Showing 102001 words to 105000 words out of 127932 words

Chapter 35 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6714

idon ya zo  yace ga wacce yake so  har suka gaji,su kai fushin har suka gaji ganin wanda suke yi dan shi bai ma san suna yi ba.

gajiya malam yayi da shirun nashi ya sake mashi maganar, ko da yayi mashi maganar sai cewa yayi gini yake yanzu so yake sai ya kammala tukunnan,malam yace to ya kamata ya kira su uncle ahmad ya sanar da su, da to ya amsa, ya kuma kira su ya sanar da su, balbale shi da faɗa uncle Ahmad yayi dan mi bazai sanar da su ba tuntuni sai yanzu da lokacin da suka bashi ya ƙare, haƙuri ya bashi ya kuma sanar da shi ya kusa kammala ginin ai saura ka ɗan , jin yace hakane yasa uncle ahmad haƙura ya ƙara mashi wasu wata uku, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma shazim ba dan shi kwata kwata bai shirya yin aure yanzu ba neman kuɗi kawai yasa a gaban.
tun da uncle ahmad ya amince da maganar gini daya ce yana yi yasa ya fake da ginin har akayi shekara ɗaya bai ce ya kammala ba bai ce ga mata ba, sai da malam ya tasa shi gaba da faɗa sannan ya kammala,gida ne mai girman gaske kusan part uku ne gidan,  kuma yana kammalawa yace su koma gidan da zama, malam cewa yayi sai dai shi da ammy da fatima su koma(da yake noraiz na makaranta shi da su mahmud)  amma shi ba yanzu ba sai yayi aure sannan zasu dawo shi da ummy, ba yanda bai yi da malam ba amma ya ƙi amincewa dole tasa shazim haƙura suka koma shida su ammy duk da da farko da malam yace bazai koma ba ammy itama cewa tayi bazata koma ba sai tare da su malam amma sai malam yace ta koma suma sunan za su dawo.

_*CIGABAN LABARI*_

Aunty safiya ce tsaye bakin ƙofar parlorn mus'af tana nocking amma ba'a buɗe ba , ba kuma a bata izinin shiga ba, da dai ta gaji da tsayuwa ne yasa ta fara kiran sunan mus'af ɗin tana faɗin " wai lafiya kake ne? , ana nocking amma kayi shiru ka kuwa san ƙarfe nawa yanzu kowa na waje kai ka ɗai ake jira "
daga ciki mus'af yace " gani nan zuwa, ina gama shirya wasu kayan ne "
"amma kai ko anyi shiriritacce, yanzu da baka gama shirin ba kenan,  yayi maka kyau, to kayi sauri ina nan ina jiran ka "
zaune yake bakin gado sai dialing number Aairah yake amma bata picking ga umma dake bakin ƙofa tana faɗa mashi shi kaɗai su ke jira, ganin dai da gaske ba ɗagawa zata yi bane ya sa shi haƙura da kiran ya miƙe trollyn shi da ke bakin gadon ya ja haɗi da sanya wayar cikin aljihu, da kaga fuskar shi zaka tabbatar da cewa yana cikin damuwa,kwata kwata ba walwala a fuskar shi duk dan saboda kiran Aairah da yayi bata picking, da ya fita tsaye ya samu ummah tana jiran shi ya fito, da kallo Aunty safiya ta bishi " wai mus'af  mike damunka ne,  tafiyar ce baka son yi ko mi"
"a'a ummah "

"idan ba ita bace ba ka son lyi ba, ace tun last month kasan da wannan tafiyar amma ace har yau baka gama shirin da zaka yi ba "

