Showing 60001 words to 63000 words out of 127932 words

Chapter 21 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6709

ɗan gwaggo Halima , ɗayar kuma bata wuce shekara 25,  sai motar da ke bayan su yar matashi yar buduwar wa ce ta fito baza wuce sa'annin su kairiyya ba, sai maza su uku, motar da bayan su kuma duka maza ne manya su huɗu,du kan su part ɗin innah su ka nufa da sallama a bakin su, innah na zaune kan sofa ita matar da ta fara shigowa , tashi innah tayi tana faɗin " lale marhabun , sannun ku da zuwa" wurin zama ko wannan su ya samu, wa su kan sofa wasu kan carpet,   feenah ce ta shigo  da gudu daga ita sai vest da da wando gyelen da ta ɗaure kan ta da shi a hannu ta shigo da shi ta nufi wannan  matashiyar wacce za su yi sa'annin, hugging ɗin ta tayi "oyoyo sister yau she rabon da na ganki "
"ai baki son zumunci ne feenah "
"kaji sai kace kema zumunci kike so"
"wallahi kin san gara ni da ke "
"ba wani nan, yau she rabun ki da abuja, zaki wani ce gara ke "
babban da ke cikin su ne ya daka ma feenah tsawa yana faɗin " ke baki da hankali , baki ganin  mutane zaki wani shigo da gudu ko sallama babu, ji kayan da ke jikin ki " faɗuwa gaban ta yayi dan shaf ta manta da wane kaya ne jikin ta, ta kuma manta cewa harda ya usman za'a zo, dan bala'in shakkar sa take
"iskanci ki na nan ko,ki shiga hankalin ki da ni, kina son kafin na bar garinnan jikin ki yayi tsami, sa karya kawai " innah tace "A'a usman da kata daga shigowar ka baza ka ta kura ma yarinya ba, kai shikenan bazata nuna murnar ganin ƴar uwar ta ba "
wannan matar ce wacce ta shigo daga baya  gwaggo Halima tace "dama mama  har yanzu baki daina goyan bayan  feenah ba, ki duba fa yan da ta shigo ko sallama babu, ji kayan da ke jikinta  "
"dan Allah ya isa haka sadiya, daga zuwan ku za ku ta kurama yarin ya, sai ɗoki take ku zo amma kun zo za ku fara tasa ta gaba da masifa "
"to shikenan , nayi shiru "
Usman yace "zaki fice kije ki canza kayannan ko sai na ɓaɓɓalaki wa wuya kawai"
jan hannun matashiyar budurwar feenah tayi su ka fice, su Fatima ne su ka shigo su  da momy  bakin su ɗauke da  sallama, amsa masu sallamar su kayi cikin parlorn su ka shiga, gaisawa momy ta shiga yi da su gwaggo uwani, su fatima gaishe da  su su kayi,gwaggo Halima ce kawai ta amsa gaisuwar da fatima tayi masu , amma gwaggo uwani yi tayi kamar ma bata san da fatima ba a parlorn sai ma tashi da tayi ta nufi ɗakin innah,da idanu kawai fatima ta bi ta idanun ta na kawo ƙwalla, gwaggo Halima ce ta lura da halin da fatima ta shiga, dafa kafaɗar tayi "Fatima ya Ammyn ku, ina su noraiz da shazim " tayi mata tambayar ne dan ta kau da mata hankali daga abun da gwaggo uwani tayi mata,
"ya noor na tare da ya mahmud, ya shazim ne dai ban san inda yake ba amma ina tunanin yana tare da ya mansoor "
"masha Allah, ya su malam"
"lafiya lau su ke " janta da fira tai tayi har sai da ta saki ranta
"Fatima mu baki ganmu ba ne " wata kyakyawar budurwa ce zaune kusa da sa'ada
"Allah sarki Aunty farida so nake mu gama gaisawa da gwaggo, ina wuni, ya hanya?"
