Showing 12001 words to 15000 words out of 127932 words
are my wife" ya fada yana washe baki, destiny dai na gefe tana kallon su bata ce masu kala ba sai da taga Victoria na niyyar fita da ga dakin sannan taba Victorian hakuri shi kuma Samuel ce mashi tayi ya fita ya basu wuri tun da shi ba shi da hankali , Victoria tace bata son shi to mi yasa zai ta kura ma rayuwar ta, Komawa Victoria tayi ta zauna sai wani cika take tana batsewa, suna kammala cin a binci fita su kayi bakin wani fanfu suka wanke hannu Victoria ce tace "destiny zan tafi gida domin nayi shirin zuwa church din kuma kin ga momy bata san nafita ba, kar ta dawo bana nan
"kawai dai kina son zuwane amma aikin san bata dawo ba, da ta dawo da mun iske momy ( mahaifiyar destiny ) a gida, tun da wurin business din su daya" kuma tare su ke fita su dawo tare"
to kawai Victoria tace, komawa su kayi dakin, destiny tace "kin san Adu'a da nake kuwa Victoria?"
"Aa sai kin fada" Victoria ta fada tana sauraron mi destiny zata ce
"so nake wannan wawuyar hidaya ta taya ki bama dr hakuri kamar yarda da tace, a samu sa'a ya haƙura kuma ya maida ke bakin aikin ki,uhmmm zata sha mamakin abun da zamuyi mata,dan sai munrabata da eko ma gaba daya yanda ba zata sake ganin dr ba"
"nima haka nake buri, zata sha mamaki In dai ya mai da ni wuri na,sai tayi data sanin sani na a rayuwarta" dariya su kayi harda ta fawa suna nan suna shirya yan da za su yima hidaya mahaifiyar destiny ta shigo gidan ,suna jin shigowarta su ka fito daga dakin gaishe da Ita su kayi yayin da destiny ke amsar kayan da momynta ta shigo dasu, Victoria ce tace "ni na tafi"
"to saina shigo gidan" destiny ta fada, ficewa victoria tayi daga gidan, gida ta shiga momynta ta samu a dakin zaune" good afternoon momy"
"afternoon daga ina ki ke na shigo baki nan momyn tafa da?"
"ina gidan su destiny ne momy" ok kawai momyn tace, wurin 5:00 suka shirya domin zuwa church ( suna zuwa church su duk ranar Asabar domin gyaregyre sbd lahadi ) gidan su destiny , Victoria taje daga chan suka wuce church din....
_Katsina._
Mom ce zaune a main falo suna fira da baaba larai, Abdallah ne ke saukowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya, wurin su mom ya zo yana faɗin"cewa fira kuke ne nagan ku a zaune"
"ai kuwa, sai ina haka naganka da jallabiya"
mom ta fada amsa ya bata da cewa "zan ɗanje wani wuri ne daga can zan tsaya sai an kammala sallah tukun zan dawo" mom tace "ah kace wurin ɗiyata zaka, amma sai ka je mata da jallabiya sai kace wani limami"
murmushi kawai yayi yana cewa "mi za ki yi da wata ɗiya, ke da ki ke da yan biyu duk mata a gaban ki" wanj kallo mom ta mashi " duk da ina da su ƙari ai ba ya ƙin daɗi koh baaba larai?" ta faɗa tana kallon baaba larai
"haka ne kuwa hajiya” baaba larai ta bata amsa, Mom ce ta kuma cewa" ni dai yau she zaka kawo man surukata gidan nan" murmushi abdallah yayi yana faɗin" kar ki damu mom dana samu wacce ta dace dani zan kawo maki Ita har gida"
"hmmm Allah ya shirye ka Abdallah, watan kana nufin har yanzu baka samu wacce ta dace da kai ba ko, nasan maganinka ai, xan sa abie din ku ya zabo maka mata tun da kai ka kasa"
