Showing 24001 words to 27000 words out of 233624 words

Chapter 9 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2512

basason juna ba no they re united kawai dai wai wani cikinsu yasayo specific gift yabashi wlh basu tababa sai yau da Hamad yamai so abun ya mugun tabashi he was even speechless saiya kalli agogon saiya kalli Hamad da kanshi ke kasa, gently Hamad yaji Ya Mustapa ya rungume shi cikeda so yace  thank you Hamadi wani irin kunya ne yakama Hamad kaman zai nutse awajen yadan shiga komawa baya alamun ya sakeshi abinma sai yabama Ya Mustapha dariya, yasakeshi yakai hannu yadanja kunnenshi yace  even a hug from you big brother kunya ko kanshi na kasa har lokacin bai magana ba, Ya Mustapa yace  thank you Hamadi, nagode juyawa yayi da sauri yahau machine ya kunna yabar wajen Ya Mustapa yabishi da kallo harya fita daga gate na hospital na su, yasake kallon agogonshi yayi shiru sannan ya maida ya rufe yasa a jakan yawuce ya koma cikin hospital din.
Wuraren 2 yakai gida a falo yaga Gwaggo tanacin alalen gwangwani da akayi da sunkai guda 6 da manja ga kaji a gefe ga ruwa ga maltina na gwangwani tana ganinshi ta washe baki tace  oyoyooo Hamadi na yadawo, yaka zokaci abinci ga mamakinta saitaga yataho, yaune rana na farko datake kiranshi yazo Hamadi yazo, ta shiga mikewa da sauri tana wani Irin murna tace  bara na daukoma cokali tayi hanyar kitchen zama yayi yaciro gyalenta ya ijiye mata yamike, daidai Gwaggo na dawowa taga bashi awajen but ga gyalen awajen data tashi da sauri ta ijiye cokalin tadauki ledan gyalen tashiga warwarewa tace  menake gani haka? Hameeda zo zo zo taho yau danki yayi abun arziki Hameeda Gwaggo ta shiga warware gyalen Mami na fitowa daga bangaren Abba tazo Gwaggo tace  kinga Hamadi ya sayamin mayafin salla ni Madina oh dama yaron nan nada kirki da hankali haka dubi mayafin nawa fa sosai Mamie taji dadi tace  Masha Allah akashe lafiya Gwaggo Gwaggo tace  ni nasan Hamadi yayi kudi na more ba sauran gantalallun da matansu kadai suke kashema kudiba, jibi abinda yaron da baya aiki ya siyamin na salla banda ke dakika bani atampan codivowel, shikuma Abubakar yamin leshi da atampa gwara gwara likita yamin takalmi amman sauran ko hoda basu sayamin ba, kiga wannan gyale kaman wata Amarya da Hamadi ya sayamin ohh Allah, Allah ka karama yaron nan lafiya ka kuma bashi aiki sabida zamu huta, ahhh zamu huta Madina Mamie murmushi tayi tace  cinye abincin ki toh Gwaggo dasauri Gwaggo tace  hakane ungo linkemin ki maidamin ita cikin leda zanje namai godiya kinga ya sayamin mayafin amman kunya ya dingaji harya gudu banmai godiyaba linkemata Mamie tayi tawuce sama abinta takoma bangaren Abba tana hadamai kayansa tsaf ta gama tafito dakinta ta shiga saitaga yar leda kan gadonta dasauri tawuce ta dauka tabude taga sarka mai kyau da dan kunne da warwaro harda zobe, shiru Mamie tayi saikuma tafito kai tsaye tawuce dakinsu tabude kofa yana zaune akan gadonshi yabude system dinshi ya daura kan cinya yana dandannawa jin anbude kofa yasa yadago kanshi ganin Mamie ce ta maida kofan ta rufe tace  who asked you to spend money like this eh Hamadi? Sauke kanshi kasa yayi, Mamie tace  I ve seen yanda kai aiki for days on this project yauda kagama shine zakaje ka kashe kudinka kaida yakamata akara maka ma kudin so that you will establish something shine kake kashemana eh kanshi na kasa har lokacin baice