Showing 66001 words to 69000 words out of 233624 words

Chapter 23 - UWA KO UKUBA COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

2532

ba yace  kije takarasa karya dayan hannunki duka kinga saiki huta shiru tayi bata sake cewa komiba kanta na kan pillow tana kallon wayansa tashiga lumshe idanu ahaka bacci yayi awon gaba da ita.

Sai wajajen 11 nadare yashigo gidan kawai dan kar ace this and that ne da yau yakoma Kano sabida kunya shigowa gidan yayi yahayo sama zai shiga dakinsu Abba yace  Hamad dago kansa yayi yasauke yace  na am wucewa yayi gaban dakin Abba daya shiga yabisa abaya Mamie na zaune tana kallon wani shiri da akeyi a tv takalli Hamad din daya kasa kallonta kasa akasa yace  Mamie ina yini  sannu da dawowa Mamie ta fadi, Baba yadauki bandir na 1k din yadago yace  gashi dazu Baba yazo nemanka yabaka bakanan, sadakin Asmeey ne karike mata idan tadan sami lpy saika bata lokacin muna kano kallon kudin yayi saiya kasa karba yasake sauke kansa kasa Abba yace  ha a wai ba sako nake baka ba koko cewa nayi kudin naka ne? Kudin matarka ne karba kaje ka ijiye yana ahaka kansa akasa kaman mai tsoro yadaga hannuwansa yamikama Abba duka biyun yakasa dagokai saura kadan Abba yayi dariya yasamai kudin a hannu Hamad ya karba kaman flash yajuya dasauri yafita daga dakin, dakinsu yawuce ahankali yabude kofan bakaramin dadi yaji dayaga Hameed na bacci ba shigowa yayi yamaida kofan yarufe yatafi wajen akwatinsa yaduka yasaka kudin achan kasa sannan yatashi yafada bayi yafito yahau kan dadduma sannan yadawo gadon ya kwanta yayi shituuuu ahaka bacci am yayi awon gaba dashi.

Surutun Gwaggo ma yau yasake tadata daga bacci bude idanu tayi ahankali Gwaggo na saman kanta tana tafamata uban yawu a hannu wai addu a take dauke hannunta tayi tana turo baki Gwaggo tace  bazaki bari nagama miki addu a ba bakiga kin denajin zafi ba ahankali tace  ni har yanzu zafi yakemin baki Gwaggo tasaki tace  ahhhh lallai kin dace da Hamad dan bakin halinku daya Asama, ohh ni Allah baya amsan adduata kenan ko bakina baida tsarki tashi tashigayi Gwaggo tace  wai bazaki zauna najarasa ba ahankali tace  ni fitsari nakeji tawuce bayi Gwaggo tabita da kallo tace  hartadan fara kumari zaki iya tsarkin da hannu daya konazo namikin tsarkin? Juyowa Asmeey tayi ta kalli Gwaggo tace  huu um Gwaggo ta kwashe da dariya tace  ai shikenan jeki abinki nima daman nayi maganan ne amman ina tunanin warin dazan shaka idan kin hada da kashi maida kofan tayi dasauri ta rufe tafito da alwala tazo tahau dadduma ahankali take salla da hannun.

