike da sauri Hameed yarikeshi yace  Hamadi wai I can t gist with u, if I don t tell you wats going on in my life wazan gayamawa? Besides ma idan baka koyi all this ba how will you get married? Tayaya zaka raya sunnan ma aiki da iyalinka ? Fizge hannunshi Hamad yayi dasauri yayi hanyar kofa, Hameed ya kwashe da dariya yace  wlh matarka ba kunya zataci ba atoh banza kawai bugomai kofan Hamad yayi da karfi, habawa me Hameed zaiyi inba dariya ba abun Hamad is too much shifa Hamad ko kallon mata baya iyayi, you will never see Hamad with any friend aduniya, you will never see Hamad a inda ake maganan banza, ko abu zaiyi on google idan irin advert din banzan nan yayi popping up yahakura kenan wlh, just look at yanzu because of conversation na kiss yagudu yatafi masallaci, Wlh he s not sure Hamad yamasan yanda ake sex taraya da iyali, he remembers suna yara a fiqhu duk ranan da za ayi wani baabi na wani abun kunya he will leave the class, Allah yama Hamad kunya da jin nauyin anything raw and bad he just can t stand it, he just wants to see ranan da Hamad zaiso wata ko ranan aurenshi kai he will love to see matan Hamad da ciki cus yanaso yasan tayaya zaima matanshi ciki ko a ruwa zata sha Hamad fa ko kaya baya iya cirewa gabansa hmm, Allah ya kyauta.

Bayan sallan asuba kowa yadawo banda Hamad daya tsaya muraji a sai wajejen 9 ya shigo gidan the way yake tafiya ka kalleshi saika kara kallonshi, yana taku cike da izza da natsuwa da haiba da kuma kwarjini, farin jallabiyan jikinsa nawani irin sheki, yau Saturday ko maybe saisa yaga motocin yayyinshi agidan dan yawanci on a Saturday sukanzo suyi breakfast tareda Abba ayi catching up rannan ba aiki.
Gently yayi sallama yashiga falon dukansu suka amsa Abba ne zaune akasa kan lallausan carpet dinsu yana sanye da jallabiya da yar hula akansa ga charbi a hannunsa yana kallon Hamad din, sai Ya Mustapha dake zaune kan kujera kusada Abba, sai Ya Abdullahi shima sanye da jallabiya zaune kan 2 sitter, ya Faisal na zaune kusada shi, sai Hameed dake zaune akasa kusada Abba, ga upan atampopi da lace sunkai kusan 50, each da shaddodi anan tsakiyan dakin, ahankali yakarasa cikin falon har zuwan gaban Abba anatse yace  ina kwana Abba kanshi Abba yashafa yace  yaya karfin jikin? Kanshi akasa yace  dasauki tashi yayi yabama Ya Faisal hannu cikeda girmamawa yace  ina kwana murmushi yamai cikeda so yace  ya jikin gyadamai kai yayi yabama Ya Abdullahi shima yacemai  ya karfin jiki hannu yabama Ya Mustapha kanshi akasa yace  good morning Ya Mustapha anatse yana kallonshi yace  how are you? Wat time katashi? Ahankali yace  3 yajuya zai wuce Abba yace  dawo kazauna cikin yan uwanka ba musu yadawo ahankali yazauna kusada Ya Mustapa, Ya Abdallah yayi murmushi kawai daidai Mamie na shigowa falon duk suka gaidata Abba yace  Maman Dr zoki zauna kicirema kowa nasa inaso da safen nan Faisal ya aika da komi Bauchi Gyadamai kai tayi tace  toh Masha Allah Abba yace  Doctor tashi kadauki naka danasu Areef gyadama Abba kai yayi yatashi yadauki shaddan su yadi goma ya isheshi shida yaran yace  Allah amfana Abba .
=ث?UWA KO UKUBA?=ث?





'

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn


EPISODE 5??
