Showing 33001 words to 36000 words out of 233624 words

Chapter 12 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2551

magana dasu ganin an gama lallen, bude kofa akayi aka shigo Ya Mustapa ne da sauri yaran sukai wajenshi suna gaidashi Ramla ya kalla yace  come here Ramla dasauri Ramla ta taso taje wajen kofa dayake, jakunkunan ice cream din hannunshi yabata yace  gashi ki raba muku gyadamai kai tayi dukansu sukai godiya yawuce yafita Ramla tashiga rabon ice cream din na supreme manyan robobi tanaba kowa nasa, tazo gaban Asmeey hakan yasa Asmeey tace  kibani strawberry Ramla tarike last strawberry tace  nawane shi vanilla zan baki dasauri Asmeey tace  ai kafin ki dauki strawberry nace miki ni shinakeso Ramla tace  to baza a bayar ba kallon Ramla Asmeey tayi cikin ido sai kawai ta dauke kai tace  ki hada duka ki shanye banso ran Ramla baci yayi jin abinda Asmeey tace, cikeda masifa tace  ohh kullum akaina ne kikeda bakin rashin kunya ko ? Dasauri Nana tace  Ya Ramla kiyakuri tashi zaune Asmeey tayi daga kwancen ta harari Nana tace  wayace kisa baki? Da ke akayi? Akufule Ramla tace  wai ba Baba yace kidenamin rashin kunya ba? Dani kike magana kaman kinyi da sa an ki? You re a rude stubborn girl wawiya kawai ran Asmeey yabaci jin zagin da Ramla tamata tace  ni dai ba wawiya bace hannu Ramla tasa ta dungure mata kai saida Asmeey takoma baya tsabagen yanda Ramla ta dunguruta tace  okay nine wawiyan kenan? Ki kara magana kiga wlh sai kinsha mari akan kumatun nan naki daya saba shan mari dasauri Yusra tai wajen kofa tabude tafice ganin Ya Ramla da Ya Asmeey na chachan baki akan ice cream& .
Ganin bataga su Baba ba yasa tai wajen motoci inda taga Ya Mustapa tsaye tareda Ya Hamad tai wajensu tana haki tace  Yaya ga Ya Ramla chan da Ya Asmeey suna fada a falo sabida ice cream  because of ice cream ? Ya Mustapa ya maimaita, gyadamai kai tayi tana zaro idanun gulma tace  she prefers strawberry itakuma Ramla tace vanilla zata bata tace bataso shine Ya Ramla tashiga dungure mata kai tace mata wawiya wai zata mareta akan kumatunta da suka saba shan mari Ya Mustapa yace  wuce muje binta yayi zai wuce daidai nan sai ga Mom data zagayo daga backyard tashiga flat din hakan yasa Ya Mustapa yace  ga Mom chan tafi kawai bari basai naje ba wucewa yayi yakoma inda Hamad yake tsaye dan shi baiyi motsi ba daman.
