Showing 27001 words to 30000 words out of 233624 words

Chapter 10 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2514

tace  nagode Baba takai bakinta tadan kurba, gently Baba yasake kai hannunshi gefen kuncinta anatse yace  tell me the truth Mamanki ne tadakeki haka ? Dasauri ta girgiza kai tace  Baba faduwa nayi dazu Mom bata dakeni ba shiru Baba yayi yana kallonta ganin haka yasa tashiga shan madaran gabanta na faduwa, saida ta shanye Baba yace  tashi kije waje wajen kitso da lalle kema amiki tashi tayi tace  toh tawuce tayi wajen kofa tafice yayi shiru sannan yadauki wayanshi yasa a kunne kai tsaye yace  meet me in my room ba a wani jimaba Mom tashigo sai kamshi take dubawa Baba yabita da kallo ranshi abace yace  Salima nina sa aka kira masu lalli har gida da masu kitso sabida ama yarana mata akan wani dalili zaki ijiye Husna adakin ki bazaki barta taje tayi ba Mom na kallonshi tace  au haka tace maka ? Ran Baba abace yace  babu abinda Husna ta gayamin rannan nan I told you kibimin yara ahankali wai shi karatun nan dole ne? Law school zata iya zuwa aduk sanda taga dama akanme zaki tasamin y a agaba? This is the last time dazan miki wannan maganan ba dole bane Husna saita gajeki ba! Ni dan kasuwa ne mesa bance Munir dole sai yazama dan kasuwa kaman ni ba? Kibar yara suyu abinda sukeso, the next time zaki takurama yar nan wlh saina dauki mummunan matankin da saiya baki mamaki! Imagine yau baki zanyi mahaifiyata da yan uwana suna hanya ke?e babba agidan nan amman bata ayyuka da abincin da zasuci kike ba, I will not say anything ku cigaba da halinki gida biyu maganin gobara kada ki komi ko yaya kikeso kiyi amman yarana kidena takura musu na gaya miki Mom na kallonshi tace  shine kakemin ihu ?  Wacece ke da baza amiki ihu ba yana maganan yawuce ya shiga bedroom dinshi ya barta nan tsaye.
=ث?UWA KO UKUBA?=ث?



'

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn


EPISODE 9??
Dakinsu ta shiga bayi tashiga tai wanka dan batai wanka ba tun safe fitowa tayi tabude sip taciro wani gown na atampa mai kyau yanada blue floweres shiryawa tsaf tayi tasaka sannan tazo gaban madubi takalli fuskanta har lokacin fuskan yayi ja sai kawai taji har kunya kunya takeji ma tafita mai ta dauka ta shafa a fuskanta sannan tazo dauki kwalli tasaka duk dan tai looking normal hakan saiya rage redness na fuskanta amman saitayi bala in kyau gashinta ta warware a wanke yake har tsakiyan bayanta gashi baki gwanin kyau batada full gashi sai tsayi but is scanty and silky combing tayi sai kawai ta dauki blue veil ta yafa tadan fesa bodyspray dinta ta tashi ta kalli madubi murmushi tayi saita fito ta sauko kasa babu kowa a falo saita fita tana tafiya ahankali zuwa wajen masu kitso Ramla dahar an gama mata kitso tace  wat happen to fuskanki? Zama tayi kan tabarma tace  faduwa nayi laaaa lallinki yayi kyau Ya Ramla tai maganan da sauri dan ta kauda maganan, takalli lallin Yusra tace  Yusri iyyeee Irin naki za a min Yusri ta washe baki Amina tace  Ya Asmeey kiyi irin kitsona dasauri tace  shiko zanyi Yusra tace  ga Mom tafito wani kalan