Showing 99001 words to 102000 words out of 233624 words

Chapter 34 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2586

yau bata fita ba wayanta yahau ringing dauka tayi ganin Hamad ne saitadan tashi daga wajen takai wayan kunnenta anatse tace  Hamadi dan shiru yayi cikeda bala in jin nauyin Mamie tunda aka tashi daga salla duk inda zaije ba a bude ba, ahankali tace  hello Hamadi murya chan ciki yace  Mamie sh& .she is not feeling fine ya katse wayan, shiru Mamie tayi sai kawai tajuyo tawuce sama kai tsaye tai knocking kofan babu amsa but taji alamun kuka dasauri tabude kofan tashiga tundaga kettle heater su daga Lipton dinsu tissue Mamie ke kallo kafin ta kalli Asmeey dake zaune kan gadonsu but ta kifa ciki dasauri Mamie takamata tace  Asmeey meke miki ciwo? Muryanta bamaya fita sosai tace  cikina dasauri Mamie tace  Subhanallahi sannu sannu before you know it Mamie tahada mata ruwan wanka, tana wanka Hamad yabude dakin da sallama ganin Mamie tsaye wajen bayi yasa da sauri ya sauke kai kasa Mamie tace  ka samo mata magani? Gyadama Mamie kai yayi ya ijiye jakan sai kawai yajuya yafita Mamie tawuce ta dauki jakan tabude pad taciro guda biyar yakawo sai leda medic plus pharmacy magani ne aciki Mamie tafice takoma kasa takawo mata kunu da kosai tsaf Mamie ta tayata ta shirya tabata magungunan tasha tadan sha kunun da kosai sai kallon kofa take har ita Mamie saida ta lura tace  tunda kindanci bari naje zan dawo anjima na dubaki gyadama Mamie kai tayi ahankali Mamie tafice, ko 1mins ba ayi da fitan Mamie ba Hamad yabude kofan yashigo, hada ido yayi da Asmeey dake kwance kan gadon tana sanye da atampa ba dankwali akanta tayi wani irin kyau but idanunta sunyi jan kuka, tana ganinshi tai raurau da ido maida kofan yayi yarufe yazo bakin gadon ya zauna hannunsa yamika ahankali yakama nata yace  how are you feeling ? Gyadamai kai tayi awani irin hankali tace  zansha coke abin yaso yabasa dariya yadanyi murmushi kadan yace  coke? Gyadamai kai tayi tsareta yayi da idanu dasauri tasauke kanta kasa, sakin hannunta yayi yamike yafice tabisa da kallo saukowa kasa yayi yawuce kitchen fridge yabude yadauko coke mai sanyi yafito Gwaggo tace  kaga nima bani Lemun goran nan  jeki dauka Gwaggo ta ballamai harara, wucewa sama yayi yabude kofan dakinsu ya shiga kokarin tashi tahauyi da sauri yakaraso wajen gadon, ijiye coke din yayi yadagota ta zauna tareda jingina da bango ya zauna gefenta yadauki coke din yabude yabata karba tayi takai baki takafa tafara sha yanda ya tsareta da idanu yasa tasauke coke din dasauri daga bakinta ta boye fuskanta da hannu kunya taji, murmushi yayi yace  sweet tooth murmushi tayi tacigaba da sha tass ta shanye tadanyi gyatsa ahankali zata koma ta kwanta kawai saiya rikemata hannu dasauri ta kallesa dan lumshe idanu yayi yabudesu sai kawai ya fizgota jikinsa and just hug her so tight, dan rawa jikinta yafara wani irin kunya nakamata, patting bayanta yashigayi yana sauke ijiyan zuciya ahankali, Ya Hamad hardly talks but action dinsa speaks with volume na so much care for her, suna ahaka taji jikinsa yasake bacci ya kwashesa a zaunen rikeda ita.
EPISODE 3?? 8??



