Showing 78001 words to 81000 words out of 127932 words
kyauta ba amma hukuncin zai mashi yawa "
"kai ka ga haka "
Shazim ne ya ce " ko da bai kira su ba ni sai na kira su, kuma wallahi na tabbatar da ya ci mutuncin fatima, wallahi kaji na rantse sai yayi daya sanin sani na a rayuwar shi, sai ya gommaci kiɗa da karatu daga shi har mahaifin na shi daya iya ƙoƙarin ɓoye ta dan kar wani ya sani " yana gama faɗar haka ya shige part ɗin su, mansoor yana ji yana gani ba shi da yanda zai yi haka police ɗin suka fice da luqman daga estate ɗin cikin dare, bin bayan su shazim yayi dan ya duba jikin fatima.
kusa da dady Abba ya matsa " Ibrahim kayi haƙuri kar ka sa kanka a damuwa in sha Allah ba abun da zai faru da luqman zai dawo gobe da izinin Allah, ka kwantar da hankalin ka "
"amma yaya mi nayi ma shazim a rayuwa da zai saka man da irin wannan abu, ai ko darajar kasancewata ƙanin mahaifin shi ya duba ya ƙyale luqman, amma saboda bai ɗauke ni a bakin komai ba bayan yayi mashi dukan mutuwa shine ya haɗa shi da jami'an tsaro, mi nayi mashi har haka "
"ka kwantar da hankalin ka ba abun da kayi mashi kawai ranshi ne ya ɓaci, amma nasan nan da zuwa wani lokaci zai huce kuma zai nemi afuwan abun da yayi maka "
"shikenan yaya, ya jikin feenah na manta tun ɗazu ban tambaye ka ba "
"jikinta da sauƙi gobe da safe za su ma dawo gida in sha Allah"
"Allah ya kaimu " dady ya faɗa, da Ameen Abba ya amsa haɗi da tashi yana faɗin "ka tashi kaje ku kwanta, ka lallashi turai naga hankalin ta yayi matuƙar ta shi " da to dady ya amsa haɗi da tashi ya nufi ɗakin momy, ficewa Abba yayi zuwa part ɗin shi lokacin da ya shiga duk sun shige ɗakunan su hakan yasa ya nufi ɗakin shi ya kwanata
Zaune dady ya samu momy bakin gado tayi tagumi sai share hawaye take,abun zallah ban tausayi tana ji tana gani an kama mata ɗa bata yanda zata yi, zama dady yayi kusa da ita, ɗan shiru yayi na wani lokaci can ya dafa kafaɗar ta " dan Allah turai kiyi haƙuri, ko mai zai wuce da izinin ubangiji, in sha Allah gobe luqman zai dawo kiyi haƙuri kinji "
fashewa tayi da kuka mai tsumarai dady shima kukan ne yazo mashi amma sai ya danne shi bai yi ba, jawota yayi jikin shi yayi hugging ɗinta yana ɗan bubbuga bayan ta haƙuri ya cigaba da bata har sai da tayi shiru ta koma tana sauke ajiyar zuciya, a haka har bacci ya ɗauke ta, kwantar da ita yayi kan bed haɗi da jan blanket ya rufe mata jikin, sannan ya nufi toilet ɗinta bayan kamar ten seconds ya fito, switch ɗin ɗakin ya nufa ya kashe masu sannan ya nufi gadon ya hau sai da ya rufe jikin shi da blanket sannan jawo ta jikin shi yayi hugging, idanu ya rufe ba bacci yake ba tunani ya shiga na abun da ya faru ya daɗe yana tunani har shima bacci yayi awan gaba da shi.