Yauma haka aka wuni agidan Hamad baya nan only God yasan ina yake zuwa ansan he will definitely do that so babu wani cikin bothers dinsa daya nemesa.
Yau all through Gwaggo na dakinta hakan yasa Asmeey takasa zuwa wajen Mom but zuciyanta na zuci zucin tunanin Mom, sai bayan Isha i Gwaggo tasa Mamie takamata ta kaita kasa dantai bacci da asusuba zata tashi tahada kaya tunda Allah baiyi zuwansu kauye ba sabida ciwon yarnan Asama.
Sallama Baba yayi hakan yasa Asmeey tadago kanta ganinsa yasa tashiga kokarin tashi dasauri Baba yakarasa wajen gadon yakai hannunsa yadagata yana saka mata pillow abaya yace  sannu ya jikin ? Ahankali tace  dasauki Baba zama yayi bakin gadon yana facing nata yakai hannunshi ahankali yadauki hannun nata da aka kulle yana kallo yayi shiru fuskanshi yayi wani iri kasan he s hurting hakan yasa gently Asmeey tace  Baba bayamin zafi yanzu wlh dan kallonta yayi har yanzu fuskanta bai dawo daidai ba kana ganinta kasan taci duka wlh, sai yaji kaman Allah zai kamasa for all the pain she went through, Asmeey is the most beautiful daughter dayake dashi mai kyawun hali da hakuri da biyayya she s going through this pain duk baisani ba and yana gidan, ijiyan zuciya ya sauke yace  mesa baki sanar dani kalan dukan da Mamanki ke miki ba ? Dan zaro idanu tayi tace  Mom bata wani dukana Baba sai once in a while kawai idan na bata mata rai ne lumshe idanu Baba yayi yabude yace  naga jikinki Husna, i saw duka dukan, i saw hands naki sauke kanta kasa tayi da sauri lips dinta yashiga rawa chan tace  nike mata laifi Baba ajiyan zuciya Baba yasauke anatse yace  Asma u hakanan taji gabanta yafadi tace  na am Baba ahankali Baba yace  jiya da rana bayan sallan azahar na dauramiki aure da cousin dinki, Yayanki Hussain, Hamad! Wani wawan faduwa gabanta yayi dasauri takalli Baba gabanta na bugawa beyond measure dan har Baba saida yagani yasa hannu yakama hannunta anatse yace  I dont know mesa mahaifiyarki kemiki abinda take miki but ban haifeki dan wani ya kashemin ke ba and Munir ya sanar dani komi dan yajuyo maganan datake gayamiki adaki kan tamiki miji da yanda tazage yan uwana harda kiran mijin naki mara aiki da abinyi Baba yace  amatsayina na mahaifinki ni da Yayana muka hada aurenki da Hamad kawai sai hawaye sharrr ya sauko daga idanun Asmeey tasauke kanta kasa tanaji kaman mafarki take Baba yace  sadaki dubu dari nabawa mijin naki yarike miki kudin kukaje kano zai baki, gobe da izninin Allah zaku tafi Kano aduk sanda komi yazama daidai za a tsara lokacin da za a kira mutane ayi yinin biki wato walima, dazu nasaka yayarki Aya tahada kayanki tsaf itada Ramla ankai mota Baba yasauke ijiyan zuciya yana kallon ya da take share hawaye Baba yace  iya abinda nasani shine kin gama university Asma u, zancen zuciyanki law school lies a tafin hannun mijin naki sabida shine keda iko dake, idan yaga dama yabarki kije idan yaga dama yahana shine mai iko dake yanzu Baba yasake yin shiru sannan yakai hannunsa yakama hannunta ahankali yasake daura dayan hannunsa saman kanta yace  Asma u nasan yanda kikeda tarbiya da natsuwa mijinki Hamad for now baida wani tsayayyen aiki, ki zama mata mai tsoron Allah da kaunar mijinta domin Allah, kada ki takuramai da siyan abubuwan kyalekyalen duniya siyamin kaza, siyamin kaza, ki zama mai godiyan Allah kiyakuri da abinda ya iya samu yabaki, kada kice dan kinga matan yayyinsa da kaza sai kema yamiki kaza, wata