Abba yace  Abdallah saikai tashi yayi yadauki 5yard yace  Allah amfana Abba Allah kara budi Abba yace  Faisal tasowa Faisal yayi yadauki 5yrd shima yace  Abba Allah saka da allhairi Abba yace  Hassan sai kai tashi yayi ahankali yadauki 5yard Abba yace  zabi another one ku baku da iyali so kala bibbiyu zan muku murmushi Hameed yayi yakara another color daya yace  nagode Abba Abba yajuya yakalli Hamad dake zaune kusada Ya Mustapa yace  saikai Hussaini tashi yayi ahankali yadaura hannunshi yadauki the first two shadda dake in line Mamie tace  iri dayane duka change color cikin calm voice nashi yace  Mami zaban mini Hameed yace  toh yaron Mamie Abba yace  ina ruwanka hararansa Mamie tayi tasa hannu ta zaba masa irin na Hameed ya karba kanshi akasa yace  Jazakallah Abba murmushi kawai Abba yayi yace  to cire mata naku Hajjaju ina Gwaggo ? Mamie tace  taje makota anyi haihuwa wai an mata takwara Abba yadanyi murmushi kawai tadauki atampa daya lace daya tace  gana Ramla tasake ciro wasu biyu tace  gana Asma u  Yusra da Amina Abba yace  to kwasan ma mazan ma Shadan su su Munir haka Mamie tacirema duk wani yara na danginsu kayan salla sai mai aikinsu Lami da yaranta Faisal yahada kayan a babban gana masgo yafita yakai mota yadawo Abba yakalli Mustapa yace  yau salla saura sati biyu ko Abdalla yace  saura 13days Abba Abba yace  okay ina ganin ana gobe salla zamu wuce Bauchin akwai abinda zanyi yakalli Abdallah yace  next week sai akai duka motoci ayi musu service ko Abdallah yace  toh Abba Abba yace  Masha Allah yataba aljihunshi yaciro 50k guda biyu yabama Hameed daya yace  gashi kudin dinki da kudin takalmin salla dasauri Mustapha yace  Abba don t worry about that zan basu please dawainiyan yayi yawa dasauri Hameed ya karbi nashi 50k yace  Ya Mustapha kudi baya yawa Abba ya girgiza kai yakalli Hamad yace  Hamad zo ga naka kin motsi yayi tausayin Abba yakeji sosai baida arziki kaman da kuma sai kashe kudi yake anatse yace  Abba kabarshi inada takalmin salla atare dukansu sukace wanne? Dan kallon Abba yayi kadan yace  Ya Mustapa bought sabon takalmi last week for me dashi zanyi amfani Abba yace  dudda haka amsa wannan nina baku nace kusaya take it kasa tashi yayi yadan kalli Ya Mustapa dayamai alamu da idanu ya amsa hakan yasa yatashi yasa hannu biyu ya amshi kudin ahankali yace  nagode Abba Abdallah yace  zansa mai dinki na yazo ya amshi kayan ya aunaku I will pay for the 2 of you Mamie tawuce aka kawo breakfast kunu ne lafiyayye da kosai Abba kuma aka dumamai tuwo cus he can t do without tuwo, ko half cup na kunnun bai iya sha ba yawuce yatafi sama kowa ya kalleshi but aka barshi gamaci Ya Mustapa yayi yawuce sama Hamad na zauna kan gadonshi yana taba laptop dinshi Ya Mustapa yashigo gently ya ijiye laptop din, Ya Mustapa yakarasa wajen yace  too much sitting is not good for you allow system dinka to rest okay, da lafiya ake komi zama yayi yaduba ciwon is looking very good magani kawai yabashi da allura sannan ahankali yace  do you need anything? Girgizamai kai yayi
Ya Mustapha yace  zamuyi tafiya next week going to family house for salla you know how you get so tell me idan kana bukatan anything for traveling din ahankali yace  bakomi gyadamai kai yayi yace  okay zanje hospital yanzu anjima i will call you sai muje tare na siya maka desktop dinka tunda na da ya lalace Dasauri ya kalli Ya Mustapha hancins a Mustapha yaja yace  dudda you will never say it out loud I know how much all this su system and desktop dinka daya lalace means to you, my tech little bro so we will get it today anyone kakeso baki yabude zaiyi magana Ya Mustapha ya harareshi yace  yimin shiru just complete project din daka fara and send it to Microsoft muga abinda Allah zaiyi, in sha Allah you will win, I also speak to wani friend dina za a nema maka aiki idan an samu any slot, idan kuma babu I think I will just enroll you kafara phd muga abinda Allah zaiyi kafin aiki yazo saikai aure dawani irin sauri Hamad ya sunnar da kanshi kasa abin saida yasa Mustapa yayi dan dariya sannan yawuce zai fita, harya taba handle gently Hamad yace  Yaya juyowa Mustapha yayi yakalleshi batare daya amsaba, sauke kanshi kasa yayi ahankali yace  thank you Yaya murmushi Mustapa yayi yajuya yabude kofan yafice, daukan laptop din yayi yasa ajikinshi yashiga site dinshi yana duba message da mutane sukamai he s into creating website, building application, prototype, software development and maintenance and so much more anything tech he just knows it, banda haka yana program daban daban a online yana karban certificate, kwanan nan nema baya iya aiki sosai sabida operation din nan, aiki kadan yayi ya ijiye laptop din akan gadon Hameed yana lumshe idanu bacci na neman kwashesa.