"lafiya lau fatima, ya lagos, ina Ammy"
"Ammy na lagos "
ɗaya bayan ɗaya fatima ta bisu tana gaishe da su, wasu su amsa wasu yi banza da ita,har da masu sarka mata habaici,  da ta gaji da ganin abun da suke mata tashi tayi ta bar part ɗin ta nufi na su, hawayen da take ɓoyewa ne su ka shiga gangaro mata, tarasa miyasa gwaggo uwani bata ƙaunar su ita da ƴaƴen ta, ta ci kuka kamar mi ita ka ɗai a part ɗin har bacci ya ɗauke ta kan sofa.
A can part ɗin Innah kuwa, gwaggo Halima ce ta kalli su Aunty maryam da su Aunty Amina tace "yanzu ku da hankali ku da wayan ku kuke abu kamar wasu ƙananan yara, musamman ke maryam da girman ki zaki biye ma su Asma'u "
Aunty maryam tace "mi nayi kuma mama "
"ina kallon ku ke da su Asma'u  Fatima ta gaishe ku Zainab ce da Fiddausi kawai su ka amsa mata, miyasa kuke haka da hankalin ku"
"mun fa amsa baki lura bane "
tsaki ya usman ya jaya " wallahi har mamaki ki ke bani maryam ko yaro ƙaramin bazai yi abun da kike yi ba , ku kuma ku shiga hankalin ku" ya faɗa haɗi da nuna su da yatsa, mama ce ta shigo su ka gaisa da gwaggo Halima, bata wani jima ba ta koma part ɗin ta, mai aikin momy da mama ne suka shigo da manyan tray ɗauke da ruwa da lemu, bayan sun ajiye masu gaishe da su suka yi, sannan su ka fice suka kawo masu abinci da snacks .
Mansoor ne ya shigo parlorn, wuri ya samu kan sofa yana gaishe da su gwaggo uwani wacce   fito war ta kenan  daga bedroom ɗin Innah, hannu ya miƙa ma usman su ka gaisa "ya usman kwana da yawa, ka shige jos ba'ajin ɗuriyar ka"
"ba wani na shige jos, ai kai da shazim ba mutunci ne da ku ba, musamman shazim sai ya shigo jos sau ba a dadi amma ban taɓa ganin ƙeyar shi ba"
"Ka san shi da aiki ya Usman, may be shi ke hana shi zuwa in da kake"
"ba wani aiki kawai dai ba ya son zumunci ne"
gwaggo Halima ce tace"mansoor yana  ina ne   abokin naka "
"wai shazim?"
"Eh shi "
"Ina tunanin yana part ɗin su,na kira maki shine?"
"a'a ƙyale shi na san zai shigo " tsaki gwaggo uwani ta ja tana ce ma mansoor "kai je ka kira shi, tun da shi ya fi ƙarfin ya shigo gaishe da mutane"
"da kin  ƙyale shi yaya, na san zai shigo zuwa anjima kuma ma duka mintin mu nawa da shigowa, ra bu da shu Mansoor ba sai ka kira shi ba  "
"haka ku ke dama ke da su yaya, yaro yaita abun da yaga dama  amma ku baku gani, da ance kaza za ku kare shi"
"ba haka bane, idan har kika ga munyi goyi bayan shi to fah yana da gaskiya, haka nan baya abu batare da dalili ba"
" haka ku kaci rani, in dai shazim ne za mu gani "
banza gwaggo Halima tayi da ita kamar ma ba da ita  take maganar ba,
Mansoor yana nan zaune  noraiz da mahmud su ka shigo, wuri suma suka samu kusa mansoor su ka zauna, gwaggo uwani ce tace " ai nayi tunanin kai ma kafi ƙarfin gaishe da mutane kamar ɗan uwan ka " bai amsa mata tambayar ta ba sai ma gaishe ta da yayi, haushi abun ya bata , ta so ya bata amsa amma sai yayi kamar ma ba da shi take ba, da lafiya ta amsa mashi
suna gama  gaishe da su , su kayi  fice war su, su noraiz basu jima da fita ba  ba mazan ma su ka  tashi har da mansoor suka fice, shi da anwar part ɗin su shazim suka nufa sauran kuma suka nufi part ɗin da aka tana da domin su, a can su saude su ka kai ma su abinci.
