Showing 72001 words to 75000 words out of 127932 words
Halima yayi "ina su shazim ɗin su ke "
"ina jin suna part ɗin su, nima su kairiyya ne suke faɗa man abun da ke faruwa "
"ok gani nan zuwa " ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran.
"ga Abban ku nan zuwa, amma da mamaki abun ina zata nufa, ku tashi muje, ke sa'ada je kikira man usman kice ya same ni a nan part ɗin " da to ta amsa haɗi da tashi ta fita.
Lokacin da mansoor ya fita part ɗin su shazim ya nufa, noraiz ya samu a parlor mahmud ya fita, tambayar shi yayi "ina shazim ɗin" amsa noraiz ya bashi da "ya shiga ciki yanzu " ok kawai mansoor yace haɗi da nufar sama part ɗin shazim,ba nocking ba komai ya tura ƙofar da ƙarfi ya shiga
ɗago da idu shazim yayi jin yanda mansoor ya shigo kamar an jeho shi da idanu shazim ke binshi, magana ya fara "yanzu dan wulaƙanci shazim ace kun nemi fatima baku ganta ba amma ka kasa faɗa man sai da sa'ada ta faɗa man, wai wannan haushin nawa da kake ji na minene"
"dan Allah ka barni naji da abun da yake damu na"
"ok abun da ke damun ka ko "
"haba dan Allah kaine da wata magana, yanzu fa nake shirin kiran ka sai gaka ka shigo "
"uhmm" kawai mansoor yace sannan yace "to ina ta tafi "
"nima ban sani ba, bawani wuri ta sani ba bare nayi tunanin ko tana can" dan jinjina kai mansoor yayi yana faɗin " haka ne gaskiya" can kuma ya matso kusa da shi ya zauna yana faɗin "ɗan kira number a hashim kaji ko fatima taje gidan su" wani kallo shazim yayi mashi " ban gane ba, mi zai kai fatima gidan a wannan lokacin "
"dan Allah dai ka kira shi "
"ni bazan kira shi ba, kai mi zai hana ka kira shi " mansoor yace
" kai matsalata da kai kenan, to bani wayar ka na kira shi tun da baza ka kira shi" ɗaukar wayar yayi ya shiga kiran number A Hashim, bugu biyu yayi picking ko sallamar da yake mashi bai amsa ba yace "Fatima na tare da kai?"
"Fatima kuma?" a hasale shazim yace "taya ina tambayar ka kana tambayata"
"ba dole na tambaye ka ba, ni yaushe rabon da naga Fatima,in ba ma rainin wayau ba a wannan lokacin zaka tambaye ni fatima " har ya ɓuɗe baki zai yi magana mansoor ya fisge wayar dan ya san abun na iya koma masu faɗa, kara wayar yayi a kunne yana faɗin "sorry Abdallah, ka gane neman ta muke ne, an kira wayar ta bata yi picking ba tun ɗazu mu ke neman ta , shine sai nayi tunanin ko tazo gidan uncle ne wurin Ameera"
hankalin A Hashim yayi matuƙar tashi jin ya ce ba'aga Fatima ba, cikin tsantsan tashin hankali yace "amma ina taje mansoor "
"wallahi shine ba mu sani ba" Abdallah yace "ya ilahi" haka kawai ya ce haɗi da yin rejecting ɗin kiran, ta shi mansoor yayi ya fita daga parlorn ya nufi main parlor, yanda ya bar Noraiz haka ya same shi har da mahmud da ya shigo yanzu, gwaggo Halima ce ta shigo ita da kairiyya da sa'ada sai usman , har time ɗin kuka sa'ada keyi, kairiyya na lallashin ta, kusa da su mansoor ya matsa, haƙuri ya shiga ba ta akan insha Allah za'a ganta, fitowa shazim yayi bedroom ɗin shima ya nufo main parlor wuri ya samu kusa da noraiz ya zauna, ya usman ne yace " shazim tun yaushe ne kuka duba baku ganta ba "
