Showing 90001 words to 93000 words out of 127932 words

Chapter 31 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6704

ba'a fito da ruma ba likitocin ma ba wanda ya fito, hankalin nuraddeen ya kai ƙololuwar tashi, sai da wasu awannin suka shuɗe sannan wata nurse ta fito daga ɗakin hannun ta riƙe da jariri cikin towel, da sauri nuraddeen da bilkisu suka nufo nurse ɗin suna tambayar ta jikin ruma,miƙa ma bilkisu jaririn tayi tana faɗin "ana gyarata ne,idan an maida ta ɗakin hutu sai ku ganta" da to su ka amsa mata , amsar jaririn bilkisu  tayi tana kallon shi kyakyawan gaske a cikin  kamannin ruma babu abun da ya baro kamar tayi kaki, idonun shi rufe da a lama bacci ya ke, barin wurin su nurse ɗin tayi, hankalin nuraddeen duk a tashe so kawai ya ke yayi ido biyu da ruma,  sake buɗe ƙofar theater room ɗin aka yi dr ne ya fito yana cire safar hannun shi, da sauri nuraddeen ya ƙarasa wurin shi yana tambayar shi wane hali matar shi ke ciki,  "  Allah ya bamu ikwan cetan jaririn amma mahaifiyar shi ta sha wahala sosai,  yanzu dai munyi mata allurar bacci tana ɗakin hutu,ko da  za ku  ganta sai  zuwa anjima"
"to shikenan dr, nagode "ya faɗa haɗi da miƙa ma mashi hannu su kayi musaba ha, dr yace "babu komi, Allah ya bata lafiya"da ameen nuraddeen ya amsa, wuce wa dr yayi zuwa office ɗin shi,nuraddeen  komawa yayi idan da  bilkisu take ya amshi jaririn yana kallon shi, ji yake  kamar ya mai da shi ciki tsabar yanda ya ke son shi, ruma bata farka ba sai wajen ƙarfe 9, nurse ce tazo ta sanar da su farkawar ruma, ta shi su kayi suka bi bayan nurse ɗin nuraddeen har yan tuntuɓe saboda sauri.

Kwance take kan gadon marasa lafiya, jin an buɗe ƙofa ne yasa ta buɗe idanuwan ta dake rufe, binsu take da idanu ko ɗan ya tsanta bata iya ɗagawa, ba ƙaramin jin jiki take ba, zama nuraddeen yayi kan kujerar dake kusa da gadon, bilkisu kuma ta zauna kan gado, sannu su ka shiga yi mata,bata amsa masu ba sai ma hawayen da ke bin kumatun ta, hannu nuraddeen yasa yana share mata hawayen"ki daina kuka ruma Allah zai baki lafiya" jinjina kai tayi, hankalin nuraddeen duk ya ta shi ganin ko magana bata iyayi, yunƙurin tashi take zaune,pillow yasa ya  taimaka mata ta ɗan jingina da bango sannu kawai su ke mata, kiran sunan nuraddeen tayi , da sauri yace na'am, hannunta ta miƙa ganin tana son kama hannun shi ne yasa shi sauri kama nata hannun yana ƙara mata sannu, da ƙyar ta buɗe bakinta tana tamabayar ina abun da ta haifa, da sauri bilkisu ta miƙa mata jaririn da ke hannunta, amsa tayi ta zubama jaririn ido tana kallon shi hawaye na bin idanun ta, gaba ɗaya duk tabi ta karya masu zuciya da kukan da take, ta ɗauki tsawan lokaci tana kallon jaririn daga bisa ni ta miƙa ma nuraddeen shi,amsa yayi yana kallon ta, murmushi ta sakar mashi, da ƙyar magana take fita daga bakinta tace "ina so kasa mashi sunan mahaifina dan Allah, sannan  kayi man alƙawarin baza ka taɓa bari yayi maraici ba, ji nake kamar bazan tashi ba "
"dan Allah ki dai na cewa haka cuta ai ba mutuwa bace in sha Allah zaki samu lafiya "