Mom na shiga dakin tagansu suna chachan baki hade giran sama da kasa tayi yaran kowa yayi tsit kaman anga dodanniya gaban kowa na faduwa harda ita Ramlan ganin Mom, maida kofan Mom tayi tarufe takaraso falon yaran kowa na komawa baya, Ramla ta kalla strictly tace  what is going on here ? Ice cream na hannunta Ramla ta nuna mata tace  Mom Ya Mustapah ne yazo yabani ice cream yace narabamana, kingani nabama koya shine nazo naba Asmeey this Vanillah agaban kowa agaban yaran nan tahaumin rashin kunya harda cemin wawiya wai kawai dan ban bata strawberry b& &  Kafin takarasa maganan Asmesy ta tari numfashinta muryanta na rawa tace  wlh Mom karya takemin itane tafara cemin wawiy& & .. tassssssss! Mom ta dauke Asmeey da lafiyayyen mari da saida ta ijiye kafafunta na lallen kunshi akasa saman tiles hands nata suka kwalbe ajikin chair, ita kanta Ramla saida kirjinta yabuga bata taba kawowa Mom zata daki Asmeey over this silly ice cream issue ba, idanun Asmeey harwani baki sukayi gashi a left side Mom tamata marin inda tamata dazu da safe, Mom namata wani mugun kallo cikin kakkusan murya tace  is this tarbiyan dana baki? Are you stupid kike kiran yayarki dake gaba dake makaryaciya! Are you stupid Asmeey! Mom ta daka mata tsawa da saida falon ya amsa idanun Asmeey sukai jaaa ga duka kannenta awajen, she felt embarrassed, baki tabude zatai magana amman kuka yasa ta kasa magana cus tana bude baki zata fashe da kuka ga kanninta awajen, Mom dake huci sosai tana kallonta tace  okay I m talking to you kin sauke kanki kasa ni ga shashasha eh? Dago kanta tayi ta kalli Mom sai kawai jikinta yahau rawa ganin idanun Mom tace  so& .s& &  saikuma sorry yakasa fitowa sabida kuka, ran Mom yayi masifar baci tawani fizgo gaban rigan Asmeey haka yarinyar ta taso fuuuu kafafuwanta sukai daba daba akasa skirt nata ya sauka kan black lallin Ramla naso tabata hakuri cus she s regretting telling Mom amman tsoro take ahada da ita, Mom tashiga daga murya tana jijjiga Asmeey yace  don t you know how to apologize Asmeey ko saina daddakaki zaki bada hakuri rawa bakinta yashiga yi idanunta sunyi fiki fiki sun kankance daidai lokacin Gwaggo tabude falon ta shigo tundaga lallin da taga ya kwalbe akasa ta shiga kallo da yanda Mom tarike yarinyar tana kallon yanda hannayen Asmeey da jikinta ke kyarma kawai Gwaggo ta kurma mahaukacin ihu tana bude kofa da saida gidan kap ya amsa.  Ihuuuuuuuu zatai kisan kai jama a ataimaka zatai kissan kai! Tundaga su Mamie da Ammi dake backyard dasu Ya Mustapa da Hamad dasu Baba dake masallaci harda Ustaz da su Ya Hameed saida aka fito da gudu ana yowa flat din jin ihun Gwaggo, Mom ta dauke kai daga kallon Gwaggo dake ihu babu ko dar a zuciyanta ta shake wuyan rigan Asmeey dake kyarma tace  I said apologize now! Ta daka mata tsawa ahankali cikin muryan ban tausayi jikinta na rawa sosai tace  so& .so& sorry  Sorry Wa ne ? Mom ta sake dauketa da mari a same kumatu for the second time mercilessly, Gwaggo tai ihu ta taho tana ture Mom tace  wai ke yarnan bataki bace ko yar riko ce? Mom dako gezau batayi ba da tureta da Gwaggo keyi tana rike da Asmeey tace  speak! Bakinta na wani kalan rawa tace  so& & sorry Ya Ramla daidai lokacin su Ya Mustapa na shigowa falon Ya Hamad biyeda shi, awani kalan zuciye Mom ta hankada Asmeey saitin center table dake tsakiyan falon da mugun karfi sai kasa tamugun buge da center table din a gefen cikinta daidai kan idon Baba dasu Mama da kowa hadda matan su Ya Mustapa, Mom tajuya fuuuu tawuce stairs Baba kawai yayi mutuwan tsaye yakasa magana ganin yanda Mom ta buga yarsa da center table mugun buguwa ma, Gwaggo ganin yanda yarta sandarewa tayi ta kankame awajen cike da mamaki kowa na falon was freeze har ita Mama yar fadan Mom,