Fitowar shi kenan daga toilet ta farka a firgice tana kiran sunan shi da Ammy da malam har noraiz sai bige bige take tana ƙoƙarin cire drip ɗin da aka sa mata da sauri ya ƙarasa wurin ta yana sa hannu ya riƙe hannuwanta da take bige bige yana kiran sunnan ta da cewa " dai na kuka gani nan a kusa da ke " jin muryar mutum ne a kusa da ita yasa ta ƙoƙarin fisge hannun ta tana kiran sunan shazim a ruɗe " ya shazim ka zo ka taimake ni kashe ni ya luqman zai yi dan Allah ka taimake ni " gaba ɗaya a firgice take ta dai ji muryar shazim amma bata san yana ina ba dan bata san shine a kusa da ita ba duk a tunanin ta luqman ne, sai ko kawa take zata ƙwace hannun ta da shazim ya riƙe jawo ta yayi jikin shi da sauri yana faɗin " kwantar da hankalin ki ni ne a kusa da ke ba luqman ba " duk da haka bata daina yunƙurin fisgewa daga riƙowan da yayi mata ba, ganin dai da gaske a tsorace take bazata tsaya ba ne yasa shi jawo ledar magungunan da yasa aka siyo mata allurar da ke ciki ya ciro dama ya haɗata, hakan yasa bai tsaya wata wata ba ya yayi mata allurar a damtsen hannun ta,dan danan allurar ta fara aikin ta cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauke ta, jin jikinta yayi sanyi ne yasa shi fahimtar tayi bacci, kwantar da ita yayi kan gadon ya ja mata blanket, ya daɗe zaune yana kallon ta saƙawa da kwan cewa kawai yake , muddun gwajin da ya tura asibiti sakamakon ya fito, abun da yake zargi ya tabbata , ya rantse babu abun da zai hana shi yin shari'a da luqman har da mahaifin shi, ya jima yana saƙawa da kwancewa daga bisani ya tashi ya nufi parlor wurin Abdallah da mansoor, zaune ya same su kan sofa kowa yayi shiru yana tattaunawa da zuciyar shi, wuri shima ya samu kan sofar ya zauna
Abdallah ne yace " har yanzu bata farka ba " ɗaga mshi kai kawai shazim yayi, yan da suka ga rana haka suka ga dare kowannen su a zaune ya kwana, har luqman da ke station a tsaye ya kwana har gari ya waye
_*WASHE GARI*_
Haka su ka tashi da jiki su ku ku ba bu walwala, har lokacin kuma fatima bata farka ba, kowa da ke estate ɗin ya shigo ya duba jikinta har da dady,sa'ada ke zaune kusa da fatima ta zuba mata idanu.
da safen ma ba irin haƙurin da su ya usman basu ba shazim ba akan ya haƙura a saki luqman, amma fir yace bai san wannan zancen ba dole sai anyima fatima gwaji ya tabbatar da luqman bai mata komai ba sannan, har station ɗin suka je ko za'a basu belin shi amma ina saboda shazim ya hana ba yanda su ka iya haka suka dawo estate suka zuba ma sarautar Allah ido, ba wanda ranshi bai ɓaci ba da shazim, shi kuwa abun da ke gabansa kawai yake, har estate ɗin ummah matar uncle ahmad ta zo domin duba fatima kuma duk wani gwaji da shazim ke so ayi ma fatima ita tayi mata da yake likita ce tafiya tayi zuwa hospital dan ta bicika awan da tayi ma fatima,kowa zaman jiran dawowar ta yake da saka makon da zata zo da shi dan shazim yace dole sai sai yaga sakamakon ko da zai yarda aba da belin luqman, shiyyasa suka zauna zaman jiran tsammani kowa adu'ar shi Allah yasa luqman bai mata komai ba kamar yanda yake faɗa, kafin ummah ta dawo su