Bilkisu hawaye ne kawai ke zuba daga idanunta duk ta karaya
"ina so dai ka ɗaukar man alƙawari "
"In sha Allah zanyi maki yan da kike so fatana Allah ya baki lafiya " nuraddeen ya faɗa,"na gode, ina so kowannan ku ya yafe man duk wani abun da nayi mashi, duk wani wanda kuka san na taɓa mu'amula da shi ina son ku roƙar man shi ya ya feman "
sai haƙuri su ke bata ciwo ba mutuwaba ne, sai dai tayi murmushi idan su ka faɗa mata haka, nurse ce ta shigo ta sanar da nuraddeen likita na son ganin shi,  tashi yayi ya bi bayan ta har office ɗin dr , wurin zama dr ya nuna mashi,  zama yayi yana zuba dr ido yana sauraron mi zaice, magana dr ya fara " da man ba wani abu bane yasa na kira ka, game da jaririn ya kamata a nemo mashi madara saboda lafiyar shi zuwa  wani ɗan lokaci sai mahaifiyar ta shi ta cigaba da shayar da shi,sannan ita ma akwai wasu  magunguna da ya kamata ita mahaifiyar tashi ta riƙa sha " dr nagama faɗa ya rubuta mashi sunan magungunan da madarar da ya kamata a riƙa ba yaron kafin mahaifiyar shi ta cigaba da shayar da shi, yana gama rubutawa ya miƙa mashi, amsa yayi haɗi da yima dr godiya ya fice zuwa ɗakin da ruma take kwance,yana buɗe ƙofa ya samu bilkisu ta kifa kai da bango sai shashekar kuka take ruma kuma jikinta rufe yake da farin ƙyalle,wani irin  faɗuwa da gaban shi yayi jikake dam dam, dafe saitin zuciyar shi yayi yana nufar gadon da take kwance hannun shi na rawa ya yaye farin ƙyale da aka rufe ta da shi, fuskarta ta bayyana idanuwan ta a rufe suke fuskarta da alamun murmushi, suma tsaye nuraddeen yayi lokacin guda ya tsinci kanshi ciki wani yanayi mara daɗi, hawaye ne suka shiga sakkowa daga idanun shi,zubewa yayi ƙasa kan gwiwowin shi  yana faɗin "yanzu shikenan na rasa ruma har abada,kai hakan bazai yiwuba " sai sambatu yake kamar wanda ya zare, jin maganganun da yake ne ya ƙara karya zuciyar bilkisu ta ƙara sautin kukan da take.

_*ALLAH SARKI RUMA UBANGIJI ALLAH YA JIƘANKI DA RAHAMA ABUN DA KIKA BARI ALLAH YA RAYA SHI*_

A wannan yana yin faɗa maku tashi hankalin da nuraddeen, bilkisu, iyah, mahaifiyar ruma suka shiga ɓata lokaci ne, sun shiga tashin hankali mara misltuwa.
bilkisu ta cigaba da kula da jaririn har aka yi adu'ar uku, sannan nuraddeen yayi ma yaron huɗu ba da suna Abubakar sadiq,ya ciki alƙawarin da ya ɗaukar ma ruma,  har akayi arba'in da rasuwar ruma sadiq na hannun bilkisu, da ta tashi komawa katsina da sadiq ta tafi har aka yaye shi, san da aka  yaye shi mijin bilkisu ya nemi  da abashi sadiq,amma sai nuraddeen yace a'a shima yana son yaron shi ya taso a gaban shi,bilkisu ta so ace nuraddeen zai bar mata sadiq a hannun ta amma bata da yan da zata yi haka ta dawo da sadiq hannun mahaifin shi,lokacin da  mijinta aka tura shi ƙasar china jakadancin nigeria, har kurfi ta zo ta sake roƙon nuraddeen daya bata sadiq ɗin ta tafi da shi, amma yace a'a idan dai sun zo nigeria zai riƙa zuwa masu hutu, taji haushin ƙin bata sadiq da nuraddeen yayi amma bata da yan da zata yi tun da ɗan shi ne dan dole ta haƙura ta tafi da kewar yaron.