faduwa gaban Asmeey yayi da sauri ta sauke kanta kasa Mom tashiga tahowa wajen fuskanta kaman bata taba dariya aduniya ba tana sanye dawani simple gown na Cotten irin na Egypt din nan masu manyan mayafi sai wani mashahiurin kamshi take idanunta akan Asmeey dataga tai wanka harda chanza kaya, Yusra na ganinta tayi murmushi tace  Mom saura ni ana gamama Amina za amin kitsona asamin beads Amina tace  Mommy lalle na yayi kyau dan murmushi kadan tayi tace  yayi sosai takalli Asmeey da kanta ke kada cikeda authority da isa da iko tace  ayi miki kitso only banda lalle ba Asmeey kadai ba hatta su Yusra yara da su masu lallen da masu kitson da Ramla saida suka kalli Mom, wani iri Asmeey taji cus tanason lalle duk salla Allah yasani lalli da kitso da saka sabon kaya are the measure things she looks forward too, amman saita gyadama Mom kai ahankali muryanta nadan breaking tace  tt& .toh Mom strictly Mom tace  good! You re going to law school bayan sallan nan, henna kowani iri is not allowed sake gyadama Mom kai tayi ahankali kanta akasa, Mom tajuya tawuce abinta batare data kara kallonsu ba tana tafiya kaman itace mai gidan masu lalle da kitso suka bita da kallo asace ana mamakin gadaran matan, duk yanda Asmeey taso ta daure takasa kawai saiga hawaye sharrr dasauri takai bayan hannu ta share kafin wani ya lura dan kanta na kasa, me lallen tace  menene law school Ramla? Ahankali Ramla tace  makarantan dakake zuwa kazama cikakken lawyer, da gaske ba a barin lalle mai lallen tace  amman ai yanzu lalle nan da nan yake gogewa kuma shampo na goge lalle lokacin yayi aisaita goge lallen Ramla tace  tunda Mom tace kartayi kartayi mubar maganan nidai Asmeey tai shiru zuciyanta baya mata dadi kawai kitson ma kaman kartayi but tasan Baba zaiyi magana, haka aka gama na Yusra sai akahau mata kitso shiku mai bala in kyau yan kanana ana cikin mata Kawu ya iso daga Gombe.

Tashi duka yaran sukayi bata tashi ba Ramla tace  tashi muje mu gaida su Kawu ahankali ta tashi suka wuce wajen motansu, wani magidanci na mai kama da Abba na Kano sosai tareda wata mata da yara mata, Matar tace  ana kitso ne Asmeey ba a gama ba dasauri Asmeey tace  eh Mama ta rungume  Nana da Baby tace  Nana, Babyyyy suma suka rungumeta Nana is 15, Baby kuma 12 sai sauran yaran Maza ne guda hudu, daidai nan Kawu ya gama magana da masu gadi yazo wajen yaran duka suka gaidasa idanunsa nakan Asmeey yace  meya sameki a fuska Asma u kafin tai magana Yusra tace  faduwa tayi Kawu ahankali yace  sannu bakiji wani ciwon bako gyadamai kai tayi tayi murmushi still ya tsareta da idanu dan kaman mari daidai Baba na fitowa daga flat, Mom da Ammi kuma suna zuwa daga backyard, wani kallo Mom tama Asmeey hakan yasa tajuya ahankali tawuce takoma wajen kitso, Baba yayi hugging dan uwansa cikeda farin ciki suka shiga gaisawa while masu gadi na kai kayansu side nasu, Asmeey takoma wajen kitso tazauna aka cigaba tana kallon yanda kowa ke murna, su Nana suka taho wajen basuyi lalle ba suma Ramla tace  kuje kuhuta ku chanza kaya kar lallen yabata wannan sai kuzo amuku wucewa sukayi dan chanza kayan.
