Showing 159001 words to 162000 words out of 233624 words

Chapter 54 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2525

I will talk to him ahankali Mamie tace  kaikuma yaushe zaka dawo? Murmushi yayi yace  kewana kike ne Mamie na dan shiru tayi idanunta na tattaro hawaye ahankali tace  ina kewanka sosai Mustapa baka ba Hamadi, sai marasa jin nan kuka barmini Oga Hameed da Faisal, dama dama ma Abdullahi dan dariya yayi yace  awwwn nima ina missing Mamie na sosai, this week zan dawo kinji so don t cry again, clean those tears hannu tasa ta goge fuskanta tass tasauke ijiyan zuciya Ya Mustapa yacigaba da hira da ita har tadan warware kafin suyi sallama yana murmushi Mamie na son dukansu Matar akwai big heart

Haka rannan all through Asmeey ta wuni ko abincin kirki bataci rannan ba sabida ciwo bawai zazzabi takeba kawai batajin dadin jikinta zuciyanta kawai tashi yake kome takai baki saita amayar wuraren 10 daga Abba har Mamie sukabar dakin bayan sun dubata sunyi kusan awa daya tareda ita, Suna bar1n dakin saitaji kaman duk wani ni ima na dakin sun tafi dashi duniyan yamata zafi wayanta ta dauka ahankali jikinta yayi wani sanyi tai dialing number Hamad yashiga wayan unlike other day yanata nuna mata ringing amman harya gama ringing bai dauka ba sai kawai zuciya taji yakawo mata wuya she can t hold it any longer kawai ta shiga typing message.
Zaka iya kirga yau kwana na nawa baka kirani ba? Talking to me is a waste of time ko? I m no longer in your agenda, you have a busy schedule which your wife don t happens to be among Mr Hamad! Shikenan dagayau bazan kara kiranka ba bazan kara daukan wayanka ba kuma Allah ma yaciremin tunaninka nima nahutama rayuwana dan banga amfanin tunanin wanda shi baya tunani na ba he can go days weeks without talking to me idanma wata kagani kanaso achan kuyi aurenku nina hakura.
Asmeey ta tura message din tana vibrating sosai zuciyanta namata zafi saitaji dakin ma is hot for her all she wants is inda za a mata surutu sai kawai ta taso ta dauki hijab ta sanya tareda bude kofan ta ahankali tafito tasauko kasa dakin Gwaggo tawuce tabude kofa ahankali Gwaggo na kampatsa uban hamma tana magagin bacci taga mutu dasauri tace  wayyoo akufule Asmeey tace  nice kekuma tashi Gwaggo tayi tana chanza wutan dakin zuwa mai haske Asmeey tawuce tazauna bakin gado Gwaggo tace  lafiya? Ubanme kikazo yimini a daki kallon Gwaggo tayi cikeda masifa tace  kice nafita nafita mana ganin masifa Asmeey keji yasa Gwaggo ta taso tareda rike baki tace  ke diyar yar boko waya gabaki gayamin gaskiya banza tama Gwaggo tahau gadon tashige ciki tai kwanciyanta, murmushi Gwaggo tayi saita taso takama hannunta tanamata tausa tace  kece kibini muje unguwa baki zuwa kullum kina gidan nan ai sai cuta ta kasheki bakiga ko ciwon kai banyi ba, ina zan zauna