Showing 75001 words to 78000 words out of 233624 words

Chapter 26 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2548

zai dauki yarta ya aurar batare daya shawarce ta ba? Bamata sani ba, did Baban Aya have any idea who she is kuwa? Barrister Salima AKA Mrs Saraki! Ita zai mara! This is an insult to her profession! Her dignity! Her worth! Shaking tafara tadaga waya, Yayanta ta shiga kira kusan 3miss calls ta mishi ana hudu ya dauka cikin kumfan zuciya tace  Yaya kaga abinda Baban su Aya yamini ya aurar mini da yarinya batare dana sani ba ?  Hakan shine daidai, niko ya kirani cikin mutunci da girmamawa kuma nazo har gidan nan har masallaci na shaida daurin auren Asmeey kuma nasa albarka, remember rannan danazo miki fada kin tuna amsoshin da kika bani? Salima kin dauka duk zafinki da fadin ranki da girman kai da sauransu kinfi karfin Allah ne? Kin dauka u own ur kids? Forget mu uba bamu cika zama da yaranmu ba sabida zuwa kasuwa da fita aiki but we own our children, mahaifi ba abin wasa bane, but ke gani kike kaman kece mai yaranki ke kadai, just take this as Allah ne ke sakama yarinyarki, zaluntarta dakike yayi yawa Allah ya dauketa yacireta daga hannunki muryan Mom nawani irin shaking ganin ita kawai Baban su Aya ya maida mara daraja, kaskantacciya, sannan yaranta da yan uwanta duka sun munafunceta tace  Yaya so yanzu kasani, ka yarda that jobless boy mara abinyi ya auri y ata? Ka bari mahaifinta ya aura mata shi? Alhaji Mahmood yace  sanda kika auri naki mijin he was jobless too da yar secondary school dinsa but mun hanaki? Mun kirasa jobless? Look at him today he s among the few best businessmen we have here a Bauchi, that Hamad is better than mijinki asanda kikai aure, shi at least yanada kwali har masters garesa, kuma yana aiki so many abubuwa na online, gashi hafizin Al Qur ani, ga ilimi ga natsuwa, so don t be suprise idan yara kalansu becomes president tommorow Salima! Dan hakin daka raina shiyafi tsole idanu muryan Mom na shaking but ta hana kanta kuka cus she s a strong woman, and Baba is too small to hurt her saidai ita tai hurting wannan mara ilimin tace  Yaya hardakai aka yaudareni yanzu? This is unbelievable cikin zafi Alhaji Mahmood yace  kika yaudari kanki dai and lemme tell you this as a brother tun wuri ki maidama mutanen nan gidansu, zunubanki da hakkin kanki are way too much that you ve already started paying for them ina gujemiki ki kara dana gado, dan haka return that gidan gado to them yadanyi shiru saikuma yace  Salimah dadan takaici yakira sunanta saikuma ahankali yace  Salima wat is wrong with you? Open your eyes mana and look at mutumin dakikema all this rashin mutunci? Muhammadu Sani ne fa? Mutumin nan supported you all through career naki, he sponsored your education, wace kasa ne bawan Allah nan bai kaikiba? He loved you regardless of yanda bakison yan uwansa da basu miki komiba, saisa ya karo miki aure, I don t want to see you kin rasa komi, ni kadai kikeda shi we are orphans bamuda Mama ba Baba kar zuciyan nan naki da girman kai yakaiki kirasa komi miji da yaranki please Salima kinji, me kikeso ne haka? Shaidan sai kada miki ganga yake yana taka rawa, Salimah Alhaji Mahmood yayi maganan cikeda lallashi yace  Salimeme yakirata da sunan tsokana, ijiyan zuciya Mom ta sauke tace  all this things dakake gayamin daga baya kenan, tunda har za a kiraka a sanar dakai batun aure u will not call me and tell me ina sister ka and katako kazo gidan nan ayi komi agabanka you didn t give me hint yanzu kazo kanamin Salameme kaman kana sona, Yaya do you know how painful it is a aurar da yarka kana mahaifiyanta baka sani ba? I m highly disappointed in you Yaya ka nunamin waye naka, I am not your sister kaje ka nemi wata zata zare wayan daga kunnenta Alhaji Mahmood yace  Salima wai kin dauka tsoronki koko shakkan ki akeji? Dakatawa Mom tayi bata katse wayan ba Alhaji Mahmood yace  sabida kowa na miki shiru shiru ana kyaleki kina yanda kikaga