bedroom ɗin sa suka nufa, mansoor yayi nocking har ya gaji, wayar shi ya ciro daga aljihu ta lalubo number shazim ya kira, har ta tsinke bai yi picking ba sai da ya sake kira sannan yayi picking, yana ɗauka mansoor yace "kai wai kana lafiya ake ta nocking " kwance yake kan bed ɗin Abdallah a gidan uncle Ahmad, ɗan ya tsina fuska yayi yana faɗin "bafa na nan, na fita tun ɗazu"
"ok kana ina ne?"
"ina wurin Abdallah "
"yaushe zaka dawo,su Anwar fa sun zo kuma gwaggo  Halima na neman ka"
"may be  sai dare ko gobe" amsar wayar Anwar yayi yana faɗin "muna gidan zaka ce wai sai gobe, wasa dai kake ko"
"Anwar ya hanya "
"Alhmdllh, ina nan ina jiran shigowar ka"
"to shikenan sai na shigo "
"ok ina zama jira "yana gama faɗa yayi rejecting kiran, barin part ɗin su kayi zuwa part  ɗin mansoor.

Sai da yamma liƙis su  Abbah  suka dawo daga wurin aiki  nan part ɗin innah su ka yada zango a parlor, suna firar yaushe gamo da ƴan uwan su,
Auny uwani ce tace" yaya ba naji kamar kace shazim da noraiz suna garinnan ba da muka yi waya da kai "
Uncle Ahmad yace "eh suna nan, basu shigo kun gaisa ba ne "
"banga ƙeyar ko ɗaya daga cikin su ba, dama noraiz me ɗan iya gaishe da mutane inya gansu, shi ko wannan uban marasa kunyar yafi ƙarfin gaishe da kowa"
Uncle Ahmad yace "haba uwani, wai miyasa a kowane lokaci kike ma shazim musammanar fahimta ne,yanzu haka baya nan ne , shi yasa baizo ya gaishe da ku ba "
"dama nasan haka zaka ce yaya, da anyi magana kan shi sai ku   goyi bayan shi "
gwaggo Halima tace"bawai an goyi bayan shi bane, kece dai baki fahimci shi ba, kuma ai noraiz ya shigo nan kun gaisa da shi "
"to naji, ai naga ke yazo ya gaishe ki ke da kika fahimci shi" girgiza kai kawai gwaggo Halima tayi ba tare da tace komi ba,
Uncle Ahmad yace
"ya isa haka, idan ya dawo zai shigo ku gaisa "
"Allah yasa "a cewar gwaggo uwani
sunjima a part innah suna fira, sai da aka fara kiraye kirayen sallar magrib su ka bar prt ɗin zuwa masallaci, su ma gwaggo Halima ta shi su kayi su ka shiga ɗakin Innah domin gabatar da ta su sallar, har sai da su kayi isha sannan su ka dawo parlor , sai bayan sallar isha kairiyya ma ta shigo gai she da su, su Aunty maryam kamar su cinye ta dan bata zo tun ɗazu ba, haƙuri ta ba su akan bata jin daɗin ne shiyyasa ba shigo ba, bata wani jima ba ita ma ta koma part ɗin su.

feenah tun korar da usman yayi mata bata sake shigowa part ɗin ba sai yanzu ta shigo ita da ilham, a nan parlor suka zauna suna fira da su Aunty maryam.