gida babu kananun yara sai randa marasa mutuncin nan suka ga daman kawo mana Areef zasu kawo shima Abdallah haka gashi sai gayu suke sun tsufa basuson su hayayyafa, bari kiji Asmaa kina haiho wannan kafin shekara ta zagayo ki haiho na biyu ba a bata lokacin yanzu kiyi kigama saikiga kin tsufa da kyanki bakiga Mamie ba yanzu kaman ba ita ta haifi gardawan nan ba Gwaggo tace  yanzu dai gobe zaki bini muje makota daman za ayi bikin diyar Hajiyayye sunanta Firdausi kinga yarinyar akwai rashin kunya da tsiwa kaman ke ki shirya muje gobe kinji zakije? Gyadamata kai Asmeey tayi tace  eh zanje Gwaggo Gwaggo tawani kwashe da dariya tace  ko kefa inada fura nabaki kisha tasowa zaune Asmeey tayi tace  bazai sani amai ba? Inata amai yau Gwaggo Gwaggo tace  gwada sha mugani yar fridge nata na dakin tabude tacirowa Asmeey guran aiko Asmeey tasha sosai yayi sanyi tabalain jin dadinsa tanasha ta lapke sai bacci Gwaggo ta gyara mata kwanciya tana rufa mata bargo tace  ke bakisan nafi kowa dadin zama ba da kin lapke chan baki zuwa wajena yanzu zaki gane nine nafi kowa dadin zama Allah dai ya saukeki lpy, Allah yamuku albarka keda Hamadi

Rabon da Asmeey datayi baccin daya mata dadi harta manta sai yau ko harda huran data sha ne haka ta lapke Gwaggo tai juyin duniya Asmeey ta tashi da asuba tai salla takasa wuraren 5:30 arude Mamie tazo dakin Gwaggo ijiyan zuciya ta sauke ganin Asmeey na bacci a dakin Gwaggo ta sallame salla tace  kaman yarnan irin laulayinki ta dauko mai fitina jiya datazo ta tasani agaba harna fara bacci fa saida natashi nabata hura dan murmushi Gwaggo tayi tace  tafi abinki zan tada ita anjima kadan tai salla, masu ciki nada uzuri dan Allah juyawa Mamie tayi tafitoo around 6 Asmeey ta tashi mikewa tayi tashiga bayin Gwaggo tayo alwala tazo tasaka hijabi tai salla tana idarwa tai azkar tasake komawa gado sai wajajen goma Gwaggo ta daka mata duka tace  wai bazaki tashi mutafi biki diyar Hajiyayye ba tashi Asmeey tayi ahankali tana shafa inda Gwaggo ta daketa tace  bari naje nai wanka tawuce tafito saita wuce kitchen Mamie na magana da mai aiki she woke up good yau kawai saita rungume Mamie tace  Mamie ina kwana, Mamie zanbi Gwaggo muje biki layinsu ne bikin just 2house tsakaninsu ko itama zata shiga bikin sai zuwa anjima amman hakan yasa Mamie tace  tom kije amman jeki wanka sai kizo kiyi kari gyadama Mamie kai tayi tasaketa tawuce tafita Mamie tabita da kallo shes not happy with yanda take raman nan sai duwawu datake karayi da nono shikenan da hasken fata, sama Asmeey taje tafada bayi brush tayi wanda saida tai yellow amai ta lallaba tai wanka tafito daga bayin wayanta data bari dakin na ringing wucewa tayi wajen gado ta tsaya tana kallon wayan Hamad ne hararan wayan tayi tawani juya dudda zuciyanta namata tadauka but tayi alkawari zata daure.