Innah su ka dawo daga asibiti da feenah, ta ji sauƙi kamar ba ita ba sai dai damuwa da take ciki, kwata kwata bata da walwala,har ƴar rama tayi duk a kan shazim, part ɗin innah su ka nufa gwaggo halima da mama ne suka shigo su kayi ma feenah ya jiki, feenah na kwance kan sofa tayi matashi da cinyar innah , su ya usman ma sun zo gaishe ta ganin noraiz ne yasa innah cewa " ai ku nayi tunanin kun tsufa da tafiya ashe kuna nan, kenan zuciyar da uban naku hau ba wata bace" shiru noraiz yayi bai ce mata ƙala ba gwaggo halima ce tace "dan Allah mama kiyi haƙuri daga dawowar ki " tsaki kawai innah ta ja ba tace komai ba,can kuma tace " ina su Ahmad ne "
gwaggo Uwani tace " nima dai naga ban gan su ba, kuma wai mike damun ku ne nagan ku duk sai a hankali "
"nima abun da zance kenan, sai kace kunyi zaman makoki" innah ta faɗa tana tsare gwaggo halima da idanu
"ba komai innah kawai saboda jikin feenah ne, amma tun gashi kun dawo Alhmdllh " shiru kawai su innah su kayi bawai dan sun yarda da abun gwaggo halima ta faɗi ba, feenah ce ta tashi tana cema innah zataje part ɗin su dan ta watsa ruwa, da to innah ta amsa mata, tashi tayi Ilham ta bi bayan ta, a bayan part ɗin innah su ka tsaya feenah tace " dan Allah Ilham ki faɗaman mike faruwa ne na ganku duk sai a hanli " ɗan nisa wa Ilham tayi sannan ta faɗa mata duk abun da ya faru da basu nan, kuka feenah ta fashe da shi tana faɗin "wai dan Allah mi yasa ya luqman bai gudun abun magana ne wani lokacin mi zai sa yayi ma fatima haka laifin mi tayi mashi har haka "
Ilham tace "gaskiya kam bai kyauta ba, amma baki ga irin na damar da yayi ba, yayi daya sanin yimata haka "
"ba abun da dady yayi a kan ya luqman ɗin "
"ba abun da yayi, domin ya shazim ya hana a bada belin shi wai har sai ya tabbatar da bai mata komai ba "
"shikenan " feenah ta faɗa part ɗin su suka nufa, tsit suka same shi ba motsin kowa, bedroom ɗin momy su ka nufa zaune su ka same ta bakin bed ta zuba uban tagumi gaba ɗaya damuwa tayi mata da bai bayi, sai sallama suke bata ma san suna yi ba tayi zurfi cikin tunani har sai da feenah ta dafa ta sannan ta san da shigowar su, ajiyar zuciya ta sauke haɗi da wai gowa tana kallon su, shafa kan feenah tayi tana faɗin " kun dawo kenan " ɗaga mata kai feenah tayi " to ya jikin " da sauki feenah ta faɗa " momy ina dady yake "
"yana ɗakin shi "
"ok, momy abun da ya luqman yayi kenan " ta faɗa idonta na tara ƙwalla shiru momy tayi batace komai ba
"momy wai miyasa ya luqman bai jin magana, yanzu yana ganin ya kyauta, duk ya saku a cikin damuwa "
"feenah dan Allah ki bar maganar nan abun da ya faru yariga da ya faru "
" amma momy..... " da katar da ita momy tayi
" daga dawowarki ki feenah, kar ki dawo man da abun da yariga ya wuce, in sha Allah ba abun da zai faru "
"shikenan momy, bari naje ɗakin dady " ɗaga mata kai kawai momy tayi, hannun Ilham taja zuwa ɗakin dady basu same shi a parlor ba hakan yasa feenah ta nufi bedroom ɗin shi Ilham kuma ta zauna kan sofa, a bakin ƙofar ta tsaya haɗi da yin nocking, izinin shiga dady ya bata a hankali ta tura ƙofar ta shiga tsaye ta same shi sai kai kawo yake, sallama tayi haɗi da maida ƙofar ta rufe, juyowa dady yana kallon har ta ƙaraso kusa da shi tayi hugging ɗin shi, shafar sumar kanta yayi " ya jikin naki "
"da sauki "
"Allah ya ƙara sauki " da Ameen ta amsa sannan tace " dady yaushe za'a bada belin ya luqman "
"daga dawowar ki waya faɗa maki abun da ke faruwa, nima ban sani ba feenah, amma in sha Allah na san zuwa anjima za'a sake shi "
