Showing 36001 words to 39000 words out of 233624 words

Chapter 13 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2526

tace  Ma u gashi yayinki yasayo miki ice cream kowa na falon saida mamaki ya kashesa barin ma Hameed daya wani zaro idanu irin na gulman nan, Asmeey ta kalli Mamie saita kasa tashi ta amsa Gwaggo tace  tashi ki amsa Hamadi ya siyamiki yaga kinci bakar duka uwa jaka tashi tayi zuwa wajen Mamie akunyace tasa hannu takarba ice cream din Mamie tace  kije daki kisha abinki batai musu ba tawuce dakin Gwaggo tana kallon ice cream din daya dadada mata rai, dan satan kallon sama tayi kafin tabude dakin Gwaggo ta shige.
Gwaggo tace  Doctor kaika aikashi ya sayo abin ne? Girgizamata kai Ya Mustapa yayi ya mike tace  bari na sayo mata magani su Abdallah suma sukama Mamie sallama suka fice flat nasu.
Hakan yasa dasauri Hameed yatashi yazo wajen Mamie cikin whispering yace  Mamie Hamadi buying ice cream for a gurl this is unbelievable hararanshi Mamie tayi tace  munafincinka yakesa Hamad baya shiga harkan kowa cus u give meaning to anything me dan ya sayama Asmeey ice cream? Ba agabansa taci duka ba yanada tausayi Hameed yana wani murmushi yace  Mamie kodai kodai he he& . Tallabemai keya Mamie tayi tace  kaga saida safe ta tashi tana murmushi tayi stairs abinta ta shige dakinta shima yatashi yace  bari naje na sami dan iskan nan dakinsu Hameed yabude Hamad baya ciki it seems yana bayi kayan jikinshi yarage dagashi sai singlet da boxer yazo gaban bathroom din ya jingina da bango yayi folding hands nashi yana jiran yafito, kusan 5min yayi awajen Hamad ya bude kofa yayi wanka yana sanye dawani ash color joggers da white t-shirt na polo mai kyau ga kayan daya cire abayi a hannunshi, hada ido sukayi da Hameed dakemai wani kalan kallo da sauri ya dauke kai ya fuske yafito zai wuce karaf Hameed yasha gabansa yace  wat is that you did earlier? Chak ya tsaya batare daya kalleshi ba yace  I don t know wat u are talking about dariya ke neman kufcema Hameed yace  karya kake munafuki why did u buy ice cream for Asmeey? Tambayan kaman zaisa ya nutse akasa sai kawai yama juyama Hameed baya kaman zai kara komawa bayin Hameed yarikeshi ya fashe da dariya cikeda iskanci yace  so you are in love watsar da kayan hannunshi yayi akasa yace  stop Hameed leave me alone tsabagen son yakureshi Hameed yace  to kaida bama kasan ya ake sex ba how would you be intima& &  wani kalan tura Hameed yayi da karfi kaman zaki yawuce da sauri ya sunkuci laptop dinshi zai fice daga dakin Hameed yadaga murya yace  google wat is sex and start learning tun yanzu kafin asami matsala bayan aure da sauri Hamad yafita yana bugo kofan me Hameed zaiyi inba dariya ba dariya haryana faduwa gaban bayi is not like Hamad baisan sex ba but he can swear baisan yaya akeba wlh kuwa kunya irin na Hamad daban ne aduniya, he hates maganan banza, he hates looking at abubuwan banza ko iskanci ko tsiraici ko maganan kiss baiso ayi a inda yake yanzu sabida dan maganan nan zai iya harsu koma Kano yadena zama dakin nan kenan yadinga avoiding nashi, ba lallai yanason Asmeey ba bama ya tunanin tsokanane kawai yasan tausayi yarinyar tabashi yasayo mata ice cream kaman yanda suma sukace zasu saya mata, da kyar yagama dariyan yaduka ya kwashe kayansa yaje ya ijiye masa yafada gado abinsa sai bacci.
Babu kowa a falo hakan yasa yawuce dinning kawai yama ijiye laptop dinshi yawuce kitchen yadauko ruwa yaja kujera ya zauna yabude ruwan yasha yana sauke ijiyan zuciya sannan yafara aiki.
Almost 30min shi kadai afalon yana aiki aka bude kofan aka shigo hakan yada yadago kanshi karaf suka hada ido da Ramla wacce tana ganinshi taci burki gabanta na faduwa hakanan cikin duka yayyinsu ba ita kadaiba all of them sunfi shakkan Ya Hamadi cus babu wacce yake wasa da ita babu wacce ta taba ganin hakorinsa baitaba mata magana ba, gashi yanada kwarjini wani kallo yamata dayasa batasan sanda ta sauke kanta kasa ba tace  uhnnn dama& ..daman wajen Asmeey nazo bayabo ba fallasa yace  get out! Har tsakiyan kanta taji muryanshi kusan tunda tasan Ya Hamad this is the first maganan dayake mata wlh kuwa gyadamai kai tayi tace  tom saida safe Yaya tajuya tabude kofa tafice.