Wani lace mai bala in kyau sky blue taciro ta zaro sky blue gyale ta shirya tsaf tayi makeup sosai tasa dan kunne ta fesa turare tadauki handbag tazo tadauki wayan datake harara ta jefa ciki tadauki car key kuma da motanta zataje tafito Gwaggo da Mamie kallo suka bita da shi Gwaggo tace  yau naga abu Asama bikinki sai ashirin ga watan gobe wannan gayun ai saikifi Fiduh kyau Mamie tayi dan murmushi tace  zoki kari zuwa tayi ta zauna Mamie tabata tea sai waina da pepper soup tea tasha tasha pepper soup ko waina daya bata tababa tana gamaci ta mike tace  muje Gwaggo tashi Gwaggo tayi tace  saikin shigo Hamida Asmeey tace  Mamie bye bye dan zuwa is wajen Mamie tayi saita karbi gyalen Asmeey ta yafamata daga saman kai tace  saikin dawo
Suka wuce suka fita Mamie takoma kitchen ga mamakin Gwaggo wajen motanta Asmeey tayi tace  Gwaggo da mota zani nagaji ban iya tafiya Gwaggo tace  nan da nan Asama ni zaki kashe bari kiji banda motar Doctor babu motar wanda nake shiga agidan nan hakanan ku kasheni bude mota Asmeey tayi tace  nidai natafi Asmeey ta tada motan tana murmushi tai reverse ta juya Gwaggo tasaki baki Asmeey tai gate abinta mai gadi yabude Gwaggo tabita da kafa tana fita waje tamaga gidan bikin danga mutane awajen saita wuce wajen tayi parking a layin motocin wajen tana jiran Gwaggo takaraso ga maza sosai awajen sai bin motanta ake da kallo thank God tinted ne, Gwaggo na zuwa wajen ta tsaya Asmeey tabude kofan ahankali tafito tanama Gwaggo dake hararanta murmushi sunyi wani irin kyau tace  bakene kikaki shiga ba rufe motan tayi Gwaggo tasa hannu tawani kama hannunta tace  muje ina rike da ke kafin ki bata sukai gate din ana kallonsu ahankali sukaji ance Gwaggo. Dasauri Gwaggo tajuyo ganin wani matashi sanye da manyan kaya farare masu kyau da zaiyi tsaran Hamad yasa Gwaggo tace  Aliyuuuuuuu! Aliyuuu gizo idanunta ke mini dan murmushi yayi yace  nine Gwaggo Asmeey kuma tajuya abinta tana kallo cikin gidan inda yanmata ke rawa DJ nasaka kida, murmushi yayi yana satan kallon Asmeey yace  ina kwana Gwaggo daidai nan Asmeey ta fizge hannunta daga na Gwaggo tai cikin gidan, Gwaggo tace  kika bace baruwana Aliyu yabi Asmeey da kallo yace  wacece ita Gwaggo yaushe Mamie ta haifi mace ? Dariya Gwaggo tayi tace  yar wajen Muhammadu Sani ce, yarona na biyu dake Bauchi Aliyu ya gyadakai yana kallon Asmeey dahar taje ta zauna akan kujera tana kallon Amarya sa masu rawa, Gwaggo tace  kaga bari naje Gwaggo ta wuce cikin gida tace  ga Gwaggo gaGwaggo dagudu Fidduh tawani rungume Gwaggo suna rawa zokaga yanda aka zagaye Gwaggo Asmeey tai shiru tana kallonsu tana murmushi dole Gwaggo tadinga gantali sonta ake sosaitazama Gwaggon kowa da kowa, ringing wayanta yashiga yi ba kakkautawa dasauri tabude jakanta taciro wayan Ya Hamad ne ke kiranta, amman taki dauka harya katse yana sake kira taki dagawa harya katse yasake kira na uku saitai wani murmushi dadi na lullubeta ashe yadamu ta duba from jiya zuwa yanzu yamata 23missws calls, ganin he s still calling and zuciyanta na gayamata bazai hakura ba saita amsa yasa tamike tai waje tana tafiya ahankali tafito tabude motanta tashiga daidai yana sake kiranta this time video call hade fuska tayi tasa hannu ta dauka taki kallon screen dinma dan bataso ta kallesa zuciyanta ya karaya, ijiyan zuciya Hamad ya sauke ahankali yana zaune