Showing 39001 words to 42000 words out of 127932 words

Chapter 14 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6701

banza yayi mata kamar ma ba da shi take ba,gaishe da shi ɗayar tayi, cikin sakin fuska ya amsa yana faɗin "ya kika kairiyya"
"lafiya lau, ya hanya?"da Alhmdllh ya amsa mata,hugging ɗinta fatima tayi tana faɗin" nayi kewar ki aunty kairiyya"da fara'a a fuskarta tace "nima nayi kewarki" wasu maza ne suka ƙaraso wurin su su biyu sanye da uniform, suna ƙarasowa suka ce 
"barkan ku da zuwa ranka ya
daɗe" kallon su shazim yayi yana cewa "barkan ku dai aminu ya kwana biyu"
"Alhmdllh ranka ya daɗe" wanda aka kira da aminu ya ce,ɗayan ne ya ce "yallabai ya lagos?" shazim na kallon shi ya ce "Alhmdllh kamal,ya aiki?"
"lafiya lau ranka ya daɗe" sannan su ka gaishe da noraiz fuskarshi ɗauke da fara'a ya amsa, sannan fatima ta gaishe da su, amsa mata su ka yi  cikin kulawa fuskar su da fara'a,suka amshi trollys ɗin noraiz  da na shazim  dake hannun noraiz aminu na  cewa "mu tafi koh ranka ya dade" ok kawai shazim yace yana kama hanya,su aminu na gaba da trollys ɗinsu, sa'ada ce ta amshi na fatima, wannan budurwar ta gaban su tazo ta wuce fuuu kamar zata tashi sama, fatima ce tace "Aunty feenah abun ba magana" juyowa tayi ta kalli fatima sama da ƙasa fuska a haɗe tace "sannu" ta juya tayi gaba, da idanu kwai fatima ta bita, taɓe baki noraiz yayi, fuskar sa'ada da ɗan damuwa ta kama hannun fatima tana faɗin "sorry sister" ɗan yaƙe fatima tayi tana faɗin "bakomai" tsaki kairiyya ta ja a zuciyar ta tana faɗin "ko yaushe feenah zata dai wannan banzar ɗabi'ar "
parking lot ɗin airport  ɗin su ka ƙaraso time ɗin har shazim ya shiga bayan mota ya zauna, aminu na saka kayan su cikin booth, amsar trolly ɗin dake hannun sa'ada kamal yayi ya saka a booth,buɗe ma su  baya yayi, noraiz ya shiga sa'ada ta ce "kamal mu zamu tafi a motar aunty kairiyya"
"to shikenan hajiya" kama hannun fatima tayi suka nufi inda motar kairiyya  ta ke, tsaye suka same ta bakin mota,
sa'ada tace
"lafiya dai aunty kairiyya"
"babu komi, ku nake jira ne "
sa'ada tace "aunty feenah tafiya tayi?" eh kawai kairiyya tace haɗi da buɗe motar ta shiga, suma shiga suka yi fatima na gaba kusa da kairiyya sa'ada na baya,key tai ma mortar haɗi da yin  reverse tabi bayan motocin da su shazim ke ciki, suna tafiya kamal na tambayar noraiz  ya lagos da ammy, da Alhmdllh noraiz ya amsa mashi sosai su ke fira da shi har su ka kawo wata danƙareriyar anguwa ta ji da faɗa, gidajen dake anguwar ka ɗai sun isa su sa ka fahimci cewa anguwa ce ta manyan mutane, gidaje ne naji da faɗa, road road ne gasunan kala kala kowane road kalar tsarin ginin   gidajenta daban, karya kwana animu yayi ya shiga wani road bin bayan shi su kamal su ka yi shi da kairiyya , masha Allah wani haɗeɗen  estate ne su ka nufo,aƙalla gidajen dake cikin estate ɗin za su kai 20 duk da akwai wandan foundation kawai a kayi ba'a fara gina su ba,   tsarin gidajen dake cikin estate ɗin yafi na sauran gidajen dake sauran road ɗin  haɗuwa da tsari,komai na gidajen iri ɗaya ne,  tafiya su ka yi mai ɗan tsayi, sannan su ka kawo bakin main gate ɗin estate ɗin,securitys ne zaune kan bench a bakin gate ɗin estate,ɗaya daga cikin su ne