"tun fitar da tayi ɗazu da ana meeting, nayi tunanin ko tana nan ɗakin ta ko wurin sa'ada "
"ya salam" ya usman ya furta haɗi da cewa "amma ba inda kake tunanin zata "
"ina zata je yaya bayan ba wanda ta sani a abuja " kallon sa'ada ya usman yayi "ke sa'ada kin kira ƙawayen ki ko taje wurin wata daga cikin su "
"yaya ai ni bana da ƙawaye,kuma ma tun da tazo gidan su momy kaɗai muka je sai gidan uncle ɗin ya Abdallah "
"waye kuma Abdallah "ya usman ya tambaya, mansoor ne yace "wani course mate ɗin shazim ne kuma ma mun kira shi bata can " shiru su
kayi ba wanda yasake cewa komai, kowa na tunanin inda ta shiga, shazim kuwa alƙawari ya ɗauka duk abun ya same ta wallahi bazai ƙyale kowa dake cikin estate ɗin ba tunda ai sune silar shigarta wannan halin har tasa ƙafa ta bar estate ɗin, damuwarshi yanzu shine ina taje awane hali take dan yasan duk in da take zai yi wuya ace ciwanta bai tashi ba, ya usman ya tashi yana faɗin "ina zuwa wannan zaman bazai mana maganin komi ba " tashi ita ma gwaggo Halima tayi "haka ne usman bazama ya kamat muyi ba " tashi su kayi duk suka fita aka bar mansoor da shazim
mansoor yace "ina mamakin inda taje, to wai mi zai sa ta bar estate ɗin nan" shazim yace " wallahi muddin wani abu ya sameta ran kowa sai ya ɓaci " shiru kawai mansoor yayi baice komi ba, can kuma sai yace "yo wai ma an tambayi security ko sunga fitar ta " sai da mansoor yayi maganar sannan hankalin shazim ya kai ga nan "hakane kuma mansoor wallahi ni duk banyi wannan tunanin ba "
"idan tafita dole zasu ganta ko da ta ƙaramin gate ta fita, tashi mu tafi " mansoor ya faɗa haɗi da ɗaukar wayar shi su ka fita zuwa main gate da ya usman suka ci karo shima main gate ɗin ya nufa, a tare suka ƙara sa, securityn na zaune kan benchi da suke zama,su ƙara so inda su ke, gaishe da su security su kayi a taƙaicw suka amsa masu mansoor na faɗin " tambayar ku muke son yi"
babban cikin su ne yace "Allah yasa mun sani yallabai "
a hassale shazim yace " kunga ficewar fatima "
"gaskiya yallabai ba muga fitar ta ba, motar Alhaji ce kawai ta fita shi da su innah in ba dai atare da su ta fita ba "
Mansoor yace "kun tabbata baku ga ficewar ta ba, kuma bawani driver da ya fita da mota "
"gaskiya babu, bayan Alhaji Ahmad ba wanda ya fita da mota " wuce wa shazim yayi batare da ya jira su mansoor ɗin ba, juyo suka yi suma zasu bi bayan shi sai ga mota ta nufo main gate daga waje, tsayawa su kayi dan suga waye, ɗaya daga cikin security ne ya nufi motar ba kowa bane face ya Abdallah ya kasa zama hankalin shi ya ƙi kwanciya tun da aka ce ba'aga fatima ba, izinin shiga ciki security ya bashi, ciki ya shigo ganin su mansoor ne yasa shi tsayawa wurin su sai da yayi parking sannan mansoor ya gane shi, mansoor ce mashi yayi" ya shiga ciki kawai shazim ma yanzu ya wuce" ciki ya shiga yayi parking a parking lot, part ɗin kawai ya nufa , tsaye ya samu shazim a parlor, gaba ɗaya hankalin Abdallah a tshe yake tsare shazim yayi da tambayar ina taje ne Fatimar, amsa kawai shazim ya bashi da bai saniba, gashi malam da Ammy sai kiran shi su ke yace zasu dawo yau gashi har dare yayi babu su babu labarin su.
