Showing 30001 words to 33000 words out of 127932 words
compound yana amsa waya"
Ko rufe baki noraiz bai yiba shazim ya shigo, shima wurin su Ammy ya nufo, gaishe da Ammy yayi , ya nemi wuri kusa da Ammy kan sofa ya zauna, Ammy ce tace "ga abinci, kan dinning"
"to" kawi yace,dinning din suka nufa,suna kammala dinner din, fatima ta gyara wurin,su kuma kan sofa suka koma, Ammy na tambayar shazim yaushe zasu tafi abuja
"gaskiya ina tunanin sai upper week,zanje jos wani hospital ne suke son ganina next week"
"amma shazim naso ku tafi next week, jiya sai da Ibrahim ya kirani shi da innah nace masu kuna nan tafe next week, yan zu idan suka kira nace kun fasa gani za su yi kamar ni ke hana ku je"
shazim yace "to ammy suyi haƙuri na dawo mana kiran emergency ne, patient sun fi su buƙatar gani na"
"shikenan Allah ya kaimu upper week ɗin" da ameen suka amsa su duka, fira suka dan taba sannan kowa ya nufi ɗakin sa domin bacci......
✨katsina ✨
Kwance suke kan bed
ko waccen su sanye take da pajamas ɗinta , Aaimah da najma color ɗaya white sai Aairah dake da pink color , labari kawai suke a kan yanda walimar zata ka sance
Aairah tace "wallahi harna ƙosa naga gobe tayi"
Aaimah tace "faɗi kike anaji, ni baki san yan da nake jiba, Allah dai ya nuna mana goben lpy"
da ameen suka amsa, sun jima suna tattaunawa a kan yanda walimar zata kasance , har bacci yayi awon gaba da su..
WASHE GARI
Tun da safe suka tashi, shirye shirye kawai suke na walima, har mai makeup Mom ta ɗaukko, wacce zata yi masu kwaliyya, zuwa anjima, Idan lokacin walima yayi , su Mom kuwa suma tun da suka yi sallar asuba suke cikin kitchen ita da Aunty Rabi da baaba larai, suna ida shirya abubuwan da basu gama shiryawa ba jiya.
a chan compound kuwa yasha decoration, mai kyan gaske.
wurin karfe biyu na rana gidan ya fara cika da mutane, saboda bayan la'asar za'a gabatar da walimar , har gida ya Abdallah ya je ya dauko Dadi, sai Aunty safiyya wace mus'af ya kawo,yan uwan abie ba wanda baizo ba da ƴaƴen su , sai wasu daga cikin ƙawayen Mom , hakama ƙawayen su Aairah na islamiya da boko duk sun zo, sai abokan abie dake nan katsina ba laifi suma sun zo , gida dai ya ciki Alhmdllh.....
✨Ammy ✨
Zaune take kan sallaya tana adu'a,
wayar ta dake bedside drawer ce ta fara ringing, miƙa hannun ta tayi ta ɗauki wayar haɗi da yin picking bakin ta ɗauke da sallama on the other hand cikin wayar muryar wata dattijuwar mace ce tace "wa'alaikumu salam" ammy ta ce "ina wuni innah " amsa ma ammy tayi da "lafiya" ammy tace "innah yasu alhaji ahmad da su hajiya turai" da katar da ammy matar yi da faɗin "dakata aisha bawai na kira ki bane dan kiyi taman tambayoyi, na kira ne kan maganar da muka yi da ke, naga yau kusan wata kenan amma bangan su sun zo ba" ammy ta ce "dan Allah innah kiyi haƙuri, ko