"kiyi haƙuri na gama yanzu " 

gaba tayi tana faɗin "ka taho mu wuce kowa na waje yana jiran ka "

bin  bayan ta yayi, a compound su ka samu abba da su najma su kawai su ke jira, suna isowa wurin su ba ɓata lokaci kowa ya shiga mota su ka fice faga gidan zuwa airport, mus'af duk a takure Aairah  taƙi kiran shi, bini bini ya duba waya amma shiru har su ka iso airport  tun yana sa ran ganin kiranta har ya fidda rai, parking su kayi a parking lot ɗin airport ɗin, fitowa su kayi su ka ɗunguma zuwa ciki, saura 25 minutes jirgin su ya tashi, zama su kayi kan chair's ɗin da aka tana da domin zama, mus'af gaba ɗaya ya kasa sukuni sai zuba idon ganin Aairah yake amma shiru har dai Abba da ummah su ka lura da halin da yake ciki, Abba yace " lafiya dai ko mus'af"
"lafiya lau Abba "
"A'a ba dai lau ba, ko a kwai wanda ka ke jiran zuwan shi ne " girgiza ma Abba kai yayi alamar a'a, har lokaci ya rage saura  15 minutes jirgin su ya tashi Aairah bata kira shi ba ba kuma ta zo ba, sai da ana saura 8 minutes sai ga su sun zo ita da Aaimah harda mom ya Abdallah ya kawo su, sunje gidan  mai gadi yake sanar da su ai sun tafi airport ɗin tun ɗazu, shine su ka biyo bayan su, mus'af har wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin Aairah,da sauri ya nufe ta ganin mom da ya Abdallah ne yasa shi waskewa ya nufi mom ɗin, murmushi Aairah tayi dan ta san wurin ta ya nufo ,so yake su ƙeɓe domin suyi ban kwana amma  Abdallah ya kasa ya tsare,sai dai kowannan su ya ƙurama ɗan uwan shi ido ba yanda su ka iya dole su kai ban kwana kamar  kowa,kowa da kewar ɗan uwan shi, jirgin su na ta shi kowa ya nufi mota, mom bin su Aunty safiya tayi zata je gidan granny, da mom zata tafi Aaimah  ba yan da bata yi ba akan tana son su bi mom gidan granny amma ya Abdallah ya hana, Aairah daman bata tanka ba dan ta mafi so su tafi gida,suna isa gida parking yayi a parking space,yana gama parking ko kashe motar bai yi ba Aairah ta buɗe ta fice, bedroom ɗin su direct ta nufa,tana shiga ta faɗa  kan bed fashewa tayi da wani kuka mai tsuma zuciya sai kace wacce akayi ma wani abu, a haka Aaimah ta shigo ta same ta, kallo ɗaya Aaimah tayi mata haɗi da taɓe baki tace " amma wallahi kin haɗa kanki da aiki, daman wannan cika da batsewar da kike yi a mota kuka ne kike ɓoyewa ashe, ah lallai sannun ki " banza Aairah tayi da ita sai ma ƙara sautin kukan ta da tayi, tun Aaimah nayi mata iya shege har dai ta koma lallashin ta " dan Allah Aairah kiyi haƙuri in dai ya mus'af ne zai dawo ki kwantar da hankalin ki, karatu kawai fa yaje ba wani abu ba " haka Aaimah tai ta lallashin ta har ta sa mu ta ɗan yi shiru sai sauke ajiyar zuciya take.

"ni banga abun da zai sa ki tashi hankalin ki ba Aairah, in dai ya mus'af ne zai dawo karatu ne ya tafi ba wani abu ba "

magana Aairah ta fara cikin muryar kuka
"ni fa ba tafiyar da yayi bace ta sani kuka ba "

"idan ba ita bace to minene ya saki kuka ana zaman lafiya?"

