Showing 147001 words to 150000 words out of 233624 words

Chapter 50 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2567

introducing software din kafin asalin rannan lunch.
Tashi yayi daga kujera dauke da system dinsa ahankali yatafi gaban smart board ya kunna system nasa kowa na kallonsa gabansa nadan faduwa saiya tuna da Mamie then Asmeey then Ya Mustapa, addu a yadan karanto aransa, babu wanda yama gayamai ga yanda zaiyi connecting system dinsa to smart board din kawai yayi yadauki remote sannan ya kalli kowa na dakin da full confidence cikin harshen turencin sa mai dadi da zaki just simple layman accent yace  good morning ladies and gentlemen, I m Hussain Hamad Abubakar from Nigeria and I designed this software name it SOFT AI, so what makes this SOFT AI different from all other AI in the global market? What are its unique features? Wato shi farin jini, da ilimi dakuma baiwa duka na Allah ne, dan conference room din nan dayake dauke da mutane kusan 27 babu wanda baiji Allah ya daura masa son Hamad ba nothing like racism ko shi baki ne ina, all they see is potential na yaron da kalan kudin dazasu samu daga jikinsa and how genius the boy is, dudda he s a little bit wiredo guy but that is also a spec da sukaji they extremely love, Hamad na gama presenting CEO yamike tsaye daga kujeransa yana tafi yana kallon Hamad hakan yasa kowama yatashi yanama Hamad tafi ana kallonsa sauke kansa kasa yayi eyes dinsa na twitching kadan kadan sabida yanda ake kallonsa ana masa tafi he s not use to it, shima Barrister Kamal sai murmushi yake yanama Ya Mustapa sending video dayayi har yanda ake tafama Hamad sannan yadawo aka zauna sai next is reviewing document da agreement nan ne bangaren Barrister yafara duba komi Kamal yanama Hamad explanation, abu na farko is sunaso su daukesa yadawo permanent staff nasu, banda kudin dazasu biyasa na albashi still yanada some percentage a software daya musu developing for each user dayazo yayi amfani da abun Hamad nada 5 percent from koma mene akai generating daga user, they will take care of accommodation nasa, health insurance, access to many incentives ciki harda summer and winter vacation to country of his choice all expense paid trip, car, security, yanada two major break in a year da he can decide at any time yakeso yaje sai option na kawo any family member with kid if any, Hamdala Hamad yayi bayan Lawyer yagaya masa komi yanuna ya yarda yayi signing CEO ma yayi signing akai clapping ana raising toast dabai shaba cus is alcaholic drink.

Sannan aka kawo katon board check na kudin dayaci wato 500MillionDollars akace yazo ayi picture da kyar ya daure yaje shiya tsaya kusa da CEO da kyar aka musu picture, dudda haka saida ya karkata kai camera man yace sai an sake CEO yakalli Hamad yace  is that okay Mr Hussain? Gyadamai kai Hamadi yayi this time around da kyar da kyar ya kalli camera aka dauka shima Kamal ya dauka sannan aka dawo aka zazzauna aka shiga kawo lafiyayyen abinci ana cigaba da meeting ana mai introducing team nasa yanada secretary wata mace baturiya, yanada attendee daga gobe zai fara aiki sabida dole ayi adjusting akuma yi kare kare akan software ta yanda it will go with standard na Microsoft, so he needs to also work with chief IT tech nasu shima yazo suka gaisa da Hamad wani wired guy dashi kaman mahaukaci but guru ne like Hamad, and Hamad kinda like him sunansa Ali from Lebanese, balarabe ne but irin wayanda basa sallan nan but lokacin salla shiyakai Hamad prayer room yaje sukayi shida Kamal kafin _u dawo ayi finalizing komi agama meeting secretary takai Hamad office dinsa Ya Allah! Sai Hamad yayi shiru is this really him? Baitaba sani in his life zaiyi aiki in this kind office ba, Office nashi kaman wani AI design office sabida kyau Secretary tace  looking forward to start working with you Mr Hussain I m Mona gyadamata kai yayi yawuce kawai suka tafi elevator sukaje suka shiga mota suna fitowa Kamal yace  tom sai munyi waya natura maka pictures da video a watsapp Hamad ya gyadamai kai suka wuce, yana zaune motan yana kallon hanya wayan tasa tai kara na message yana dagawa yaga alert $500million dollars ya sauka sai yayi shiru yana kallon kudin is this kudi his yanzu? Shi? Shi Hamad din da ba komi ba? Shi Hamad da yan uwansa ke basa kudi? Aka hada kudi akamai aure? Aka sayamai machine? Aka ginamai gida? Shine mai kudin nan? Shi? He s inside car yanaso yayi sujjada ba hali but saiya kifa kansa a chair ahankali yace  Alhamdulillah! Duk wanda yayi dogaro ga Allah hakika Allah ya isar masa, baitabajin wani iri ko yacema Allah mesa bai basa aiki ba dudda yan uwnasa sub samu tare yagama school da Hameed tare sukai applying aikin banki Hameed as accountant shi as IT, cus lokacin Ya Mustapa yatura musu offer two slot din ake nema har interview sunje Hameed yaci shi baiciba baitaba feeling bad ba yasan his time will come, no matter situation dakake cikin dont feel pressure komi na hannun Allah within a blink on an eye Allah can change your life.