Wuraren ƙarfe 9 ya motar shi ta shigo estate ɗin, a hankali yake driving  kamar baya son yi, part ɗin su ya nufa yayi parking, ya jima zaune a mota yana  waya, sai da ya kammala wayar shi tukunnan ya fito ya nufi cikin part ɗin tsit babu motsin kowa kamar ko wane lokaci, bedroom ɗin shi ya nufa, kayan jikin shi ya shiga ragewa bayan ya ajiye wayar shi da key ɗin motar da ya fita, toilet ya shiga, bayan kamar   10 minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe, bakin window yaje ya tsaya yana kallon   cikin estate ta baya  kamar mai tunanin  wani abu , ya jima a tsaye a wurin,daga baya ya saki curtain ya bar jikin window ya nufi clothes set ɗin shi, pajamas ya ɗauko riga da wando, wandon iya kar shi gwiwa sai riga mai garen hannun,cire bathrobe ɗin jikin shi yayi daga shi sai short, pajamas ɗin ya ɗauka ya sa, bayan ya gama sawa,cap ya ɗauko irin ta sanyi black color ya sa,fehe jikin shi yayi da turaren shi mai ƙamshi,  wayar sa da ya ajiye kan bed ya ɗauka ya zura ta cikin pocket ɗin wando, flip flops ya zura a ƙafar shi, fita yayi daga bedroom ɗin main parlor ya nufa fita yayi daga part ɗin zuwa part ɗin mansoor,yana shiga main parlor su Amina,  Asma'u da farida ya samu zaune kan sofa suna fira sai  kairiyya  da ke kwance kan sofa,ɗauke kai yayi daga kansu,  amsa mashi sallamar da yayi su kayi, gaishe da shi su ka shiga yi, ba tare da ya tsaya ba ko ya kalli inda su ke ba yace lafiya, iya abun da yace kenan ya haura sama wurin mansoor, tura ƙofar parlorn yayi ya shiga, samun mansoor yayi zaune kan doguwar sofa shi da Fiddausi suna fira ( ɗiyar gwaggo Halima ce,  ita ce budurwar shi da suke waya )  a bakin ƙofa ya tsaya yana kallon su, daga baya kuma ya shigo cikin parlorn, mansoor yace "ok ashe zaka dawo " ba tare da ya amsa mashi tambayar da yayi mashi ba, fuska a ɗaure ya kalli Fiddausi yace "ke tashi ki ba mutane wuri
Episode 34_35

Wani ɗan iskan kallo shazim ke bin mansoor da shi
"kasan Allah ko ma wane irin kallo zaka man sai dai kayi amma ba in da zata, tun da ba kai ka kawo ta ba "
"ok haka kace "
"Kwarai kuwa haka nace, kayi duk abun da ka ga dama " Fiddausi dai na bayan mansoor tana zare idanu ƙes take jira ta watsa a guje, kallon ta shazim yayi yana faɗin "ke zaki zo ki wuce ko sai ranki yayi mumunnan ɓaci "
fitowa tayi daga bayan mansoor zata fice, jawo hannun ta mansoor yayi yana faɗin "in wasa da ke ne " hawaye suka fara sauka daga fuskar ta, girgiza mashai kai tayi alamar a'a, "to koma kan sofa ki zauna " ƙin komawa tayi saima sake ɓoyewa da tayi bayan mansoor ɗin, nufo su shazim yayi gadan gadan, ai ba shiri ta watsa da gudan, dan bata san mi zai yi mata idan har ya kamta,sai da ta kusa shiga parlor sannan ta tsaya kan stairs case tana mai da nufashi,  kallon ta su Asma'u su kayi, Amina tace "ke lafiya daga ina haka, sai kace wacce wani abun tsoron ya biyo " bata bata amsar tambayar da tayi mata ba sai ma binsu da take yi da idanu, sai da ta ɗan dawo cikin hankalin ta sannan ta ƙaraso cikin parlorn ta nemi wuri kan sofa ta zauna,sake tambayar ta Amina tayi "yo yana wuce ya shazim ne ya koro to" acewar Asma'u,
Amina tace "wai baza ki yi magana bane"
Sai a lokacin ta samu damar cewa "ya shazim ne ya koro ni ya mansoor yace ba inda zani, ganin yace ba idan za ni ne yasa nayi zama na, wallahi ina faɗa maku kaɗan ya hana bai make ni ba "