Wuraren 11:30 Asmeey tafarajin munsharin Gwaggo sosai ahankali ta lallaba ta sauka daga gadon batare datai making sound ba tana rike da veil nata a hannu tazo wajen kofa kaman barauniya tabude kofan ahankali tafito tana maida kofan tarufe tajuya da sauri tana tafiya ahankali ahankali sadaf sadaf tana warware gyalen tana kokarin yafawa danta rufe gashinta tai wajen kofa daidai takai kofa tasa hannu zata bude kofan taji saukan zazzakan murya that is so calming and soothing a kunnuwanta.  Where do you think you re going ? Amahaukacin firgice tajuyo karaf suka hada idanu da Ya Hamadi dake zaune a dinning ga laptop gabanshi da bottle water a gefe ya tsareta da crazy eyes nashi kawai saitaji ta dimauce jikinta yayi wani iri, she couldn t stand his gaze at all tama kasa magana gabanta sai faduwa yake sai kawai tajuyo ta wuce hakanan saita sake samun kanta da so ta kalleshi dago idanunta tayi kaman mara gaskiya ta kallonshi hada idanu sukayi mugun faduwa gabanta yayi tabude kofan dakin Gwaggo da sauri ta shiga daidai Ya Mustapa na shigowa da ledan magani a hannunshi dinning ya wuce ya zauna yana kwalama Asmeey kira.  Asma u Asma u daga ciki Asmeey tace  na am fitowa tayi ganin Ya Mustapa a dinning a yasa taje wajen ta tsaya gefensa batare data yarda ta kalli inda Ya Hamadi yake ba, magunguna guda biyu yaciro yace  2 2 zakisha, duba fridge idan akwai ice kisa a kumatunki karya kumbura idan babu kisa ruwa a leda yayi kankara zuwa anjima gyadamai kai tayi tawuce kitchen shikuma yatashi yakalli Hamad dake aiki yace  good night gyadamai kai yayi Asmeey tafito da bottle water ganin babu Ya Mustapa duk sai taji wani iri magungunan tadauka daga dinning tawuce dakin Gwaggo da sauri.

WAYYO ASMEEY=ؔ?=ؔ?
AFADI GASKIYA MAMIE HAMADI YA SIYAMA ICE CREAM KO ASMEEY??
=ث?UWA KO UKUBA?=ث?



'

M SHAKUR TA IYA LITTAFI>?)?>?)?
THANK YOU ALL FOR READING>?)?
GAYAMIN ME KIKEFI SO GAME DA THIS BOOK +2347012181461



EPISODE 1?? 1??



