Showing 39001 words to 42000 words out of 233624 words

Chapter 14 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2560

wai sai tai bacci Abba yabi duka yaran nashi da kallo sunyi kyau sosai kallo saya Hamad yama Mamie yaga sarkan saya sayamata Abba yasa agogon Ya Mustapa ma yasaka agogon daya sayama hakan yamai dadi sosai.

Bata wani jimaba tafito ta zazzage ledan harda cream Ramla tasa mata sharp sharp tasa kayan atampan da Abba yamusu mai kyau gold atampa mai blue ne embellish an mata riga da skirt da suka zauna ajikinta sosai, bata daura dankwali ba hijab kawai ta saka ta fesa turare tasake kallon madubi she feels pathetic she feels down she s feeling like the most ugliest girl in the world zuciyanta yayi baki kirin ba dadi ta daga hannuwanta takalli lallinta da duk sun gwalje nothing is right about her banda kitso da dinki she s having a very very dark salla sai kawai taji tana kunyan ama ganta gashi batada nose mask anan adakinsu akwai daga waje taji Mamie ta kirata.  Ma u kingama ahankali muryanta na cracking tace  eh takalmin sallanta wanda yake hill gold mai kyau sosai very expensive shoe tasaka sannan taja wuyan hijabinta gaba sosai sannan takama hijab din tagaba tarufe kumatun tazo wajen kofa kanta akasa tafito ahankali kowa na falon har Abba kallonta suke banda Hamad dayayi kaman baimasan wani abu na faruwa ba Abba da baison wani yayi maganan fuskan yasata kuka yace  toh kumutashi muje muje muje Husna Hamad yafara tashi kai tsaye yawuce kofa abinsa yabude yafice, Gwaggo takoma daki taciro gyalenta ja ta yafa wanda Hamad ya siyamata tace  billahillazi banga wanda yakaini kyau agidan nan ba yau fitowa sukayi sukai wajen motocin gidan da an wanke gasu Nana da Ramla duk an fito suma sanye da irin kayan dake jikin Asmeey, Ramla sai kallon, ahankali ta tsaya gefe daya wajejen taki zuwa wajen su Ramla Munir daya fito daga flat dinsu yana sanye da shadda hadade tasha guga idanunshi akan sister shi yafara sauka yanda yaganta ita kadai tajawo hijabi gaba da sauri wajenta yafara zuwa ya tsaya yadan leka fuskanta yace  mehaka Ya Asmeey kin rufe fus& .. kasa karasa maganan yayi lura da kumburin fuskanta sai yayi shiru yana kallonta ahankali yace  na dauko miki nose mask? Gyadamai kai tayi da sauri yajuya yakoma flat dinsu daidai Mom na fitowa daga flat din tareda Mama dasu Ammi mugun bugawa kirjinta yayi Mom ce kadai bata sanya kayan da Baba yamusu ba wani HKG atampa ta saka ta daura designers after dress akai ta zuba gwalagwalai awuya da hannu tana tafiya kaman she owns the floor rawa hannuwan Asmeey yafara tajuya tana kokarin zata zagaya ta bayan motan Ya Mustapa yace  Asmeey arude ta juyo yakalli Hamad ya mikamai key sienna motan Baba yace  all the children su shiga this sienna drive them, get in Asmeey dasauri kafin Mom ta iso wajen tawuce, ta shiga chan last roll na motan Ramla itama tashigo tazo ta zauna kusa da ita sauran kannensu suka shiga motan kowa na shiga motan Mom ta iso ta gaisa da kowa aka amsata banda Baba daya shige mota abinsa Mom tawuce ta shiga motanta Mama ta shiga tareda ita, Mamie ta shiga mota daya da Ammi da Gwaggo Hameed ya jasu Ya Faisal yaja matayensu shikuma Ya Mustapa yaja su Abba Munir yafito yazo ya shiga gaban motan Ya Hamad yashigo ya rufe motan Munir yajuyo yaba Yusra nose mask yace  mikama Ya Asmeey . Black glass Ya Hamad yasaka yaja motan duk akabar gidan, hannu Ramla tasa ta karbi nose mask din tajuyo tamikama Asmeey da ke kallon gefe daya ahankali tace  Asmeey take juyowa Asmeey tayi batare data kalleta ba tasa hannu zata karbi nose mask din dasauri Ramla tarike hannunta hakan yasa Asmeey ta kalleta da rinannun idanunta sosai Ramla taji she s feeling guilty barinma kumatunta data gani sai taji tai nadama taruwa hawaye yayi a idanunta murya chan kasa tace  I m sorry Asmeey kiyakuri kinji shiru Asmeey tayi tana kallonta tana tuna abinda tamata jiya tayi kokarin fizge hannunta Ramla tarike muryan Asmeey na rawa sosai tace  ki sakeni ta madubin gaban motan Hamad ya kallo bayan, yaran ma duk suka juyo Ramla tace  kice kin hakura tukunna ranta na tafarfasa tabude baki zatai magana takasa tashiga kokarin fizge hannunta, Munir da iya shiganma yar uwanshi yace  Ya Ramla ki saken mata hannu ahankali Ramla tace  hakuri nake bata cikin tsiwa Asmeey tace  bazan hakura ba and baruwana dake kifita harkana you lied kince nace miki wawiya and I never said that, ai yanzu you are happy ko daman kince nasaba shan mari a kumatu kema zaki karamin kumatun is swollen I hope you re satisfied niki sakeni tafashe da kuka sosai datake rikewa sake kallonta Hamad yayi ta madubin sai kawai ya dauke kanshi ya maida kan titi Ramla ta rungumeta da sauri tana kuka itama tace  Asmeey dan Allah kiyakuri I m sorry for whatever I said jiyan nan kiyakuri kinji shiru Asmeey tayi sai chan ta gyadamata kai Ramla tace  tsaya na samiki nose mask din hannu rasa ta sharemata fuska sannan tasa hannunta a hijabin tasa mata nose mask ahaka sukakai mosque kashe motan Hamad yayi Munir ya sauko yabude musu duk suka shiga fitowa gabanta sai faduwa yake tadan kalli gaban motan ganin Ya Hamad na zaune dauke kanta tayi da sauri tafita daga motan ahankali daidai Mom na zuwa wajen dawani irin sauri tadawo cikin motan hakan yasa Hamad yajuyo hada idanu sukayi dauke kai tayi da sauri sannan tafita daidai su Mom sun wuce tabi baya ya sauko yarufe motan suka wuce sahu tayi gefen su Gwaggo Mom nadaga chan.