Dan dago kanta kadan Asmeey tayi daga kirjinsa takallesa wlh yayi bacci, in her entire life bata taba ganin mutum kwara daya that was as caring as Hamad is to her ba, Munir is very caring also yana sonta but dudda haka not like Ya Hamad, actions na Ya Hamad deeply screams I care for you and I will take care of you no matter what, ranan dayayi saving nata ta tuna yanda taga kofan ya karcesa har a hannu suna jini but baidamu ba he just wanna save her at that moment, bai damu da pain dinsa ba sai nata, if she s hurt because he cares yasan she s hurt, shi kadai yagane marinta akayi rannan, so many things dudda hardly yake magana but he knows better than kowa, yau kuma tun 2 yafarka sabida ita baikoma bacci ba, bai nuna yagaji da kukanta, koda yanda takemai shagwaba ko shigemai jiki ba, she don t really know exactly what she s feeling game da shi, idanma abinda takeji shine love din then she s very very happy she loves him, sosai take kallonsa he looks super calm even while sleeping gashi he s very fine, kawai bataso tafita daga jikinshi even for once second, shi kadai takeso taga tanama kuka yana kallonta dinnan even though bata tabajinsa ya furta sorry ba but the way yake lallashinta speaks sorry to her body, his looks are damn comforting sama da sorry or yakuri or even sannu, anytime yarike mata hannu she feels happy and calm is this love? Sannan bataso taga yafita wlh ko masallaci zaije saitaji wani iri batasan mesa ba kowa na gidan nan is her family ga Abba is Babanta ga Mamie gasauran su Yaya duk suna sonta but dukansu batajinsu kaman yanda takejin Ya Hamad, da kowa na gidan nan ya lallasheta gwara Ya Hamad ya lallasheta, idan kowa na nan Ya Hamadi bayanan she s not happy, ita kawai taita ganinshi agabanta.
Sauke idanunta tayi kan lips dinshi dasauri ta kulle idanunta bataso ta tuna jiya kwata kwata dan yanzu zataji jikinta yafara ciwo, so take ya kwanta yanda yake zaune jikin gadon dauke da ita yana bacci looks exhausting to ya zatayi ta kwantar dashi? Daddagewa tayi ita adole mai karfi ta kulle hannuwanta abayansa zata kwantar dashi ko gezau baiyiba saima dan bude idanunshi dayayi kadan cikin bacci ya kalleta da sauri tai wani rauuuu da idanu tace  ka kwantar dani ahankali cikin bacci kawai ya kwanto gadon tareda ita batare daya saketa yahau patting bayanta ahankali yana sauke ijiyan zuciya he loves sleep gaskiya most times idan yagama aikin dazaiyi a system bacci yake toh ba aiki garesa ba, sosai Asmeey ke kallonshi wlh dadi takeji yanda take jikinsa hannunsa abayanta yana shafawa kaman wata yar yarinya yana bacci murmushi tayi aranta tace  he s my husband kirjinsa tabi da kallo da wuyansa dan gashi ta hango dasauri tacire idanunta takai kusan good 1hour kallon mijinta takeyi ta kalli nan ta kalli chan kafin bacci yayi nasaran kwasanta ta kankamesa ahaka itama.