dama baya nufin ana tsoronki and lemme tell you this, yes ban fadamiki ba sabida ni kaina I was happy inaso Asmeey tafita daga hannunki, tayaya zaki hada yarinya da wannan yaron Fawaz waye baisansa anan Bauchi ba? Wlh wlh da ko Babansu ya yarda ya aurama Fawaz ita ni saina hanasa wat nonsense is something wrong with you sabida kinga ina lallabaki? Me Asma u tamiki dazaki iya hadata da kasurgumin dan iska suje wani wuri? Salima yarda kika haifa fa da cikinki kin tsana konine saina aurar da diyar for peace kuma kice ba a 0sa a gwada miki kinyi ba daidaiba, this is the problem of girman kai yafara shiga brain dinka, you feel kinfi karfin amiki fada, yaron nan saida ya karya Asma u he almost raped her Allah ya takaita but still he traumatized that poor girl akan me mahaifinta bazai aurar da itaba? Gwara daya hadata da cousin dinta so just shut up ki dauki takardun gidansu ki kaimusu inba hakaba nan gaba idan karma ya cimmiki don t come running to me for help you are 47 not 27, ke ba yarinya bace go and ask mijinki for forgiveness ki basa gidansa ku shirya, he still loves you tunda saki daya yamiki da nine da uku zan danna miki Alhaji Mhamood yakatse wayan Mom takara kamawa da wuta wani zuciya na ingizata taje tama Baba rashin mutunci tama koresa ya tattara matarsa da yaransa subar gidan but kuma she feels bazata iya zaman gidan just she kaman mayya ba kuma tasan tana koransa abin zaimai ciwo dan gidan nan means alot to Baba but kuna yanada wasu gidan da zai maidasu abinda taketa contemplating kenan.
Ta zauna tai shiru tana saka da warwara sai kawai ta daga waya number Asmeey tai dialing amman baya shiga ta ijiye wayan tanajin wani takunkumin bak1n ciki awuyanta data rasa yanda zatai dashi tana kara cewa  ni Babansu Aya zai aurar da Asmeey batare daya sanar dani ba .

WAYYOOO MOM BABA YA KYAUTA DA MARIN NAN?
=ث?UWA KO UKUBA?=ث?




'


EPISODE 2?? 6??

Tundaga gidan nan kuka Asmeey take akirjin Hamad har suka shiga hanya kuka take, she's crying about many things tsinuwowin da Mom tamata, sakin Mom dataji Baba yayi, marin Mom dataga Baba yayi, she's blaming kanta for everything cus tasan sabida itane komi yafaru, her biggest fear shine Mamanta da Babanta basa tare, she wants both her parents together, Babanta slapped her Mom all because of her, fitowa tayi daga jikinshi takoma gefe daya tanaji kaman an ijiye mata dutse a kirji, hatta Mamie bata mata magana ba cus kowa yasan she needed to cry this cry sabida taji dadi, aiko tayi harta gaji chan ta dago kanta tana share fuskanta tana kallon hanya tai lamo a kujera ijiyan zuciya kawai take saukewa, ko 3min batayi ba wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, Mamie tadan leko daga gaba jintai shiru tace
"Alhamdulillah tasami bacci" takalli Hamad da kansa ke kasa baka gane wani state yake ciki sai batace komiba tamaida kanta gaba, Faisal bini bini yana kallosu ta mirror, cikin bacci Asmeey tawani kwanto tashi daya kanta yayi resting akan shoulder sa dasauri yajuyo yadan kalleta sai yadauke kai da sauri kunya tawani irin kamashi sabida Mamie da Ya Faisal dake gaban motan, dan satan kallon Asmeey yayi she's deeply asleep hawaye duk sun bushe a fuskanta, sai ijiyan zuciya take saukewa na kuka, lips dinta sunyi so pinkish tana kamshi that's simple mai dadi tana sauke ijiyan zuciya na wayanda sukai kuka sosai, taba Mamie Ya Faisal yayi asace irin ta kalli baya tagani, Mamie ta kallesa da baki yamata alamu ta kallesu ganin bata gane meyake cewa ba, dakuwa Mamie tamai da hannu alamun kaci mai garinku, turo baki Ya Faisal yayi ganin Mamie batada wassup da Hameed ne da yanzu sun sami chapter, Mamie tabude littafin azkar nata tana dubawa abinta shikuma Ya Faisal bini bini yana satan kallonsu, Asmeey is resting her head sosai on his shoulder peacefully tana bacci shikuma Hamad kansa akasa but bai tureta ba abin ya kashesa da mamaki haka dazu data rungumesa bai cireta ba Hamad yasoma zama shege fa Faisal yafadi aransa.