Tana shiga cikin dakin Gwaggo ta maida kofa tarufe ta jingina da kofan hannayenta biyun dake rike da bottle water da magani duka ta daura kan kirjinta dake bugawa nonstop, why is her heart racing sabida Ya Hamad? Saikace yauta fara ganinshi toh kodan bai taba mata magana bane? Anytime sukazo salla ma hardly take ganinshi dan baya shiga mutane, wani zubin daga ranan dazasu zo sai rannan salla take kara ganinshi, takai almost 2min tsaya awajen sannan tawuce ta zauna bakin gadon tabude maganin tabude ruwa tasha, at first batason magani but dukan Mom yasa ta koyama kanta shan magani da kanta, cus drawer su na daki Baba na ijiye musu basic magunguna haka irinsu paracetamol, Ibuprofen maganin ciwon mara da first aid kit she learn to take care of kanta, kallon gadon tayi yanda Gwaggo ke maka uban minshari abinta ta rakube ta kwanta gefe dudda ga uban space tai shiru gabanta sai faduwa yake she wanted to go back to side nasu hakan zaisa laifinta yaragu gashi an hanata fita anan and she knows, Mom tasan ba a side nasu ta kwana ba, hannunta takai saman kumatunta da taji yana mata zugi takai hannunta saman cikin nata shima dake mata zugi saitai shiruuu hawaye ya gangaro mata bata taba iya bringing kanta to ask her self maisa Mom is always beating her? Mom bata tausaya mata, Mom hit her kaman she s not her Mom, tana son Mom but Mom bata sonta, dazu data rungume Mamie she wished Mom ta rungume haka, hawaye ta kara sharewa ahaka tagama tunane tunanen ta bacci yayi awon gaba da ita.
Around 1:00 yagama abinda yake dan har Abba saida yashigo still bai gamaba kashe system dinshi yayi yadan kalli kofan dakin Gwaggo saikuma ya mike tsaye ahankali yawuce kitchen freezer yabude yadauki ruwan data saka dayaga yayi kankara yadauka yadauki bowl yasa, yasa wasu ruwan a freezer incase zatai amfani dashi gobe, yafito daga kitchen din yana tafiya ahankali yawuce gaban dakin ya tsaya yayi dan jimmm, hannu yadaga yadaura kan kofan yayi knocking kadan he could hear minsharin Gwaggo daga wajen, sake knocking yayi ahankali but still shiru yasake yin jimmm, ataushashe cikin yar kankanuwan murya dake ratsa mind yace  Asma u! Firgigit Asmeey tafarka tabude idanunta dan har cikin zuciyanta taji yanda aka kirata, da muryan bacci dake a hargitse tace  uhnn na am dan jimmm Hamad yayi, kusan 10seconds sannan calmly dan yasan bacci take karya firgitata yace  open the door tashi tayi daga gadon dasauri ta sauko batare datama san dankwalinta baya kanta ba bata da kayan bacci anan so gown din atampan ne ke jikinta ta taho wajen kofan kai tsaye tasa hannu daya tabude kofan while dayan hannunta nakan idanunta tana murzawa sabida bacci, sauke gentle eyes dinshi Hamad yayi kan fuskanta she s not even looking at him sosa idanu take sabida bacci, idanunshi yadaura kan lafiyayen hadadden kitson da aka mata dayayi kyau sosai da sauri yasauke kanshi ya maida kan fuskanta for the second time ahankali yace  Asma u! Dasauri ta dago kanta takalleshi tana janye hannunta daga kan idanunta da suka kada sabida bacci ga kumatunta daya kara ja inda aka mareta gabanta na faduwa sabida yanda yakira sunanta, tsareta da idanu yayi na kusan 10secs dukansu babu wanda yayi magana this time around shine yafara janye idanunshi daga kanta yamika mata bowl da ruwan ice ke ciki yace  put this a fuskanki bowl din itama ta kalla saita gyadamai kai ahankali tasa hannuwanta kan bowl din zata amsa sai bai saki ba hakan yasa tadago kanta ta kalleshi ganin bai sakin mata ba, hada idanu sukayi yanda taga yana kallonta yasa ta sauke kanta kasa da sauri har lokacin hannuwanta nakan bowl din tana jira ya sakin mata, cikin yar kankanuwan murya da ita kadai zata iyajin maganan sa Hamad yace  next time if anyone tries to slap you use your hands or elbow ki kare fuskanki, dan dago kanta tayi tadan kalleshi har tsakiyan zuciyanta takejin muryanshi dakeda bala in dadi, ga kamshin dayake yi daya cika wajen, bawai fuskanshi ko expression nashi shows he care bane but his words are so deep a heart nata that translates as he cares, baiso yaga kumatunta sunyi jan mari, sauke kanta kasa tayi sannan ta gyadamai kai ahankali tace  tom, thank you 4 d ice cream Ya Hamad sakin mata bowl din yayi ta hanyar jaye hannayenshi daga kai yajuya da sauri kaman wanda yaji kunya murya ciki ciki yace  Mamie na siyama not you yawuce dinning da sauri hakanan saita kasa komawa ciki ta tsaya awajen kaman an kafata he looks so cute, godiyan datamai ne yabasa kunya? His shyness is charming, laptop dinshi ya dauka daya kashe da ragowan ruwan bottle water daya rage yajuyo hada ido sukayi da sauri tajaye nata idanun gabanta na faduwa takoma cikin dakin da sauri ta maida kofan tarufe, dauke kai yayi yawuce yakashe wutan parlour kafin yayi stairs yashiga dakinsu Hameed yayi nisa a bacci, ijiye komi yayi yafada bayi yafito daure da alwala, dadduma ya shimfida yayi nafila sannan yatashi yazo yahau gadon ya kwanta ahankali.