Sa'ada lokacin da suka fita daga part su shazim part ɗin su ta nufa, ta shiga bedroom ɗin momy ta shiga bata same ta ba tunawa da tayi ɗazu momy part dady ta nufa ne yasa fita ta nufi part ɗin dady, tunkafin tashiga ta fara jin muryar momy tana faɗin "amma ban taɓa tunanin baka da hankali ba luqman sai yau, dama ashe shashasha ne kai ban sani" muryar dady taji yana faɗin "dan Allah ki daina ɗaga murya turai "
"ok in daina ɗaga murya ko.... " bata ƙarasa ba saboda tura ƙofar da sa'ada tayi ta shiga tsaye ta samu momy da dady sai luqman da ke zaune kan sofa jikin shi sai rawa yake kamar wanda zazzaɓi yayi ma mugun kamu,jin anturo kofa ne yasa shi tashi da gudu ya nifi bedroom dady,ganin sa'ada ce yasa shi tsayawa yana haki kamar wanda yayi wasan tsere, dady ne yace "ke kuma daga ina haka "
"dady fatima fa ake nema ba'a ganta ba "
"to naji fita ki bamu wuri"
" dady amm..... " bata ƙarasa ba ta dalilin tsawar da dady ya daka mata yana faɗin
"nace fita ko so ki ke sai ranki ya ɓacin"
ba shiri ta fita, amma sai ta ƙi tafiya ta tsaya tana sauraron mi suke cewa, bana ji mi take ji naga dai taja baya da sauri tana kallon ƙofar can kuma ta fita dagu.
Episode 40_41_
ba shiri ta fita, amma sai ta ƙi tafiya ta tsaya tana sauraron mi suke cewa, bana ji mi take ji naga dai taja baya da sauri tana kallon ƙofar can kuma ta fita dagu tana kuka, bedroom ɗinta ta nufa tana shiga ta faɗa kan bed fashewa tayi da wani matsanancin kuka, kuka take kamar ranta zai fita sai birgima take kan bed ɗin tana faɗin "wayyo Allah nah, Allah kasa abun da kunnuwana suka ji ba gaskiya bane, idan har haka ta kasance bazan taɓa yafe maka ba ya luqman " sai kuka take tana ta roƙwan Allah yasa ba gaskiya bane tashiga tashin hankali da jin abun da su dady ke tattaunawa sai ta baka tausayi yan da ta dage tana rokwan Allah yasa ba gaskiya bane,can kamar an tsikareta ta tashi ta fita daga bedroom ɗin da gudu ta nufi sama part ɗin dady har tasa hannu zata buɗe ƙofar part sai aka turo ƙofar dady ne sai momy dake bayan shi da kaganta kasan tana cikin damuwa idanun ta duk sun kumbura ba ƙaramin kuka tasha ba,tsaye su kayi suna kallonta sai kuka take dady ne yace "wai wannan kukan da kike na minene, miya dawo da ke nan ba nace ki wuce ba " ƙara sautin kukan tayi ba'a ma jin mi takecewa sosai " dady ƴar uwata "
"dan Allah kiyi haƙuri sa'ada za'a ganta yanzu ma wurin su shazim ɗin zan tafi, kiyi shiru kinji" ya faɗa cikin sigar lallashi
"to dady, amma maganar wa naji kunayi, wacce ya luqman....... "
bata ƙarasa ba dady ya katseta ta hanyar daka mata tsawa" wai ke wace irin yarinya ce sa'ada, nace maki za'a ganta kuma maganar da kike cewa munayi ba'a kanta bane, ki kwantar da hankalin ki " ya ƙarasa maganar yana lallashin ta
" amma dady dan Allah ka bari naga ko wacece pls "
"miyasa baki jin magana ne sa'ada, wuce ki tafi bedroom ɗin ki ki kwanta kar ki haddasa ma kanki ciwan kai kinji za'aga fatima "
fashe tayi da kuka "ni dai dady ka bari naga ko wacece " tsawa ya daka mata "ina wasa da ke ne, ko ki bar wurinnan ko ranki ya ɓaci shashasha"
