Showing 123001 words to 126000 words out of 127932 words
isa ba shazim,kuma Allah bazai kama mu da lafin wani ba tunda hukuma muka ba kayan kuma muna kyautata zaton tayi adalci ne"
"majeed ina so ka fahimci wani abu a lamarin ƙasar nan cin hanci yayi yawa muna ba da kayan nan zai ba da cin hanci ne a bashi batare da tausayin bayain Allah ba da aka ɓata ma rayuwa ba, yau da ace ƴaƴansu zasu ba da bazan da mu amma inaji ina gani bazan bari a cuci al'ummah ba "
"haka ne shazim, amma duk da haka mu miƙama hukuma ko dan su Ammy dan gaskiya ina jin tsoron abun da zai biyo baya idan muka cigaba da riƙe waɗannan kayan "
" to idan kana jin tsoro ka kira shi kace kai ba ruwanka, Amma ni ba gudu ba ja da baya " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi wata ƙofa dake kallon in da yake zaune, tashi majeed yayi yana faɗin " miyasa zaka ce haka shazim, ko da naji tsoro ai bazan iya tsame hannu na ba na barka "
Shigewa ciki yayi ba tare da yace mashi komai ba, bin bayan shi majeed ɗin yayi, tura ƙofar ɗakin yayi ya shiga, ma daidai ci ɗaki ne mai kayan gaske harda ɗan madaidaici family bed a cikin sa da sofa masu kyau guda, tsaye ya hango shazim bakin wani ɗan ƙaramin fridge ya na ɗauko robar ruwa, sofa dake ɗakin ya nufa haɗi da samun wuri ya zauna, shima zama majeed yayi yana faɗin " Please shazim ina so ka fahimce ni ne, bana so mujefa wani daga cikin ahalin mu acikin matsala ne shiyyasa na ce haka" ajiye robar ruwan shazim yayi yana faɗin " majeed akwai wani ɗan adam daya isa yayi ma bawa abun da Allah bai ƙaddara ba "
"A'a shazim "
"to inaso ka fitar da wannan tsoron a ranka ka fuskanci gaskiya, duk wani barazana da zai yi mana yana yi ne dan muji tsoro "
"to shikenan, yanzu ya zamuyi "
"karka damu zanyi shawara komai na yanke zan sanar da kai "
"to shikenan bari na koma office na barshi ba kowa "
"to shikenan, ka ja man ƙofar idan ka fita" shazim ya faɗa, tashi majeed yayi ta fita haɗi da rufe mashi ƙofar kamar yan da yace.
Zamewa yayi ya kwanta kan sofar, idanuwan shi ya rufe kamar mai bacci.
Duk yinin ranar a wannan ɗakin yayi shi ko sallah a nan yayi ta, sai da yamma bayan sallar asr ya tashi ya koma cikin office ɗin kayan da ke kan table ɗinshi ya tattara ya zuba cikin locker sannan ya ɗauki briefcase ɗin shi da wayar shi ya fice zuwa parking lot in da ya ajiye motar shi, briefcase ɗin ya fara ajiye wa sannan ya zagaya ma zaunin driver ya zauna, key yayi motar haɗi da reverse ya nufi gate, da katar da shi mai gadi yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu, parking yayi a bakin gate ɗin yana ce ma maigadin " lafiya dai ko?"
"lafiya lau ranka ya daɗe, dama wasu mutanen suka zo neman ka ɗazu"
"Suna ina?"
"ban barsu sun shigo ba yallaɓai sun tafi "
"saboda mi mudi, nan fa asibiti ce dan mi zaka hana su shigowa idan suna tare da patient ne fa "
"yallaɓai abun da yasa na hana su shigowa shine basuyi kama da marasa lafiya ba yallabai wallahi da ƴan dambe su kayi kama duk sun wani sha baƙaƙen kaya kamar sheɗanu "
"mi suka ce maka da suka zo?"