"haba mom kamar ni za'a zaɓa ma mata,ai kuwa dana faɗo,yo ai sai abokaina su yi man dariya"
" to in dai baka son auren dole ka fito da mata kayi aure,kai ko kunya baka ji shekara kusan 30 amma ace baka da mata haba ina amfani"
"dan Allah mom kibar batun auren dolen nan,In dai aure ne very soon zanyi in Allah ya yarda"
"Allah ya yarda" mom ta fada, "ni na wuce sai na dawo" ya fada hadi da nufar kofar fita, a dawo lafiya mom ta fada, fira mom suka cigaba Ita baaba larai suna a nan zaune su Aaimah suka shigo da
alama daga Islamiyya su ke, sanye suke da hijab blue color gaishe da su mom su kayi sannan su ka nufi bedroom din su, wanka su kayi tare da alwallar magrib,kaya marasa nauyi su ka sa, a daki suka zauna har sai da su kayi sallah isha tukunnan su ka fita falo,fira su ka ke ɗan taɓawa akan Islamiyya anan mom tasa me su har da abie wanda baijima da dawowa daga masallachi ba, zama su ka yi Abie na tambayar su ya islamiyya,da Alhmdllh su ka amsa mashi har 9:00 suna parlorn zaune,sannan su ka tashi su ka nufi dinning dan gabatar da dinner,bayan da su ka kammal ne kowa ya nufi ɗakin sa bayan sun yi ma mom da Abie sai da safe
su na shiga daki wayar Aairah na ringing,dauko wayar l dake ajiye kan bedside tayi tana sakin murmushi ganin mai kiran nata, Aaimah ce tace
"halan ya mus'af ne?" a cewar Aaimah,ɗaga mata kai Aairah tayi
"to sai da safe,domin nasan ke ba yanzu ba" Aaimah ta fada tana nufar bed ta kwanta, blanket taja, Ita kuwa Aairah zama tayi bakin bed ta cigaba da waya, ba Ita bace ta gama wayar ba sai wurin 10:55 pm tukun ta kwanta bayan tayi adu'a ta shafa hadi da shafa ma Aaimah sannan taja blanket Ita ma bayan ta kashe bulbs da bedside lamp.
Ep 7_8
_Washe gari........_
Zaune suke kan sallaya suna adu'a da tasbihi, tashi Aaimah tayi daga kan sallayar ta nufi in da suke Ajiye Alqur'ani , ɗaya ta ɗauko, kusa da Aairah ta dawo ta zauna tana miƙa mata" sister amsa in karanto maki haddar da nayi, in da nayi kuskure saiki gyara man,"
"to in dan na gama maki nima sai ki amsar man" da to Aaimah ta amsa
karatu ta fara cikin ƙira'a mai daɗi ,Aairah na sauraron ta in da tayi kukure sai ta gyara mata, sai da suka gama amsar ma junan su hadda tukun su ka mai da qur'anan wurin da su ke a jiye su , fita su ka yi daga bedroom saboda gari ya yi haske sosai, lokacin Ƙarfe 7:00 na safe, main parlor su ka nufa a kitchen su ka samu mom da baaba larai suna hada breakfast, gaishe da su su kayi ,cike da kulawa su ka amsa masu su Mom na faɗin" ina fatan dai kungama hardar ku ta yau, eh mom,to masha Allah,Allah ya taimaka"
baaba larai tace " kace muna da bikin hadda dana kammala makaranta gagarumi gidan a nan, to Allah ya taimaka ya nuna mana lokacin lafiya" har hada baki suke wurin cewa ameen, kama masu aikin su k ayi har su ka kammala, su Aairah su ka jera kan dinning, bedroom din su su ka koma domin shirin zuwa Islamiyya ( Islamiyyar harda suke, in suka tafi tun safe sai yamma duk ranar weekend, Idan kuma ba weekend bane karfe 2:30 suke zuwa su taso da yamma, amma ban da ranar Friday in kuma an yi hutun school to kullum ne ban da friday .)