Asma'u tace "dama nasan za'a rina, ni narasa miyasa ya shazim yake wannan isa da mallakar, samun ya mansoor ɗin yayi " Amina tace
"Wallahi kuwa rainin wayaun shi yawa gare shi, sai kace wani ɗakin shi da zai wani koro ta "
Asma'u tace " samun ya mansoor ɗin yayi da har zai nuna mashi wannan isa da mallakar " farida ce tace "wallahi babu ruwana kun ga tafiya ta, dan zai iya fitowa a kowane lokaci kuma kun san mi zai biyo baya idan ya kama ku kuna gulmar sa "
tsaki Asma'u taja tana faɗin "matsoraciyar banza da wofi kawai, yo to sai mi dan ya kama mu "
"Wallahi kun san mi zai biyo "
"duk abun da zai biyo baya bawai muna tsoron shi bane "
"ok haka kuka ce Allah ya fito da shi inga ta tsiyar cika baki " tana gama faɗa ta shige war ta ɗakin kairiyya

*✨SHAZIM✨*

A can bedroom ɗin mansoor, bayan fitar Fiddausi da gudu, kallon shazim mansoor yayi yana faɗin "wallahi kaji kunya, sai kace kai ka kawo ta da zaka wani kore ta, idan kai baka soyayya  an gaya maka kowa irin ka ne wanda  bai san in da ke mashi ciwo ba"
"Wannan kuma ki ake ji, ko yanzu nasa ke ganin wata acikin su sai na ɓata mata rai yanda baka tunanin, inga abun da zaka iya "
"Zan kira ta sai inga abun da za kayi, mara mutuncin kawai "
"Oho dai koma mi zaka ce ka daɗe baka ce ba, na mamajo kawai "
"Naji ni na mamajo ne, wanda bai san inda ke mashi ciwo ba fa "
"Kai ake ji idan ma ka fita kasa kairiyya ta kawo man tea " ya faɗa haɗi  da neman wurin zama kan sofa yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya
"Wannan ne kuma baka isa ba "tsaki shazim yaja ba tare da ya bashi amsar maganar shi ba, ficewa mansoor yayi daga bedroom ɗin zuwa parlor, kamar yanda Farida ta bar su Asma'u na gulmar shazim haka mansoor yazo ya same su,bakin benan ya tsaya yana sauraron duk abun da suke faɗa, kairiyya ce da ke kwance ta hange sa ta witsiyar ido, gyaran murya tayi masu amma hakan bai sa sunyi shiru ba sai sake ba da ƙaimi da su kayi wurin yin maganar "da alama  sara kuke  baku duba bakin gatarin ku " jin haka ne yasa fahimtar akwai abun da take son su fahimta, ɗagowar da Amina zatayi karab idanunta kan mansoor daya harɗe hannuwan shi kan ƙirji yana kallon su, duƙar da kai su ka yi ƙasa  , ƙara sowa mansoor yayi cikin parlorn"sannun ku da ƙoƙari ko " ya faɗa yana binsu da idanuwa,ba wacce  ta ce ƙala a cikin su saima tashi da su kayi sumi sumi su ka bar parlorn , tashi Fiddausi tayi zata bi bayan  su , muryar mansoor taji yana faɗin "koma ki zauna " dawo wa tayi ta nemi wuri kan sofar da ta tashi, ɗuƙar da kai tayi tana wasa da ƴan ya tsun hannunta, tashi kairiyya tayi zata bar wuri da katar da ita mansoor yayi ta hanyar cewa "ki kaima shazim tea " da to ta amsa haɗi da nufar kitchen,haƙuri mansoor ya ba Fiddausi akan abun da shazim yayi mata" bakomi ai yaya " fira suka cigaba da yi ciki shauƙin soyayya, zuwa kairiyya tayi ta wuce ta gaban su zuwa sama hannun ta ɗauke da trayn da ta haɗo ma shazim tea,zaune yake kamar yan da mansoor ya barshi,ƙafa ɗaya kan ɗaya yana latsa wayar shi,   ciki ta shiga da sallama a bakin ta, sallamar da tayi ya amsa, ƙara sawa tayi cikin parlorn kan table ɗin dake ɗakin ta ɗaura mashi trayn, tnxs yace, fice wa  ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login