"ya Abdallah fa shi ya hana mu muyi bankwana, ya tsare mu da idanuwa ni na rasa mi yasa baya son soyayyar mu ni da ya mus'af, shima abie baya goyan baya"

dafa kafaɗar ta Aaimah tayi "sister ba wai baya son soyayyar ku bane, kawai dai abun da nake tunani ya na ganin ƙanƙantar ku ne ku duka "

"amma idan haka ne miyasa mom da Aunty safiya da Abba basa gani sai shi da Abie kawai "

"to Allah ka ɗai ya san dalilin su, amma tabbas na san ba wani abu bane "

"Allah yasa haka, amma wallahi ina matuƙar ƙaunar ya mus'af ban san ya zanyi ba idan su abie su ka ƙi goya man baya ba, ina son shi sosai "

"ki kwantar da hankalin ki in sha Allah ma za su amince,amma ki ta adu'a  Allah ya zaɓa maki abun da yafi zama alkairi, nima zan taya ki da adu'a "

Kwantar da kanta tayi saman kafaɗar Aaimah tace "Ameen sister nagode"

mangare mata kai Aaimah tayi haɗi da cewa tace" dama a kwai godiya tsakanin mu "
murmushi Aairah tayi tana shafa inda Aaimah ta mangare ta  " sorry my lovely twiny"

Aaimah tace " sister ni fa ko na ƙagara mu samu addimisson mutafi makaranta na gaji da zaman gida "
"nima Allah na gaji, ai naji ya Abdallah yace cikin satinnan za su fara bada addimisson"
"Allah ya kaimu, har na ganni a school nama so ace a hostel zamu zauna  amma abie yace A'a "
"ni daman nafison gida, ko ƙarfe nawa zan kai gida dai zan dawo " a cewar Aairah
"gaskiya na fi son zama hostel dan sai na fi karatu a can "
"ko a gida idan ka sa kanka zaka yi ai "
"ki kace koh, amma ni nasan sai na fi jin daɗin yi a hostel " sun jima suna firar sai daga baya su ka nufi main parlor Abdallah su ka samu kwance kan sofa da waya kare a kunnan shi, raɗa Aaimah tayi ma Aairah a kunne tana faɗin " ina fa zargin yaya buduwar yayi, any time yanzu cikin waya yake"
jinjina kai Aairah tayi haɗi da cewa " ni ban ma lura ba "
"kice jirgi ya bar  ki tasha, wallahi tun da ya dawo daga abuja ya koma waya kowane lokaci  "
"ah lallai kam jirgi ya bar ni a tasha "
Aaimah tace " wallahi kuwa, zan so naga wacece yaya yake kashe ma murya hak..... " bata ƙara sa ba ta dalilin make kanta da aka yi Aairah tun kafin taga wanene ta watsa dagu sai kitchen sai da ta shige ne tafara leƙen parlorn, ya Abdallah ta hango riƙe da kunnan Aaimah yana mata ƙoso a kai sai faɗin " dan Allah yaya kayi haƙuri wallahi da zafi " ta ke
"amma gulma bata da zafi ko "
"wallahi yaya ba gulma muke ba kuma ba da kai muke ba labarin school nake bata "
"Allah ko " Abdallah ya faɗa, ɗaga mashi kai tayi cikin sauri tana faɗin
" ka tambaye ta kaji "
tana faɗin haka Aairah da ke leƙen su da sauri ta koma cikin kitchen haɗi da turo ƙofar ta rufe, abun ma har so yayi ya ba Abdallah dariya, sake jan kunnan Aaimah yayi yace " daga yau idan na sake jin kuna maganar wani ko da ba tawa ba sai nayi maganin ku"ɗaga kai Aaimah tayi kamar ƙadangaruwa tace
" wallahi baza ma mu sake ba dan Allah kayi haƙuri dai " mangare mata kai yayi yana faɗin "wuce ki bani wuri " yana sakar mata kunne da gudu ta nufi up stairs tana sosa kunnen ta, Aairah dake cikin kitchen jira kawai take taji ana nocking ta shige store.
mai da wayar yayi a kunnen shi yana faɗin " hello ƴar qanwer ta"
daga cikin wayar fatima tace "ya dr kai da waye naji kamar kana magana da wata "ta faɗa cikin muryar da ke nuna bata ji daɗin jin yana magana da wata ba,  duk abun da yake faɗa ashe duk tana jin shi ,up stairs ya nufa yana  murmushi haɗi da cewa
"ba nace maki ina gida ba"
a shagwaɓe  tace " eh haka kace, amma wacece kuke magana "
"to ai sai ki tsaya na faɗa maki, wata younger sister na tace"
"twins?" ta fafa cikin sigar tambaya
"eh ɗaya daga cikin su ne "
"yaya yaushe zaka basu waya mu gaisa "
"yanzu bana kusa da su amma ki bari zan kira ki sai na ba su"
"shikenan yaya, yaushe zaka zo "
"very soon zan zo " sun jima suna waya daga ƙarshe su kayi sallama