Sallame sallan sukayi kaman ance tadan juyo karaf suka hada idanu da Mom wani kallo da Mom tamata ita kadai tasan meaning dinshi cikinta wani kuka yayi dasauri ta sauke kanta kasa tashi Gwaggo tayi tace  kumuje Billahillazi yunwa nakeji dabino na yana mota shi zanci hannunta Ramla takama tace  muje ahankali ta mike dasauri tabi Ramla suka wuce Mom tamata wani kallo ganin kallon data mata dazu baisa ta tsorata tace a motanta zata koma g1da ba ko gaisheta ina kwana batayi ba tafarfasa zuciyanta yashiga yi suka wuce itada Mama.

Wajen motarsu sukaje suka jingina suna jiran Ya Hamad da Munir ganin Mom na zuwa wajen wani kalan dukewa tayi ta tsugunna dan kafafunta sun kasa daukanta ko kallonta Mom batayiba tawuce wajen tata motar abinta tashiga ta kunna tana duke ahaka saiga Ya Hamad da Munir suna zuwa ahankali Ramla tace  tashi muje
Tashi tayi Munir yabude musu motan duk suka shiga tunda ta shiga motan tai shiru dudda anata hira but Mom kawai zuciyanta ke kawo mata _undan bata lokaci kafin sukai gida parking akayi saukowa sukayi ahankali tawuce flat dinsu Ya Hamad yadan kalleta yadauke kai mazan suka wuce wajen raguna dan tanka su Mamie kuma suka wuce backyard daidai zata shiga flat dinsu Gwaggo tace  zonan Asama tunda komawa inda ake neman kasheki kikeso kiyi Dan waigowa tayi ta tsaya Baba dayake tsaye kusa da Gwaggo yace  badake ake magana ba juyawa tayi tayi hanyar flat dinsu Abba Mom data fito daga mota takalli Baba dayayi kaman bai ganta ba zata wuce flat Gwaggo tace  eh aje acire kaya afito ayi aiki ko kallonta Mom batayiba.
Kananun yaran gidan tea aka shiga basu Ammi tace  Ramla kutashi kuje kuda su Nana ku jera carpet a tsakar gida da kayan abinci anan za aci tashi duk sukayi, Asmeey na shiga dakin hijabin ta cire ta zauna ahankali tana zare nose mask daga falo taji Gwaggo tace  kifo Asmeey an saku aiki tasan aikin already hakan yasa tadauki gyalenta na dakin blue ta yafa akai tadan zazzago dashi tafito slippers data gani so well kept anan side na chair a falon ta zura kafafunta aciki sun mata yawa Ramla dake kallonta tace  jiya da daddare saida nazo na ganki but Ya Twins bansan ko Ya Hamadi ko Hameed bane da zuciya daya Asmeey tace  maisa kwallin? Gwaggo dake zaune ta buga salati tace  Hamadi kike cewa maisa kwalli Asmeey ai gashinan yana jinki ? Dawani irin sauri daga Asmeey har Ramla suka juyo daidai yagama saukowa daga stairs gashi bakajin footstep nashi, arude tajuya zata fice gabanta na faduwa calmly yace  my flops chak Asmeey ta tsaya saita sauke kanta ta kalli kafafunta da sukai dan firit a takalmin, awani irin hankali tajaye kafafunta daga ciki sannan ta sauke kanta sadaf sadaf tafita ahaka Ramla tabita suka shiga warware carpet suna shiryawa a compound din ga pillows sun jefa anyi setting sannan suka tafi backyard su da matan yayansu nafito da abincin da aka dafa daban daban kusan 45mins aikin ya daukesu su Baba kuma an gama gasa musu some part na layyan dasukayi duk akazo aka zauna dan cin abinci Mama tace  bari na kira Maman su Aya .
=ث?UWA KO UKUBA?=ث?