komiba, shiru Mamie tayi tana kallon sarkan saikuma ta tako ahankali tazo wajen gadon ta zauna gefenshi tasake kallon sarkan ta kalleshi sai kawai taji hawaye sun zubo mata da sauri takai hannayenta tadaura saman fuskanta ta share, jikin Hamad yayi sanyi sosai ijiye laptop dinshi yayi a gefe yadan juyo yakalli Mamie dake share hawaye har lokacin fuskanta na nuna wrinkles kawai yau saiyaga Mamie shi tafara tsufa sai zuciyanshi yasake yin wani iri, murya chan kasa mai taushi da sanyi da nuna so yace  You ve done alot for me Mamie yadan sakeyin shiru kanshi akasa ahankali yace  I am always troubling you da rashin lafiya ahankali yace  you re always constantly worried sabida ni cikin kuka Mamie tace  shine aka cema ka you have to buy something for me? You have to repay me? I m your mother Hamad I don t need gift sabida kullum ina cikin dawainiya dakai, you re my son Hamadi, it s my duty to take care of duka yarana dan juyowa yayi yakalleta saikuma gently yakai hannunshi yadaura saman fuskanta ya share mata hawaye yace  don t cry Mamie hannunshi tarike tana kallonshi tace  promise me bazaka dinga kashe kudin daka samu a aiki hakaba save your money kaji, kai kadai ne baka da aiki, babanku karfin hali ne kawai baida jari yanzu, yayyinka nada iyali duk ta yanda zasukai ga kula dakai wata rana zasu gasa barinma idan yara suka fara tasawa, dama inada niyyan bayan salla zan saida gwal dina na baka saika bude cafe tunda ka iya abubuwa da computer ahankali yace  Mamie don t sell your gold, just pray for me I can take care of myself and you kinji gyadamai kai yayi sai kawai sai kawai ta rungumeshi yayi lamoo ajikinta, inhar babu kowa he accept hug din Mamie but da wani zai shigo dakin yanzu zai saki Mamie, sun dade ahaka sannan tadago shi ta kalli sarkan tana goge fuskanta tana murmushi sosai tace  nagode Allah yamaka albarka, Allah yabaka abinda kake nema, Allah yabaka nasara a ayyukanka Hamadi, thank You Hussaini, Allah yamaka albarka murya chan kasa yace  Ameen sabida baiso Mami tasani daga baya tamai fada yasa yace  I got wristwatch for Abba and turare for my brothers Mamie sarai tasan yana fada mata ne sabida kartazo taji daga baya tamai fada, dan shiru tayi chan tace  nawa aka biyaka for aikin dakayi? Ahankali yace  250k  nawa yarage yanzu? Dan shiru yayi chan yace  20k saikuma dasauri yace  inada wasu kudi a account shiru Mami tayi tana kallonshi chan ta shafa bayanshi tace  it s okay but next time kada ka kara kashe kudin aikin ka haka duk sun fika kudi sunada tsayayyan aikin yi mai albashi kaji gyadamata kai yayi, daidai an bude kofan dasauri yafita daga jikinta dudda haka saida Hameed yagani yawani zaro idanu yace  Mamie dama yaron nan na hugging naki ko gizo idanuna kemin dawani kalan sauri Hamad yatashi zai wuce bayi Hameed yashigo da gudu yarikeshi yace  so you can hug Mami Hamad amman ni baka taba bari nai hugging naka to wlh sainayi yau yataho zaiyi hugging nashi da sauri Hamad ya fizge kanshi yace  Mamie Mamie dake dan dariya tace  mehaka Hameed ka kyaleshi please dariya Hameed yayi yataho wajen Mamie tamikamai sarkan tace  kalli abinda ya siyamin yasami kudi duka ya kashemana murmushi sosai Hameed yayi yace  kafito daga bayi ina nawa? Yakalli Mami yace  ga Gwaggo chan takasa hayowa sama tana jiranku itama ta nunamin gyalenta Mamie tace  bari naje kuhada kayanku ku kuka rage yace  toh Mamie tawuce.