Mamie ce ta iya motsi cikin kowa takarasa tsakiyan dakin ta duka tasa hannu ta dago Asmeey data kasa motsi idanunta har lokacin duhu duhun mari suke mata, ahankali Mamie tace  Ma u sannu tashi, kinji ciwo ? Jikinta na wani irin kyarma totally destabilize ga lallen da aka mata ya dame duka har center table yabaci shima da lallin da sauri ta girgizama Mamie kai har lokacin bata gani da kyau ga kunya yagama kasheta ga jikinta rawa kawai yake, tajuyo tana kokarin neman Mom dabata gani a falon ba kowa na kallonta, ahankali Mamie tace  Doctor zoka dubata dasauri Asmeey ta kalli Mamie jikinta na rawa yana kyarma amman takakalo murmushi muryanta ciki ciki yayi rauni tace  babu abinda kemin ciwo ai ban buge ba dasauri Yusra tace  duk Ya Ramla taja Mom ta daketa and she lied cus Ya Hamad ai bata cemiki wawuya ba kene kika kirata wawiya because of ice cream ran Ammi taji yabaci tashigo tsakar falon tace  are you the reason aka daketa haka? Ramla do you even love your sister? Kalli kumatunta, kalli lallinta, kalli yanda jikinta ke bari, bakida imani ne Ramla ke ba mai marba Asmeey ice cream bane bakene babba ba? Wace kalan muguwa ce ke ? Tadaga hannu zata daketa Abba yace  dakata! Karki daketa!Yarane ba a raba yara da irin kananun fada haka musamman wajen rabo amata afuwa, Husna da sauri Asmeey ta kalli Abba idanunta sunyi firfirr ba hawaye tace  uhmmm na am Abba magana Abba zaiyi but sai yayi shiruuu ganin yanayin yarinyar yace  kaita ta wanke hannayenta da kafafun Maman Doctor, Nana ku gyara inda yabaci da lallen yunkurin dagata Mamie tayi tace  tashi muje Asmeey takasa tashi bakinta zaiyi magana sai kawai ta kasa sai hawaye yataru a idanunta ta juyar da fuskanta irin na neman inda zata saka kanta dinnan Mamie ahankali tace  zo Asmeey come Mamie zata kamata Asmeey zata fita daga jikinta takasa da sauri ta shige jikin Mamie duk yanda takeso ta daure ta danne takasa tafashe da kuka sosai jikin Mamie mara kara sai shesheka da jikinta dake motsi irin kukan nan mai taba zuciya tana huci mai bala in zafi a jikin Mamie, Baba ya yunkura zai wuce sama Abba yarikemai hannu alamun no dan yaga yanda Baba ya zuciya kuma babu kyau hukunci acikin fushi hakan yasa ya tsaya, Munir yawuce ahankali wajen ya tsugunna kusa da Mamie da Asmeey ke jikinta yadaga hannunsa yadaura saman bayan Asmeey yayi shiruu idanunsa sunyi jazur, ahankali Hamad yajuya yafice daga falon yarufo kofa, Gwaggo da sai alokacin tadawo daidai tace  toh wlh wlh tunda dai abinda akema yarnan agidan nan kenan zan tattarata natafi da ita, kuma dagayau tabar shashin nan, idan uwarta ta isa tazo inda nake ta tabata, bantaba ganin muguwa Uwa irin mahaifiyarta ba, wlh kekuma sarai ai kinsan halin uwarta koda tamiki laifi ai sai ki rufamata asiri ba yar uwarki bace? Kuma ai kina sane ai haushi takeji ansata tayi lalli alhalin tahana ba dole ta dirketa ba, ga lallin nan tasa yabaci hankalinta ya kwanta, Mara Imani da idanunta kaman na mutan da, saisa Allah yahanata tsayi kaman in kifeta da kwando, muguwa dunkulen magi kawia ai gajeren mutum akwai bakin hali Gwaggo na fadin haka ta karaso takama hannun Asmeey dake jikin Mamie tace  tashi muje fitoda ita daga jikinta Mamie tayi tace  tashi kuje Asmeey idanunta akasa taki kallon kowa ta kasa tashi, rai abace Baba yace  badake ake magana ba tashi ahankali ta tashi da dauriya da kyar, Gwaggo tariketa tajawota aka mammatsa suka taho Ya Mustapa yabi yanda ke tafiya da kallo dakuma gefen cikinta suka fice sai kawai Mamie itama tabisu abaya haka sauran matayen, Mama kuma tawuce sama abinta wajen Mom danta bata hakuri Ya Mustapa yajuya yafito kowa ma yafito.