'

EPISODE 1?? 2??

KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???

JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA=?%?

GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA=?H?

CHAT ME UP DON SHIGA
wa.me/+2347012181461
EPISODE 1?? 2??



Babu wanda yace mata wani abu ta mike ta wuce Asmeey kanta na kasa Ammi da Mamie suka shiga serving kowa saiga Mom tafito tareda Mama tasami waje ta zauna tana murmushi da Mama, Baba ya tsareta da idanu she never cared about family nashi bata shiga harkansu, this is the measure reason yasa ya karo aure lokacin, Gwaggo ta watsama Mom harara tace  aikin kenan bakar muguwa wani kallo Abba yamata yasa tace  ai nayi shiru uhmm tunda an hanani magana abincin kowa yakeci banda Asmeey data kasa ci sabida zuwan Mom, dan dago kanta tayi tana kallon Mom she just wish inama zata mata murmushi she loves her Mom amman Mom murmushi take da Maman su Nana, dan karkato da idanunta tayi karaf suka hada idanu da Ya Hamad dake kallonta shima bayacin abinci he s not comfortable, da sauri ta sauke kanta kasa tadebi rice takai baki kadan, Mom ta kallota ganin she s eating abinta ta dauke kai zuciyanta na radadi da suya, Ya Hamad yafara tashi kansa akasa yawuce babu wanda yamai magana yamayi kokari yau yafito cus baitaba fitowa aci abincin tareda shi ba, Gwaggo tace  makiyin abinci mai shegen zurfin ciki da rashin son jama a Ya Mustapa yakalli Asmeey yace  once you finish eating go and put ice a fuskan nan take your drugs and sleep kada kiyi komi gyadamai kai tayi Baba yakalleta sai kawai yadauke kai.
Tashi Mom tayi takoma ciki ganin tadena cin abincin Baba yace  jeki dauko ice din kisa saiki kwanta gyadama Baba kai tayi ta tashi tawuce, ice ta dauko a fridge tawuce dakin Gwaggo this time tadaura tasaka sosai tasha magani ta kwanta agadon tayi shiruuuuuu ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Babu wanda ya tadata bata farka ba sai around after 4 na yamma tai maza ta fada bayi takalli kumatun wow yadan sabe yarage ja tayo alwala tafito tayi salla azabar da la asar tayi shiru zaune kan dadduma she has lot of karatu she suppose to do tun jiya da Baba yasa tawuce wajen lalle bata kara karatu ba gashi yau ba a bari taje side dinba wat will do now? Tashi tayi tahau gadon ta kwanta bawai daman wani danna waya take ba so she s okay, tana kwancen lamo aka bude dakin dasauri takalli kofan Munir ne da plate na soyayyen kayan ciki da yaji a gefe tashi tayi zaune ahankali ya maida kofan yarufe yana murmushi yace  yauwa kin tashi nazo yafi sau biyu kinata bacci Mamie tace kar atasheki maganin dakika sha ne, zomuci kayan ciki da zafin shi inason salla wlh yayi maganan yana zama kusa da ita kan gadon ya ijiye plate din databi da kallo saikuma ta kalleshi, her life is so dark da bataga mema takejin dadinshi ba she has typically no one, yayinta don t care about her ko Mom ne kehanasu oho, she has no friends, yanda tai shiruuu yasa Munir yace  you re worried about Mom ko ? Gyadamai kai tayi sai kawai ta matso kusada Munir ta daura kanta akan kafadanshi ahankali tafashe da kuka mara kara cus she learnt kuka mara kara sabida Mom ta hanata kar ajisu, cikin murya tace  Munir I am just tired of everything, I know ankawoni nan sabida Mom karta tabani ne but wlh I feel more worried da tashin hankali ma anan da fargaba compare to inachan side namu, I know Mom is very angry with me, I m scared Munir zuciyana is not at ease is constantly beating tunani nake ko gaishe da Mom banje nayi ba I am a bad daughter, metayi da za a ce nadawo nan? Ramla ce tayi karya akaina da batayiba da bazata dakeni ba, Mom wants wat is best for me, I just want to see Mom smile at me I feel bad anytime nasan nine da reason for her anger, I am a bad daughter Munir ahankali gudun kar ajisu Munir ya girgiza mata kai yace  you re not a bad daughter wallahi, Mom ce is a bad mother dake enjoying giving you pain, giving us pain especially you sabida taga kinada tsoro, sabida you don t speak up bakisan right naki ba, what kind of a mother ce zatama yarta irin abin nan data miki koda yes kinyi laifin da Ramla tace kinyi ne? Look at you rannan salla kalli kumatunki kalli lallen ki eh? Wai tsaya Ya Asmeey bakida saurayine kicemai yafito yazo yaga Baba kiyi aure kibar gidan nan? Dago kanta Asmeey tayi ahankali ta kalleshi irin kallon wannan wace kalan maganan rashin hankali ne, dasauri Munir yace  oh no bakida shi ta inama zaki samu when Mom is in control of your life, inama take bari ki taba waya balle kiyi dawani! I ve never ever seen a Mother kaman Mom dinmu wai wat does she get by hurting you? Wani kalan tsana tamiki ne ahankali Asmeey tace  stop talking about Mom haka bata tsaneni ba nine ke mata laifi nake bata mata rai, the problem is me not Mom Allah kuwan cikeda takaici Munir yace  tayaya? How? How are you the problem Asmeey? You think abinda Mom take miki is okay? How are you the problem tell me ? Munir yafadi cikeda gardama da jin haushi, dan shiru Asmeey tayi trying to remember laifukanta chan tace  kaga nine bana gama files data bani dawuri, courses na law school datake min ban cika ganewa ba, ni Ramla tagayama namata laifi dasauri Munir yace  an so fault dinki ne you re a slow learner? Kowa da kalan brain din da Allah yamai haba mana, in the first place ma was law ever choice naki? She forced you to study law yanda Munir ke magana fuskanshi na nuna so much bitterness akan Mom saitaji kaman tana aikata wani babban zunubi ahankali tace  stop talking about Mom like this please, A mother is the best thing arayuwan d a! Kome Mom tayi mana daidai ne, stop talking about her like this kadena jin haushin Mom Munir  naji yar Mom, I just wished she appreciate wannan son dakike mata, Mtsww let s eat nidai favorite soyayyen kayan ciki nakawo mana da zafi naman ta kalla saita dauki daya tasa abaki tai shiru Munir na kallonta, he loves Asmeey, kofan tare suka taso but he loves Asmeey sama da elder sisters dinshi su Aya da Aysha, he loves Asmeey beyond words he s just being strong for her, suna tare bai bar dakin ba saida aka kira magrib yafita.