Almost 1:30mins tayi ahaka tana bacci sannan chan tabude idanunta ganinta kusa da mutum yasa tashiga dago kanta ahankali ganin kanta na shoulder Ya Hamad dasauri ta tashi akunyace batare data kalleshi ba kawai taji kanta na juyawa yamata nauyi saita rike cikinta dataji yana juyawa zuciyanta na tashi sosai, ahankali takalli Ya Hamad, gently Ya Hamad yakalleta ya zuba mata mayun idanunsa kaman yana karantan ta, wani irin raurau tamai da idanunta kaman wata yar karaman yarinya tarike cikinta da hannu daya tana shafa wuyanta tana wani iri da fuska da jajayen idanunta dasuka ci kuka, anatse Hamad yace
"park the car Ya Faisal" dasauri Faisal da Mamie suka juyo Mamie tace "Asmeey kin tashi yaya? Meke miki ciwo"? Kasa magana tayi sai kakarin amai data shigayi daidai Ya Faisal na parking a gefen hanya da sauri tabude kofa tana fita sai amai kaman jira yake. Mamie tafito da sauri daga motan Hamad yasa hannu yadauki bottle water yafito shima, Ya Faisal ma yafito, Mamie ko kyama batajiba ta tsaya kusada ita tana buga mata baya tace "sannu Asmeey, sannu kinji, bani gyalen karya shiga amai" Mamie ta sa hannu tacire gyalenta dake kokarin shiga cikin aman ta maida mota daidai sauran motocin yan gidansu na parking, fitowa Abba bai bari kowa yafito ba kafin adauka hatsari ne motocin hanya su fara parking ataru Ya Mustapa biye da shi duk suka kalli Asmeey dake amai gwanin ban tausayi yace "meya sameta"?
Mamie tace "I think bata taba tafiya ba saisa cikinta ke juyawa zuciyanta na tashi" Abba yakalli Mustapa yace "akwai dabino a motanka Mustapa"? Dasauri yace "I don't know lemme check" yawuce, Mamie tace "bani ruwan Hamad" bata ruwan Hamadi dake kallon Asmeey yayi ahankali bayan ya bude, Mamie ta zuba mata tana kuskure bakinta sai Mamie ta debi ruwan da kanta ta wanke mata fuska dashi, daidai Ya Mustapa na dawowa wajen yace "Mamie ciremata dan kwalin kisa mata ruwa akai, Gwaggo na hayaniya zata fito Hameed yasa lock" Abba yace "gwara haka" hannu Mamie tasa tazare mata dan kwalin gashinta yawani bayyana da kitsonta mai kyau kananu, Faisal yajuya yakoma mota sabida kawai yaji yana kunyan ya kalleta yanzu kaman da dudda kanwarsu ce, but yanzu tadawo matan aure, shikuma Ya Mustapa ya tsaya awajen abinsa danshi baitaba kallon kannensa otherwise ba, he looks su Asmeey kaman yaran cikinsa ma da yayi aure da wuri daya haifi kamanta, dagota Mamie tayi batada karfi tace "sannu" Ya Mustapa yace "meke miki ciwo yanzu"? Girgixamai kai tayi idanunta na tattaro da hawaye, Abba yace
"koma mota ku sauke glass kasa muka sami dabino gaba saita ci ko 7up" ahankali Mamie tasata abayan motan, Hamad yazagayo ya shigo Mamie ta shiga gaba, Ya Faisal yatada motan, duksai taji ta galabaita zazzabi yawani rufeta, tadan matso inda Ya Hamad yake saita kwanto tasaka kanta ta dayan side din ta daura kanta saman hannayenta ta lumshe idanu tana sauke ijiyan zuciya ahankali, kanta juyawa yake sosai still kwanciyan datayi saitaji kaman abin na karuwa cikinta na kara huntsunewa, tashi tasakeyi zaune ta kalli ahankali Ya Hamad hada ido sukayi dan he has been looking at her tunda suka dawo mota, kawai sai tasakemai raurau da idanu bamatasan meke damunta ba, she's not just feeling good physically and emotionally, rasa yanda zatayi da rayuwanta da inda zatasa kanta taji dadi ga tashin zuciya sai kawai ta matso kusada shi kaman yar baby tana sauke idanunta kasa cus takasa jure kallon dayake mata but she just wanna to come closer to him, murya chan kasa ta yanda babu wanda ya isa yajishi cikin motan nan sai ita, bazama ka gane he's talking ba