Gida sukakai security yamai sallama bayan yakawosa har gaban dakinsa Hamad yamai godiya yashigo kayan jikinsa yarage saiya zauna akan kujera ahankali yayi screenshot na alert din yashiga watsapp yaturama Ya Mustapa yakirasa watsapp call wayan na gabda katsewa Ya Mustapa yadauka anatse yace  Hamadi naga hotunan u look good Alhamdulillah! And u speak so well Goodjob! Ahankali Hamad yace  Yaya sun biyani I sent you the screenshot, inaso naturo maka kudin gabaki daya yanzu dan murmushi kadan Ya Mustapa yayi yace  so kake EFCC su bincike ni? Hamad yayi shiru baice komiba, ahankali Ya Mustapa yace  this is your money Hamadi! Your hard earned money hold kudinka and enjoy kudinka!
EPISODE 7?? 0??




Shiru Hamad yayi jin abinda Ya Mustapa yace kafin ahankali yace  Yayaaaa Ya Mutspa understand Hamad so well hakan yasa ahankali yace  tell me wat is ur plan akan kudin ? Dan ijiyan zuciya ya sauke ahankali yace  inaso nayi renovating gidanmu mu gyara gidan gabaki daya, sai business din Abba shima mu samai kaya mu gyaramai shago akasuwa ahankali yace  inaso kamana establishing company na dukanmu mufara business, sai inaso kasayamana fili dazamuyi kaman 5 terrace more like a mini estate kowa na flat dinsa inaso dukanmu mu zauna tare, our children should grow up together, Ya Abdullahi nakeso yayi handling harkan ginin gidanmu da renovation na gidanmu tunda he s good with those kind things da design, Yaya kai I want you to be in charge of the company dazamu bude saikaje China for survey and know wani business zamuyi, Ya Faisal nakeso yayi handling mota, I want to buy car for Abba da Mamie yadanyi shiru saikuma ahankali yace  I want to buy car for Matana, saikuma ku dan murmushi Ya Mustapa yayi jin Hamad na addressing Asmeey as matarsa wato kunya tasoma raguwa, ahankali yace  i want Mamie tahadama ni da Ya Hameed akwatin auren mu, but wedding din should be towards sanda gidanmu zai kammala, I want our house project yafara as soon as possible gobe ma idan za a samu land asaya ko Yaya ? Gyadamai kai Yaya Mustapa yayi yace  okay ahankali Hamad yace  I will buy MacBook and other things from here na aiko Yaya is for my wife zata fara rubutu dan murmushi Ya Mustapa yayi baice komiba, anatse Hamadi yace  Abba da Mamie da Matana and su Anty Asiya suje Umara sai afara aikin gidansu Abba suna Umara ko ? Ya Mustapa yace  tom Hamad yace  inaso a gyara masallacin anguwan mu, then kukai abinci and clothes gidan marayu akai ma asibiti kudi, kabama su Baba da Kawu kudi, with Munir and my other cousins Yaya kai zakayi komi, bayan su Mamie sun dawo daga Umara inaso every Friday ana abincin sadaka murmushi Ya Mustapa yayi yace  toh Hamadi he s just so proud of Hamadi kudinsa dayawa billion dubu dari bakwai duka abubuwan nan dazaiyi ba lallai sumaci up to billions ashirin ba wai that is harda kampanimsu ma, anatse yace  I will seat with Yayyinka let s make quotation na komi Hameed will be good at that shine sarkin lissafi sai musan nawane kudin yakama gyadamai kai Hamad yayi, Ya Mustapa yace  go and rest we will talk later ya katse wayan, yanada current account kawai yana office nasa yaga alert na 200 Billion Naira sai yaga kaman account dinsa na rawa ma ohh Allah kenan! Wai Hamad ne yayi kalan kudin nan dahar yana iya turo billion dari biyu ohh Allah! Message yama kanninsa yace  su zo gidansa akwai meeting bayan magrib bayan magrib duk sukazo Anty Asiya na ciki Ya Mustapa ya sanar dasu komi da kudin da Hamad yaturo dukansu suka karni wayansa suna ganin alert din sai sukahau rawa Hameed yace  wlh gobe zanyi resigning daga bank dinnan Faisal yace  nima Abdullahi yace  ni da zan fara project na gida my first official project nawa banawasu ba ai resigning yakamani murmushi kawai Musty yayi yana kallonsu yace  ku zauna let s have calculation nan suka fara, Abdullahi nada masu duba fili yakirasu gobe zasuje, Faisal nada masu saida mota Ya Hameed he knows harkan Umara yanada babban aboki agent nan da nan ya karbi kudin Umara wanda na manya zasuyi VIP 8million each, su goma harda Baba da Kawu banda matansu sabida ansan Mama na ganin Asmeey Mom kaman taji, Hameed ya karbi 80M na Umaransu ohh wai kudin Hamad ake rarrabawa haka, bawasu extra vagrant car za a saya ba, Asmeey as per wife of owner Benz suka sayamata latest mai kyau yar 15M, sai Baba bayason wata flashy car Camry aka sayamai ta 13M, Mamie ta 13M itama sai _u Hameed irin Benz din Asmeey yakeso, sauran yayyin sukasai Toyota masu kyau suma Ya Mustu shi bai sayaba mitansa is very okay Faisal ya karbi kudin motocin sis wajen 12 aka gama komi kowa went home happy.