Aaimah ce ta fara shiga toilet domin yin wanka ita kuma Aairah uniform dinsu na Islamiyya ta dauko masu tare da bags dinsu , Aaimah na fitowa itama ta shiga, shaf shaf Aaimah ta shirya cikin uniform din, Lokacin da Aairah ta fito har Aaimah ta gama shirin ta ita ma cikin kankanin lokaci ta shirya suna gamawa suka fice zuwa main parlor, dinning suka nufa domin yin breakfast, suna gamawa part din abie da na mom suka nufa domin su ka yi masu sallama,a dawo lafiya suka yi masu , fita su kayi harabar gidan anan suka samu mudi na jiran su dan shine ke kaisu, sai wurin 10:00 su mom su kayi nasu breakfast din kasancewar weekend ne..
✨ _SHAZIM_ ✨
Yau ta kasance sunday baya zuwa aiki , kwance yake kan sofa a bedroom din sa ya baje papers da laptop din sa yana aiki,tun da ya gama sallar asuba ya ke nan wurin yana aiki har bacci yayi awan gaba da shi,sanye yake da jallabiya, ya ajiye wayarsa saman cikin sa yayin da ya sa ɗayan hannun sa ya rufe fuskar sa, wayar sa dake saman cikin sa ce ta fara ringing, hannun sa dake kan fuskar ya zame yana ya tsina fuska alamar an katse mashi baccin sa , daukar wayar yayi "Brother" shine sunan daya bayyana akan screen din wayar picking call din yayi hadi da Kara wayar a kunne " hello Yaya" na cikin wayar ya fada, "ba zaka chanza ba ko noraiz , ina amfanin wani hello kana ɗan musilmi"
"a fuwan big bro" noraiz ya fada
"Allah ya shirye ka" kawai shazim ɗin ya faɗa
"ameen,Yaya ka tashi lpy yasu Ammy da fatima?"
"duk su na lafiya,kaifa,Ina fatan kai ma kana lafiya??"
"ina lafiya Yaya"
"Masha Allah shazim" ya fada hadi da cewa
"ya maganar dawowar ka yau, domin da na ga kiranka nayi tunanin za kace man ka iso dan na san halin ka da chanza lokaci idan za ka dawo"
"A'a ba haka bane Yaya ina nan zuwa yau In sha Allah, kawai dai ban samu biyo jirgin safe bane shiyyasa na kira ka na faɗa maka sai dai da yamma in sha Allah"
"ok Allah ya kawo ka lafiya" "ameen Yaya sai an jima"
ok kawai shazim ɗin ya ce yana rejecting kiran ya ajiyeta kan center table, sai da yayi 5 minutes a kan sofar tukun ya tashi,papers din da ya baza ya kwashe da laptop ya saka cikin briefcase ɗin shi, cire jallabiyar dake jikin sa yayi ya koma da gashi sai short,toilet ya nufa, ya ɗan jima a toilet ɗin tukun ya fito ya nufi dressing mirror ɗin sa,anan ma ya ɗan jima yana yan shafe shafe kai kace mace ce, bayan daya.kammala ne ya nufi clothes ɗinsa shiryawa yayi cikin jeans da T_ shirt, ficewa yayi daga bedroom din zuwa part din Ammy,
a parlor ya same ta Ita ka dai, fatima na Islamiyya, gaishe da Ita yayi , amsa mashi tayi wuri ya samu ya zauna kusa da ita, Ammy tace " ga breakfast dinka chan kan dinning, tun ɗazu har nayi tunanin yau ba ka fitowa a daki za kayi weekend"
"wane ni Ammy, kina a gida na zauna a daki, ai dole na fito na tayaki fira,tun da auta na Islamiyya kuma rigimenmen ki baya nan duk da yau zai dawo"
murmushi Ammy tayi tana cewa "ka yi waya da shi ne, naji yace da safe jirginsu zai taso"
"kin dai san halin kayanki Ammy da chanza lokaci in zai dawo,wai kuma yanzu sai yamma tukun" girgiza kai Ammy tayi
"Allah ka shirya mai babban suna,Allah ya kaimu yamma lafiya"
ameen Ammy ya fada yana tashi ya nufi dinning, warmer din dake kan dinning din ya shiga budewa yana duba abun da ke cikin su. cup ya dauka ya hada tea sannan ya zu ba arish, wurin Ammy ya dawo ya zauna,suna fira shi da Ammy yayin da shi kuma yake cin abincin duk ba wani sosai yake magana ba,sun jima suna fira har lokacin sallar zuhur yayi,tashi Ammy tayi ta nufi dakinta shi kuma ya nufi part din sa domin yin alwala...