Fitowa Hamad yayi kana gani kasan wanka yayi but he s still wearing kayan daya saka dazu sabida damuwan Hameed bai bari yadauki wani kaya ba ko kallon Hameed baiyiba yazo wardrobe yadauki jogger da t-shirt yawuce yakoma bayi ya shirya tsaf yafito yajefa kayan daya cire a laundry basket sannan yazo Hameed yace  ina nawa Hamadi jakan shi yabude yaciro nashi ya bashi yaciro na sauran yayi shi ya ijiye a gefe Hameed was so happy with the perfume sai murmushi yake yace  tashi toh muhada kayanmu kwanciya kan gado yayi yace  I m tired hararanshi Hameed yayi yasauko da box nasu yahada musu kayan tsaf yasama Hamadi kayan zama gida da jallabiya guda biyu da turarukanshi duka ciki da takalman daya saya musu na salla da hula da agogo tsaf da sabulan wanka, yadebi few novels na Hamad ya samai, ka ida ne duk babban salla a Bauchi sukeyi 7days kuma sukeyi a Bauchi kafin su dawo, gama hadawa yayi yawuce shima yaje yayi wanka.
Around 9 yashigo gidan daga mosque Abba yagani zaune kan carpet ga kwalin agogon daya siyamai ga Gwaggo gefensa akasa ta kishinguda da gyalenta amman bacci ya kwasheta tsaresa da idanu Abba yayi ahankali yace  sannu da dawowa Abba murmushi Abba yamai yace  zonan Hamad karasawa wajen Abba yayi ya zauna ahankali, Abba ya kalli agogon saiya kalleshi yace  naga abinda ka siyama kowa harda ni Allah yayi albarka, kaima Allah yasa naka yaran su maka abinda yafi haka sannan Allah ya sanyama hanyar nemanka albarka, Allah yakawo tsayayyen aiki gyadama Abba kai yayi murya chan kasa yace  Ameen Abba yatashi yawuce sama Abba yasake binshi da kallo sannan yakalli agogon kafin yakalli Gwaggo dake munshari.

Around 7AM Ya Mustapa yazo gidan da matarsa da yaransa biyu Areef and Arfat, shima Ya Abdallah yazo gidan da matarsa da yarsu Amra tasha lalle ta tafi wajen Mamie da gudu tana nunama Mamie lallinta saiga Ya Faisal shima da matarsa ita har yanzu bata haihuba duk suna falo an gama loda kaya tsaf, Hameed ya sauko yana sanye dawani ash color yadi mai kyau Abba dake wasa da jikokinsa yace  Ina Hamadi? Shikadai ake jira  gashinan zuwa Abba shiryawa yake gyadamai kai yayi, Hameed yazo ya zauna abinshi bai gaida kowa ba, kusan 10minutes saiga Hamad yana saukowa yana sanye da ash color yadi exactly irin na Hameed sai kamshi yake, yadin yamai bala in kyau bambamcinsa da Hameed is just eyes, idanun kwalli garesa and it s so obvious kansa akasa anatse yake tafiya daidai cikeda kamala da natsuwa kuma, ya shigo cikin falon calmly yazo gaban Ya Mustapa da matarsa ke zaune kusa dashi kanshi akasa yace  ina kwana Anty murmushi tayi sosai tace  Alhamdulillah Ya Hamadi ya karfin jikin an warware ko gyadamata kai yayi yatako zuwa gaban ya Abdallah kanshi akasa anutse yace  ina kwana Anty cikeda so tace  lafiya lau Ya Hamad ya jiki bai amsaba yadai gyada kai takawa yayi zuwa wajen Ya Faisal yace  ina kwana Anty kanta tasauke akasa cus Hamadi ya girmeta she s just 25 amman baida girman kai tace  ina kwana Ya Hamadi kasa amsawa yayi yawuce gently kusada Mamie duka yayyinshi na binshi da kallo ya zauna, Gwaggo tashigo taci gayu wani bubu da zani da mayafi tasaka na hadari lace tace  mutafi yaufa jajubari akwai go slow tashi Abba yayi kowa yatashi aka fito Mamie takashe wutan kowani daki ta tofa addu a duka kulle gidan aka shishiga mota
Abba yaje yana sallama da mai gadi yabashi makullin gida da kudade da motoci hudu sukai tafiyan motan Abba sai motan Ya Mustapa Ya Abdallahi Ya Faisal, motan Abba Hamad ya shiga gaba kusada dreban Abba, Abba da Mami suka shiga baya, shikuma Hameed ya shiga motan ya Faisal, Gwaggo tashiga motan Ya Mustapa suka wuce.