kan gado dagashi sai wasu fararen pajama masu kyau da farin hulan sanyi akansa, duk yayi wani iri kaman ma baida lafiya, binta yayi da kallo da motan datake ciki da gayun datayi calmly cikin voice dinsa mai bala in dadi yace  kina ina! ? Ya Allah! Wani irin faduwa gaban Asmeey yayi jin calm sweet voice nasa datai missing for days har lokacin taki kallon screen din wayan kai tsaye cikeda jin haushi da fushi tace  biki! Saikuma cikeda jin haushi yanda dai mata keyi idan sunaso sukai maza bango tace  biki nazo shiru Hamad yayi yana kallonta ranshi ya bala in sosu cus bikin nan ba a tambayesa ba, baisan da bikin ba, baimasan nawaye ba but takama ta fice and look at yanda taci gayu da gyale on her shoulders ana ganin gashinta ta keya sosai data gaban kan ga kirjinta a bude dan bata rufe chest nata da mayafi ba, danne zuciyarsa yayi yace  kin sanar dani about bikin nan? Bikin waye? Wa kika sani? Waya baki izinin fita Asma u? Juyowa Asmeey tayi ta kallesa cikin ido cikeda masifa zatai magana akai knocking motanta dasauri ta juya ganin mutumin dazu yasa aranta tace  ko Gwaggo ta aika anemota ne da sauri ta birkito hakan yasa wayan hannunta ya karkace shima Hamad was able to see d glass ya hango wani a tsaye Asmeey ta sauke glass kasa da sauri ta kallesa Aliyu dabai lurada wayan ba at all yace  wat are u doing a mota ke kadai Pretty? Wani iri Asmeey taji kafin tace  wani abu yana mata wani kallo bayama iya boye yakam1 yace  Gwaggo ke nemanki but tunda kina mota bari naje nagaya mata ko gyadamai kai tayi ya juya Asmeey taja glass din sama hakanan kawai saitaji gabanta yafadi tana addu a Allah sa Ya Hamadi baiji ba tajuyo ta kalli wayan wlh yanda taga fuskansa saida gabanta yayi mummunan faduwa but ta dake takuma ki magana saima sauke kai tayi daga kallonsa, da kyar Hamad dayakeji kaman zai mutu yace  na barki agida baki tambayeni ba kifito kizo wani biki God knows where har maza na miki magana calling u pretty Asma u!
Itama Asmeey cikin fushi tace  na mutu acikin gida kakeso? Ka kamani ka kulle banda saloon bana zuwa ko ina kiran mutum bakayi how many times nake kiranka baya zuwa? The ones that I m lucky wayan ya shiga kuma dauka kakeyi? Ai kaima u are there Allah kadai yasan how many women surround you tunda kazama crush din kowa why would you complain dan wani yamin magana kai mijin nawa kamin ne! ?
EPISODE 8?? 0??




Asmeey tai maganan cikeda tsiwa zuciyanta na tafarfasa tace  kuma duk wanda yamin magana saina amsa dan kaji, ai kaima kana amsawa har shaking hannun mata kanayi yanzu! Kuma nima I will shake duk wanda yabani hannuns& &   Asma u! Hamad ya daka mata tsawan da saida ta firgita yace  nabaki one minutes kiwuce ki koma gida ko ranki yabaci! Dudda ta firgita da yanayin data gansa amman ta daure tace  ni biki nazo ba yanzu zan koma ba wani iri sosai Hamadi yaji yace  shikenan ki koma ki cigaba da hira dashi a wajen bikin cikeda tsiwa tace  eh zan koma mucigaba at least yafi wanda baya kirana tunda yaje wani gari, kuma karka kara kirana ta katse wayan jikinta har rawa yake sabida masifa da bacin rai ta kifa kanta akan kujera sai kuma taji ranta yabaci kawai tafashe da kuka ta tada motan tana reverse tajuya tawuce gida tai horn aka budemata, shiga gidan tayi tai parking takashe motan ta kifa kanta a sitari tafashe da kuka sosai kaman zata kama da wuta takeji.