ya taso ya nufo motar,sauke glass ɗin motar aminu yayi,  gaisawa yayi da security ɗin, tambayar shi securityn yayi daga ina, amsa aminu ya bashi "daga airport muke, yallabai shazim ne ya zo " leƙawa security yayi yana cema shazim "ranka ya daɗe barka da zuwa, ya hanya"da Alhmdllh shazim ya amsa masu, sauran security ɗinma tasowa su ka yi suna gaishe da shazim sannan suka nufi motar da su noraiz ke ciki suna gaishe su,cikin sakin fuska su ka amsa masu,buɗe masu gate security yayi ,ciki aminu ya danna kan hancin motar kamal na biye da shi, sai da su ka ɗanyi nisa da tafiya sannan su ka iso bakin wasu gidaje biyar dake jere duk da akwai yar tazara tsaka nin su, huɗu girman su ɗaya, ɗayan kuma yafi su girma sosai,mai girman dake tsakiyar su aminu ya nufa ,  parking aminu yayi bakin wannan ƙaton gidan wanda yafi sauran gidajen girma da haɗuwa,parking space ɗin  gidan ya nufa yayi parking, motoci ne da a ƙalla zasu kai biyar an rufe su, fitowa aminu yayi ya buɗe ma shazim ƙofa amma sai shazim yace kawai ya ɗauki kayan ya wuce, hakan yasa shi  nufar  booth ɗin motar ya fito  da trollys ɗin su ya nufi entrance ɗin shiga gidan ya tsaya,  kamal ma ya nufo nan yayi parking a parking space ɗin,fitowa noraiz yayi, su fatima kuma wani part kairiyya ta nufa da su tayi parking, fitowa sa'ada da fatima su kayi, sa'ada ta  buɗe booth ta fito ma fatima da trolly ɗin ta,ta window Fatima ta leƙa tana faɗin "aunty kairiyya sai mun shigo" da to kairiyya ta amsa, reverse tayi ta nufi wani part tayi parking, ficewa tayi ta nufi cikin part ɗin.
kallon motar feenah dake parking space sa'ada tayi, aranta tace kenan gida aunty feenah ta dawo,trolly fatima ta ja suka nufi entrance ɗin gidan ,kamal na parking noraiz ya fito ya nufi aminu dake tsaye yana jiran fitowar shazim ya kai masu trolly ɗin cikin gidan  amma bai fito ba, noraiz na isowa ya tambayi aminu lafiya, amsa aminu ya bashi da shazim ya ke jira ya fito   noraiz ya ce "ok muje kawai" da to aminu ya amsa yana gaba noraiz  na baya, buɗe ƙofar aminu yayi  su ka shiga har time ɗin shazim bai fito ba yana zaune cikin mota,haɗeɗen parlor ne mai kyan gaske dan inka shiga sai kayi tunanin ba a cikin estate ɗin kake ba, babu motsin kowa aciki sai sanyi ac dake tsara ko ina na parlorn haɗe ƙamshi fresheners,up stairs aminu ya nufa,ɗakuna ne saman sosai, wata yar hanya aminu ya bi nanma wani parlorn ne wanda yafi na ƙasa haɗuwa da tsari, wani stairs ɗin su ka ƙara nufa nanma parlor ne shima ya haɗu ga tsari mai kyau,sannan suka nufi wani ɗan corridor,bedrooms ne kusan guda huɗu anan aminu ya tsaya yana ajiye trollys ɗin yayi ma noraiz sai anjima, godiya noraiz yayi mashi sannan ya ja trolly ɗin shazim ya shiga ƙofar dake kusa da shi, ɗan ƙaramin parlor ne mai kyan gaske kusan tsarin shi ɗaya da parlorn shazim dake lagos, nan ma kamshi ne ke tashi mai daɗin gaske ga sanyin ac, bedroom ya nufa nan ma ya haɗu shima kamar na lagos ne sai dai yafi na lagos girma da wasu abubuwan, har cikin wardrobe noraiz ya saka ma shazim trollys ɗin shi,sannan ya fice daga ɗakin yanufi nashi, shima na shi ya haɗu sosai banbancin shi dana shazim bawain mai yawa bane bedroom ya nufa ya rage kayan jikin shi ya nufi toilet domin ya watsa ruwa ..