Kulawa  sosai sadiq ke sa mu wurin mahaifin shi da kakar shi iyah, ganin yan da iyah da nuraddeen ke kula da sadiq ya sa maijidda ɗaura mashi karan tsana duk da yake ƙaramin yaro, ƴan uwan shi na son shi amma ta hana su ma'amula da shi, ko wasa suke ya zo wurin su sai ta sa su kore shi ko su dake shi,  tun basu ɗaukan abun da take sa su har hakan yayi ta siri da sadiq ya shiga cikin su zasu yi ta kyarar shi da hantarar shi, haka zai raɓe yana kuka ta kuma ja mashi kunne akan muddin ya faɗa ma nuraddeen sai tayi mashi dukan tsiya, bawan Allah haka zai shiru bai taɓa faɗa ma mahaifin shi ba, wani munafuncin na maijidda idan a gaban nuraddeen sai ta nuna tana tausayi sadiq tayi ta riritashi amma idan nuraddeen baya gida wahala iri-iri babu wacce bata sa sadiq har aiki wanda ya fi ƙarfin shi sa shi take yi lokacin yana da shekara shidda  amma sai ta sashi abun da ya fi ƙarfin shi,lokacin ta ƙara haihuwa yaron na da shekara ɗaya a duniya, sunan yaron Ibrahim kyankyawa ne dan yafi su  magaji kyau shiyyasa ita ma tafi son shi a cikin su,   haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiq ya taso cikin ƙiyayyar yan uwan shi, kwata kwata baya jin daɗin zama da su, sauƙin shi ɗaya idan mahaifin shi na gida ko kuma yaje gidan iyah ko su magaji na makaranta daya ke ba makarantar su ɗaya ba ta nan kawai ya ke samun sauƙin  wahalar da yake sha ta su magaji dan har tafi wacce yake sha wurin maijidda, wurin iyah ya koma da zama dalilin wani bugu da su magaji suka yi mashi har suka ji mashi ciwo, daya je gidan iya ya faɗa mata har gida tazo ta samu maijidda tayi mata zagin wulaƙanci akan ita ta sa su magaji su ka daki sadiq, haƙuri ta shiga bama iyah ta na cewa "kiyi haƙuri dan Allah iyah, wallahi sadiq ƙarya ya ke faɗuwa yayi amma ba dukan shi su magaji suka yi ba " ji suka yi an ce "wayyayi iyah cu yaya ne cuka buge ci" Ibrahim da ke tsaye bayan maijidda ne yayi maganar lokacin yana da shikara uku, maijidda kamar ta nutse saboda baƙin cikin abun da Ibrahim ya ce yaro ne amma sai wayen tsiya,gashi  kuma bala'in son sadiq yake dan wani lokacin idan maijidda ko ƴan uwan shi suka daki sadiq nan zai zauna yana kuka da kuma mahaifin su ya dawo zai sanar da shi, murmushi iyah tayi tana faɗin "kaga ɗan albarka, dama na  san ƙarya kike,  da ma chan na lura ba son sadiq kike ba saboda kinga mahaifin shi ya fi son shi, idan bai fi son shi ba ya ki ke  so yayi yaron nan ana haihuwar shi mahaifiyar shi ta rasu  to dan mi mahaifin shi bazai nuna mashi kulawa ba, amma kinbi kin tsani yaro kin ɗaura mashi karan tsana kin hanashi wasa da ƴan uwan shi kin sa sun tsane shi saboda tsabar zalunci, to bari kiji wallahi ki shiga hankalin ki in ba haka ba zakiyi mamakin abun da zanyi maki shashasha kawai" tana gama faɗa ta ja hannun sadiq suka koma gidan ta, haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiq  na hannun iya har ya kusa  gama primary school,  yan primary  5 lokacin magaji ya kammala secondary yana bin mahaifin su kasuwa ,  uwani na ss1 halimatu na jss 3 Ibrahim kuma na primary 2 Allah yayi ma iyah rasuwa sosai sadiq ya shiga tashin hankali mara misltowa ya ci kuka kamar ranshi zai fita ana bashi haƙuri, bayan an gama zaman makokin iya sadiq ya koma gidan mahaifin shi da zama, sadiq ya ga rayuwa, wahalar maijidda  yake ci sosai ba kaɗan ba  ita da uwani, saboda magaji tun da ya girma ya watsar da huɗubar mahaifiyar shi ya kama ɗan uwan shi ganin magaji yana son sadiq yanzu yasa halimatu ita ma take janshi a jiki dama shi Ibrahim baya da matsala tuna farko, uwani ce dai dama can ita bata da mutunci  sak halin maijidda gare ta, sosai sadiq ke shan wahalar ta kai sai ayi rabon abinci a manta da shi sai  dai halimatu da Ibrahim su bashi nasu a ɓoye dan idan maijidda ta sani dukan tsiya take masu shi daman magaji baya gidan yana kasuwa tare da mahaifin