hawayen da momy ki ɓoye wa ne suka zubu "wallahi Alhaji ina jiye maku abun da zai biyo baya"
dady yace "dan Allah turai kiyi man shiru, kija ta ku bar nan wurin "
"dole na faɗi haka Alhaji, an cuc..... " bata ƙarasa ba dady ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"wai miyasa kike da taurin kai ne turai, nace ki jata ku bar nan "
jan hannun sa'ada tayi tana faɗin "zo nan kinji kiyi haƙuri ki daina kuka, kinji jikin ki harya ɗauki zafi " momy ta faɗa haɗi da jan hannunta, fisgewa sa'ada tayi ta nufi ƙofar zata buɗe, da sauri dady ya fisgota ɗauke ta yayi da wani mumunnan mari har sau biyu, tangal tangal tafara zata faɗi ƙasa, da sauri momy ta taro ta zuwa jikinta ta rugume ta tana kuka " kijata ku bar nan"
"ba inda zan kai tai, ku faɗa ma yara in da ƴar uwar su take, ko wallahi naje na kira su duk abun da zai biyo baya ya daɗe bai biyo baya ba "
"turai haka kika ce, kin kuwa san mi kike faɗa kuwa, kina cikin hankalin ki kuwa"
"cikin hankali na nake, nasan mi nake, wannan ai zalunci ne " tana gama faɗa ta ɗago da kan sa'ada tana faɗin "sa'ada tashi ki kira man mansoor ko shazim " shiru sa'ada bata amsa ba bakuma ta motsa ba, ashe tun marin da dady yayi mata momy ta tare ta suma tayi batare da sun sani ba, da sauri momy ta ɗago ta kalli dady tana faɗin " ta suma Alhaji, Innalillahi" ta faɗa tana bubuga ta tana faɗin "tashi kinji, dan Allah ki tashi " momy gaba ɗaya hankalin ta ya tashi, key dady yasa ma part ɗin shi ya rufe ya yafita ya bar momy da sa'ada durƙushe a ƙasa momy sai kuka take,daƙyar ta samu ta ɗauki sa'ada ta nufi ɗakinta da ita, kwantar da ita tayi kan bed sannan ta nufi dressing mirror ɗakin ta ɗauki robar ruwan da take ajiye wa duk dare, a hannu ta tarfa ruwan ta nufi fuskar sa'ada ta yayyafa mata sai da ta sake yayyafa mata sannnan ta ja wani dogon numfashi,Alhmdllh momy ta furta hadi da kiran sunan sa'ada, jin muryar momy ne yasa ta tashi zambur kamar wacce aka zungura " momy ina fatima, ina ƴar uwata take, momy dan Allah ki faɗa man in da take " ta ƙarashe maganar tana kuka
"kiyi haƙuri sa'ada ƴar uwar ki bata ɓata ba kiyi shiru kijin, kar ki ja ma kanki ciwo "
"amma wacece a part ɗin dady naji kuna faɗin ya luqman yayi raping" da ta faɗi haka har sai da gaban momy ya faɗi " momy kinyi shiru,idan har ba ƴar uwata bace pls momy wacece " hawaye ne suka taru a fuskar momy, girgiza mata kai tayi " sa'ada nima ban san wacece ba, dadyn ku yaƙi bari naga ko wacece "
"momy amma a ɗakin na same ki pls momy ki faɗa man " shiru momy tayi batace mata ƙala ba, tana son kowa ya san halin da ake ciki amma ta tsoron wane irin hukunci luqman zai fuskanta, ganin tayi shirune yasa sa'ada faɗin "momy ki faɗa man, ko naje na kira ya shazim da ya mansoor su zo su ɓalle ƙofar ɗakin dady "
"sa'ada karki kira su ba fatima bace "
"idan har banga kowa cece ba hankalina bazi taɓa kwanciya ba" tana gama faɗa ta fice daga ɗaki da gudu,k'wala mata kira momy ta shiga yi tana fad'in ta dawo ,amma ina ko wai wayen momy bata yi ba , fashewa momy tayi da kuka "ya Allah ka kawo sassauci a wannan lamarin ya Allah "