jiya da daddare munyi maganar da shazim akan zowan naso,to shine yake sanar man anyi mashi kiran gaggawa jos baza su samu zuwa ba sai sati na sama" katse ammy tayi da faɗin "dan Allah dakata man aisha, kina nufin sai abun da shazim yace kenan, ko mi kike nufi"ammy ta ce "ba haka nake nufi ba innah" on the other hand "to mi kike nu, tun yau she muke magana sai dai kice man ranar kaza za su zo amma kuma basu zo sai anyi magana ki kawo ma mutune wani uziri" shiru ammy tayi tana sauraran ta, da kaga fuskar ammy kasan cike take da damuwa "to bari kiji in gaya maki, ba ku isa ba daga ke har wannan mara kunyar, zumunci ne Allah ya riga da ya haɗa kuma dole ne ayi shi, bar ganin nayi shiru na barmaki yaran a hannun ki bawai hakan na nufin bazan iya ƙwatar su daga hannunki ba ne, saboda yara basu da wasu dangi a duniya bayan mu ɗinnan dai da kika gama rainawa ki ka sa ƴaƴanki suke ganin kamar bamu da amfani" sosai matar ta rufe ammy da masifa ammy na bata haƙuri tana gama faɗar abun da zata faɗa ko jiran mi ammy zata ce bata yiba ta kashe wayar, shiru ammy tayi ta ƙura ma wayar ido, chan kuma ta ɗaga hannun ta sama tana adu'a wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, gefen hijabin ta ta sa ta goge tana faɗin "Allah sarki yaya,Allah ya jiƙan ka ya haskaka kabarin ka " na ce ameen ammy, tashi tayi daga kan sallayar ta linke ta ta saka cikin wardrobe da hijabin da tayi sallah fita tayi daga ɗakin, fatima ta samu zaune kan sofa tana ta latsa sabuwar laptop ɗinta wacce shazim ya saya mata, ɗago da kanta tayi tana faɗin"barka da fitowa ammy" da yawwa ammy ta amsa mata haɗi da neman wurin zama ta zauna, fuskarta da tsantsar damuwa, lura da hakan yasa fatima cewa"lafiya dai ammy,kamar kina cikin damuwa?" ce mata ammy tayi "bakomai Fatima,mi ki ka gani"
"naga duk kinyi wani iri ne ammy" amsa ammy ta bata da "gajiya ce"
"to ammy ai da kin kwanta kin ɗanyi bacci kafin la'asar tayi"
to shine kawai a bunda ammy ta ce mata.....
✨KATSINA✨
bayan sallar asr ɗakin su Aairah a ciki yake da ƙawayen su na boko da islamiya,mai makeup ta fara tsara ma Aairah makeup mai kyan gaske, wayar Aairah ce ta fara ringing,cema Aaimah tayi ta duba mata taga wake kira , Amsa ta bata da alaramma ne ( malamin su na Islamiyya ) tana picking bakinta ɗauke da sallama, bana jin mi na cikin wayar yake faɗa,"to shikenan malam" shi ne kawai abunda Aaimah tace sannan tayi rejecting tana ce ma Aairah "ya ce sun ƙaraso,su na waje"
"to Please ki fita ke da Aeesha ku shigo da su,ko ki faɗama abie sai ayi ma su iso l"
"bari dai na faɗama abie ɗin kawai,dan na san babu hanyar wuce wa"
Aairah tace "to shikenan faɗa ma abie ɗin kawai"
dialing number abie Aaimah tayi, picking abie yayi yana cewa "lafiya Aairah , kun gama shiryawa ne?"
"Aaimah ce abie "
"Ok kun gama ne?"