" to Allah ya kaimu " da Ameen dady ya amsa, ta ɗan jima a part ɗin dady daga baya ta fita ita da Ilham , duk abun da ke faruwa har lokacin innah da gwaggo Uwani basu sani ba har sai da ummah tazo da sakamakon gwajin da tayi ma fatima, sanna su innah suka san abun da ke faruwa, innah tasha kuka zagi kuwa na duniyar nan ba irin wanda bata yima shazim ba, har papah dake kwance cikin kabarin sa bata bari ba sai da ta zage shi tas shi da maifiyar shi kakar su shazim, har part ɗin su taje ta samu shazim, zaune ta same shi a part ɗin su ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, su Abdallah da ummah har da Ameerah duk suna zaune kan sofa, kowa ya zuba ma shazim ido, jira kawai su ke ya gama karanta takardar dan suji minene sakamakon gwajin fatima , kamar daga sama suka ji muryar innah tana faɗin
"dama ubanka ko kafin ya bar duniya sai daya tozar ta man ɗana, wallahi duk abun da ya samu luqman bazan bar ka ba daga kai har uwar taka, mara mutunci kawai" masifa iri iri sai da innah ta sauke ma shazim, zagi kuwa ba wanda innah bata sauke ma shazim ba duk masifar da take mashi ko kallon in da take bai yi ba,takardun dake hannun shi kawai yake aikin dubawa, gwaggo halima ce ta shigo tana bama innahr haƙuri amma ina masifa ta rufe ma innah ido har su dady sai da suka sa baki amma taƙiyin shiru, shazim yana gama karanta takar dar gawajin , sallama yayi ma ummah da godiya, ba tare da yace ma kowa ƙala ba ya tashi ya nufi bedroom ɗin sa inda ya kwantar da fatima,sai magana su mansoor suke mashi akan ya faɗa masu sakamakon amma yayi banza da su ya nufi ɗakin shi , ummah su ka tambaya ce masu tayi itama bata karanta ba, shikenan kawai su kace, rakata parking lot mansoor da Abdallah su kayi, sai da ta tafi sannan suka dawo parlorn,
Kamar dai yanda take jiya yauma haka take kwance,goshinta da bandage jikinta duk a bushe yake,
sa'ada na nan zaune kusa da ita ta zuba uban tagumi, ɗagowa tayi jin shigowar mutum da kallo ta bi shazim daya shigo,ce mata yayi taje bedroom ɗin fatima ta ɗauko mashi trollyn ta, da to ta amsa mashi haɗi da ficewa ta nufi ɗakin fatima, noraiz ne ya taso ya nufe ta yana faɗin" ya akayi naga kin fito "
"kaya yace na ɗauko ma fatima da trollyn ta "
Ok kawai noraiz yace haɗi da nufar bedroom ɗin shazim ɗin samun shi yayi a bakin wardrobe ɗin shi, sallama noraiz yayi mashi haɗi da faɗin " yaya minene sakamakon, hankalin kowa a tsahe yake kai kawai su ke jira ka faɗa masu sakamakon ka kuma taso ka shigo ɗaki.... "
"dakata man dan Allah noraiz, ka wuce ka fita yanzu zamu wuce "
"amma yay.... "
"bana son jin komai daga gare ka, kayi abun da nace kawai " da to kawai noraiz ya amsa haɗi da nufar bedroom ɗin shi laptop ɗin shi ya ɗauka haɗi da kashe duk wani abu wuta a ɗakin sannan ya fito dama trollys ɗin su suna cikin mota tun jiya
bedroom ɗin shazim sa'ada ta koma da trollyn fatima da ta ɗauko, lokacin da ta shiga shazim harya canza kayan jikin shi zuwa baƙar t_shirt da cargo trouser shima baƙi da p_cap sak shigar da yayice jiya sai dai ba kayan bane wasu ne yasa irin su, a tsakiyar ɗakin ta tsaya da trollyn
"buɗe ki ciro mata doguwar riga mara nauyi " shazim ya faɗa, da to sa'ada ta amasa haɗi da ɗora trollyn bakin gadon, buɗe shi tayi doguwar rigar abaya mara nauyi ta ɗauko mata ajiye ta tayi gefe ta rufe trollyn , kallon shi tayi tana faɗin "yaya gashi "
"ok,kina iya samata?"