Wuraren 1 yashiga bude idanunsa da kyar yakalleta yanda suke rungume da juna yayi shiru how did he ended up sleeping ma baisaniba dan kunya yaji kadan irin shine haka with a girl ajikinsa, gashinta yabi da kallo da kitsonta yana calculating kwanakin kitson tun ana gobe salla kitson na neman 10days yanzu, taji sauki he will take her to the saloon ayi wani, gently yatashi yana zare jikinsa batare daya tadataba yamike tsaye yawuce bayi kafin yayi wanka saida ya wanke kayayykinta na bacci tsaf ya shanyasu ajan bayin yayi wanka fitowa yayi ahankali daure da towel a waist yadan kalli gadon ganin tana bacci yawuce ya shirya cikin wani soft matron yard yasaka hula yabude kofa yafito yana kamshi sosai, Mamie bata falo baiji muryan Gwaggo ba yauta tafi gantali kenan Hameed na wajen aiki sai yamma Mamie ce kawai maybe itama tana daki sallan zuhur wucewa yayi yafice, salla yayi yafito daga mosque yana takowa anatse kansa akasa zuwa gidansu yaga wata faran benz gaban gidansu anyi parking karasawa yayi yadauke idanunsa daga kallon motan daidai yazo gaban kofan gidan aka bude mota aka fito yarinyar ranan nan ne dasuka hadu da ita randa ya siyo laptop kallo daya yamata ya dauke kai tana sanye da Atampa gown yamata kyau yabi jikinta sosai da dan karamin mayafi a shoulder ta zai shige gidansu kawai tashiga gabansa ta tsaya jikin kofan dasauri tace  Hamad it s Aneesah oh daman itane Aneesah daketa damunsa da chat, kansa akasa cus he can t even look at her with the kind dressing dayake jikinta anatse yace  excuse me zan shiga gida muryanta na breaking tace  I& .i know& . Tayi shiru tana kallonsa kaman zata hadiyesa tace  I know is not proper nabiyoka har gida haka but narasa yanda zanyi kayi blocking dina a watsapp da calls, sometimes ko da bazakamin reply ba but naga ka bude message dina ka karanta shi kadai na kwantarmin da hankali wlh ina tsananin sonka tun rannan dana fara ganinka a hospital din Daddy ahankali tace  wlh I love you anatse Hamad yadan juya cus bama yason yanda take gabansa tace  inada mata she s enough for me kiyakuri hawaye Aneesah taji sunzo mata tarikesu da kyar tace  idan na roki matar taka fa! Wani kalan juyowa Hamad yayi for the first time yamata wani mugun kallo dayasa gabanta yafadi ta sauke kanta kasa da sauri yace  get your priorities straight! I have a wife Miss I belongs to her ita kadai I don t have any business with you, step aside yafadi adan zafafe, matsawa Aneesah tayi Hamad yashiga gidan yarufo musu gate, Aneesah tabisa da kallo hawaye na gangarowa daga idanunta tawuce mota tabude tashiga wannan wani kalan jarabawa ne? She has so many suitors masu sonta but hakanan daga ganin wani tech guy yazo yima Dad installing software a hospital shikenan? Da yaya ma tasami number sa da kyar manager Dad ya nemo number yabata dayaya tai tracking gidansu? Rannan nan tabiyosu daga wajen system din nan that plaza tabisu har asibiti taga yafito kam machine tabisa taga gidansu.

Komawa cikin gida yayi Mamie yagani a dinning ta ijiye abinci da kula a tray tana ganinsa tace  zoka daukan muku abinci karasowa yayi tace  this pepper soup na Asmeey ne zai rage mata ciwon cikin gyadamata kai yayi yadauka yawuce sama kofa yabude yashiga Asmeey is still sleeping ijiye abincin yayi he s hungry jiya baici wani abincn kirki ba white rice da stew yadeba kadan yakoma desk dinsa yafara ci yana taba system wayansa yakalla saiyasa hannu ya dauka watsapp yashiga yaduba block yaga number yafito wajen calls yaduba shima yaga block saiya juyo ya kalli Asmeey saiyayi shiruuuu sai kawai yayi murmushi yamaida wayan ya ijiye yacigaba da cin abincinsa.

Wuraren 2:30 ta farka baccin yamata bala in dadi yau dan motsi tayi hakan yasa Hamad yajuyo da kujeran ya kalleta saikuma yatashi yazo wajen gadon yadan kalleta suna hada idanu tasauke idanunta, mugun kunyanshi takeji tun jiya bata iya hada ido dashi dagota yayi tamike tsaye murya chan kasa yace  are you feeling better now ? Gyadamai kai tayi murya chan kasa na bacci tace  zansha coke Ya Hamad dan dariya kadan yayi yace  I guess this is the period carvings dana karanta dazu yayi maganan ahankali yana wucewa da ita bathroom nasu kayanta taga ya wanke akunyace ta sunnar da kanta ruwan zafi yatara mata a bucket sannan yafito drawer yaja yadauki ledan pad da pant yawuce nayin yasake knocking yabude ya ijiye mata komi yawuce yafita Asmeey tabisa da kallo he s so damn caring, he just knows everything.