"A'a abie dama su alaramma ne su ka iso"
Abie ya ce "to bari na sa abdallah ya shigo da su, amma fa ku yi sauri bana son lokaci ya ƙure"
"to abie in sha Allah mun kusa"
"to shikenan" abie ya faɗa haɗi da yin rejecting call din
"sis mi abie ɗin ya ce?" Aairah ta faɗa
"gashi can zai sa ya Abdallah ya shigo da su"
"to kira su ki ce ga ya Abdallah nan fitowa"
kiran su Aaimah tayi ta faɗa masu, sannan ta ajiye wayar, ana kammala ma Aairah ita ma aka yi mata bayan an gama mata aka yima najma, sai friend din su Aeesha, sosai su ka yi kyau kamar ka sace su ka gudu mu samman ma su Aairah, baƙaramin kyau su ka yi ba, shiryawa su kayi cikin wata atamfa super ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya amshi jikin su ba ƙaramin kyau atamfar tayima fatar su ba,farar alkyabba su ka ɗaura saman atamfar, faɗin kyan da alkyabbar tayi masu ɓata lokaci ne, kamar wasu ɗiyan sarakai, mom ce ta shigo ɗakin sanye take da wani haɗaɗɗen lace ɗinkin doguwar riga,wuyan ta da kunnan ta da hannu sun sha ado"kai masha Allah,kuce kun shirya,amma kunyi kyau sosai,kamar zan kai ku gidan miji"
dariya friend ɗin su da ke ɗakin suka yi suna faɗin"mom ai wannan ranar sai sun fi haka ba da kala" su dai su Aaimah ban da murmushi babu abun da suke mom ta sake cewa "to ku zo ku fita ku kaɗai ake jira " da to suka amsa mata, fice wa mom tayi daga ɗakin, suma tashi su ka yi su da friend ɗin su su ka fice can compound, suna gaba friend ɗin nasu na baya,maƙil su ka iske compoud ɗin da mutane, wurin da aka tana da domin su suka nufa suka zauna,ba ɓata lokaci aka shiga gabatar da walima, alaramma yayi wa'azi, sannan su Aaimah suka yi karatu, sosai walimar tayi kyau ta kuma ba da ma'ana, su Aairah ba ƙaramin burge mutane su ka yi ba, sun kuwa sumu kyaututtuka daga islamiyyar su, haka ma abie, mom, ya abdallah , dadi, granny, papi,aunty safiya, ƙannan abie duk sun basu kyauta, sosai su ka tara kyaututtuka daga wurare daban daban, su aunty rabi da aunty safiya su ka yi rabon souvenirs, sai wurin karfe 6:40 ana shirin kiran sallar magrib sannan aka tashi, kowa ya tafi yana yaba hazaƙa irin ta su Aairah da kuma ganin nagartar islamiyar su.
Episode 16_17
Aaimah zaune take saman sallaya bata jima da kammala sallah isha ba Najma ta shigo hannunta ɗauke da wani madaidaicin kwali,kallonta Aaimah tayi tana faɗin"ke kuma daga ina haka da wannan ƙaton kwalin" amsa najma ta bata da"saƙwan Aairah ne inji ya mus'af " ta faɗa yayin da take ajiye kwalin kan bed, ta sowa Aaimah tayi daga kan sallayar tana faɗin "ya mus'af dai, mu gani" buɗe kwali suka shiga yi, fitowar Aairah kenan daga bathroom jikinta ɗaure da towel,tsayawa tayi tana kallon najma da Aaimah dake kokuwar buɗe kwali, kayan da ke cikin kwalin suka shiga fitowa,qur'an ne da carpet sai counter da watch na mata haɗe da turare.
kwalin turaren su Aaimah suka buɗe suna ta fesa ma jikin su suna faɗin "ah lallai ya mus'af abun yar wariyar launin fata ce, to bari muji kalar ƙamshin turaren" ita dai Aairah ban da bin su da idanu babu abun da take, dan kwata kwata bata fahimci mi su ke nufi ba, barin bakin ƙofar bathroom ɗin tayi ta nufi dressing mirror tana faɗin "wai ku lafiyar ku ƙalau kuwa, dare ne amma sai wani fesa ture ku ke baji ba gani, wai ma ina ku ka same shi ne" najma ce tace "naki ne inji ya mus'af, tun da mu bazai bamu ba shi ne muke fesawa" tasowa Aairah tayi daga gaban dressing mirror ɗin tana faɗin "kuji tsoron Allah, shine kawai za kuyita fesawa koma ku faɗa man" Aaimah ce tace "to yanzu an faɗa maki shikenan ko" kayan Aairah ta shiga dubawa tana faɗin "kai amma nagode sosai ya mus'af, Allah ya bar ƙauna"da ameen su najma suka amsa, tashi Aairah tayi ta shirya cikin pajamas ɗin ta sannan suka shiga buɗe sauran kyaututtukan da su ka samu, sai da suka gama harma sun kwanta sannan ta ɗauki wayarta ta kira mus'af, sunjima sosai suna waya har su najma suka yi bacci, itama suna gama wayar bacci ta kwanta.