Driver sa Hamad yakira yazo yadaukesa Apple shop yaje duk wani abu na Apple saida ya siyama Asmeey, laptop, iPad, headphones, pen, charger, case, watch dakuma waya 16pro max yabita kudin komi yafito, sai kawai yasaki kanshi da shiga wani Dior shop yasaya mata jaka da takalmi fa kayan makeup da turaruka na doir, driver yakaisa wani delivery company yatura kayan Nigeria kano to Hameed danya karba yakaimata yawuce yakoma gida.
***


Yau Asmeey tadanji sauki Alhamdulilllah, saidai tayi zuru zuru ta rame, everyone is taking care of her agidan nan, ganin Munir kuma make her extremely strong at least ba ita kadaine karama a gidan ba, tana zaune a dinning itada Munir suna gyarama Mamie wake yana bata labari Mamie kuma na kitchen tareda mai aiki waya Asmeey dake wajen yahau ringing Snapchat call dan Munir yamata komi, dasauri ta kalli wayan dan Ya Hamad kadai ke kiranta kafin tamayi wani abu Munir yace  Oga ya kira iyyeee see blushing dasauri ta dauki wayan tana hararansa tawuce dakin Gwaggo tabude kofa tamaida tarufe tadauki wayan takai kunne da yar karaman murya tace  hello
EPISODE 7?? 1??





Dan ijiyan zuciya Hamad ya sauke jin muryanta tun rannan nan sai yau yake kiranta, cikin daddaddiyar murya yace  my baby gyadamai kai tayi ashagwabe tace  ina kwana ahankali yace  lpy lau, how are you? Murya chan kasa tace  fine tai shiru chan tace  Ya aiki? Ahankali yace  Alhamdulillah! Kinci abinci? Gyadamai kai tayi tace  eh kaifa? Ahankali yace  nima naci shiru suka sakeyi, murya chan kasa Asmeey tace  inaso naje nai kitso Yaaya dan shiruu yayi chan yace  okay i will asked Ya Hameed yakaiki saloon on Saturday, yace yanaso yakaiki wajen Zee, do you want to go? Gyadamai kai tayi tace  eh anatse yace  tom kije na yarda ahankali tace  Ya Faisal ya karbi passport dina dazu da safe gyadamata kai yayi yace  okay murya chan kasa yace  i miss you Asmeey sorry ban kiraki jiya ba hawaye taji yazo mata da sauri tashare tai shiru batace komiba, murya chan kasa yace  an biyani jiya wani murmushi tayi sosai tace  congratulations Yaaya Allah sa albarka murmushi yamata yace  Ameen write everything kikeso and send to me okay ? Gyadamai kai tayi ahankali tace  tom bayason yagayamata she s going for Umara, or car or her laptop is suprise maybe gifts din suyi cheering nata up and lift her mood, ahankali yace  I have to go now, saina kira anjima take care ko ? Ya Hamad baida yawan magana idan yakira tanaso suyita hira kaman karya kashe but Ya Hamad bai iyaba, highest 2min-3min yagama magana, bayan hannu takai tashare fuskanta tace  tom bye ta katse wayan saikuma tafashe da kuka kaman taita ihu she s missing him sosai but it seems shi baya missing nata ta aikinsa yake.
***

Mom takoma Kano but as usual bata kula kowa ta lura Munir baya gudan kuma tasan sunyi hutun school girman kai yahanata ta nemesa kota kirasa dudda taga calls nasa kwanakin baya datana Kano but bata dagaba yau tanaso taje gidan Hajiya Ramatu da Yamma ta nemi Fawaz cus fadansu is turning into another thing damuwa yamata yawa sai rama take ga BP dayaki komawa yadawo daidai tana zaune adaki akai knocking tai shiru Gambo kadai ke shigowa side dinta gyaramata itakuma sallama take bude kofan akayi Baba ne yana sanye da faran shadda yaci Babban kaya ya tsare Mom da idanu dayaga ta ramemai a idanu she looks sick ma has been sick all this while saisa bata gida, dudda kalan laifuffukan datamai saiyaji tabasa tausayi.