*_✨SHAZIM✨_*

Zaune yake a office ɗin shi dake eko yana aiki a laptop , wayar sa ce ta fara ringing, hannu yasa ya jawo wayar yana ganin mai kira yayi tsaki haɗi da yin rejecting ya cigaba da aikin da ke gaban sa,wani kiran ne ya sake shigowa ,banza yayi da wayar aikin dake gaban sa kawai ya ke ,haka wayar taita ringing mai kiran bai daina kira ba shi kuma bai yi picking ba ,message ne  ya fara shigowa ba k'ak'autawa,papers d'in dake gaban sa ya ture da laptop ɗin.
dafe kansa yayi yana fad'in "da alama yarannan so su ke na koya ma su hankali " ya fad'a had'i da jawo wayar  yana shirin kashe ta wani message d'in ya shigo wata number ce daban buɗe message din yayi ya fara karantawa

_GM dr da fatan ka wayi gari cikin ƙoshin lafiya, a ko da yaushe dai ina k'ara miko ƙoƙon barata fatan zaka amshi tayi na wata rana ,ka huta lafiya daga ni masoyiyarka 🌹.._

yana gama karantawa ya ja wani dogon tsaki yana ,a zuciyar shi yana fad'in " dole nayi maganin ki yau" yana gama fad'a ya jawo landline din dake kan table din,dialing wasu numbobi yayi ,ana picking ko sallama da na cikin wayar ke mashi bai amsa ba yace
"Am waiting for you" yana gama fad'a yayi rejecting had'i da tashi daga kan kujerar da yake zaune ya koma kan sofa.
bayan kamar 5 second akayi nocking k'ofar office din ,izinin shigowa ya bada ,turo k'ofar tayi ta shigo ,kamar ko da yaushe sanye take cikin  uniform din ta farare ,sallama tayi had'i da cewa "dr gani "
batare da ya amsa sallamar da tayi ba yace
"ina wayar ki take " gaban ta ne yayi wani mummun faɗuwa ,da sauri ta d'ago tana kallon shi ,cikin in ina tace " wa...ya.. ta ...kuma d..r? " ta k'arasa maganar cikin sigar tambaya , jifar ta yayi da wani sakaran kallo haɗi da cewa  "A'a tawa"
"dan Allah kayi hak'uri dr mi zaka yi da wayata?"

"bana son jin wata magana ,zaki bani  wayar ko saina b'ata maki rai "

_abun da hidaya bata sani ba tun lokacin da ta amshi number shi a hannun dr kabir ta fara tura mashi messages yasan cewa ita ce ,dan  dr kabir ya kira shi ya fad'a mashi cewa zata kirashi ta damu akan yanayin da ya bar hospital ranar ,saboda  yasan zai yi wuya idan ta kira shi ya ɗauka dan ba kasa fai yake d'aukar baƙuwar number ba_   