✨lagos✨
Fatima da ammy ne a kan dinning suna dinner, fatima ce kawai ke cin abincin dan ammy bata wani ci sosai ba ta tashi tana faɗin "ni zan shiga ciki, idan yan uwanki sun shigo kice masu na kwanta sai da safe" fatima ce tace "to ammy,amma lafiya naga kin tashi ba tare da kinci komai ba?"
"naƙoshi ne fatima, sai da safe "ammy ta faɗa, bedroom ɗin ta ta nufa, binta kawai da kallo fatima tayi, aranta tana faɗin "ko mike damun ammy ne yau"shiru tayi dan bata da mai bata amsar tambayar ta, ammy bata jima da tashi ba shazim su ka shigo shi da noraiz bakin su ɗauke da sallama, amsa ma su sallamar fatima tayi, dinning ɗin suka nufo , warmars ɗin da ke kan dinning noraiz ya shiga buɗewa yana faɗin "mi aka dafa ne autar ammy " girgiza kai Shazim yayi yana faɗin "ina ammy ne, na ganki ke ka ɗai? "
"ta shiga ɗaki "
"lafiya dai koh? "fatima ta ce "gaskiya yaya da sauƙi dai". shazim ya ce "mi kuma ya same ta yanzu"
"wallahi yaya har yanzu mood ɗin ta sai ahankali kuma na ƙara tambayar ta mike da munta, sai cewa tayi wai lafiya lau, kuma fa yanzun ma bata ci komai ba wai ta ƙoshi" ɗan shiru Shazim yayi kamar me nazari can kuma sai ya ce "ok shikenan sai da safen ku " ya wuce part ɗin sa, noraiz yace "nifa ina tunanin wani abu ke damun ammy wanda bata son faɗa mana ba" fatima ta ce" abun da nake tunani ke nan ya noor "sun ɗan jima suna tattaunawa a kan canzawar mahaifiyar su, sannan suma suka tashi suka nemi wurin kwanciya su....
WASHE GARI...
Ammy na kan sofa a parlor, Shazim ya shigo da ga motsa jiki, wirin da ammy ta ke ya ƙara so, gaishe da ita yayi, amsa mashi tayi cikin kulawa, tashi yayi da nufin barin parlor tayi saurin ce mashi
"ina za ka je? "
"zanje ne na shirin tafiya yau zan tafi jos "
"ok ashe yau zaka tafi?"
"eh ammy" ya bata amsa, ammy ce ta sake magana tana faɗin "to dawo,ina son magana da kai" to kawai yace haɗi da dawowa ya samu wuri ya zauna,magana ta fara "wai ni kam shazim mi ke da munka ne kai da ƙannan ka?"
ɗago da kansa yayi yana faɗin "bakomai ammy, mi ya faru? "
"ba komai,nayi maku maganar zuwa abuja amma babu wanda ya sake ce man komai akan tafiyar, Noraiz ma da na tambayeta shi ceman yayi ya manta" ajiyar zuciya Shazim ya sauke sannan yace "ba komai ammy, ni aiki ne yasha kaina shiyyasa" ammy tace "to yanzu bangane mi ka ke nufi ba?"