Suna chanza kaya suka dawo, suna cikin kitson Munir yazo wajen kaman bacci ma yayi dan idanunsa yayi ja bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey ana mata kitso ba dudda yana ganin fuskanta yasan aikin Mom ne yazo wajen yadan harari Nana dake kallonshi yace  ni tsaran wasankine kike kallona kallon Ramla Asmeey tayi Ramla ma takalli Asmeey suka wani kwashe da dariya bakaramin dadi yaji dayaga Asmeey tayi dariya ba, Ramla tace  sannu Ya Munir itakuma Nana jibi yanda tawani sunnar dakai kaman irin Ya Mustapa asalin Babban yayanmu namata magana hararan Ya Ramla yayi yasake tamke fuska sosai shi adole babba sannan yakalli Asmeey yace  Mom is calling you yajuya abinsa, faduwa gaban Asmeey yayi sosai ta tashi da rabin gashi akitse tawuce Nana tadan saci kallon Munir da tun tana yar karama take sonshi Ramla tace  dalla kidena tsoronshi murmushi tayi tace  cikamin ido yake Ya Ramla baki Ramla tabude tace  Munir din ahhh babban magana shigowa falon sukayi ga Baba da Kawu akan carpet sunashan shayi dake kamshi sosai Baba dake kallon Asmeey tun shigowanta yace  ina zaki da gashi haka ba kallabi da sauri ta taba kan tace  Mom ke kirana yanzu na manta da kallabin wajen kitso ne gyadamata kai Baba ta wuce sama afalon Mom taga Mama, Mom na shiri da Mama sosai da Kawu but Mamie kano ne dai basu cika shiri ba dakuma Abba suma bawai fada suke ba kawai dai haka suke sunfi shiri da Ammi su, Mama dakecin samosa tace  Hajiya Salima I trust you dan Allah Asmeey ma ki sama mata gangariyan miji gaskiya dan matar manya ce yarinyar nan ga kyau ga diri dudda naga sai karewa take maybe zullumin zuwa law school ne akunyace Asmeey tadan sauke fuskanta kasa, Mom tahade fuska tace  zonan rawa hannayenta suka fara har Mama saida ta lura amman taja baki tai shiru kafin ta shiga black book din Mom, wucewa Asmeey tayi gaban Mamanta wani kallo Mom tamata tace  wuce ki daukomin kayan dana dinkama Maman ki da wanda na dinka miki dasu Nana wucewa tayi bedroom din Mom, Mama tace  ohh baki gajiya Hajiya Salima! Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah kara girma da daraja kawo kayan Asmeey tayi bakin Mama har kunne Mom nada kudi so manyan exclusive atampopi ne Mama tace  Allah dai yaja zamaninki wlh Babansu Aya shi kanshi yasan yayi dace saisa har yau har gobe kece yar gaban goshi, Aya zatazo namata godiya ko, mijinta ya fitar da zakka dubu dari biyar ta aikamin wlh murmushi Mom tayi na isa irin abin nan takeso Asmeey ta kalli Mom tace  Mom natafi ? Mom tace  yaron nan has been calling you go and talk to him kafin ki koma wani iri Asmeey taji, badaman yakira bata dagaba saiya kira Mom, wucewa tayi tafita daga dakin, dakinsu ta wuce ta zauna kan gadonsu tadauki wayan taga 5miss calls nashi, instead of takirashi back sai kawai ta kwanta ahankali kan gadon tarike wayan a hannu within 2mins bacci mai dadi ya kwasheta cus tun asuba data tashi bata koma bacci ba tana wajen Mom, kusan 1hr tana bacci sannan wayanta ya shiga ringing firgigit tabude idanu tana tashi zaune tana mamakin yanda bacci ya saceta haka, daukan wayan tayi takai kunnenta ahankali tace  hello  Wifey how are you ? Abu taji ya tokare mata wuya she hates d name sosai, da kyar tace  fine yana murmushi da tana iyaji a muryansa yace  sorry banzo ba har yau ban dawo garin ba sai yau, ya shirye