Hameed na zaune tareda su Ya Mustapa a estate dinsu wanda anyi like 60% of work done yahadu wayansa ya shiga ringing ganin Hamad ne yasa yadauka yace  what happened 2days kennan ina kiranka baya shiga are you okay? Duk mun damu ahankali yace  I was in the hospital please don t tell Mamie and Asmeey dasauri Haneed yace  hospital meya sameka? Tasowa yayinsa sukai da sauri hakan yasa Hameed yasa wayan a speaker, dan shiru Hamad yayi ahankali yace  I had one food I got food poisoning dakuma allergic reaction ance banso habanero pepper and I have cold also sanyi jikin Hameed yayi yace  ya jikin yanzu? Ahankali yace  I am good this morning nadawo gida don t worry gyadamai kai Hameed yayi duk yayi wani iri, murya chan kasa Hamad yace  kana ina? Ahankali yace  ina site tareda Ya Abdullahi da Ya Faisal bakaga gidanmu ba sai kyau yake gyadamai kai yayi ahankali yace  kasan wani wedding Asmeey taje? Dasauri yace  wedding Asmeey! Wata sani? Wani wedding zataje kodai wasa take? Girgiza kai yayi muryanshi na breaking yace  no she went to a wedding but I think da Gwaggo take tare dasauri Hameed tace  ohh right gidansu Aliyu ne fa Neigbours dinmu ahankali Hamad yace  one& one& .guy is calling her pr& ..etty& .. saikuma yakasa karasa maganan sabida yanda zuciyansa keyi, anatse Hameed yace  okay bari naje but common Hamadi don t get worked up like this mana, probably is just a random guy daya ganta wajen biki, kace mata takoma gida ijiyan zuciya ya fuzar muryansa na dan shaking yace  she s not listening to me! She s angry with me! Hameed yace  Hamad please don t cry I know how it feels& . Murya chan kasa Hamad yace  tace she will talk to duk wanda zai mata magana since ni bana mata&  voice dinsa na cracking dayasa anatse Hameed yace  Hamadi nasan bani yakamata na sanar dakai this ba daman ance saika dawo but kasan Asmeey has been in and out of he hospital kuwa! ? Wani irin faduwa gaban Hanad yayi, Hameed yace  2days da tafiyan ka she got seriously sick Ya Musty managed her, and yau duka duka yaushe ma aka sallameta Ya Faisal? Faisal yace  3days ago ahankali Hameed yace  baka kiranta bata da friends bata fita is not easy plus she s pregnant kuma wani irin bugawa kirjin Hamad yayi bakinsa yashiga rawa yace  she& & she& ..she s w& .at? Karban wayan Faisal yayi yace  toh dan iska ance she s pregnant, ciki ne da ita, ashe kunyi coitus Hamad? So ka iya komi harka durama yar mutane ciki before kabar kasan ? Dip Hamad ya katse wayan feeling extremely happy yana kokarin kiran Asmeey kiran Ya Mustafa na shigowa wayansa dasauri yadaga yace  Yaya! Dama Asmeey is uhnnnnnn ? Yakasa maganan sai wani murmushi dayake mai sauti da Ya Mustapa yaji yace  she was unconscious 3days ago da aka kaita asibiti aka ga she s pregnant 8weeks but tanada Malaria she was there for a day wani irin murmushi Hamad yayi yaji ya warke daga duk ciwon dayake ji, kawai ya ijiye wayan ya sauka yayi sujjada just now fa he was angry but this news flushes out the entire anger daga jikinsa yadauki wayansa yasa a kunne Ya Mustapa yace  Mamie called me and complained about you not calling matarka Hamadi why? Shiru yayi ko kafin yayi rashin lafiya baya kira sosai saikuma ciwo yahadunmai ahankali yace  Yaya zan chanza dagayau I promise you I was sick ne Ya Mustapa yace  meya sameka? Ahankali yace  is just allergies sai cold anatse Ya Mustafa yace  mekaci ahankali yace  pasta awani ittalina restaurant Murna yasa yace  Yaya can I call u back? Gyadamai kai Yaya yayi yace  okay wayan Asmeey yakira but baya shiga yakira normal call but wayan akashe saiya kira Mamie, Mamie na shirin fita tadauki wayan tace  Hamadi murmushi yamata yace  Mamie ina Asmeey wayanta baya shiga? Mamie tace  yanzu taje ta kwanta da fita zanyi bari na bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login