Showing 57001 words to 60000 words out of 127932 words

Chapter 20 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6716

uncle Ibrahim shi da mansoor dake kwance kan sofa, ko sallama babu ta faɗo tana faɗin "wallahi bazata saɓuba bindiga a ruwa,ina luqman ɗin yake"miƙewa luqman yayi ya nufe ta "dan mi zaka tsaya wannan yaron mara mutuncin  yayi maka duka irin haka sai kace jaki" uncle Ibrahim ne yace
"haba innah yaza kice haka,bayan kin san halin luqman da rashin kunya dole yana da laifi"
"hakama za ka ce yaron yayi mashi irin wannan dukanl, amma kace shine mai gaskiya"
"ba wai na goyi bayan shi bane,  a'a nasan halin luqman ne da rashin kunya shine kawai , kuma kema nasan kinsan halin shi sosai" tsaki innah taja tana faɗin "shima ai ba kunyar bace da shi, kuma wallahi bai daki banza ba, idan da ya dake shi nayi shiru lokacin da yake yaro yanzu bazan yarda ba ace da girman shi ya dake shi ba in zuba ido ina kallo   idan kai bazaka ɗauki mataki ba ni zan ɗauka da kaina"
"yawwa innah shiyyasa nake ƙara sonki kin fi dady sona "
"karka damu zanyi maganin shi, fita ka bamu wuri zamuyi magana "da
to innah ya amsa sannan ya kama hanyar ficewa daga parlorn,  kallon uncle Ibrahim tayi sannan tace "kai kuma zauna "zama yayi kan sofa dake kallon wacce innah ke zaune..
  
Da yamma innah ta aiki feenah  kiran uncle ahmad, tana zuwa part ɗin ta samu su noraiz a parlor, yi tayi kamar bata san da su a parlorn ba ta nufi sama,faisal ne yace "lallai ma wannan yarin yar uncle ahmad na zaune a parlorn shi, mama na zuba mashi fura a cup ta shigo da sallama,amsa mata suka yi uncle ahmad na cewa"mamana zo ki zauna "ya faɗa haɗi da nuna mata kusa da shi, zuwa tayi kusa da shi ta zauna,"daga ina mamana? "
" daga wurin innah na ke , tace na kira mata kai "
"to, kice mata gani nan zuwa" da to feenah ta amsa haɗi da ficewa ta bar part ɗin ta koma na innah.

lokacin da suka fita daga part ɗin uncle Ibrahim part ɗin su ya nufa ya shiga bedroom ɗin shi,da ƙafa ya tura ƙofa da ƙarfi  har yaso da tsema mansoor hannun dake bayan shin, ja da baya mansoor yayi yana kallon ƙofar kamar shazim ɗin a wurin,tura ƙofar yayi ya shiga zaune ya gan shi bakin bed, ƙarasawa cikin yayi ya zauna kusa da shi yana faɗin "shazim miyasa ka dake shi, mi yayi maka"banza shazim yayi da shi har saida ya ƙara tambayar shi, still banza yayi da shi ran mansoor ne ya ɓaci, cikin masifa yake ce ma shazim "wai bakaji ina maka maganane, ko nima shashasha ka ɗauke ni ban sani ba"
ɗan nisawa shazim yayi, sannan yace"dole nayi banza da kai mana"
"ok haka kace koh "
"eh" abun yayi matuƙar ɗaure ma mansoor kai, cikin lallashi ya ce"kayi haƙuri nasan kana ganin kamar na goyi bayan luqman ne"shiru shazim yayi kamar ba da shi mansoor yake ba
"haba shazim na san kana jina"
"ina jinka mana" haƙuri mansoor ya shiga ba sai da ƙyar ya sa mu ya shawo kansa har ya dai na fushin da ya ke.