Flat din su Mamie Gwaggo tashiga da ita har lokacin fada take sosai dakin dake kasa tawuce dan ita duk dakunan kasa nakowani flat nata ne cus duk inda taga dama take kwana tabude tashiga tace  wuce kije ki wanke hannunki wucewa tayi ahankali ta shiga bayin ta maida kofan tarufe takarasa wajen wash hand basin tadaga hannuwanta da akama lalle duk sun gwalje both baki da jan tai shiru sai kawai hawaye suka sauko daga idanunta tabude tap din ta wanke hannayen tasss and lallin yayi mata bala in kyau inda ta gwalje ne yayi wani iri, lallin yayi dan ja, Kuka takeso tayi but saita hana kanta gabanta har lokacin faduwa yake, Mom sai fadomata take arai bazata taba kwana anan ba sabida kar ran Mom yabaci zata bari Gwaggo tai bacci saita tafi wanke, kafafunta tayi suma tass ta dauro alwala dan batai salla ba ta kalli kumatunta da sunyi jaa sosai abunka da fara ko yaya aka mareta kalan fatar fuskanta saiya chanza towel na bayin tasa ta tsane fuskanta sannan tabude bayin tafito Mamie tagani tsaye kusa da bayin tace  alwala kikayi? Dasauri ta gyadama Mamie kai tana kakalo murmushi tace  eh banyi salla ba shizanyi yanzu Mamie na kallonta tace  babu abinda ke miki ciwo? Gyadama Mamie kai tayi Gwaggo tace  wannan ai ko zata mutu bazata fadi ba uwarsu yanda kikasan ta tsafesu ni zoki salla muje falo muci abincin dare yunwa nakeji dan takowa Mamie tayi dab da ita gently takai hannunta ta daura saman kumatunta dayayi ja tana kallon idanunta, wlh tunda Mom ta mareta koda yanzu tai alwala tasa ruwa a fuskanta bataji sanyin dataji kaman sanyin dataji yanzu da Mamie ta daura hannunta kan kuncinta ba sai jikinta yayi sanyi sai taji jikinta ta ciki yadaina radadi cikin murya mai sanyi dakuma so Mamie tace  ya isa! Calm down zanma Mamanki magana dakaina kinji, next time koma menene karkima nagaba dake rashin kunya, kinfi kowa sanin mahaifiyarki macece mai bama yaranta tarbiya yanda yakamata bata yarda danta ko yarta ya taka na gabansa ba, next time respect Ramla kinji no matter what don t talk back at her just like yanda Mom bazata bar su Yusra ko su Nana sumiki rashin kunya ba kema bazataso kima na gabanki ba, but ya isa okay gyadama Mamie kai tayi idanunta na cicciko da hawaye, ahankali Mamie takai hannunta gefen cikinta tace  wajen namiki ciwo nasa Doctor yakawo miki magani? Girgizamata kai tayi tace  a a bayayi Mamie tace  to yi salla abinki Gwaggo taja tsaki tace  wlh takara taba yarnan tagani yo ita ubanwa naga tana girmamawa? Girmamani take? Mata sai girman kai jitake tafi kowa sabida tayi boko, bokon da agidan d ana tayi kuma da kudinsa banza kai shashasha muzuba ni da ita zan nuna mata matsayinta
Mamie dai tawuce tafita Asmeey ta dauki hijabin datagani kan gadon wajen tasaka tai salla magrib da isha i ma da akayi Gwaggo da tunda tafara salla take kallonta tace  kiwa Allah Asama kitashi kicire hijabin nan muje muci abinci cikina sai kuka yake tashi tayi ta cire hijabin tawarware mayafinta tasa aka yadan sauko mata shoulder Gwaggo tai gaba ta biyota abaya su Ya Mustapa duk suna falon Ball ma suke kallo a tv falon da Ya Abdallah da Ya Faisal da matarsa ke basa abinci, shi kadaine be ciba sai Ya Hameed shima.