shi, haka rayuwar sadiq ta cigaba da tafiya kamar mara galihu mara gata, shi da gidan mahaifin shi amma bashi da sakewa  sai in mahaifin shi da yayan shi magaji na gida,  wata rana wani aminin  nuraddeen alhaji abdulƙadir wanda suka taso tun ƙuruciya,lagos yake tun bayan rasuwar iyayen shi ya koma wurin ƙanin baban shi da zama acan yayi karatun shi ko da ƙanin mahaifin nashi ya rasu bai dawo kurfi ba a lagos ya cigaba da zama , duk da yana lagos nuraddeen na kurfi tare suke  harkar kasuwanci , sai dai shi alhaji abdulƙadir yana zuwa har  ƙasashen waje ,alhaji abdulƙadir yafi nuraddeen ƙuɗi nesa ba kusa ba,   matar shi ɗaya hajiya zainab balarabiyar ƙasar  Morocco  ce, sun haɗu ne a chan ƙasar har Allah yasa suka  yi aure, shekarar su kusan goma amma basu da ɗa ko ɗaya, zainab  tana haihuwa amma ƴaƴan basu zuwa da rai,   ko da ya  kawo ma nuraddeen ziyara bai nufi kasuwa ba gidan shi ya nufa direct , nan ya ci karo da sadiq bakin ƙofar gida yana kuka,dafa kafaɗar sadiq alhaji abdulƙadir yayi yana cewa "yaro yaya sunan ka? " cikin shashekar kuka sadiq yace "sunana sadiq "
"masha Allah, amma miyasa kake kuka, ina mahaifin ka? "sadiq ya ce
"bakomi, babana yana kasuwa"
"to ko zaka iya rakani wurin shi? " da to sadiq ya amsa mashi, har kasuwa ya raka shi wurin nuraddeen, sosai nuraddeen yayi farin ciki da ganin alhaji abdulƙadir dan sun ɗan dade basu haɗu ba, gida suka koma, nan suka shiga firar yaushe gamo, anan alhaji abdulƙadir ya nuna yana son ya tafi da sadiq logas ,ƙin amincewa nuraddeen yayi, saboda ba ƙaramin son sadiq yake ba baiso ko kaɗan yayi nesa dashi, ko da ya shiga gida fuskar shi da ɗan damuwa, tambayar shi  maijidda tayi akan mike da munshi, nan yake faɗa mata "wallahi wani aminina ne yazo, to shine ya buƙaci da na bashi sadiq, to gaskiya gani nake kamar zai ƙara ma kan shi wahala ne, dan nafi shi rufin asiri ne sa ba kusa ba, to abunda ya sa ki gannin ciki da muwa ban so yaga kamar na hanashi sadiq ne saboda ni Allah ya bani , da yake shi bai da ɗa ko ɗaya " wani da ɗi ne ya rufe  maijidda tana ganin wannan ce hanya mafi sauƙi da zata raba sadiq da nuraddeen, kuma da taji mutumin talaka ne abun ya ƙara mata daɗi sai dai  bata ji daɗin ƙin amincewa da nuraddeen yayi ba , ta so ace ya ba da sadiq ɗin ko dan ta huta da ganin shi, kuma tana ganin idan sadiq ya tafi daga nan nuraddeen bashi da wanda zai so sai ƴaƴanta, haka ta shiga zuga nuraddeen akan ya ba abdulƙadir sadiq, ita duk a tuna nin ta da gaske  abdulƙadir talaka ne bai da komi,dan bai faɗa mata Abdulƙadir bane dan ta san Abdulƙadir sosai rashin faɗa mata ko waye yasa  tai ta zuga nuraddeen,kallon ta kawai nuraddeen yake, dama yace mata aminin shi ne kuma   talaka ne dan yaga mizatayi yayi ne daman dan ya gwada ta, sai kuma yaga farin cikin ta,  hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa da gaske maijidda bata son sadiq ko ƙaɗan,  ko da magaji yaji labari shima haɗa mahaifin shi  da Allah yayi akan ya bari a tafi da sadiq ko ba komai zai samu kwanciyar hankali, sai daga baya shima nuraddeen da yayi tunani yaga da cewar ya ba abdulƙadir sadiq, ko dan shima sadiq ɗin ya huta da tsangwamar da maijidda keyi mashi ,  dan abdulƙadir mutumne mai mutunci, yana da kirki sosai kuma zai ruƙe sadiq kamar ɗan daya haifa,ya san kuma rayuwar sadiq zata chanza, har masauki ya samu abdulƙadir   ya faɗa mashi ya amince zai bashi sadiq, ba ƙaramin daɗi abdulƙadir yaji ba ya kuma yima nuraddeen godiya sosai, sannan yace ya shirya sadiq ɗin gobe da man zai koma lagos da safe , sunjima suna fira har kusan yamma sannan nuraddeen yayi mashi sallama, yana komawa gida yasa halimatu ta haɗa kayan sadiq cikin jaka, Ibrahim sai kuka yake za'a tai mashi da ɗan uwan shi wani wuri, lallashin shi sadiq yake amma ya ƙi haƙura, ita kuwa maijidda sai jin daɗi take sadiq zai shiga cikin wahala.