Kusan 10min tabata abayin tafito tray tagani na abinci ya ijiyemata agado ga coke mai sanyi dasauri ta dauka coke din tana kokarin zamaya shigo hararanta yayi akunyace ta sauke kai magungunan ta ya dauka yabude su yazo gabanta ya tsaya ya mika mata karba tayi tasha da coke Ya Hamad kawai ya girgiza kai ganin she s in coke era yawuce ya zauna, pepper soup tasha taci rice itama kadan rannan haka suka wuni he was just taking care of her kaman kwai ko fita palor batayi ba all through rannan, Mamie ma saidai tazo ta gaidata daga kofa batare data shigo ba.
******


Bayan 4days

Yau day5 na MP!
Kwata kwata batasan tanada son bacci hakaba sai agidan nan ashe ta iya bacci, babu abinda takeyi wlh tsinke bata dagawa, Ya Hamad yajuyo gyara daki ya wanke mata kaya yamata guga yakaita bayi yahada mata ruwan wanka yafito mata da kayan sawa yakawo mata abinci yabata magani iyakanta, tai wanka tashafa mai tasaka kaya sai kyau take kara yi Ya Hamad yasayo mata wani cream mai kyau na Olay da shower cream dinsa, fuskanta ya warke tsaf kaman ba a taba marinta ba jikinta ma haka sai yan tabon da baza a rasaba, kullum tana daki especially this days kuma Ya Hamad bai kara mata komiba dudda baida magana baida yawan surutu but idan yana kula da ita is as if he s communicating with her.
Yau Saturday around 11:30AM ta farka Ya Hamad tagani gaban desk dinsa yakifa kai yana bacci murmushi tayi tashi tayi tabude wardrobe ahankali tadauki wani lace baby pink taciro yau kawai tanaso tayi gayu bayi tawuce dasu tai wanka ta shirya tsaf abayin tafito, cream ta shafa ta feffesa turare saita saka kwalli bata iya tasaka dan kunne da daura dankwali ba man baki tashafa taciro baby pink veil dinta tajuyo takalli abincin dake wajen bataso taci, indomie kawai takeso taci slippers ta zura tana gyara gyalen kanta tabude kofa tafice, ahankali take tafiya muryan su Abba taji a falo da yayinsu harda Gwaggo wani kunya taji kaman ta koma daki but tasan sun ganta hakan yasa tashiga saukowa kanta akasa, shi karan kansa Abba daya ganta saida yace  Masha Allah Asma u, kin fito ? Gwaggo tace  yau kwanan ta nawa gidan nan jibi yanda yarinya tai kyau jama a daman Asama nada kyau haka ? Hameed yace  ta ina zamu sani kullum muna ganinta da kumburaren kumatu da lips da jan idanu Mamie ta hararesa yayi shiru, karasowa falon tayi akunyace tana lullube bakinta da gyale tana murmushi tace  Abba ina kwana Gwaggo tace  toh mayafin zakisa abaki murmushi Abba yayi yace  lafiya lau yarinyana ya karfin jiki ya hannu ? Ahankali tace  fine Mamie tace  kinyi kari? Girgixamai Mamie kai tayi ahankali tace  indomie zanje na dafa Mamie tace  zaki iya dafa indomie da hannu daya konasa Lami ta tayaki dafawa ai tana kitchen ? Akunyace sabida yayinta tace  zan iya Mamie takalli su Ya Mustapa tana rufe fuska tace  Yaya ina kwanan ku duk murmushi sukayi Ya Mustapa yace  rannan Monday zakuzo asibiti za a bude hannun ayi xray agani gyadamai kai tayi, Ya Abdullah yace  Amarya anyi fresh dariya Faisal da Hameed sukayi tawani lullube fuskanta cikeda iskanci Faisal yace  mijin naki fa? Bata gane sarcasm dinsu ba hakan yasa da zuciya daya tace  bacci yake Yaya Hameed yace  wayyoo Allah na aure, Abba ai gobe ne zuwan ku gidansu Zee ko ? Dakuwa Abba yamai yace  kaci mai garinku Hameed Gwaggo tace  ahap na gayamaka idan baka aurar da takadirin nan ba saiya hanamu zaman lpy agidan nan Mamie takalli Asmeey tace  jeki dafa indomie ki gyadama Mamie kai tayi tamike tawuce kitchen har Gwaggo kallonta suke, Asmeey tayi kyau, tayi fresh sai sheki take, tawani kara kumari tayi haske ga fara a a fuskanta.
Gwaggo tace  wlh banyi nadaman wannan aure ba, aiko jiya Muhammadu Sani yakirani nake gayamai idan yaga yanda yarsa ta chanza zai rantse ba Asmeey bane toh babu mai dukanta kullum saidai naga Hamadi ya goyo wannan jakan katuwa ya sayawa matarsa kayan dadi yawuce sama baya sammin duka yayyin saida suka wani harari Gwaggo, Faisal yace  kaga Gwaggo da magana ke matarsa ce dazai sammiki ? Gwaggo tace  yoh to ubanwa ya haifi ubansa? Baniba tunda dai shine mukeda shi agidan nan mai mata ai kamata yayi yakawo kayan dadin sai nima asammini nasa albarka tashi Abba yayi yace  bari nadan kwanta yau natashi da ciwon kai duka yaran harda Gwaggo sukace  Allah sawake Abba wucewa yayi Mamie tabisa abaya yayyin suka cigaba da zama, ka ida rannan asabar tareda iyayensu suke zuwa suyi breakfast idan ba sunada wani abinyi ba basa bar1n gidan sai wuraren azahar.