rana sai labari shi arziki na Allah ne, kuma yana bawa duk wanda yaso, Hamad nada kwazo zai kula dake iya gwargwado, iya karfinsa kuma kinji gyadamai kai tayi tafashe da kuka maganganun namata wani iri, Baba yace  Hamad baida gida, yanzu kukaje kano a flat din Abba da Mamie zaku zauna kafin agama gina flat dinku, Abba Yayana ne kuma matsayin mahaifina yake bazai taba bari ki cutu ba hakama Mamie, ki kula dasu Asmeey kinga sun soma gajiyawa jiki ya tsufa ki zama mai taimaka musu da abubuwa da dama tundaga kan girki da sauransu kinji Asma u Baba yasa hannu yaciro wayanta da Ramla takawo mai dazu yace  ga wayanki nan nacire sim naki nada zan ijiye wajena zuwa nan gaba, nasaka miki wata SIM card danake dashi ki dinga amfani dashi, Asma u ina sonki nayafe miki duk wani abu dakika tabamin da Wanda na sani da wanda ban sani ba sannan ina neman yafiyanki ina matsayin mahaifinki but i couldn t protect you kalleki yau Asma u kiyafema Babanki kinji dawani sauri Asmeey ta rungume Baba tana kuka murya kasa kasa tace  Baba bakamin komiba baka tabamin komiba dan Allah kadena rokona Baba tafashe dawani irin kuka, Baba yadagota yakai hannu yashare mata fuska yace  I am sure babu wanda zai kara dukanki agidan Yayana, Mijinki, Yayinki da Abba will shield you Asma u thank you for being a good daughter to me, me rufama iyayenta asiri, mai hakuri da juriya da kwazo, ina alfaharin zama mahaifinki kara rungume Baba tayi tana kuka, Baba yayi murmushi yana shafa bayanta yace  go and start a new life kinji ? Dagowa tayi ahankali takalli Baba tace  Baba Mom tas& . ? Baba bai barta ta karasa maganan ba yace  mahaifiyarki mahaifiyarki ce har abada Asma u but kaman yanda banda wani iko akanki yanzu itama batadashi kina karkashin Hamadi yanzu ba muba kinji gyadama Baba kai tayi gabanta na faduwa ita kadai tasan ya zuciyanta ke mata sai wajejen 11 Baba yabar dakin ta kwanta tai shiru tana kallon sama jitayi bakinta ya bushe dasauri tatashi zaune da kyar takalli side drawer tabi duka dakin da kallo babu bottle water da dane data kira Mamie but hakanna saitaji tanajin nauyinta bamataso su hada ido, ahankali tasauka dagakan gadon tamike tsaye tunda Baba yafita bataji any motsi ba maybe kowa yayi bacci tunda gobe zasuyi tafiya, daya daga cikin gown din Ya Aya tasaka red mai botura agaba ya tsaya mata a gabada guiwa but baikai har kasa ba, babu dan kwali akanta ko hula, rigan short hand garesa, slippers tasaka tabude kofan ahankali tafito tana tafiya, hannunta always feels kaman kaya sabida nauyi ko na daurin da aka matane oho, staircase tahau tasauka a first matakalan da kyar tana shirin sauka na biyu& .  Ina zaki? Chak Asmeey ta tsaya sabida muryan Ya Hamad dataji da kamshinsa duka at the same time, wani kalan nauyi taji tajuyo balle ta kallesa yau, sai kawai tasauke kanta kasa lips nata yahau rawa kaman yar baby tace  ruwa zanje kitchen na dauka murya ciki kaman baiso yayi magana yace  go inside, I will bring it for you gyadamai kai tayi still taki kallonsa ta taka bene dayan data sauka akai tahayo nan falon sama tawuce dakin Mamie, Hamad dake sanye da joggers ash color yana sanye dawani black t-shirt dayamai bala in kyau yawuce yasauka kasa, kitchen ya shiga yadauko bottle water marasa sanyi guda biyu yahayo sama, kofan dakinsu yakalla sannan yawuce dakin Mamie ahankali yabude kofan batare daya bar door din yayi kara ba ya shiga ciki.
=ث?UWA KO UKUBA?=ث?