✨Shazim✨

wayar shi dake cikin aljihu ya fiddo, number ammy yayi dialing sai da ta kusa katsewa sannan ammy tayi picking bakin ta ɗauke da Sallama, amsa sallamar shazim yayi yana faɗin ammy ya gida, da lafiya lau ta amsa tana tambayar shi ya gajiyar hanya da kuma mutanen abuja "gajiyar tafiya akwaita ammy  Alhmdllh" murmushi ammy tayi mai ɗan sauti tana cewa "gajiya sai kace wanda yaje a mota ko a ƙafa" kwantar da kanshi yayi jikin saet ɗin motar yana shafa kanshi ya ɗan lumshe ido yana faɗin "da gaske nake ammy" ammy tace
"to yayi, ya mutanen gidan? "
"wallahi ban sani ba dan ban shiga ba"
"to saboda mi, ina fatima da mai babban suna? "
"fatima na part ɗin uncle Ibrahim, noraiz kuma na part ɗin mu"
"to kai kana ina? "
"ina cikin mota, yanzu muka iso ne ammy, na tsaya in kira ki ne "
"ok miyasa ku baza ku sauka part ɗin Ibrahim ba kona yaya ahmad "
"bakomai ammy, shi da kanshi uncle Ibrahim ɗin yasa aka gyara mana nan"
"duk da haka shazim da kuna zauna part ɗin shi, nasan shima dan ya san halinka ne, ya san ba zaka zauna part ɗin shi ba yasa aka gyara maku nan"
"ammy ba haka bane"
"to yaya ne in ba haka ba? "
"kawai ya san zamufi sakewa ne apart ɗin mu shine kawai"
"shikenan shazim, amma da mun gama wayar nan  ku shiga part ɗin innah ku gaishe ta dan Allah "
"to" kawai yace dan wallahi kwata kwata bai son ganin tsohuwar
"to sai anjima, in ka shiga kace ina gaishe da su dan Allah "
"to in sha Allah za suji "daga haka yayi rejecting ɗin kiran,number malam ya lalubo bugu ɗaya malam ya ɗauka da Sallama, gaishe da shi shazim yayi, cikin kulawa malam ya amsa da tambayar shi hanya da su fatima, sun jima sosai suna waya da malam sannan suka yi Sallama, cikin aljihu wando ya maida wayar, sannan ya buɗe motar ya fice, part ɗin su ya nufa,  ko da ya shiga bedroom ɗin shi ya nufa yayi wanka ya kwanta kan bed, nocking ya ji anayi daga parlor, shiru yayi kamar yana bacci dan ya san bazai wuce noraiz ba ne, kuma ya san  ya zo ne dan su tafi parts ɗin uncles ɗin su, shiyyasa yayi shiru dan bai shirya zuwa wurin kowa ba yanzu, jin shiru yasa noraiz tunanin koh yayan nashi barci ya ke, barin bakin ƙofar yi  ya fice daga part ɗin, gidan dake kusa da wanda kamal ya aje fatima da sa'ada noraiz ya shiga da Sallama, parlo ne mai girma ya ji furnitures masu kyan gaske,tsit yake ba kowa a ciki, wani ɗan corridor ya nufa ya shiga wata yar ƙofa,nan ma wani ɗan ƙara min parlor ne,  shiga ciki yayi da sallama, kyakyawar  tsohuwa ce   zaune kan carpet jikinta sanye da atamfa ɗinkin riga da zani  sai feenah da ke kan sofa kusa da ita fuskar ta duk hawaye. jin sallamar noraiz ne ya sa feenah goge  hawayen da ke fuskar ta,zuba ma noraiz ido tsohuwar tayi har ya ƙara so  cikin parlorn  ya  neman wuri ya zauna kan sofa yana faɗin "ina wuni innah" amsa mashi tayi da "lafiya,ai nayi tunanin kaima kafi ƙarfin ka zo ka gaishe da ni kamar ɗan uwan ka mara kunya, dan nasan idan ba Ibrahim ya kira shi ba bazai taɓa shigowa nan ba saboda aisha ta riga da tasa ya gama rainani baya ganin mutunci na "