"wai maigidan su ne ya aiko su wurinka,daga ganin ba su da gaskiya shiyyasa ni da su isya muka hana su shigowa "
"koma dai minene, daga yau idan su ka sake zuwa ka kirani ka faɗa man kaji ko "
"eh naji ranka ya daɗe, insha Allah su ka sake zuwa zan kiraka na sanar da kai "
"to shikenan, buɗe man gate na wuce"
"to yallaɓai " mudi ya faɗa haɗi da nufar gate ya buɗe mashi, ficewa yayi ya daga Asibitin ya hau kan titin da zai sada shi da gida.
Wayar shi dake ciki briefcase ɗin shi ce ta fara ringing, banza yayi da wayar dan ya san bazai wuce wannan shashashan mutumin ba ne, wani kiran ne ya sake shigowa, tsaki yaja yana faɗin
"sai kuma kayi ta yi"
Kira ne yai ta shigowa ba ƙaƙautawa amma ko kallon briefcase ɗin bai yi ba bare ya ɗauki wayar har ya iso gida, horn yayi a bakin gate mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga yayi parking a parking lot ya jima a motar bai fito ba wayar shi ya ciro cikin briefcase ɗin dan ganin wane mahaluƙin ne yayi tayi mashi wannan kiran duk da yana da ya ƙinin waɗannan mutanen ne sai dai kuma da ya duba mai kiran nashi number mansoor ya gani da ta Ammy sai noraiz da fatima, faɗuwa gaban shi yayi yana faɗin
"Ya Allah, mike damun su Ammy su ke man wannan kiran" a hanzar ce ya buɗe motar ya fita ko briefcase ɗin shi bai ɗauka ba ya fice zuwa cikin gida yana shigowa main parlor tsaitsaye ya samu su Ammy har da mansoor wanda zuwan shi kenan, sallama yayi ya nufi Ammy yana faɗin "Ammy lafiya mike faruwa ne ??"
"Feenah ce ta fita tun ɗazu da safe tace man zata je gidan su ummy to shine tun ɗazu bata dawo ba da muka yi waya da ummy nake ce mata feenah wai yaushe zata dawo naga yamma tayi ko nan zata kwana shine take ceman wai wace feenah ita duk yau bata ganta ba, na kira wayarta ni da su fatima yafi a ƙirga amma a kashe kuma ka san bata da lafiya "
A jiyar zuciya shazim ya sauke yana faɗin " wallahi Ammy ba kuji yan da kuka tayar man da hankali ba, yanzu duk dan wannan yarinyar ta fita ne kukai ta man wannan kiran kuma kuka tashi hankalin ku"
"shazim ba asan inda taje ba fa nace maka kuma an kira wayarta a kashe amma kake faɗin haka "
"Ammy ina wannan yarinyar zataje da har zata ɓata, kawai dai taje yawan banzan ta da ta saba amma kina nan zata dawo da ƙafar data fita "
ran mansoor ne ya ɓaci jin abun da shazim ke faɗa ya rasa miyasa shazim bai ƙaunar feenah , amma sai yayi shiru baice komai ba
"haba shazim ya za kace haka, feenah fa yarinya ce ina zata je a garinnan da bata sani ba,dama a abuja ne sai nace taje gidan su mahaifiyar ta ko gidan ƙawayen ta "
"Ammy ki kwantar da hankalin ki in dai akan wannan yarinyar ne ba in da zata shige a garin nan ta ɓata, tana yawan da ta saba ne amma ba ɓata tayi ba "
"wai shazim minene matsalarka da feenah duk kabi ka tsani yarinya kawai dan ta nace tana sonka shine zaka riƙa jifar ta da waɗannan kalaman " slowly shazim ya juya yana kallon mansoor dake tsaye bayan shi fuskar shi a murtuke,tsantsar ɓacin rai ne a idanuwan shi, side smile shazim ya saki yana faɗin " kai kuma saukar yaushe?"