'

EPISODE 2?? 2??



Hakanan gaban Asmeey yawani fadi ganin Ya Hamad yashigo dakin yamaida kofan yarufe kawai yau saitaga Ya Hamad yafi koda yaushe mata girma, saitaga yamafi Ya Mustapa tsayi da cika, maida kanta kasa tayi dasauri ganin zai juyo, juyowa yayi yadan kalleta tana zaune bakin gadon kanta akasa, yatako yafara zuwa sai kawai Asmeey tafara wasa da fingers nata she s just so nervous and tense jikinta namata wani iri harya karaso gaban gadon ya ijiye gora daya kan side drawer hannunta Asmeey ta mika dakedan rawa zata karbi dayan bottle dake hannunsa sai taji shiru bai bata ba. Dan daga kanta tayi kadan ganin bai bata ruwan ba, budemata goran ruwan yake idanunsa nakan ruwan da fararen hannunsa kumbunansa agyare gwanin ban sha awa, maida kanta kasa tayi ahankali, bude ruwan Hamadi yayi yakalleta tareda mika mata calmly kaman wanda baisan yanda ake daga murya ba yace  take hakanan kawai saitaji hannunta na rawa she s trying to control it takasa tashiga mikamai hannun yana kallon hannun samata bottle din yayi a hannun ta karba tadawo dashi jikinta still hannun rawa yake tadaura kan cinya tarike trying tadan natsu cus she s shaking too much and she doesn t know why, kusan 3secs tayi ahaka kafin ahankali takai ruwan baki tasha da dan yawa sannan tacire abakinta tamikamai hannu yakawo zai karba ta dauka ya amsa kawai tasaki, goran yafadi akasa dasauri ta kalla tace  sorry bansan bak& . Ta sauko daga gadon zatai tafiya ruwan yajata zata zamiye tai baya dawani irin sauri Ya Hamad yariketa ta hanyar kama waist nata da kafadanta tadan shigo jikinsa bawani sosai ba yana kallon floor din batare dayama lurada abinda yayi ba kawai tashi tsigan jikinshi yayi sosai dasauri ya kalleta itama Asmesy ta kalleshi gabanta na faduwa asanyaye eyes nawa nawani shinning, her body is so warm da yanajin warmth din a hannunsa dake waist nashi ga idanunwanta tana kallonshi dayaji cikinsa yafara juyawa da sauri yacire hannunsa daga waist nashi dana shoulder nata atare dukansu suka sauke idanunsu Hamad yadan koma baya kadan,
dasauri takoma baya adan daburce tajuya zara wuce, murya kasa kasa yace  ina zaki ? Asanyaye tace  mop zan dauko juyawa yayi yace  don t worry wucewa yayi yabude kofa yafita bai jimaba yadawo da mop, Asmeey tamikamai hannu zata amsa sai kawai yawuceta yashiga gabanta yafara goge ruwan Asmeey ta tsaya tana kallonsa adan sace takasa denawa, he s so calm! He s kind, and yanada good heart, gashi da tausayi, and he s respectful! Dago da kansa yayi suka hada ido dasauri ta sauke kanta kasa kaman wata munafuka, jingina mop din yayi abango ahankali yasa hannunsa yadanja zanin gadon ya gyara yasa hannu yayi dusting dudda babu any dirt agadon sannan yadan matsa gefe batare daya kalleta ba ahankali yace  zoki kwanta gyadamai kai tayi ta taho ahankali ta shiga kwanciya da kyar yadan tsaya yana kallonta saikuma ya matso gadon dasauri ta kalleshi kallonta shima yayi right in the eyes dawani irin sauri ta lumshe ido, bargon yadauka yana rufa mata saiya sauke gaze nasa kasa yajuya dasauri yadauki mop daya jingina a bango kafin chan kasa kasa yace  good night Husnah! Wani kalan runtse idanu Asmeey tayi da karfi tanajin wani iri ajikinta, the way he called that name Husnah sai kawai taji no one does it better than him, saitaji tafison ana kiranta Husna than Asmeey ma, bude kofa taji yayi hakan yasa tadan bude idanunta kadan daidai yana fita juyoda kansa yakarayi da gudu ta runtse idanun sai taji yafice ya maido kofan yarufe ahankali. Bude idanunta tayi tana sauke wani irin ijiyan zuciya she s feeling some wired movement ajikinta especially her tummy kaman butterflies na tashi, murya chan kasa tace  yanzu ni Matar Ya Hamad ce? Matarshi Matarshi? Sai kawai tawani kankame bargon murmushi takejinyi but saitakiyi, wani dan karamin waje in her heart is happy she s his wife batamasan mesa hakan ba ko menene dalilin ba, but the rest of her heart is just fear tana mamakin tayaya Mom ta yarda da aurensu da Ya Hamad cus batason mutanen kokuma Mom bata yarda ba Baba yamata auren? Or maybe Mom ta yarda sabida abinda Fawaz yamata? Sai saka take tana warwara ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
*