Shigowa dakin Hameed yayi ganin yana bacci yasa yafada bayi yayi wanka yashiga shiryawa cus one of his colleague na aure yau zasuje daurin auren tsaf ya shirya cikin wani lafiyayyen shadda ya kafa hula aka tareda fesa turare saikuma yajuyo ya kalli Hamad kafin yasa hannu yadauki turarukanshi wajen kayanshi dake nan a gyare, yarasa yaya Hamad ke selecting oil perfumes dinshi cus turarenshi smells out of this world shafawa yayi ya maida ya ijiyesu hargitse sannan yarufe wardrobe din nasu yasaka takalminshi Hermes yadauki key motarshi ya wayanshi yawuce yafito Mami ne kadai a falo tana magana da Lami dazata kasuwa tana ganinshi tace  sai ina yan samari kai ya sosa yace  colleague dina a bank ke aure yau Mamie shine zamuje mai daurin aure Mamie tace  mesa bakaje da dan Uwanka ba ? Kallon Mami yayi yace  Mamie are you seriously asking this question kema kinsan ko sama da kasa zata hade bazaije ba besides ma he s sleeping I think magungunan shi na sashi bacci Mamie tace  to adawo lafiya drive safe wucewa yayi yafice yashiga motarshi Camry ta 2010 yabar gidan.
Around zuhur ya farka yatashi zaune ahankali yana kallon dakin he hates dirt, Hameed ya bata ko ina, sauka yayi ya shiga gyara dakin ya gyara gadajen su ya kwashe kayan Hameed daya cire yasaka a laundry basket yadauki broom ya share dakin ya kwashe a Parker yazuba a leda yabari awajen yashiga bayi yadauro alwala yafito yadauki leda yawuce yasauka kasa bakowa falo yatafi mosque yay1 salla yadawo afalo yaga Mamie tana zaune tace  zokaci abinci ahankali yace  anjima .

Around 4 yadawo daga masallaci wayanshi yafara ringing, screen din yakalla ganin Ya Mustapa ne yasa yadauka Ya Mustapha yace  start coming ina hospital gyadamai kai yayi tareda katse wayan yafada bayi wanka yasakeyi batare daya bari ruwa yashiga ciwon ba sannin babu kowa yasa yafito yazo wajen kofansu yasa key sannan ya tsaya gaban wardobe nasu yana budewa yaga aikin Hameed kawai yazaro wani dark blue jean da t-shirt fari ya shirya tsaf kayan sunmai bala in kyau turare ya fesa yadauki p-cap dark blue yasa akanshi, he loves wearing p-cap sabida iska sannan yadauki wani black shade, he always put on shade idan zai fita cus idanunshi somehow makes people to be looking at him both men and women kuma he hates that, wayanshi yadauka yasa a aljihu yadauki wani key dake saman side drawer shi yasa wani easy pam yafito yana tafiya ahankali looking expensive and classy kaman wasu designers yasaka, Mamie na zaune tana sauraron wani wa azi a Sunna tv taji kamshinsa hakan yasa tadago sai kawai ta tsareshi da ido Masha Allah! Hamad is simply handsome kawai karasowa falon yayi tace  zaka fita? Gyadamata kai yayi tace  ina zaka?  wajen Doctor a asibiti gyadamai kai tayi tace  jekadauki key mota na kaje dashi girgiza mata kai yayi yace  da machine dina zani shiru Mamie tayi tace  Tom saika dawo ayi gudu ahankali gyadamata kai yayi yafice wajen lipan dake tsakar gidan fari yaje yadaga katsa yadauki tsuma ya goggoge yadade bai fita ba he hardly go out baida wajen zuwa idan yafita kawai da dalili, tass ya goge machine din dayayi kura sannan ya warware glass din yasaka ya kara gyara p-cap dinshi yahaukan machine din yayi wani irin kyau ya kunna machine din mai gadinsu yabudemai gate yafice.