**
Bauchi

Shigowa gidan Munir yayi su Yusra dasu Amina da Ya Ramla duk suna kasan bishiya da aka shimfida babban tabarma ga masu kitso da masu lalle duka ana musu, ga yaran maza da anriga an musu aski sai wasa suke a tsakar gida Ammi sai up and down take itada masu aiki a backyard ana soye soyen su cincin da kuma girki sabida su Kawu da Abba dazasuzo yau everyone looks happy the only person dabai gani ba is Ya Asmeey wucewa yayi ya shiga flat dinsu babu kowa a falo banda tv dake aiki dan duka yaran suna waje staircase yashiga hawa dakinsu Asmeey yawuce yabude kofa bata ciki hakan yasa yarufo kofan yayi jimm cus yasan tana wajen Mom wlh ranan nan dayace he wish Ammi ce mamansu bawai karya yayi ba cus look at yaranta they re so happy anachan ana musu lalle suna tsalle tsalle a compound haba gobe salla fa at least tabar Asmeey amata kitso da lalle like every other gurl but no itama tafito tayi aiki she s too big tayi Ammi ke handling komi, kullum Asmeey sai ramewa take duk tayi zuru zuru sabida jaraban Mom he called Ya Aya da Ya Aysha akan suma Mom magana tadan sassautama Asmeey but sun kasa kowa tsoron Mom yake ga Baba baicika zama ba baimasan wat is going on ba sai wanda yagani akan idanunshi, ahankali yawuce side din Mom kofan yabude babu kowa a falo sai tv dake aiki falon na kamshin turaren wuta tafiya yashiga yi yana shiga corridor dazai sadashi da bedroom din Mom yaji muryan Mom na bala i.  Kin kosan how important this property law practice yake a law school? Are you dumb da kin kasa iyawa so nawa zan koya miki? See Asmeey idan kika fadi bar exam dinki just die kafin kizo ki sanar dani kin fadi, what is so difficult about property law practice when kinada all materials duk abinda za a muku a law school na zaunar dake ina koyamiki did you know how lucky you are? Wlh kika karamin shirme sai ranki ya baci give me requirement din ina jinki muryan Asmeey yaji baya fita sosai and it s even shaking cus bayajin ma abinda take fadi wani irin yaji zuciyansa yamai har wani daci daci yakeji juyawa yayi ahankali zai tafi sai kawai yaji karan saukan mari dakuma buguwan abu Mom tayi ihu tace  idan bazaki iya zama ni ki gajeni ba just die Asma u dan banga amfaninki a doron kasa ba wajen kofan Munir yayi da sauri zai bude yakasa sabida tsoro yakafa kanshi jikin kofan yanajin kukan Asmeey kasa kasa sai kawai yajuya da sauri yabude kofa yafita ta nan window sama ya hango motan Baba alamun yadawo hakan yasa yayi hanyar dakin Baba kai tsaye yabude kofan baima tsaya sallama ba babban falo ne sosai mai bala in kyau Baba na zaune kan kujera ko takalmi bai cireba magana yake awaya yana sanye da faran shadda ganin idanun Munir sunyi ja yasa yace  Yaya saikun iso Allah kiyaye hanya bari na kira Kawu katse wayan yayi yakalli Munir yace  menene Munir ? Tahowa wajensa Munir yayi yana kokarin magana sai kawai yakasa yafashe da kuka cikeda damuwa Baba yace  Munir what happened meya faru ? Ina Munir yakasa magana, Baba yadagosa