"kiyi haƙuri innah yana nan shigowa bacci ya kwanta saboda jiya bai samu yayi bacci sosai ba "
"kai dallah yi man shiru, wane haline kuma na Abdulƙadir da ban sani ba, itama fatima tafi ƙarfin ta zo ta gaishe ni koh"
"A'a innah tana tare da sa'ada na san za su shigo ne" taɓe baki innah tayi tana faɗin "Allah sa"
da ammen noraiz ya amsa  haɗi da miƙewa yana faɗin
"innah zanje part ɗin  uncle Ibrahim"
bai jira mai zata ce ba ya fice abun shi, da harara feenah ta bishi yana fita tace "kingani koh innah shima noraiz wulaƙanta ni ya ke, dan tunda suka zo ko kallon banza bai yi min ba, da ya shazim ya dizgani a airport dariya yayi sh ida fatima "
"rabu da yan banza, zanyi maganin su ne daga su har uwar tasu,kuma shi wannan mara mutuncin nasan miye maganin sa, bari dai kawunnan nashi su dawo"
"yawwa innah shiyyasa nake sonki wallahi "
"ai kar kiji komai,su dai dawo, zai san dani yake magana, sai dai kuma abun da nake so a wurin ki shine ki kama kanki  ki daina son taɓa jikin shi dan nasan halinki da ɗabi'ar banza"
"In sha Allah innah na bari bazan sake ba "
"Allah ya sa" da ameen feenah ta amsa,  suna nan  zaune suna hira sa'ada su ka shigo ita da fatima ko da fatima ta gaishe da innah cewa tayi
"sai yanzu ki ka ga damar zuwa,ai da kinyi zaman ki ba sai kin shigo ba" haƙuri kawai fatima ta bata, ko kallonta bata yiba su ka cigaba da fira ita da feenah, ganin haka ne yasa fatima cema sa'ada ta tashi suje part ɗin su aunty kairiyya,tashi sa'ada tayi su ka fice zuwa part ɗin uncle Ahmad, anan su ka samu noraiz shida mahmud,gaishe da mahmud fatima tayi, sannan suka shiga bedroom ɗin mama ( asiya mahaifiyar su mansoor )su ka gaisa tana tambayar fatima ya su ammy, sun ɗan jima suna fira da ita sannan su ka tashi su ka nufi bedroom ɗin kairiyya.

wani matashin saurayi ne ya shigo  parlorn da sallama  hannun shi riƙe da briefcase,  da sauri noraiz  ya nufe  matashin yana cewa "oyoyo ya mansoor,nayi kewar ka sosai" rungume shi mansoor yayi yana cewa "lil bro saukar yaushe?"
"tunɗazu, ina ta zuba idon ganin ka, ya aiki?" shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "Alhmdllh,ya su ammy da auta?" muryar fatima su ka ji wacce fitowar ta kenan daga ɗakin kairiyya  tana cewa "gani anan yaya" juyawa mansoor yayi yana cewa "autar ammy, yan graduation kice tafiyar harda ke" ɓata fuska fatima tayi tana faɗin "ai ni fushi nake da ku kai da ya dr, ko ɗan text message na happy graduation" matsowa kusa da ita mansoor yayi yana faɗin "sorry lvly sis,ba haka bane munso muzo har lagos ɗin Allah ne bai nufa ba, amma kiyi haƙuri gift ɗinki na nan na ajiye maki" washe baki fatima tayi tana faɗin "tnxs big bro"
"to shikenan autar ammy ni zan shiga ciki na watsa ruwa " mansoor ya faɗa haɗi da nufar up stairs,"to sai ka fito "fatima ta faɗa" tashi noraiz da mahmud su ka yi su ka fice,fatima anan kan sofa suka zauna suna fira ita da sa'ada.