✨ _HIDAYA_ ✨
Flat house ne me kyan gaske Masha Allah na masu rufin asiri kutsa kai nayi cikin parlorn gidan wanda komai na cikin sa brown color ne, hidaya naga ni zaune kan dinning tana lunch ita da mahaifiyar ta wacce kallo ɗaya zaka mata ka gane kamaninta hidaya ta biyo, tashi hidaya tayi,kallonta mahaifiyar tata tayi tana faɗin" mi ki ke nufi ne,naga kin tashi?"
"na ƙoshi ne mama"
"wai ni kuwa hidaya mi ke damunki ne, a ce kwata kwata mutum baya son cin abinci, ko baki da lafiya ne?"
"lafiya ta kalau mama,dan nayi breakfast a makare ne yasa bana jin yunwa sosai, amma lafiya ta lau"
"to shikenan" mama ta faɗa bedroom din ta ta nufa, kayan jikin ta ta cire ta shiga toilet,ta dan jima sannan ta fito jikinta daure da da towel, dressing mirror din dake dakin ta nufa simple make-up tayi sannan ta nufi wardrobe din dake kusa da dressing mirror din, gwon ta dauko ta atamfa da mayafi, shiryawa tayi cikin kayan Masha Allah dan bakaramin kyau kayan sukai ma fatar taba,hidaya chocolate color ce,ita ba faraba sannan ita ba baka ba, wayarta dake kan bed ta dauka da jaka wurin da takalmanta suke ta nufa ɗan flat shoe ta dauko tasa , fice wa tayi daga bedroom din ta nufi na mamar ta, zaune ta same ta kan gado, sallama tayi tana faɗin" mama zan tafi gidan su maryam" mama tace "to shikenan sai kin dawo ina gaishe da hajiya lubabatu, sannan kar ki bari yamma tayi baki dawo ba, kinsan dai Baban ku yana gari"
"in sha Allah mama bazan jima ba zan dawo"
"to sai kin dawo" to tace tana ficewa daga ɗakin, a bakin gate ta tsaya tana neman abun hawa, bata jima ba ta samu adaidaita shiga tayi sannan ta yima mai adaidaita din kwatancen anguwar da zai kaita, tafiya su kayi mai dan nisa kafin su ka iso wata anguwa, a bakin gate din wani gida tace da mai adaidaita yayi parking,fita tayi ta bashi kudinsa ya wuci ita kuma ta nufi gidan, mai gadi ta samu zaune akan ɗan benchi, gaishe da shi tayi, ya amsa mata yana faɗin "yasu maman ku, suna lafiya?"
"duk su na lafiya"
da alama ya santa shiga tayi cikin gidan,part biyu ne gidan daya daga ciki part din ta nufa, shiga tayi, tsit ta samu parlorn gidan kamar ba kowa wani dan corridor ta nufa ɗakuna ne kusan guda hudu ƙofofin su na kallon juna, wanda ke farko ta shiga bedroom ne mai kyau , bed ne sai wardrobe da toilet da dressing mirror, ba kowa a dakin sai karar ruwa daga cikin bathroom alamar a kwai mutum a ciki, wuri tasamu gefen bed din ta zauna batajima da zama ba sai ga maryam ta fito daga bathroom daure da towel "a she dai zaki zo" maryam din ta fada "wallahi kuwa zan zo ya ki ke, ya gida,ya su mama?"