yace  Munir menene ? Da kyar ya tsagaita kukan yana wani irin nishi na zuciya in a very childish way yace  Baba banso ace nayi gulman mahaifiyata ko ace nafadi wani abu mara kyau akan Mahaifiyata, Baba just save Asmeey sabida idan wani abu yasameta Baba harkai sai Allah ya tambaya ni shikenan abinda nazo na gayamaka yana maganan ya fizge jikinshi daga na Baba ya ruga da gudu yafita daga dakin Baba ya tsaya looking confuse ya bisa da kallo yana maimaita kalaman Munir yakai kusan 2min ahaka sai kuma yamike, fitowa yayi daga dakinshi yabude dakin su Asmeey dake next to him but babu kowa adaki sai kawai yashiga sauka daga bene cus his believes Asmeey na waje, su Ammi da Mom na backyard suna girki yana sauka kasa Ammi na fitowa daga kitchen yace  Asmeey na wajen lalle ne? Da zuciya daya Ammi tace  a a bata waje ai tun safe datazo gaidani takoma sama ina ganin tana dakin Mamanta dasauri Baba yace  Salima bata tareda ku wajen girki ne gyadamai kai Ammi tayi tace  eh tana sama bata sauko ba inaga wani abun suke Baba ji yayi ranshi yabaci sosai sai kawai yajuya yakoma sama Ammi kuma tawuce tafita falon Mom yabude but bakowa ciki but yana jiyo muryan Mom daga ciki tana banbami, kai tsaye bude kofan dakin yayi dadan sauri Mom tajuyo ko kadan bata dauka yanzu Baba zai dawo ba sai chan anjima chak Baba ya tsaya yana kallon Asmeey dake zaune akasa gaban Mamanta ga uban files da manyan textbooks agabanta gadan jini daya gani gefen lips nata which yana shigowa akan idanunshi yaga tagoge da sauri but bata dago kai ta kalleshi ba, tashi Mom tayi tana sauke littafan dake kan cinyanta tace  Alhaji kadawo ko kallonta baiyiba idanunshi nakan Asmeeey yace  Husna dan dago kanta Asmeey tayi takalli Baba tareda kakalo murmushi asanyaye tace  Baba sannu da zuwa wani irin faduwa gaban Baba yayi ganin idanun yarinyar sunyi jaa gashi kuncinta shaidan hannu dayayi ja abunka da fara lips dinta yadan kumbura Mom takalleta tace  Babanki na kiranki kitashi kin zauna dasauri tace  toh kokarin tashi tashugayi kafafunta sunyi sanyi sai Mom tashiga gaban Baba ta kareshi tana murmushi tace  muje falo ta biyomu an kawomin kayan sallan dana maka muje kaga dinkin ko motsi Baba baiyiba kokarin kallon Asmeey dake kokarin tashi yake Mom tasake kareshi takai hannunta takama nashi tace  muje kagani fizge hannunshi yayi yamata wani kallo yace  don t touch me yawuce gefenta yaje wajen Asmeey data tashi, ahankali yakai hannunshi yakama kuncinta yana kallon wajen strictly Baba yace  meya sami fuskanki yayi ja haka washema Baba baki tayi tace  faduwa nayi dazu Baba boyayen ijiyan zuciya Mom ta sauke, Baba yace  to me kikeyi anan bakije kinyi kitso ba zo muje riketa Baba yayi yasata ajikinshi yashiga tafiya da ita ahankali sukabi ta gefen Mom suka fice dakinshi yawuce da ita kan kujeranshi ya zaunar da ita yawuce fridge dinshi yabude laban yadauko me sanyi yakawo mata yabude yabata ta amsa tana murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login