sa'ada ɗakin momy ta faɗa dagu ta maida ƙofar ta rufe, wani sabon kukan ta sake fashewa da shi, sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi ta kamar wacce ciwan hauka ya kama hau buɗe buɗen drawer's tana neman extra key's gaba ɗaya ta hargitsa ma momy ɗaki ta haukata shi kayan ta da ke cikin wardrobe duk ta watso su ƙasa, har da su ɗaga mattress sai nishi take ta haɗa uban gumi amma bata gansu ba, fitar da rai tayi da ganin su sai hawaye take kayan da ta watso ta fara kwashe wa tana mai dawa cikin wardrobe,sai da kwashe su tasa ta maida ta rufe wardrobe ɗin, zama tayi ƙasa dirshan tana share hawayen dake ta zarya a kumatun ta, tazo tashi kenan zata fita idanun ta suka sauka akan keys ɗin da take ta wahalar nema, ashe wajen watso kaya ta watso da su batare da ta sani ba , ɗaukar keys ɗin tayi ta fice da sauri.
Dady na fita daga part ,part d'in uncle Ahmad ya nufa ,a parlor ya same shi shida su mansoor da ya usman ,noraiz ,mahmud sai gwaggo halima da mama ,sunyi jugum jugum,kowa hankalin shi tashe yake da rashin ganin fatima, ya usman ya yanke shawarar kiran police ya sanar da su halin da ake ciki , Abba ne yace kana ganin za su zo,na ga dare yayi kuma ka san yana yin jami'an tsaron k'asar nan yan da su ke"
"haka ne Abba,ai wanda zan kira aboki na ne kuma nan kusa office d'in su yake "
"to shikenan " Abba ya fad'a,
ya d'aga waya kenan zai kira su sai ga dady ya shigo ,fasa kiran yayi,amsa mashi sallamar da yayi su kayi ,wurin su dady ya k'ara so ,Abba ne yace " wai dama kana nan?, amma dai baka san mike faruwa bane ko?"
Dady yace
"na sani ,akan maganar ne ma nake son mutattauna"
" in taso ne " da eh dady ya bashi amsa had'i da juyawa ya fita ,bin bayan shi Abba yayi, garden su ka nufa ,zama su kayi akan kujerun dake wurin ,shiru dady yayi bai ce komai ba har sai da Abba yace " kace za muyi magana mun kuma zo kayi shiru ,ina fatan dai lafiya ,d'an nisawa dady yayi sannan ya fara magana
"yaya kasan halin yaronann luqman bai da hankali ko ko ko alama ..." sai kuma yayi shiru, ganin yayi shiru ne yasa Abba da sauri yace " kayi shiru kuma mi luqman yayi ,kar dai kace man duk neman yarinyar nan da ake luqman ne ya d'auke ta?"
"da ace d'auke ta yayi yaya ai da sauki , saboda bai da hankali bai san in da ke mashi ciwo ba k'okarin yi mata fyade ya so saboda kawai ta nuna bata son shi "
zanbur Abba ya mike yana fad'in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ,dama yaron nan bai da hankali ban sani ba ,amma Ibrahim miyasa tun d'azun baka sanar da ni ba, yanzu tana ina"
"tana bedroom ɗina, na so tun lukacin na sanar dakai ,amma ganin kuna asibiti ne yasa ban sanar da kai ba"
"haba Ibrahim idan bana nan ka kirani ai dole na dawo ,kuma ai da ka sanar da shazim ,yanzu idan ya san cewa tun d'azu tana part d'in ka ,mi kake tuna nin zai biyo baya ,kana gani d'azu cewa kawai fa yayi yana sonta amma ji irin bacin da ranshi yayi da maganganun da ya fad'ama,"
"wallahi yaya tsoron irin hukuncin da