" ban sani ba " shine kawai abunda mansoor ya faɗa
" to fa daga tambaya "
"ka riƙe tambayar ka bana so" murmushi shazim yayi wanda ya bayyana kyawawan haƙuran shi
"wai wannan fushin duk na minene ƙarya na faɗa,bata yawan ne " shazim ya faɗa yana ɗaga mashi gira
"kanka ake ji kuma " mansoor ya faɗa
"dan Allah ya isa haka, ya muna cikin wani hali ku kuma daga haɗuwar ku zaku kama yi ma mutane jaraba " Ammy ta faɗa
mai da kallon shi yayi ga Ammy yana faɗin " kar ki damu fa Ammy zata dawo ne dan kanta " yana gama faɗar haka ya nufi sama zuwa part ɗin shi da kallo kawai su ka bishi, sun rasa wace irin tsana ce shazim ke yima feenah da har bai damu da ɓatan ta ba kuma ya san bata da lafiya.
Zaune su kai a parlor ko wa yayi shiru suna jiran tsammani har akayi sallar magrib ba feenah ba labarin ta, wasa wasa dai har tara na dare feenah bata dawo ba kuma duk in da suke zargin za su ganta sun je amma ba labarin ta, fidda rai su kayi da zata dawo, mansoor ne yace su tashi kowa yaje kwanta idan bata dawo ba gobe za su je police su shigar da ƙara kawai, kowa ya aminta da maganar mansoor haka ne yasa su ka tashi kowa ya nufi ɗakin baccin shi.
Ammya na shiga ɗaki wayarta na fara ringing, abun yayi matuƙar bata mamaki ganin number feenah bayan yanzu ta gama kira a kashe, picking call ɗin tayi da ko sallamar da feenah keyi bata amasa ba tace " feenah ina kika shige duk kin bi kin tayar mana da hankali " daga cikin wayar fashewa da kuka feenah tayi tana faɗin " Ammy ni bana son na koma abuja "
" haba feenah idan baki son komawa sai ki faɗa man, amma ba wai ki bar gida ba, yanzu kina ina?"
"ina gidan su wata class mate ɗina , dan Allah karki bari ya mansoor ya tafi da ni "
" shikenan bazan bari ya tafi da ke ba amma kar ki ƙara irin wannan shashancin kina jina"
" to Ammy bazan sake ba in sha Allah "
" to shikenan, gobe ki dawo da safe "
" to Ammy "
" yawwa sai da safe " ammy ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran, fita tayi zuwa part ɗin shazim,nocking tayi mansoor ne ya zo ya buɗe mata, a bakin ƙofa ta tsaya, mansoor yace" ki shigo mana Ammy "
" A'a ba sai na shigo ba, feenah ce ta kirani yanzu "
da sauri mansoor yace " ta na ina Ammy?"
"tana gidan wata ƙawar ta"
Shazim dake zaune kan sofa taɓe baki yayi a zuciyar shi yana faɗin " ni ai na sani "
" amma feenah bata da hankali shine bazata faɗi ba zata tayar ma mutane da hankali dan sakarci"
" kai dai ka bari kawai mansoor, wai abuja ne bata son komawa shine tayi tafiyar ta "
" lallai ma yarinyar nan, zata dawo ai ta samu mutane " a zuciyar shi kuma yace " na san ba kowa zai sata ba sai Innah "
"idan zaka tafi ita ka barta nan ɗin tun da tana son zama"
"Amma Ammy gata ga sa'ada abun zai yi yawa. "
"haba mansoor wane irin yawa ana zaman lafiya, idan ita ma Kairiyya bazata bika ba ka ƙyaleta lokacin da su ke san komawa sai su koma"
" shikenan Ammy" mansoor ya faɗa
" yawwa, sai da safen ku " Ammy ta faɗa haɗi da ja masu ƙofar, sai da safe su yayi mata, bedroom ɗin shazim ya nufa dan shi har ya shige.