"ammy ina ganin sai dai kawai fatima da noraiz su tafi, tun da ni jos zan tafi kuma na faɗa maki,da ace zan iya zuwa a ranar na dawo to da kawai sai na kai su ni sai na dawo" wani kallo ammy ta bishi da shi har ya gama faɗan abun da zai faɗa sannan ta ce "yanzu dai mi ka ke nufi ba zaka je ba, ban ga ne ba ko kuma dai wani abun ka ke nufi??? "
"A'a ammy da na dawo zanje in sha Allah " ammy ta ce "maganar sai ka dawo jos ma bata taso ba, yanda su fatima zasu je haka kaima za ka je,kai ka ɗai ne likita da baza su ne mi wani ba,in kuma maganar aikin ka ka ke nasan kafin kaje ka dawo majeed zai ji da komai na abnoor har ka dawo, in kuma eko ne da ka ɗauki permission nasan zasu baka, kuma duk abund a ya kamata ace kayi ai kabir na nan" kallon ammy kawai shazim yake, dan shifa har zuciyar shi baya son wannan tafiyar, shiyyasa ma ya kawo mata excuse ɗin zuwa jos dan kawai ta cire shi a cikin masu tafiyar, amma daga ganin yanda take magana yama san ba lallai ta barshi ba, katse mashi tunanin da yake tayi tana cewa "sai wani kallona ka ke kana tunani, tafiya ce dai dole ka yita shazim" ajiyar zuciya ya saukewa a karo na biyu yana faɗin "ammy bawai bana son zuwa bane,a kullum ke ki ke faɗaman ka taimaki mai ne man tai mako da gwargwadan abun da Allah ya hure maka, ammy yau ke ki ke cewa su ne mi wani, dan Allah ki bari naje in dai abuja ne zanje idan ma ki ka ce na wuce daga jos ɗin sai na wuce amma dan Allah karki hanani yin wannan taimakon"
"babu wani excuse fa da zaka kawo man, nariga da nagama magana, garama kawai kayi shiru dan bazan saurari excuse ɗin ka ba"
"shikenan ammy kwana nawa ki ke so muyi"
"sati biyu nake son kuyi kafin ku dawo" ɗago kai yayi da sauri yana kallon ammy jin abun da tace "haba ammy ina laifin kwana biyar"
"sati biyu za ku yi kaji na faɗa maka"
"dan Allah ammy kiyi haƙuri, ki maida shi kwana biyar"
"to naji sai dai kai kayi biyar ɗin, ammy fatima da noraiz sai sunyi sati biyu cif sannan su dawo" ajiyar zuciya ya ɗan sauke yana faɗin "ammy ina dai laifin ita fatima tayi sati biyun"
"bangane ba shifa noraiz mi zai sa ba zaiyi sati biyun ba?"
"Ammy kinga nace shi zai cigaba da kula da business ɗina,kinga bai kamata ace yayi sati biyu ba"
"ban amince ba to, ina masu kula da business ɗin time ɗin da yake makaranta"
"suna nan ammy"
"to su cigaba da kula da shi kafin ya dawo"miƙewa shazim yayi yana faɗin "to shikenan ammy, nizan shiga na shirya time yana ƙurewa" da to ammy ta bisa har zai wuce, tace "idan kaje jos ɗin kwana nawa za kayi?" murmushi yayi dama ya san bazata taɓa hana shi taimako ba,ba tare da ya juyo ba yace "dama kwana biyar zanyi, amma tun da kince ba sai naje ba zan tura majeed yaje kawai"
"to na fasa kaje ka dawo sai ku tafi" murmushi yayi yana cewa
"A'a ammy ki bari kawai majeed ɗin yaje"
"kaci gidan ku, nace kaje zaka wani ce man majeed yaje bayan nasan kana son zuwa" murmushi yayi mai ɗan sauti yana faɗin "to shikenan" yana juyowa ya zo kusa da ita yana faɗin "nagode sosai ammy na" dungure mashi kai tayi tana faɗin
"ni ka ke ma dariya ko, dan kasan dama bazan taɓa hanaka zuwa ba ko"
"a'a ammy ba da ke nake ba"
"to shikenan, tashi kaje ka shirya kar lokaci ya ƙure" da to ya amsa mata haɗi da miƙewa ya haye sama , fitowa fatima tayi daga bedroom ɗin ammy, wurin da ammy take kan sofa ta zauna tana faɗin "na kammala jera kayan ammy" ammy ta ce "masha Allah, Allah ya biyaki"
"Ameen ammy" fatima ta ce, innah asabe ce ta shigo parlorn gaisawa su ka yi ita da ammy sannan take cewa "hajiya an kammala karin kumallon"
"Masha Allah sannu da ƙoƙari, Allah ya saka "
"Ameen hajiya" innah asabe ta amsa sunan suna ɗan taɓa fira shazim ya sauko shi da noraiz, gaishe da ammy noraiz yayi shi shazim sun gaisa tun ɗazu,sannan suka gaishe da innah asabe, sannan suka tashi suka nufi dinning, shazim da norai basu wani jima ba suka miƙe shazim