innah da feenah ne zaune a parlor, feenah ta kwanta tana daddan wayar ta, innah kuma na zaune ta ƙurama tv ido, sallama su  uncle ahmad su ka  yi haɗi da  shigowa, amsa ma su  sallamar innah tayi, wuri suka samu su ka zauna, uncle ahmad yace "innah gani feena tace kina kira na, Allah dai yasa lafiya "
"lafiya lau " innah ta faɗa haɗi da kallon feenah tace "takwara tashi ki bamu wuri " da to feenah ta amsa haɗi da miƙewa ta fita,
laɓewa tayi a  bayan ƙofar part ɗin innah, maganar da su innah ke yi take saurare  sai sakin  murmushi take, alamar buɗe ƙofa taji  za'a fito taji, hakan ya sa da gudu tabar bakin ƙofar ta ɓoye bayan part ɗin, uncle ahmad ne da uncle Ibrahim su ka fito daga part, tsayawa tayi har sai da taga shun nufi part ɗin uncle Ahmad sannan ta nufi part ɗin innah da sauri, a bedroom ta samu innah da waya kare a kunnen ta, zama tayi tsakiyyar bed ɗin innah tana faɗin "dan Allah innah kiyi sauri ki gama wayar nan Please"
daƙƙuwa innah tayi mata, dariya feenah tayi, ganin wayar innah ba mai ƙarewa ba ce yasa ta kwanciya kan bed ɗin sai sakin murmushi take kamar wacce aka yima albishir da gidan aljanna, innah ta ɗan ɗauki lokaci tana waya,lokacin da ta kammala, zama tayi ita ma kan bed ɗin "ke kuma lafiya kika zo zaki ta kura man ido " ta shi feenah tayi tana ɗan ya tsine fuska tace " dama nazo ne naji ya ku ka yi da su dady "
riƙe haɓa innah tayi tana faɗin "sannu uwata, to ban sani ba" murmushi feenah tayi tana faɗin "ai naji komi kuka ce " ɗan zaro ido innah tayi tace "dana ce ki fita  kenan laɓewa ki kayi kina sauraron mi muka ce "
"a'a ai ba duka naji abun da kuke cewa ba "
"ƙarya ki ke kinji komi"
"Allah a'a, yaushe uncle Ahmad yace su Aunty uwani zasu zo "
"ban sani ba, tashi ki bani wuri "
"dan Allah innah ki faɗa man " innah tace "naƙi in faɗa" roƙonta feenah ta shigayi akan ta faɗa mata yaushe zasu zo, amma ƙiri ƙiri innah ta ƙi faɗa mata.

✨SHAZIM✨

Kayan shi ya hau haɗawa dan yayi alƙawarin sai ya bar abuja gobe da izinin ubangiji, ya gaji da zaman jiran jin kiran da su ke mashi, shiyyasa kawai ya yanke shawarar tafiya gobe  ko da shi kaɗai ne ban da su fatima, in yaso daga baya su sun dawo, yana cikin haɗa kayan mansoor ya shigo bedroom ɗin, turus ya tsaya yana kallon shazim dake ta faman haɗa kaya, yi yayi kamar ma bai ga shigowar mansoor ba yaci gaba da abun da yake matsowa mansoor yayi kusa da haɗi da dafa kafaɗar shi yace "wai shazim kana nufin har yanzu baka haƙura ba" ba tare da ya kalli mansoor ba yace
"wa yace maka fushi nake  "
"to idan ba fushi kake ba, miye na wani haɗa kaya, dan nasan halinka kana iya cewa lagos zaka koma"
"faɗi ka ke ana jinka "
"haba shazim miye abun fushi a nan"
"wai dan Allah wa yace maka fushi nake, kawai ina son na koma ne saboda aiki na da na baro,  luqman har ya kai matsayin da zai ɓata man rai ne na koma lagos "  ɗan ajiyar zuciya mansoor ya sauke "to shikenan, amma ka bari su abbah su ce ka tafi ko"
"mansoor baza ka gane bane, aikina fa na baro tsawan sati ɗaya da wani abu haba "
"haka ne shazim, amma duk da haka ya kamata ka jira kaji mi zasu ce "
"ai ba tafiya zan yi ba batare da na sanar da su ba, zan faɗa masu in son in tafi gobe "
"to shikenan "mansoor yace, kama mashi yayi ya haɗa duk wani kayan shi da ya zo da su, bayan sun gama masallaci su ka nufa su kayi sallar magrib har da isha daga nan  part ɗin uncle Ahmad su kaje, dinner su kayi bayan sun kammala ne shazim ya samu uncle ahmad har part ɗin shi ya sanar da shi yana so zai koma lagos gobe, ko da ya faɗa mashi cewa yayi ya bari sai nan da ranar lahadi, saboda family meeting da za su yi ranar asabar, ba dan ya so ba ya haƙura, part ɗin su ya koma kwata kwata baiji daɗin hana shi tafiya da uncle Ahmad yayi ba kuma, ammy ya kira ya sanar da ita, ce mashi tayi yayi haƙuri ya jira, ko ba komi zaiga ƴan uwanshi da ya daɗe bai gani ba dama waɗan da bai san su ba, dan bashi da yanda zai yi ne yasa ya haƙura, baya farin ciki da wannan family meeting ɗi.