Tashi tayi tai magriba tana kan dadduma Mamie tashigo da plate na nama da abinci tace  Ma u yaya jikin da sauki? Gyadama Mamie kai tayi tai murmushi mai kyau, Mamie ta ijiye plate din takai hannunta ta shafa kumatun daya sabe, jan shima yaragu tace  tuntuni kina daki ci abinci kije ki tayani share dakina su Areef duk sun zubamin cincin akasa zaki iya? Dasauri ta gyadama Mamie kai dan tuntuni tagaji da zama without purpose, itama Mamie that s why tadan sata aikin, Mamie ta mike tace  bari na koma backyard muna chan idan kin gama kinaso kizo kizo kinji sake gyadama Mamie kai tayi tace  toh naji fita Mamie tayi daga dakin tai shiru tana kallon abinci da batada apatite na ci sai kawai ta ijiye, tashi tayi tadauki blue gyalenta ta yafa tafito babu kowa a falo store ta shiga ta dauko broom da packer tafito tawuce sama daganan bene tanajin muryan maza da dan yawa daga dakinsu Ya Hamad karasa hayowa sama tayi takalli dakinsu kofansu arufe hakan yasa tawuce dakin Mamie, ahankali tabude kofan dakin kamshi mai dadi AC ma a kunne dakin duhu banda hasken dake shigowa ta kofan data bude wanda yake na nan corridor babu any haske a dakin, normally dakin akwai switch tanan gefen kofa but yadena aiki sai switch din wajen gado haka tasaki kofan ta shigo ta ijiye broom da packer kofan ya shiga rufe kanshi kadan kadan itakuma tawuce wajen gadon daidai kofan yakarasa rufuwa kamshin dataji ajikin Ya Hamadi taji awajen amman bata kawo komiba ta mika hannu ahankali ta danna switch din wutan dakin yakawo idanunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login