Itadai Mama ta lurada yanda aketa kuskus barinma wajensu Gwaggo dazu kuma tana flat din taga Ammi da Mamie da Abba da Gwaggo da Aya sun fito daga dakin Gwaggo ana ganinta sai akayi kaman an chanza topic which is so unusual koma meeting ne koda yaushe ana sata aciki abun kuma ya tsaya mata arai har zata kwanta saikuma tace bari taje tama Baban su Nana maganan bude kofan dakinta tayi tafito tawuce dakin Baba dake opposite her daidai zata bude kofan taji yana magana ko waya yake ko menene kawai saita tsaya tareda kare kunnenta Baban Nana yace  tunda kafadama Asmeey komi ai shikenan Alhamdulillah gobe wara haka tana dakin mijinta! Wani irin rasss gaban Mama yafadi tazaro ido tana kara manna kunnenta dantaji da kyau taji Kawu na dariya yace  Hamadi da kunya Hamadi da kunya toh Alhamdulillah yadawo gidan tunda aka daura auren nadena ganinsa baya wuni agidan wani kalan komawa baya Mama tayi tana daura hannayenta a kirji tana zaro idanu irin menakeji haka? Hamadi? Asmeey daura aure? Kai? Daura aure? Daurin aure dai? Kai aure aure dai data sani? Juyawa tayi da sauri takoma dakinta hijabi taja tasaka akan rigan baccin dake jikinta tasaka slippers tafito ahankali tasauka tawuce kofa ahankali tabude kofan ta leko tsakar gidan ganin babu kowa yasa ta shiga falla kafafu kaman zata tashi sama burintabkawai taganta dakin Mom.
Tasan yawanci basu kulle doors na flat nasu hakan yasa ta murza kofan ta shiga babu kowa a falo hakan yamata dadi tayi sama da saurinta, tana zuwa bata tsaya knocking ba tabude kofar flat din Mom ta shiga falon babu Mom sai kamshin turare da dakin keyi hanyar bedroom din Mom tayi tana kiranta da murya kasa kasa  Maman Aya, Maman Aya Mom na kwance kan gadonta da kayan bacci waya take da Fawaz jin ana kiranta yasa tace  Ina zuwa Rayuwata ta katse wayan dasauri tana mamakin wanda ya isa yafado mata flat ba sallama ba knocking ta taso tana bude kofa taga Maman su Nana dasauri cikeda isa tace  lafiya? Gefenta Maman Nana tabi tashigo bedroom din Mom tajuyo ta kalleta tana maida kofan tarufe Maman Nana tawani zaro idanu zatai magana saikuma tari da sauri tasa hannu tadauki bottle water data gani tabude da sauri tanasha Mom ta karasa kan couch na dakin ta zauna ta daura kafa daya kan daya cikeda isa da iko tana kallon Maman Aya dake bankan uban ruwa, ijiye goran tayi da sauri sannan tazo wajen Mom dake kallonta cikin wishpering tace  Maman Aya wani mummunan zance naji kuma kin sanni bazaki taba samuna cikin masu cimiki amana ba Billahillazi kada kafa Mom tashigayi dudda she s feeling tense already cus she s sensing bad energy but ta daure batason tai loosing steeze, Maman Aya tace  dazu da rana na shiga flat dinsu Gwaggo inama falo tareda Matar Musty Asiya saiga Gwaggo tafito daga dakinta ba, da Ammi da Mamie, ke harda Aya nakoga goro daga minti a hannuwansu araina nace Gwaggo ce taraba musu Gwaggo tashiga bawa yara minti tana cemusu suce Allah sa albarka sunata fadin haka Mom ta natsu tana kallon Maman Nana kafin tace  yanzun nan Allah ya jiyardani dalilin meeting din Maman Nana tasake dafa kirji, Mom tace  get to the point waya nake Maman Nana takara rage murya tace  kaman fa aure Baba ya daurama Asmeeey

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login