shazim daga wannan kwanciyar  bacci yayi awan gaba da shi ba shi bane ya tashi ba sai gab da magrib, yana tashi ya nufi toilet yayi wanka haɗi da alwala,sannan ya shirya ya fito  daga bedroom ɗin ya nufi dinning, abinci yaci kafin ya fice daga  part ɗin,ya nufi masallacin dake cikin estate ɗin,ana gama sallah ya fito ya nufi part ɗin uncle Ahmad,kairiyya da su fatima  ya samu a parlor,gaishe dashi kairiyya ta sake yi tana cewa "ya gajiyar tafiya ya  shazim " amsa mata yayi da Alhmdllh sannan yace "uncle fah?" yana sama ta bashi amsa, tashi yayi ya nufi up stairs ya shiga wani ɗan ƙaramin parlor, zaune uncle Ahmad yake kan carpet, mama na kusa da shi,sallama yayi ya shiga ciki, amsa mashi sallamar su kayi, wuri ya samu kan carpet ya zauna yana gaishe da su amsa mashi su kayi cikin kulawa uncle Ahmad na tambayar su malam da ammy "suna lafiya" uncle Ahmad ya ce "masha Allah, kaje wurin Ibrahim?" shazim yace "a'a yanzu dai zan tafi" uncle Ahmad yace
"to shikenan, bari sai ka ci dinner tukunnan sai ka tafi "
"bana jin yunwa uncle yanzu naci abinci" uncle ahmad yace "to shikenan tashi kaje wurin Ibrahim ɗin"
da to shazim ya amsa haɗi da miƙewa ya fice,yana fita bedroom ɗin mansoor ya nufa, zaune ya same shi yana waya, harara ya watsa ma shazim, murmushi yayi haɗi da samun wuri kusa da shi ya zauna  yana faɗin"my lover bro,wannan hararar ta mi ce ce" katse wayar mansoor yayi yana faɗin "amma wallahi ka rainani shazim ni nema lover ɗin koh"
"eh mana yaya"
"ni nama manta nayi maka magana fushi nake da kai "
"kaina bisa wuya minayi kuma lover bro" duka mansoor ya kai mashi ya kauce "Allah zanyi maganin ka idan har baka daina ce man lover bro ɗinnan ba"
"sorry na dai na"
"da dai ya fiye maka,kuma ka tashi ni ka bani wuri"
"afuwan ya mansoor" juya mashi baya mansoor yayi yana faɗin
"ka tashi nace ka bani wuri" hannu shazim ya sa ya riƙe kunnuwanshi alamar ban haƙuri yana cewa "haba ya mansoor dan Allah fa" kallon shi mansoor yayi yace
"hmm,ya hanya,ya su ammy da malam"
"suna nan lafiya "
"masha Allah"
dafa kafaɗar shazim mansoor yayi sannan ya ce "bro wai miya faru ne ake ta kiran ka amma baka ɗaga waya wani time ɗin ma a kashe, kasan ka ɓatama su abbah rai sosai " kallon mansoor shazim yayi "yaya su abbah sun ta kura dole sai nayi aure ni kuma yanzu bana da ra'ayin yi"
"ƙanina kasan mi? " girgiza mashi kai shazim yayi,alamar a'a,ɗan nisawa mansoor yayi sannan yace "miyasa baka son yin aure yanzu, duk wani rufin asiri na duniya Allah ya baka shi,to miyasa bazaka godema ni'imar da yayi maka ba" kwantar da kanshi yayi saman kafaɗar mansoor sannan yace "yaya bawai bana son auran ba ne kwata kwata,a'a nafiso su ƙara man lokaci  har nasamu wacce take sona nake sonta, amma yaya kowa yaƙi fahimta ta"
shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "karka damu bro ni na fahimce ka in sha Allah suma su abbah za su fahimce ka"
"Allah yasa yaya"
"Ameen "( a kwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin shazim da mansoor, mansoor ya girmi shazim bawai sosai ba, tare su ka taso har makaranta tare suka yi)
"tashi muje part ɗin uncle Ibrahim dan nasan ba inda kaje tunda ka zo"
"nayi baccine shiyyasa"
"ok tashi muje" tashi su kayi su ka fice direct part ɗin uncle Ibrahim su ka nufa, bakin su ɗauke da sallama suka shiga,momy su ka samu zaune kan sofa ita da aliyu, da gudu aliyu ya taso yayi hugging ɗin shazim yana faɗin "oyoyo yaya" ɗaga shi sama shazim yayi yana faɗin "haidar ya kake,ya school"
"lafiya lau yaya" masha Allah shazim ya faɗa haɗi da sauke shi ƙasa yana faɗin "momy anwuni lafiya"
"lafiya lau Alhmdllh,ya hanya, yasu ammy da malam"
"lafiya lau Alhmdllh" mansoor yace "momy ina wuni" 
"lafiya lau Alhmdllh, ya aiki "
"Alhmdllh momy,uncle na ciki ne"
"eh yana part ɗin shi"
"ok  bari mu shiga momy" to momy tace, tashi su ka yi suka nufi corridor dake kallon parlorn ,wani ɗan ƙaramin parlor su ka shiga, shiru parlorn yake bakowa sai ƙarar tv da ta AC, mansoor ne yace su zauna may be uncle ɗin na ciki, zama su kayi kan sofa,muryar uncle Ibrahim su ka ji daga bedroom ɗinshi cikin faɗa yana cewa "wannan ai maganar banza ce maganar wofi, amma ka bani mamaki, to bari kaji tun wuri kasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login