shiryen salla ni da Mommy na zamuzo washegarin salla gyadamai kai tayi batace komiba cus bama tasan mezata ce ba, matse murya yayi yace  I can t wait to see you my wife Asma u wani iri jikin Asmeey yamata ta runtse idanu, Fawaz yace  kullum sainaga fuskanki a bacci, I don t know why I love you this much, me kikamin ? Kin magana tayi Fawaz yace  wai yaushe zaki dainajin kunyan mijinki eh? Relax and talk to me babu abinda yakai muryanki dadi arayuwana ? Murya chan kasa mai dari dari tace  kitso akemin zan koma akarasa dan shiru yayi he feels kaman bata sonshi but he don t care, ahankali yace  okay kije toh zan kira anjima take care dasauri ta katse wayan ta ijiye wayan akan gado tanemi another blue veil karamin veil tadaura saman kanta sannan tafito Ammi tagani tana fitowa daga dakinta kaman itama ta hauro tai salla ne ganin kanta bangare daya himm bangare daya a kwance tace  meya faru ba a gama miki kitso ba har yanzu Asmeey kowa yayi nashi kitson agidan nan? ahankali tace  Ammi bacci ne ya kwasheni a daki hararanta Ammi tayi tace  wuce ni kafin in mangareki awajen nan yarinya kaman mage wucewa tayi tafita sauka kasa Ammi biyeda ita tabude kofa tafice Baba tagani da kanshi yana bude gate murmushi yalwace a fuskanshi, motan su Abba na danno kai dan nasu ne agaba hakanan gaban Asmeey yawani fadi shigowan motan zaro idanu tayi tace  Ammi Gwaggo ta iso ? Daidai nan yaran wajen lalle harda su Ramla da Munir dake wajen dasu Nana suka kwaso da gudu suna ihun.  Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyo! Gwaggo oyoyoooo Kashe motan akayi Abba ne yafara fitowa yana sanye da manyan kaya da charbi a hannunsa atare duka yaran gidan sukai kan Abba.  Abba oyoyoooo! Abba yabude hannunshi dukan uban yaran ya rungumesu, Mamie ma tafito ta zagayo ta dayan bangaren yaran suka saki Abba ta zago ta gaban motan suka rungumeta, Ammi dahar ta wuce tajuyo takalli Asmeey dake tsaye tace  wuce muje kiyi gaisuwa hakanan kawai saitaji tabajin kunya da nauyi tadajan gyalenta gaba, tawuce wajen Mamie data tsareta da idanu, sai kawai Asmeey taji tanajin kunyan su Mamie suga fuskanta dan jawo gyalenta gaba tayi tadan tsaya gaban Mamie, Mamie dake kallonta tasaki yaran tace  Ma u kene haka zonan batai wata wata ba dan tana bala in son Mamie taje ta rungume Mamie tace  Mamiee murmushi sosai Mamie tayi tace  Asmeey Ramla ma tazo aguje dasu Nana suka rungume Mamie, Baba yabudema Gwaggo mota yakamota tafito dan kafafun sunyi tsami tace  Muhammadu Sani wai Bauchin nan kullum kara nisa yake
Ne? Yaran najin muryan Gwaggo duk suka arto, Gwaggo Gwaggo sun kusa kada Gwaggo, Baba yamusu tsawa.  wai bazaku bi Gwaggo ahankali ba saukowa kowa yayi su Ya Mustapa da matayensu duk sai gaisawa ake, Mom da Mama suka fito atare sai gaishe gaishe ake everyone looks so happy har lokacin Asmeey na tsaye kusada Mamie, Baba yashiga bin ko ina da kallo