✨Ammy ✨

kwance take kan gadon ummy, gama wayar su kenan da shazim ta kwanta, tunda su shazim suka tafi abuja kullum tana gidan malam, wata ranar ma a nan take kwana, yau ma anan zata kwana, ummy ce ta shigo ɗaki da sallama, amsa mata sallamar ammy tayi, bakin bed ummy ta zauna tana wash, yanzu indai tayi tafiya ko yaya take sai ƙafafun ta su kama ciwo, sannu Ammy tayi haɗi da cewa "anya ummy baza muje asibiti ba saboda ciwan ƙafafun nan"
"a'a ba sai munje asibiti ba,  yaushe ango na zai dawo?  "
"yanzu nayi waya da shi da gobe zai dawo, amma yanzu sai ranar lahadi saboda meeting da za suyi na family "
"to Allah ya kaimu, su Ahmad ɗin sun sanar da shi kiran da suke mashin ne"
"a'a basu faɗa mashi ba har yanzu, ya dai ce man dawowar shi zai yi ko ba su faɗa mashi ba wai ya gaji da zama aiki ya bari, na daice yayi haƙurin su faɗa mashi "
"eh gaskiya ya ka mata  ya tsaya yaji kiran mi suke mashi "
"kin san halin shi ummy wani lokacin da baƙar zuciya "
"ai kuwa dole ya rage ta, tun da komi ma su kayi mashi shi ya jawo ma kansa "
"haka ne, ummy yaushe su mamy su kace zasu zo?" ammy ta faɗa
"ta ce man wani watan idan Allah ya kaimu "
"Allah ya kaimu, ina son idan za su koma na bi su na kwana biyu banje Morocco ba "
"gaskiya ya kamata kije har da yarannan "
"da su nake son zuwa musamman shazim da bai son shiga mutane "
Ummy tace "ai lamarin angon nawa ne sai adu'a " firar su suke har sai da bacci ya fara ɗaukar su, sannan ummy ta tashi ta tafi ɗakin malam..
Episode 32_33