Dudda ta karbe gidan the fact that duk haukanta batace subar gidanba shows da ragowan Imani a ranta, maida kofan yayi yarufe yashigo falon Mom dataga Baba yamata wani kyau tadauke kai daga kallonsa batare data gaidasa ba tana tuna marin daya mata da aurar da Asmeey dayayi without gayamata, zama Baba yayi kujeran dake facing nata yace  ina kwana Salima? Shiru Mamie tayi kaman bazata amsaba tadaure tace  Ina kwana Baban Aya Dan murmushi kadan yayi yace  lafiya kalau dafatan kin tashi lpy gyadamai kai tayi tana kallon gefe duk sukai shiru sai chan Baba yayi dan guaran murya yace  tunda kinfi karfi kizo kibani hakuri nina biyoki inaso mu ijiye fadan nan na maidaki yanzu dakinki dudda kina ciki but nadai maida aurenmu dan boyayyen ijiyan zuciya Mom tasauke dan tana son aurenta amman azahiri tace  bayan kagama cimin mutunci, ka mareni a bainar jama a, ka aurar da diyata batare daka sanar dani ba

Mom tashiga kada kafa, Baba yayi shiruuu yana binta da kallo shi tausayima take basa aure Rahama ne wlh dukko kudinta duktai wani iri cikeda tausasa murya yace  kinfi kowa sanin dalilin dayasa na aurar da Asma u, ba gardama nazo muyi ba face sulhu amman idan kina ganin namiki ba daidai ba bari na miki tambaya daya kacal inaso kibani amsanta Mom ta kallesa ahankali Baba yace  mesa kika tsani Asma u diyar da kika haifa da cikinki? Wani iri Mom taji taso kartai magana amman zuciya ya debeta tace  sabida Asmeey bad luck ce! Tun cikinta nadena ganin daidai arayuwana ba, na haihota the only dalili dakesa kai fada dani is Asmeey kawowa har yau sabida Asmeey ka sakeni nika saka sabida ita! Saisa na tsaneta Baba yakalli fuskanta yana ganin tsana sosai he guess there s nothing he can do only time can heal this hatred she has for that poor girl, yunkurawa Baba yayi zai bitterly Mom tace  kadauki y ata ka aurama wani jakin dabban yaro mai matsalan kwakwalwa uwa uba jobless boy mara aikinyi yasamin yarinya a daki daya wanda ko nan dakin dasuke na gidan nan yafi wanda suka sata girma ciki sai hudu, look at room nasu mana yana daukan king size bed guda biyu nata da Ramla damasu Yusra but look at bukka room da aka sata akano itada miji na zama iyaye suna ciyarda su.
Murmushi Baba yayi yadan cije lips yace  Salima kenan ba ama Allah isgili sannan ba ama bawa gori, Allah daya baki can give Hamad much more anjiman nan, and been quiet and shy doesn t mean you have mental issue Baba yadan fuzar da iska yace  tune into ko CNN kowani international news channel today or watch Microsoft broadcast today na new AI din dasuke ya talla this days I have a suprise for you, 2PM anjima don t forget Baba na maganan yabude kofa yafice.

Mom tabisa dawani kallo ganin sabida tayi maganan yarsa ma komar da itan dayace zaiyi baimayi maganan ba yafice kawai zuciyanta yafara tafarfasa saitaji kanta na sarawa dafa kan tayi ta gyara zamanta tahayo da kafafunta kujera tahau tana kwanciya she s really sick, mesa Fawaz ke mata haka? He s the only cure to her rashin lpy wayanta ta daga tai dialing number sa bayama shiga at all kaman yayi blocking dinta ko baya Nigeria ne? Ijiyan zuciya ta shiga saukewa me zafi idanunta na fito da hawaye masu dumi ta gefe batajin dadin rayuwanta karfin haline kawai dawata ce da tuni ta mutu cus a tsaitsaye a tsaitsaye ciwo take tana wajen ahaka bacci yayi awon gaba da ita wuraren 2 na rana tabude idanunta.

Wayanta ta dauka tana dialing number Fawaz again but baya shiga ijiye wayan tayi ta shiga sauke kafafunta ta yunkura zata tashi saitaji kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login