Washe gari da safe wurin ƙarfe  takwas abdulƙadir yazo domin tafiya da sadiq, halimatu ce ta fito da kayan sadiq har ƙofar gida, amsar jakar  drivern abdulƙadir yayi da ga hannun halimatu ya sa a bayan mota , nuraddeen ne da abdulƙadir suka fito magaji na riƙe da hannun sadiq, bankwana abdulƙadir yayi ma nuraddeen sannan ya ja hannun sadiq suka shiga mota, sadiq na ta ɗaga ma magaji da Ibrahim da halimatu hannu, suma suna ɗaga mashi hannun har motar ta bar anguwar,kasuwa nuraddeen da magaji suka wuce halimatu da Ibrahim kuma suka koma gida, abdulƙadir koda ya kai ma matar shi sadiq, sosai tayi murna kuma ta karɓi sadiq hannu bi biyu, gata da kulawa sadiq ke samu wurin abdulƙadir da hajiya zainab, abdulƙadir ya saka sadiq makaranta,sai dai makarantar basu sa shi ajin daya tsaya ba ya fara ne daga primary 4, kuma kamar yan da ya faɗa duk akayi hutu sadiq na zuwa kurfi,  zuwan shi na farko kurfi maijidda kamar tayi huka dan baƙin ciki ganin yanda sadiq ya koma, yayi kyau yayi fresh hasken shi ya ƙara fitowa, tayi data sannin sa baki nuraddeen ya bada sadiq, nan ta nace akan idan sadiq zai koma lagos sai ya tafi da Ibrahim, sosai nuraddeen ya ci mata mutunci ya kuma ce shi ba mutumin banza bane, sadiq abdulƙadir yace yana so to dan haka bazai tura Ibrahim ba, bala'i sosai maijidda tai ta yi akan wai nuraddeen ya nuna ya fi son sadiq shiyyasa da abdulƙadir yace ya bashi shi ya ɗauka ya bashi,kullum cikin  ɗaga ma nuraddeen  hankali maijidda take har sadiq ya gama hutun shi ya koma, shekarar sadiq ɗaya a lagos  Allah ya azurta zainab da samun ciki, zo kaga murna da farin ciki wurin zainab da abdulƙadir  sadiq ma sai murna yake za'a haifa mashi ƙani ko ƙanwa, daya dawo daga school zai tasa zainab gaba yana faɗin ummy  yaushe zaki haifa man ƙani, wani lokacin idan yayi mata tambayar sai dai tayi dariya, cikin zainab na shiga watan haihuwa, ta matsa ma abdulƙadir akan dole sai ya kaita Morocco ta haihu acan, ba dan ya so ba ya kaita, sadiq ma yasa rigima akan dole sai ya bita, haka abdulƙadir yayi masu visa yakai su shi kuma ya dawo, satin zainab ɗaya a morocco ta haifi ɗiyar ta kyakyawa mai kama da ita,ba'ayi suna a morocco ba suka dawo nigeria, da sati ya zagayo  yarinya ta ci sunan mahaifiyar zainab watau Aisha, har lagos  nuraddeen yazo ranar sunan aisha, sosai sadiq  yayi murna da ganin mahaifin shi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login