Kusan 30min yabata cus saida ya tsaya yashamai sannan yakai hospital din yayi parking yaki shiga yaciro wayanshi yakira yayanshi, Mustapa na zaune yaga kiranshi kawai ya girgiza kai yatashi batare daya daga ba yadauki key yafito yaganshi yace  let s go to my car ya wurgamai key yace  drive nagaji karba yayi suka wuce shiya jasu har zuwa computer village wani shago na slot Mustapa yace  you know wat u want pick up shiru yadanyi Ya Mustapa yace  muje wucewa sukayi direct wajen wani desktop yafara zuwa na dell yana duba spec din, HP EliteOne 800, 200 G45420 All-inOne G3Touchscreen... AiO - 6th Gen....CORE 13 11. This is the perfect desktop dayake bukata for his kind of work but ganin kudin #1,600,500.00 kawai saiya wuce da sauri yana duba wasu saiya juyo yakalli yayanshi yanunamai na wani 700k yace  this Mustapa yakalla sai kawai yawuce yakalli mai shagon yanunamai na farkon yace  wannan mukeso dasauri Hamad yazo kusada shi murya chan kasa yace  Yaya the money is too much anatse Ya Mustapa yace  but this is the spec your kind of job needs, don t think about the money think about abubuwan dazakayi dasu kasan how worried I was da desktop dinka ya lalace, you are stuck a software da kake developing sabida rashin desktop, I know Abba baida karfi sosai zamu karamai burden ne bayan responsibility na kanshi da yan uwansa, look at kudin daya kashe na kayan salla dudda baida shi kaman da but bazai taba dena abun nan ba cus it s something daya saba yi batun yauba, even if it s all my salary I will use it to get this for you, kai kadaine cikinmu da har yanzu baka kama wani takamaiman aiki ba and ka kama hanya desktop ya lalace just let me do my duty daidai yaciro katinshi Hamad ya kalli katin na UBA dinshi ne which is salary account nashi maybe ma all his savings ne zaiyi using cus duka duka salary Doctor nawane, he has family ga dawainiyan su Abba, gashi ba a dade damai operation ba duk sun kashe kudi duk sai jikinshi yayi wani iri, zare kudin akayi aka bashi ATM dinshi back mai shagon ya dauko kwalin brand new desktop din yaba sales boy nashi yace  take it to their car suka bishi suka fita ana kokari sawa a both kaman ance Musty yajuyo yaga wata yar matashiya tana kokarin bude motanta tashiga amman sai kallon Hamad da hankali shi ke kan abinda ake sawa a booth yake, dan murmushi yayi da gangan yadan taba Hamad yace  Hamadi ana magana dakai look over there juyowa Hamad yayi yakalli yayanshi ya kalli inda yake nunamai cus yadauka wani abune ganin wata ke kallonshi dawani irin sauri yadauke kai yarufe booth yawuce yakoma driver seat ya zauna yajawo kofa yarufe itakuma yarinyar ta taho harda dan gudunta sai kawai tai knocking gaban motan Hamad yadago kai yakalleta dan glass din motar tinted ne bata iya ganoshi yaki bude kofan yajuya yana jiran Ya Mustapa yashigo subar wajen, ganin Hamad yaki bude kofan yasa Ya Mustapa yazagayo yabude kofan dasauri Hamad ya kalleshi, Ya Mustapa yace  ana magana dakai sauke glass

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login