Washe gari ta kasan ce friday, sun tashi da shirye shiryen tar bar baƙi, uncle Ahmad ne yace ma  Kairiyya ta samu  Feenah da su Fatima su gyara part ɗin da ke kusa da na innah.
A part ɗin innah ta same ta kwance kan gadon innah da a'lama ma a nan ta kwana, ko da Kairiyya tayi mata magana cewa tayi   "mi zai hana a sa masu aiki su yi gyaran"
Kairiyya tace "wannan kuma abbah zaki faɗa ma haka bani ba, tun da bani nace ayi gyaran ba " innah na zaune kan carpet tana jin su amma bata ce komi ba
"To gaskiya ni  bazan   iya ba,gara ma tun wuri kije ki samu masu aiki kuyi gyaran tare,  amma ni bazan iya ba" abun yayi matuƙar ba   Kairiyya  mamaki duk da daman tasan Feenah, ba kasa fai ake sata aiki tayi ba, in dai batayi niyya ba to fa bazata  yi ba, amma ba ta yi tunanin cewa Abbah zai iya sata abu tace bazata yi ba,
"yanzu dai mi kike nufi "
" bana jin daɗi, bazan iya ba "ta bata amsa kai tsaye, Kairiyya tayi tuna nin Innah zata sa baki jin abun Feenah tace amma sai taga innah tayi kamar ba bata san da zaman su a ɗakin ba , kallon Innah tayi tace "Innah kina jin mi tace ko " Innah tace
"dan Allah ni karki dame ni, tun da tace bata jin daɗi, to sai ki ƙyale ta, ai sai  da lafiya ake komai " jinjina kai Kairiyya tayi haɗin da cewa "haka ne kam, gaskiya ne " tana gama faɗa ta tashi ta fice daga ɗakin, innah tace
"yau ga fitinanniyar yarin ya"da harara Feenah ta rakata tana faɗin "sai kace an ce mata nima yar wahala ce irin ta " ta faɗa haɗi da jan tsaki, juya kwanciyar ta tayi tana kallon Innah tace "Amma dai Innah su gwaggo uwani na zuwa yau za a yi meeting ɗinnan ko "
"sannu uwar yan gaggawa, saboda cin rabo ne abun kawai daga zuwa sai a kama meeting, ai a bari su huta "
"shikenan da ƙarfe nawa tace zasu baro kurfi"
"wannan ne kuma ban sani ba "

Kairiyya ko da ta fita daga part ɗin Innah part ɗin uncle Ibrahim ta nufa,  sumun Fatima da Sa'ada tayi, tace su zo su tai maka mata su gyara part ɗin da ke kusa da na Innah, ba musu su ka taso suka bi bayan ta, lokacin da suka isa part ɗin   a buɗe su ka same shi, duk a tunanin Kairiyya  Abba ne ya buɗe shi, sai da suka shiga ciki su ka samu laure mai aikin mama da saude mai aiki momy suna ka kaɓe ƙura, cewa tayi "ai da kun barshi " laure tace "A'a aikin zai yi maku yawa
Ashe  laure ce ta amshi key wurin mama ta buɗe part ɗin ta kira saude ta taya ta su graya pary ɗin, a ganinta ga su a estate ɗin mi zai sa su Kairiyya su yi akin, Kairiyya ta ce"ai da kun barshi, tun da gani ga fatima da  sa'ada  "      laure tace "A'a aikin zai yi maku yawa, ki bari kawai muyi "
Kairiyya tace "Allah kuwa da kun barshi za mu iya"
"A'a duk da haka dai " ganin sun nace ne yasa Kairiyya cewa sai dai suyi aikin tare,a haka su ka cigaba da aikin suna fira sun ɗauki tsawan lokaci kafin su gama,sai wurin sha biyu da minti arba'in da wani abu su ka kammala, part ɗin uncle Ibrahim su Fatima su ka nufa, wanka su kayi da sallah kowace ta nemi wurin kwanciya ba tare da sun nemi abinci ba  duk da suna jin yunwa.