hawaye ne ke sauka kan fuskar ta ,hannu tasa cikin aljihun rigar ta ta fiddo da wayar hannun ta na kyarma ta mik'a mashi ,amsa yayi ,number ta da ke cikin wayar shi yayi dialing tana fara ringing ya ɗago da kanshi ya na kallon ta ,duƙar da kai tayi tana share  hawayen da ke bin kumatunta, magana ya fara da kakausar murya
"kema ashe baki da hankali ban sani ba, ina maki kallon wacce ta san ciwan kanta ashe ba haka ki ke ba, daga yau kar na sake ganin ƙafar ki acikin office ɗina "
wasu zafafan hawaye ne suka sake wanke mata fuska, cikin muryar kuka tafara magana " dan Allah kayi haƙuri kar kace ka kore ni, wallahi kuskure ne bazan sake ba in sha Allah.... " tsawa ya daka mata
"fita ki bani wuri tunkafin ranki yayi mummunan ɓaci " kuka sosai hidaya ta fashe da shi tana bashi haƙuri, amma kwata kwata bai saurare ta ba, haka ta ja ƙafarta ta fice daga office ɗin ranta duk a jagule sai data sanin biye ma shawarar maryam da tayi take, da ta san wata rana zai ganota kuma har ya koreta da bata biye mata ba, tana fita daga office ɗin da dr kabir ta cikaro tsaye bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirji, da alama ba tun yanzu yake a bakin ƙofar ba kuma yaji duk abun da ya faru tsakanin ta da shazim, dagama yanyin kallon da yake mata ta san cewa ba abun da baiji ba...
Episode  56_57_

Fuskar shi a murtike yake  bin ta da kallon ƙasa da sama, idanuwan shi sun ƙaɗa sunyi jawur,tsantsar ɓacin rai ne a cikin su, bi tayi ta gefan shi zata wuce, da sauri ya fisgota, har sai dai da tayi ƴar ƙara saboda zafin da taji, janta yayi har office ɗin shi suna shiga ya yarfar da hannunta har sai da ta kusa faɗuwa , magana ya fara cikin kausashiyya murya dake nuna tsantsar ɓacinran da yake ciki

"dama duk abun da ke faruwa saboda shi ne, duk irin wulaƙancin da kike man dama duk  saboda shi ne?,  amma  kinyi matuƙar bani mamaki,banyi tunanin haka daga gare ki ba,mi nayi maki da zaki yi man haka, da me ya fini da har zaki zaɓi zubar da mutuncin ki na ƴa mace a idanuwan shi, why !  why !! why hidaya  "

ya ƙarasa maganar da wata kalar murya da ke nuna ya karaya,har ya buɗe baki zai sake faɗin wani abu  sautin kukanta daya karaɗe office ɗin ne ya dakatar da shi, matsawa yayi kusa da ita, ɗurƙushe take a ƙasa sai zubar da hawaye take,tausasa murya yayi yace
" saboda na nuna ɓacin raina ne kike wannan kukan, ko dan saboda ya nuna baya sonki?? "
shiru tayi bata ce ma shi ƙala ba, sake kwantar da murya yayi yana faɗin
" da ke nake magana kinyi shiru, idan ma dan nayi maki faɗa ne kike wannan kukan kiyi haƙuri, dole raina ya ɓaci ina ta fama da ke akan ki ƙarɓi soyayyata ki so ni ko da bai kai kwatan kwacin  yanda nake sonki ba amma kin ƙi, ashe duk wahalar da na ke baki gani, miyasa kika yi man haka, ko ina da wani haline wanda bai yi maki ba, idan har ina da wani abu wanda baki so ki faɗa man zan daina amma dan Allah ki rabu da shazim, shazim bazai so ki ba yasan cewa ina sonki kuma  gani yake soyayya rashin aikin yi ce, kuma zuwan da yayi abuja uncles ɗin shi sun zaɓa mashi matar da zai Aura yanzu haka tana gidan su "

Gabanta ne yayi mummunan faɗuwa jin furincin shi na ƙarshe, da sauri ta ɗago tana kallon shi da rinanun idanuwanta " ya kabir da gaske kake?" jinjina mata kai yayi alamar eh , fashewa ta sake yi da wani kukan, da sauri  ta tashi ta bar office ɗin da gudu, da sauri shima ya tashi ya bi bayan ta,ko da ta fita bata tsaya ko ina ba sai bakin gate ɗin  hospital   ɗin tana fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login