Kusan 15min Asmeey tayi a kitchen tagama dafa indomie guda daya da boiled eggs guda biyu tarike Fanta mai sanyi a hannunta tafito daga kitchen ta ijiye a dinning Gwaggo tajuyo tace  bazaki kawo muci tareba aiko su Yaya suka mata chaaaa. Ya Abdullahi yace  wai bazaki bar kanwar mu tayi kiba ba? Faisal yace  kaga uban abincin dataci taci dumamen Abba, tasha shayi da bredi da kwai, ina kallo saida taci soyayyan dankalin Ya Doctor, takora da yoghurt
Gwaggo tace  nifa inzomin ko menene takirashi bantaba ci ba shine nakeso na gwada ci naji, mijinta yanda sayo mata shi kwali guda ni bai siyamin ba sabida bakin hali sonake na dandana wlh idan da dadi Hamadi saiya sayo tawa daidai lokacin akai knocking kofa Asmeey na kokarin zama a dinning da sauri ta kalli kofan, itane karama bai kamata tana falon yayyinta su tashi bude kofa ba besides ma tunda har akai knocking baki ne dan duk dan gida kai tsaye suke shigowa daki, fitowa tayi daga dinning zatai kofa Ya Faisal yatashi yace  koma kici abincinki I will get the door Kai tsaye yawuce kofan suna swalle Gwaggo yana kallo falon direct ya hangame kofan.  Ina yini duk suka jiyo muryan mace dayasa kowa yajuyo har ita Asmeey dake kokarin komawa dinning tajuyo, wata matashiya ce zata girmi Asmeey zatayi age mate da Ya Aysha akalla she s 25 ko 26 sanye dawani abaya black mai kyau hannunta rike da iPhone da handbag tadan kallo cikin falon idanunta suka sauka kan wata kyakkywan yarinya fara kaman baturiya sanye da lace tayafa mayafi ga gaban gashinta na showing anmata kitso kanana masu kyau, yanda ta tsare Asmeey da kallo yasa Faisal yace  helloooo lafiya wakike nema? Dan murmushi tayi kadan tana kallon Ya Faisal tace  sunana Aneesah! Hamad nake nema! Wani wawan bahaggon bugawa gaban Asmeey yayi taji zuciyanta kaman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login