Tana maida kofan tasake jingina da kofan tayi shiru duk wani motsinshi a parlour tanaji harya gama kashe wuta sannan tajuyo yarufe kofa dan bakajin walking step nashi what is wrong with her? Tayi maganan ahankali, wucewa tayi gaban gadon ta zauna tadauki kankaran ta daura saman kumatunta but saitaji sanyi da sauri tacire ta ijiye a bowl din tana kallo, sake dauka tayi takai kumatun kusan 3secs ta ijiye takasa jure sanyin sai kawai ta ijiye bowl din ta kwanta sai tunanin Ya Hamad take da yanda yakirata Asma u da maganan daya mata muryanshi is so soothing she can t even explain and so calm gawani irin natsuwa da kwarjini da haiba da tunda take bata taba ganin namiji mai kalansa ba ga idanu kuma kwallin dayake sawa namai bala in kyau ahaka bacci yayi awon gaba da ita.

Wajajen 4:30 na asuba Gwaggo ta farka tana kunna wuta takalli Asmeey data dukunkune tace  ke ga jin sanyi amman kin kasa tashi ki dauki abin lulluba sauka tayi daga gadon ta wuce drawer taciro bargo tazo tabude ta lulluba mata sannan tawuce bayi tace  bari na barta tadan kara bacci nasan taci bakar wuya a hannun muguwar uwarta salla Gwaggo tafito tayi tanakan dadduma tana kallon Asmeey data kudundune a bargo harkai saijan charbinta take around 6 tafada bayi tayo wanka tazauna ta cicciro abubuwan shafe shafen ta tafara shafawa masu wired kamshi abinda yatada Asmeey kenan tabude idanunta tana yaye bargon ta tashi zaune ahankali tace  Gwaggo meke wari kallonta Gwaggo tayi zata zageta sabida yanda take kiran manta na wari tabuga salati.  Oh Innalillahi wa innailaihi raji una billahillazi idan uwarki bata rokeki gafara ba sai Allah ya soyata a jahannama, kalli suntumemen kumatu kaman an zuba yeast dasauri looking confuse Asmeey ke kallon Gwaggo dake surutu but ganin yanda take kallon fuskanta yasa gently takai hannunta saman kuncinta da Mom ta mara saitaji ya kumbura takai dayan hannun ta shafa na bangaren dama is normal hannunwanta kansu sai sukayi kaman ta daura daya a tudu daya a flat surface sai kawai ta tashi da sauri tawuce bayin Gwaggo tana bude kofa ta tsaya turus tana kallon madubi yanda kumatunta na haggu ya kumbura kaman tana ciwon hangum ko ciwon hakori harda wajen lips da jaws nata saitai looking kaman ba ita ba tai wani irin muni a idanunta wani irin sosa mata rai abin yayi batasan sanda ta duka tafashe da kuka sosai ba like she s feeling super hurt, takai kusan 30min abayi Gwaggo tace  wai harna gama shiryawa tsaf nasaka kayan salla bazaki fito kiyi salla ba da kyar ta tashi idanunta sunyi jazur tafito kanta akasa tasaka hijabi tai salla tana idarwa ko azkar batayi ba ta mike yafada gado taja bargo har saman kanta Gwaggo tace  yau naga ikon Allah tashi kije kiyi wanka yanzu zanje chan dakinku na karbo kayan sallanki mutafi masallaci taushe bakinta tayi bataso Gwaggo tasan tana kuka ta danne tace  bazanje ba tsuki Gwaggo taja tamike tace  nadawo dakin nan bakiyi wanka ba sai an jimu agidan nan tawuce tafita.