"eh " ta bashi amsa, jinjina kai yayi haɗi da jan trollyn fatimar ya fice.
da ya fito wata takarda ya ciro daga cikin aljihun trouser ɗin shi ya miƙama mansoor, amsa mansoor yayi yana faɗin " thank you,zan same ku kuwa kafin na dawo " ɗaga mashi kai shazim yayi, hugging ɗin shi mansoor yayi " shikenan sai na dawo bro " ok shazim yace, a tare su ka fita shi ya sa trollyn fatima a booth mansoor kuma ya shiga motar shi ya fice daga estate ɗin.
Mansoor na ficewa AMBULANCE ɗin asibitin su ummah na shigowa, ita ta turo da ambulance ɗin dan su samu sauƙin zuwa airport da fatima,tsayawa shazim yayi har sai da tayi parking sannan ya gaisa da drivern ambulance ɗin sannan ya shiga ciki yana faɗi ina zuwa da to drivern ya amsa, ha zai shiga ciki wayar shi dake aljihu tafa ringing, tsayawa yayi yana amsa kiran
✨SA'ADA ✨
Rigar ta shiga kiciniyar sanya ma fatima, tasha wahala kafin ta sama ta rigar saboda jikinta duk a sake yake kamar wacce ta mutu babu inda ke motsi a jikinta,bayan ta sa mata rigar ne ta nufi dressing mirror ɗin shazim man shafawa ta ɗauko ta ɗan shafa mata a hannuwan ta da ƙafafuwan ta saboda jikin ta duk ya bushe tana gama shafa mata ta fice zuwa waje lokacin da ta fita Abdallah da noraiz ka ɗai ta samu su Abba duk sun fita, fita tayi itama zuwa parking lot inda anan ta samu shazim tsaye yana waya jira tayi har ya gama wayar sannan tace " ya shazim idan tafiya za kuyi, dan Allah ka tafi da ni "
" ki bari idan mansoor zai zo sai ku zo tare "
"dan Allah ya shazim, wallahi hankalina bazai kwanta ba,dan Allah ya shazim " kai kawai ya ɗaga mata alamar to shikenan
"nagode sosai ya shazim ta faɗa " haɗi da nufar part ɗin su da sauri, zazzaune ta samu su Abba da su gwaggo halima harda innah,sallama kawai tayi masu bata jira sun amsa ba ta nufi ɗakin ta da sauri, shaf shaf ta canza kaya ita ma doguwar riga ta sa, gyalen ta kawai ta ya fa sai side bag ɗinta da wayar ta da ta ɗauka, da sauri ta fice kowa dake parlorn da idanu ya bita, gwaggo uwani ce tace " ke kuma ina zaki "
"lagos zan bi su ya shazim"
kawai tace haɗi da juyawa ta fice,da sauri feenah ta tashi jin wai shazim zai tafi, gwaggo Uwani ce ta jawo tana faɗin "dawo nan " dawowa tayi ta zauna sai turo baki take, innah tace " amma wannan ɗiya anyi ƴar banza, kenan waɗannan marasa mutuncin zata bi " Abba ne yace " ai ba komi innah dan ta bi su, nasan