Abba dake lura da shi yace  me kake nema Muhammad Baba dake kalle kalle yace  Yaya naga tundaga kan Mustapha har Hassan nagani amman banga Hussaini ba, ina Hamadi ? Kawu yace  ai wannan ka sanshi girgixakai kawai Abba yayi yace  yana mota anatse Baba yawuce wajen motan kai tsaye yabude kofan gaba yace  Hussaini har yanzu dai halin nan na nan to sauko, fito kowa na compound din juyowa yayi jin maganan da Baba yayi, ahankali Asmeey dake tsaye kusada Mamie gaban motan da Baba yabude tajuyo daidai Hamad na fitowa daga motan kanshi akasa cike da bala in natsuwa sai kawai gently akuma natse yaduka ahankali gaban Baba yace  ina yini Baba! Dawani irin sauri Baba yataroshi yace  tashi tashi Son ya gajiyan hanya yakuma karfin jiki? Aikin ya warke ko ? Gyadama Baba kai yayi still kanshi na ahaka yace  Kawu ina wuni Kawu na murmushi yace  Hamadi lpy lau ya karfin jiki Allah dai ya karamana lafiya gabaki daya dan shafa kanshi yayi kadan saikuma yatako kadan zuwa dan nesa da Mom dake tsaye tareda Ammi da Mama sai kawai ya duka yace  Mommy ina yininku bayabo ba fallasa Mom tace  barka da zuwa Hamad Ammi tace  tashi tashi kaida bakada lpy mike mikewa tsaye yayi sai yadan waiga, Gwaggo dake kallonshi tace  yanzu zai nemi Maman shi aiko aka kwashe da dariya harda Mamie sai kawai ya sauke kanshi akunyace, Baba yace  kumuje kumuje bismillah
Yaran suka shiga gaida yayyinsu, Asmeey takalli Hameed tace  ina yini Yaya?  Wat happen to your face? Juyowa Mom tayi ta kalli Hameed sannan ta kadakai tai wucewarta Asmeey tace  faduwa nayi dan hararanta yayi tasauke kai dasauri tajuya zata gaida Ya Hamad yawuce abinshi ko kallon inda take baiyiba instead of yaje flat dinsu Baba sai kawai yawuce flat din dinsu m Ya Mustapa ya kalleshi saikuma ya kyaleshi, dan satan kallonshi Asmeey tayi Ramla taja hannunta tace  muje ciki suka wuce flat nasu.
Duk zama akayi Baba yakalli kowa na falon ganin babu Hamad yasa yace  ina Hamad ? Ya Faisal yace  yawuce chan side din hada ido Asmeey tayi da Mom data 3!5ض?5???5ض?5??? wani mugun kallo mikewa tayi da sauri zata fice Baba yace  ina zaki? Ahankali tace  zanje akarasamin kitso ne Baba yace  je flat din Abban ku ki kiramin Yayanki Hamad kafin kije wajen kitson gyadama Baba kai tayi tajuya tawuce hakanan taji gabanta ya fadi, duk babban salla anan Bauchi sukeyi every year tana ganinshi sau daya tun tana yarinya amman shi kadai ne cikin yayyinta magana bai taba hadata dashi ba, shine ma wanda ba a ganinshi, shi kowa ne bayama magana, kullum yana daki saidai ranan da za a kauye, hartakai gaban flat dinsu gabanta faduwa yake hannu tasa tabude kofan falon babu kowa ciki banda akwati nan su dake nan falon da masu gadi suka kawo.
Gently tace  Assalamu Alaykum but shiru sai eco na muryanta da flat din yadauka staircase tafara hawa tana wucewa sama daidai nan falon sama ta tsaya ahankali tace  Ya Hamad! Shiruu kaman babu kowa a side din, dan tafiya tayi zuwa gaban first room dakenan falon saman ahankali tace  Ya Hamad! Jin shiru yasa ta wuce second door din saitadan taba tareda knocking tace  Ya Hamad!
Shiru babu amsa hakan yasa tace kodai ba nan ya shigo ba wani flat yaje ko boys quarters, maybe tafita taje boy quarters taduba tana tunanin ta juyo Ya Hamad tagani tsaye abayanta awajen mummunan faduwa gabanta yayi sosai har tana neman kurma ihu tahana kanta da kyar ta daura hannuwanta duka biyun akan kirjinta ta saman gyale tana wani kalan mummunan numfashi sabida tsorata datayi ta jingina da bangon wajen da sauri tana numfashi sosai kaman kirjinta zai fita tana kallonshi fuskanshi da ruwa gashin giranshi yawani kwanta sabida lema, dogayen gashin idanunsa sun tattare sabida ruwa pink lips dinshi sunyi wani pink

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login