  ✨SHAZIM✨

Kwance yake kan gado a rigingi ne kanshi yana kallon sama, idanun shi a rufe da a lama bacci ya ke, wayar shi dake kan bed side ce ta fara ringing, har kiran ya katse bai motsa ba,wani kiran ne ya sake shigowa, mutsu mutsun  buɗe idanuwan shi ya shiga yi ,buɗe su yayi yana kallon saman ceiling, ya ɗauki kusan five seconds yana kallon,  kiran na shirin katsewa ya zura hannu ya jawo ta, picking yayi ba tare da ya du ba mai kiran na shi ba, muryar majeed ce ta daki dodon kunnen shi yana sallama, sallamar ya amsa cikin kasa lelliyar murya ta masu bacci yake  faɗin"majeed kai ne "
"eh nine, kamar ma bacci kake?"
majeed ya tambaye shi amsa  ya ba shi da "kai dai bari, ya aiki"
"Alhmdllh, dama na kira ka ne saboda kayan nan da ke store, masu su fa sun fara bibiyar kayan "
"mi ya faru kace haka? "
"jiyan bayan tashi na security ya kira ni yake ce man wa su mutane sun zo bayan tafiya ta, wai sun zo da shigar jami'ain kiwan lafiya,  an turo su ne dan su yi bin cike a abnoor a kan ana ba da magani ba bisa ƙa'ida ba , sun nemi da su  buɗe masu store"
"store kuma, su yi mi kenan a ciki "
"shima tambayar su yayi mi za su yi a store shine su ka ce wai suna son su bincka magungunan da muke da su, bai dai buɗe ma su store ɗin ba dan cewa yayi ba shi ke da makullin store ba,da ya faɗa masu haka sai tambayar shi su ka yi wai hospital ɗin na waye, so ya dai ceman bai faɗa masu saboda bai yadda da su ba, in dai har da gaske turo su a kayi yasan baza su zo a wannan time ɗin ba, sun dai ce zasu dawo"
"ok yaushe su ka ce zasu dawo "
"ba su faɗa mashi ba, sun dai ce kawai za su dawo "
"ok to shikenan, nima ranar sunday zan dawo, idan na dawo za mu san yan da zamu bullo ma al'amarin insha Allah, buri na dama su fara bibiyar kayan"
"Allah ya kaimu ranar sunday ɗin"
Ameen ya amsa, sallama su kayi, mai da wayar yayi kan bed side, tunanin ya shiga"wai su waye masu wannan kayan ne?" tambayoyi yayi ta jefa ma kanshi bashi da mai bashi amsar su, ya jima a kwance shi bai koma bacci ba shi bai tashi ba, sai da aka fara kiran sallar asr, sannan ya sauka daga kan gado ya shi toilet, wanka ya sake da al'wala, shiryawa  yayi cikin wani yadi mai taushi brown color ya sa hula milk color, feshe jikin shi yayi da turare mai ƙamshi, masha kamar ka sace shi ka gudu, shoe rag ɗin sa ya nufa ta kalmi ya ɗauko brown color ya sa , wayar shi ya ɗauka da key ɗin mota ya fice zuwa parking lot, wata farar mota da bai taɓa hawa ba tun da su ka zo ya nufa, shiga yayi cikin ta yayi reverse ya nufi main gate, ya na nufar main gate wasu motoci  guda shidda su ka shigo cikin estate ɗin,ko mawa yayi yana tafiya slowly time ɗin da  ya iso bakin gate ɗin har  sun gama shi gowa, ficewa yayi ya bar estate ɗin,part ɗin innah motocin su ka nufa, parking  su ka yi, na cikin motocin ne su ka fara fitowa,wata kyakyawar mata ce ta fara  fitowa fara ce amma ba sosai ba  a ƙallah zata yi kimanin shekara 51 zuwa da biyu Aunty uwani kenan,  part ɗin innah ta nufa, ɗaya bayan su ke fitowa daga motacin, harda wata mata mai matuƙar kama da wacce ta shiga part ɗin innah sai dai tafi waccen haske nesa ba kusa ba,a ƙallah za tayi kimanin shekara 49 Aunty sadiya sunan ta ƙanwar Aunty uwani ce  , su uku suka fito daga bayan motar ita da wasu matasan  mata ɗaya da yaro a hannun ta ɗayar kuma da goyo, mai yaron  bazata gaza shekara 32  ba a duniya, sunan ta Aunty Zainab ɗiyar gwaggo Halima   ce ita ce babbar ɗiyar ta, ɗayar kuma bata wuce shekara 30,ita kuma sunan ta maryam ɗiyar gwaggo  Uwani ce,  motar da ke bayan su wasu ƴan mata ne su ka fito su hudu uku daga baya ɗaya kuma daga gaba ta fito, wacce ta fito daga gaba a ƙallah zata yi ki manin shekara 23 sunanta farida ɗiyar gwaggo Halima ce ita ma  sai  ƴan mata guda uku biyun  zasu yi sa'annin baza su wuce shekara 27  ba Asma'u da Amina kenan,dukkan su suna da aure sai dai ba wacce ta haihu Amina Anwar take aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login