Hamad yace "meke miki ciwo"? He spoke to her with so much affection and care dawata kalan tattausan gentle murya da bamata san menene ya sameta ba kawai saita fashemai da kuka mara kara batare data kalleshi ba hawaye na saukowa daga idanunta cikin muryan maraita da tausayi tace "everything" tai maganan tana sake goge hawaye abin gwanin ban tausayi, murya ciki ciki Ya Hamadi yace "rest your head on my shoulder" gently Asmeey tadago idanunta rinannu dasuka cika da hawaye ta kallesa hada ido sukayi sai kawai taji takasamai musu tana wani irin numfashin kuka lips dinta na rawa kaman wacce Ya Hamad kadai takedashi yanzu ahankali kaman mai tsoro tadaura kanta on his shoulder tayi lamooo tana sauke ijiyan zuciya tareda lumshe idanu hawaye na gangarowa daga idanunta tana wani kalan kuka mai sosa rai abin duniya yamata yawa Ya Hamad felt wani iri tabasa tausayi, hannunsa yamika kaman munafuki batare da kowa har ita Asmeey ta lura ba yadauki gyalenta dake gefensu kawai yadaura kan cinyanta inda hannunta suke ya lullube da gyalen, bude idanunta Asmeey tayi jin ya rufamata gyale a cinya da hannu, sai kawai Hamadi yatura hannunsa karkashin gyalen dasauri Asmeey ta runtse idanunta gabanta yafadi hannunta taji yakama awani irin hankali kaman wanda bai saba yiba ko yake tsoronyi yasa a tsakiyan nasa yarike hannunta calmly, faduwa gabanta Asmeey yayi sosai tanajin wani shocking, hannunshi nada girma dan hannunta cikin nasa feels kaman yarike yar baby but hannunshi is soft but ba kaman hannun mace ba, he held hannun so tight kaman za'a rabasu while fuskanshi na kallon glass yana kallon hanya kaman baya wani abu, wlh yanda yarike mata hannu gently and warmly saitaji kaman birkicewan da cikinta yayi da tashin zuciyan da rashin natsuwa da kwanciyan hankali ana zaremata su one by one, natsuwa nawani kalan shiganta by just holding her hand dayayi dan is not like yana mata wani abu daban, sai hannunta ya shiga zufama batasan mesaba saita kara lamooo ajikinsa babu wanda zai kallosu yadauka Hamad yarike mata hannu ta karkashin gyale ahaka bacci yafara daukanta Mamie tadan saci kallonsu ganin yanda Asmeey ta matsoshi sosai kanta na kafadansa shikuma yana kallon waje kaman baimasan tayi haka ba sai taji sun mugun burge Mamie, kawai saita dinga samusu Albarka tanama auren su addu'a dakuma Hamad yasami aiki ya kula da matarsa dakuma addu'an tsari daga dukkan mai sheri tundaga kan mahaifiyar Asmeey har suka shiga kano Asmeey bacci take kaman wacce tasha magani. Parking motan Faisal yayi, Mamie tace "Yaya dai?" Bude idanu Asmeey tayi da kyar tana dago kanta akunyace daga shoulder Ya Hamadi, Hamadi shima yasaki hannunta ahankali Asmeey tadan matsa gefe Faisal yace "Hamad zoka karbi motan dani da Ya Mustapa da Abdullahi zamuje wani waje" sauran motocin ma suka tsaya, gently Hamad yabude kofan yafice Asmeey tabisa da kallo Mamie takalli Asmeey dataga tanabin mijinta da kallo, Faisal yama Hamad wani matsiyacin kallo yadan rage murya kar Mamie tajisu yace "sai rungume, rungume kukemana a mota ko"? Sunnar dakai Hamad yayi yawuce yashiga gaba Faisal yayi dariya yawuce suka shiga 3rd car, while Hameed na jan dayan motan da mata da Abba dake gaba sukai inda zasu, su Hamad suka cigaba da journey zuwa gida.