Episode 66_67
Kamar yanda Ammy tace ma Feenah tun da safe ta dawo, sosai mansoor yayi mata faɗa kamar ya daketa,arziƙin Ammy kawai taci ya rabu da ita, washe gari da zai tafi ma faɗa yayi mata sosai akan ta kama kanta, in dai ta bari yaji ta aikata wani abu to zai zo ne da kanshi ya tafi da ita komai kuwa zatayi, ce mashi tayi inasha Allah ta bari bazata yi wani abu ba, noraiz da fatima da sa'ada su ka raka su airport shi da kairiyya dan shazim tun faɗan da su kayi ba su wani shirya ba shiyyasa bai raka shi ba.
_*✨KATSINA✨*_
Addimisson ɗin su Aairah abokin uncle Ahmad ya amso, sai dai kuma ba anan branch ɗin su dake abuja ba su ka basu Addimisson, branch ɗin su dake lagos su ka tura su,ko da uncle Ahmad ya sanar da abie cewa abie yayi baza su tafi lagos ba sai dai ya nema masu wata school ɗin anan katsina amma baza su lagos ba saboda shi baya son su zauna a hostel, mom ma da taji cewa tayi gaskiya sai dai suyi a nan amma bata bada goyan bayan suje lagos ba,su kuma suna so ba yanda ba suyi da abie ba akan ya amince yace A'a, sai ma kiran wani abokin shi yayi da ɗiyar shi ke school of nursing yace idan ba su gama bada addimisson ba yana so zai sama ma su Aairah.
" gaskiya ina tunanin sun gama ɗaukar ɗalibai amma zan bincika naji"
" to shikenan, komai kenan sai ka kirani ka sanar dani "
" to in sha Allah " abie ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran
" haba yaya miyasa zaka ce haka, tunda dai suna son makarantar yaya ai banga aibu ba, kabi su da adu'a kawai in sha Allah babu abun da zai faru da su har su gama " uncle Ahmad ya faɗa
" Ahmad ni bazan bar yarannan su zauna a hostel ba, ko da ace a cikin garinnan ne bare ba nan ba can wata uwa duniya, gaskiya bazan iya ba "
"yaya wai mi kake tsoro ne aciki, tarbiyya dai daidai gwargwado suna da ita nasan baza suyi abun da za muyi da mun sani ba, dan Allah ka bar yarannan suyi karatun su inda su ke so, ka bi su da adu'a kawai "
"dan Allah abie ka bar su, in sha Allah wani abu bazai faru da su ba sai alkairi " Abdallah ya faɗa wanda zuwan su kenan shida safwan yaji uncle Ahmad nama abie magana akan makarantar
"Ai kai daman bakin ku ɗaya da su "
"ba haka bane abie, tunda suna so kuma kai kan ka ka yarda da nagartar makarantar ka barsu kawai dan Allah"
"yaya idan kana tsoron rayuwar da za suyi ne, ni ina da wani aboki dake cikin makarantar a nan yake zaune da iyalin shi sai kawai su zauna a gidan shi amma dan Allah karka hana su "
"Yanzu dai sai Alhaji umar ya kirani na ji, idan an samu nan ɗin to nan kawai za su yi idan ba'a samu bane to"
"dan Allah dai ka bar su kawai suyi karatun su a inda su ke so "
"Kaga wanda kake magana abokinka ne kar mu takura mashi "
"Idan kana ganin haka yaya to su zauna a hostel ɗin shi sai ya riƙa lura da duk wani shigi da ficen su "
"abie wallahi ina mamakin yanda kake ko kwanto akan su Aaimah"
"dole nayi kokwanto Abdallah, yara ne yanzu ka haife su ne baka haifi halin su ba "