Hameed yakalli Asmeey fuskanshi ahade yace  kawomin ruwa hararansa Gwaggo tayi tace  bazata kawoba bakaga kalan dukan data gamaci ba tabe baki yayi yace  inda sabo ai tasaba yanzu wani mugun kallo yayyinsa sukamai, yadanyi murmushi, haushin Mom yakeji sosai aransa, he hates the woman wlh sabida yanda take da duka, da girman kai da fadinrai, haka su Ayah suka wahala a hannunta shi besan me Baba yagani ajikinta take zaman aure da irin matar nan ba, wucewa fridge Asmeey tayi a kitchen tana tafiya ahankali tasa ruwa a tray da cup tafito dashi tazo falon kanta akasa tazo gabanshi ta ijiye.  Gashi Yaya zata juya Mustapa yace  zonan faduwa gabanta yayi ta gyadamai kai tazo gabanshi babu wasa kan fuskanshi like a big brother yasa hannu a aljihunshi yaciro wayanshi ya kunna flash yanuna mata gefenshi yace  sit zama tayi ahankali Gwaggo tace  yauwa dubamin ita hannunshi yadaura saman kanta ya juyar da fuskanta yana haska kumatunta Mamie ma tafito ta tsaya kansu sannan yasauke wayan yace  inda kika buge namiki ciwo? Girgizamai kai tayi tace  a a Yaya hannunshi yakai ahankali yataba gefen cikin ta saman riga da kyau jin wajen is not hard yadan sauke ijiyan zuciya yana kallon yanda take runtse idanu she need drugs, hannunshi yacire dan murmushi yamata tareda shafa kanta yayi cikeda kauna ta dan uwa yace  it s okay okay don t fight with ur sister again, i will buy another ice cream for you gobe Abdallah yace  wani flavor kikeso nima zan siya miki Faisal yace  akan strawberry flavor tayi fada nima zan siyamata gobe Hameed yadan harareta yace  sweetthooth kawai i will also buy for you murmushi kadan tayi feeling so loved, ahankali tace  nagode Yaya Mamie tayi murmushi tana kallonta Gwaggo tace  sauko muci abincin Ya Mustapa yace  jekici abinci zan fita nakawo miki drugs tashi tayi zuwa kujeran da Gwaggo take ta zauna suka faraci tanadan jin nauyin yayyinta dan ba koda yaushe take ganinsu ba, but kuma tana sonsu sosai sunada kirki sosai and suna son kanninsu suma.

Parking yayi ahankali tareda kashe motan ya kalli paper bag dake gefen sa kan kujera yayi jimmmm sai kawai yatashi yakai hannu yadauka tareda bude kofan yafito yarufe yafara tafiya zuwa flat nasu ko kadan baisan yayyinshi kowa na falon ba hakan yasa kai tsaye yabude kofan yashigo tsayawa yayi ganin kowa harda Mamie duk a falon ga Gwaggo da Asmeey datai tsuri gefen Gwaggo ana kallon ball Baba ne kawai baya falon, duk juyowa akayi ana kallonsa banda Asmeey da tana ganin shine ya shigo ta maida fuskanta tv, ganin yanda kowa kallonshi yake yasa da sauri yaboye abun hannunshi abaya yajuya dasauri zai fita daga falon Mamie tace  Hamadi! Chak ya tsaya hakanan gaban Asmeey yafadi batare data dauke kanta daga tv ba, Mamie tace  ina zaka daga shigowan ka? Ina kaje ban ganka ba tun dazu? Come dan jimm yayi sai kawai yasa hannu ya maida kofan yarufe yahade rai kanshi akasa yafara takowa zuwa wajen Mamie Mamie tabi paper bag din da kallo tace  meka sayo? Agefenta ya ijiye paper bag din da sauri batare dayace komiba kawai yajuya kowa na falon yabishi da kallo yawuce stairs, Gwaggo tace  mara mutunci meya kawo miki banda ni? Koni ba mutum bace Mamie tasa hannu tabude paper bag din fari ba logo ajiki kawai saita dago kai takallo sama harya shige dakinsu sai kawai tasa hannu taciro ice cream a babban cup strawberry da akai breaking cone da chocolate da so many orishirishi ciki ga cokali takalli Asmeey da idanunta ke tv

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login