Kano Asmeey keta kallo ta glass na window dataga yamata daban da Bauchi, dama haka kanon yake?
Saikuma maganganun Mom duk suka shiga dawo mata suna mata yawo a kunne, hawaye yazubo mata tadauki gyalenta ta share fuskanta tana yafa gyalen, dan barin Ya Hamad bayannan saitaji kawai she's very very sad, sai taji kaman yadawo bayan, ahaka har sukakai anguwansu zuwa gidansu horn Hamad yayi mai gadinsu yazo yabude yana murna sosai Asmeey sai kallon gidan take
Babban gidane sosai mai katon flat guda daya rak ga space sosai as well kana ganin gidan kasan na mai kudin dane but is still fine, parking akayi sai kawai taga Anty Asiya Anty Maryam da Anty Kady sunzo sun bude mata mota atare sukace "ayiririlii Oyoyooo Amaryan mu" fashewa da kuka Asmeey tayi tana boye fuska Mamie tafito kafafunta sunyi tsami zaman mota suna gaisawa da masu gadinsu da matarsa.
Sukuma sukai flat da Asmeey Asiya takawo ruwa Asmeey tayi alwala sannan suka shiga da ita ciki
Hamad sai kallonsu yake daga mota dan baifito ba har yanzu, shigowa Hameed yayi Hamad ya kallesa yadauke kai, ahankali Hameed yace "Hamad have you seen wat happened dazu?" Kin magana Hamad yayi, ahankali Hameed yace "Allah baku zaman Ipy, l'm very worried about you, zo muje muyi salla" saukowa Hamad yayi suka wuce masallaci batare daya kulashi kan maganan dayayi ba yana idar da sallan yafice kafin Abba ko Hameed su tsaresa. Mamie shigowa falon tayi tace "Asiya ku kaita dakina" wucewa da Asmeey sukayi dakin Mamie, Mamie biyeda su abaya dakinsu Hamad dayake abude ta shiga babu komi adakin anyi fentin dakin fari anyi mopping floor tun ranan auren Mustapa yasa gateman yabude ma masu aiki, akai moving kayan dakinsu zuwa dakin dake kusadana Abba, yanzu chan Hameed zai koma, bai kamata Hamad da matarsa su zauna adaki next to nasu Abba ba saisa akai maintaining first room idan ka hayo saman asalin dakinsu nada, an gyara dakin, anyi fenti, anyi mopping, dakin ya bushe, murmushi kawai Mamie tayi idan tace she's not proud of yaranta she lied cus they contributed money sukai fentin nan ragowan kudin sunje sayo gado da carpet da study table and chair na Hamad and small stuff na daki da kuma curtains masu kyau for just door and window, dakinsu ta shiga matan mai gadi da yar aikinsu ta gyara ko'ina tsaf tsaf kuma kamshin turare Asmeey suka zaunar agado Mamie tace "Masha Allah" Asiya tace "meza'a dafa Mamie" ahankali Mamie tace "kome kuka dafa, sa akawoma Asmeey akwatinta nan tayi wanka tarage kayan nan tayi amai dazu" Mamie tawuce tafita .tashiga dakin Abba dantai salla, Asmeey na wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login