"haka ne abie, abun da nake gani kawai mizai hana su zauna a gidan su shazim,dama fatima a can shazim ya nema mata addimisson kaga kawai sai su riƙa zuwa tare suna dawowa tare, hankalin ka ma sai ya fi kwanciya "
"to zan dai fi yarda da hakan, amma kana ganin baza'a ta kura su ba "
Uncle sadiq dai na gefe yana sauraron su kamar yana fahimtar mi suke faɗa, safwan ma sauraron na su yake amma baice ƙala ba
"haba abie wane irin takura kuma shazim fa nace maka ba wani ba,yanzu idan yaji kace haka ai bazai ji daɗi ba"
"duk da haka Abdallah, ka san halin su Aairah ba jin magana su ke ba kana gani a nan idan iya shegen su ya motsa yanda ake fama da su"
"wannan abie duk rashin aikin yi ne ke damun su, Amma da sun fara zuwa makaranta za su daina wasu abubuwan "
Fitowa su kayi daga cikin gidan
Aairah na ɗauke da tray wanda snacks ne a ciki, Aaimah kuma ruwa ne acikin trayn dake hannun ta yayin da Ameerah bowl ne babba a hannun ta yanka kun kayan marmari ne a ciki, wurin su abie su ka nufa dake zaune a garden, ƙarasawa wurin su su ka yi,ya Abdallah ne ya nufe su trayn dake hannun Aaimah ya amsa safwan kuma ya amshi na hannun Aairah yana ce mata " sannu da ƙoƙari "
Yawwa tace tana ya mutse fuska
"to fa ni da yake bani da galihu shiyyasa ba'a amshi na hannu na ba " Ameerah ta faɗa, dungure mata kai Abdallah yayi yana faɗin "bani nan uwar yan ƙorafi " turo baki tayi tana faɗin " yo ai dole nayi magana ya Abdallah an amshi na hannun su amma ni ban da ni "
"to naji Abdallah ya faɗa yana ajiye bowl ɗin da ya amsa a hannunta kan table ɗin da ya ajiye saura kusa da su abie.
"to oya a koma ciki" Abdallah ya faɗa, juyawa su kayi su ka nufi cikin gidan
wurin su abie ya koma,zama yayi kan kujerar da ya taso ɗazu yana faɗin
" abie babu wata matsala za su iya zama a can "
" amma Abdallah baka ganin za'a takura su, ni dai da ka bari kawai na nemar masu wata a nan"
" abie babu wani takura, amma idan baka son zaman su a can to dan Allah ka bari su zauna hostel,babu abun da zai faru da su in sha Allah, Amma na san Ammy bazata ji daɗi ba ace tana garin su zauna a hostel "
"A'a gaskiya ba za su zauna a hostel ba "
" to shikenan ka bari kawai nayi ma Ammyn magana "
" to shikenan, kira ta ni sai nayi mata baya ni da kaina"
to Abdallah yace yayin da yake zaro wayar shi dake cikin aljihu yayi dialing number Ammy, tana picking ya miƙa ma Abie tana faɗin gashi abie, amsa yayi haɗi da kara wayar a kunne, muryar Ammy yaji tana sallama haɗi da faɗin " Abdallah "
"bashi bane abie ɗin sa ne, an wuni lafiya "
" lafiya lau Alhmdllh, ya aiki"
" Alhmdllh, ina su shazim "
" suna nan lafiya, ya su hajiya kubrah da ƴaƴa na, har yau dai sunƙi zuwa ko daya ke ba'a kawo man su ba zance ?"
" suna nan lafiya saboda su ne ma yasa na kira "
" to, Allah yasa lafiya?"
"lafiya lau, maganar makaranta ne mun nema masu makaranta ne a abuja to da suka basu addimisson sai suka tura su branch ɗin su dake nan lagos, bana son su zauna a hostel ne saboda yara yanzu suna gaban ka ma sai a hankali bare ace basa gaban ka,shine nake son su zauna nan sai su dunga zuwa suna dawowa "
" Amma