"duk su na lafiya" maryam ta fada hidaya tace " ba kowa ne gidan sai ke ka dai? "
" A'a suna nan , kawai dai suna ɗaki ne"
"ok, naji shiru ne da na shigo"
"A'a suna nan bari dai nasa kaya dai" maryam ta fada tana nufar wardrobe,kaya ta dauko riga da skirt na martial , shaf shaf ta shirya sannan ta dawo wurin hidaya ta zauna tana fadin "wai ni kam sister ya kuka kare da Victoria kinsan tun ranar da ku ka yi fada da ita bamu sake wata magana ba, ya kuka kare naga dr ya mai da ki wurin ta, kin kuwa san dadin da naji, domin nasan in sha Allah burinki ya kusa cika"
"bakomi,ba mu sake wata magana da ita ba da sunan sa in sa, dan har roƙuna su ka yi ita da destiny akan na taya ta bama dr hakuri ya maida ta wurin ta"
"to ke sai kika ce mata mi?" Maryam ta fada ta na tsare ta da idanu
hidaya tace " mi zan ce kuwa maryam, tun da ta roƙe ni mi zai hana"
"amma wallahi hidaya baki da hankali,sai kawai kije kice ma dr dan Allah yayi ma Victoria hakuri koh,hmmm ko dai yanzu kin haƙura da shi ne ba ki son sa yanzu??" Maryam ta jefa mata tambaya hidaya tace "wallahi maryam bazan boye maki ba ina son dr har zuciyata"
"to amma shine zaki taya ta kuma kinsan cewa son shi take,dama kawai take jira ta raba shi da kowa"
"to ya zanyi maryam,ko mi tayi dan kanta tun da har ta roƙeni zan taya ta mana"
maryam tace "hmm sannu uwar masu tausayi,tun da ta rokeki ai sai ki bashi haƙurin, wallahi ke ba kisan wacece Victoria da destiny ba,su kan su munafuntar junan su suke yi in ma baki sani ba to ki sani, ita kanta destiny din son dr take muna funtar Victoria kawai take,shiyyasa kike fadan haka ni da na daɗe dasu ni zan baki labarin ko su su waye su, garama tun wuri ki mai da hankalin ki a kan dr ki kyale wata Victoria da destiny chan,amma fa in kinji shawarata,dan wallahi kika tai make su,sai kinyi dana sannin haka,amma fa in kinji"
"shikenan nagode sosai da shawarar ki,amma sister sai nake ganin kamar dr bazai soni ba, kina ganin in ya shigo hospital duk matan dake hospital din bamu ishe shi kallo ba, amma zan ciga ba da rokwan Allah in har shi alkairi ne a rayuwa ta Allah ya tabbatar man"
"to ameen,amma ya ka mata kisanar dashi cewa kina son sa,ko ba komai zai san ke masoyiyar sa ce,ko ya ki ke gani"
"zanyi ƙoƙarin haka in sha Allah,amma gaskiya ina tsoron abun da zai biyo baya, karma ya zo ya da katar dani kamar yan da yayi ma Victoria,abun da bazan soba kenan"
Maryam tace " to idan baki fada masa ba taya zai gane kina son shi , ki fada masa kawai in sha Allah ba abun da zai biyo baya sai Alkairi, kuma in sha Allah zan taya ki da adu'a"
"Ameen sister nagode sosai Allah ya barmu tare"
"ameen,karki damu" maryam ta fada, canza firar su ka yi zuwa wata suna nan zaune har a kayi sallar asr , sallah suka tashi su kayi sannan suka fita daga dakin suka nufi parlorn gidan
Wannan kenan..........
✨ _Ammy_ ✨
Zaune take kan sallaya a bedroom dinta bata jima da gama yin sallah ba wayar ta da ke kan dressing mirror ce tayi ringing hannu tasa ta dauko wayar murmushi tayi hadi dacewa "Allah sarki mai babban suna ina jin ya kara so"
picking call ɗin tayi tana Kara wayar a kunnenta yayinda take sallama fuskarta ɗauke da murmushi, on the other hand na cikin wayar yace "wa'alaikissalam my Ammy ya gida"
"lafiya lau Alhmdllh mai babban suna ya hanya, ka iso ne?"
"Alhmdllh ammy,yanzu zamu ta so,in sha