Wajajen 7:15 Gwaggo tadawo da leda a hannunta wanda Ramla tahada mata komi da zata saka dan ka ida rannan salla kowa kayan da Abban Kano ya dinkama kowa yake sawa ganinta har lokacin akan gado gashi masallacin dasuke zuwa 8:00 ne salla yasa Gwaggo tace  au baki tashi ba bari kigani kayan ta ijiye tafito falo tana rapkama Abba kira.  Abubakar Abubakar, Madina kai Abubakar koda Abba yabude yashiga saukowa Mami biyeda shi ya shirya tsaf cikin manyan kaya da malunmalin ga agogon da Hamadi ya siyamai wrist nashi Mamie ma tasaka lace mai kyau ta saka sarkan da Hamadi ya siyomata shima Hameed yashiga saukowa yayi bala in kyau cikin shaddan sa sky blue da akamai jumper da aiki mai kyau. Abba yace  Gwaggo lafiya rai abace tace  kaga nida Asama ne takemin bori uwa nice na kumbura mata fuskan, wanka takiyi wai bazata masallaci ba sabida uwarta ta nakasa mata barin fuska wani kallon takaici Abba yama Gwaggo sai kawai yawuce dakin Mamie tabisa Gwaggo tabi Hameed dake kamshi tace  kawa Allah sammin turaren nan daka fesa dake kamshi ja iran chancewa tayi wai wari turarena yake Hameed yace  dama bakisan tsami turarenki yake ba Gwaggo haderai waggo tayi tace  nidai zaka tsammin ko bazaka tsammin ba ? Daidai Hamad yafito cikin exactly kalan kayan Hameed da sunmai bala in kyau yana saukowa daga stairs Hameed yace  turarensa ne ki tambayesa tsayawa Gwaggo tayi tana kallonsa yanda yake tafiya a natse tace  Oh Allah ka nunamin auren Hassan da Hussaini, kai Allah yama Hamadi natsuwa inama haka Hameedu keda natsuwa rai abace Hameed yace  me kikace ?  Uban ka nace ta amsashi tana murmushi tana kallon Hamad daya hada fuska.

Abba ne yafara shiga dakin da sallama yace  Husna dawani irin sauri Asmeey ta tashi dan gidan nan kap bataga wanda baya girmama Abba ba shine babba har Baba respecting Abba yake sosai kuma ya manyanta yaye bargon tayi ta tashi ta zauna tace  na am Abba ina kwana daga Abba har Mamie kumatunta sukabi daya kumbura gashi tai kuka sai idanunta suma suka tashi karasowa wajen gadon Abba yayi yace  subhanallahi Doctor bai baki magani bane? Ahankali tace  yabani nasha amman yace nasa kankara jiya nafara sawa sai nayi bacci bansa da kyau ba tana maganan sai hawaye suka sake fadomata ta share da sauri ta sauke kanta kasa asanyaye Abba yace  ya isa tashi kiyi wanka muje masallaci Doctor sai kara dubaki gyadama Abba kai tayi ta tashi ahankali tawuce bayi Abba yawuce yafita duk zuciyanshi ba dadi Mamie ma haka suka fito duk an shigo su Ya Mustapa kowa yaci gayu Abba ya kalli agogon hannunsa yace  inaga masallacin 8:30 zamuje ko na 9 Doctor ahmm please kaduba yarinyar nan kumatunta ya kumbura dasauri Ya Mustapa yace  batasa ice bane Mamie tace  tafara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login