Showing 126001 words to 127932 words out of 127932 words
gaskiya banji daɗi ba,yanzu akan su Aairah har sai ka ka kira da kanka, haba dan Allah "
" ba wani abu bane, faɗin ai yana da daɗi "
"duk da haka dai banji daɗi ba "
" to ayi haƙuri "
"shikenan ya zanyi tunda anriga an gama, yanzu yaushe za su fara lectures?"
" nan da sati uku ne "
"to Allah ya nuna mana lokacin, nan ai gida ne,ko da kama barsu a hostel naji labari bazan bar su ba "
"to shikenan nagode "
"wane irin godiya kuma"
"to shikenan sai sun zo ɗin "
" to Allah ya kawo su lafiya "
"Ameen ya Allah " abie ya faɗa sallama su kayi ammy na faɗin tana gaishe da mom, miƙa ma Abdallah wayar abie yayi , amma bai san yana yi ba saboda hankalin shi ba anan yake,
_har wani ajiyar zuciya ya saki daya ji ammy tace ko da sun zauna a hostel zata dawo da su ne gida, yanzu ko ba komi ya samu kafar da zai riƙa zuwa lagos ba tare da wani abu ba_
zaungurin shi safwan yayi cikin magana raɗa raɗa ya ce
" hankalin ka yanzu ya kwanta ko"
"sosai ma kuwa " Abdallah ya faɗa a hankali yanda su abie baza su ji ba "
"Amshi wayar ka na ce " abie ya faɗa yana sake miƙo mashi wayar, amsa yayi yana faɗi
"ka gani ko Abie, na san ma bazata ji daɗi ba "
"duk da haka dai tunda an faɗa mata ai shikenan nan "
murmushi uncle ahmad yayi yana faɗin "yanzu sai da ka samar ma su idan ka fi yarda sannan hankalin ka ya kwanta yaya"
"bazan ɓoye maka ba gaskiya sai yanzu naji zan iya bari suyi ne sa da ni "
"to ai shikenan tun da ka amince "
Cikin gida su Abdallah su ka nufa shi da safwan, suna shiga main parlor da hayaniyar su Aairah su ka fara cin karo suna ma Ameerah dariya tana kuka saboda ba su samu addimisson a abuja ba, ta so suyi makaranta tare amma Allah bai nufa ba shine suka tasa ta gaba suna mata dariya.
"ku har gobe baza kuyi hankali ba, ai gara ma da abie yace anan za kuyi karatu saboda baku da hankali "
tsit su kayi, Ameerah kuma bata bar kukan da take ba tsawa Abdallah ya daka mata yana faɗin " billahil'azim ko kiyi man shiru ko ranki ya ɓaci " shiru tayi amma hawaye basu daina zuba ba, tsaki yayi ya nufi part ɗin mom, safwan kuma zama yayi kan sofa Aaimah tace "dan Allah ya safwan da gaske abie bai amince ba " ɗaga mata kai yayi alamar eh,ɓata fuska Aaimah tayi tana faɗin
" Amma miyasa abie zai ƙi amincewa " dariya Ameerah ta kwashe da ita " wallahi Allah ya ƙara naji daɗi da abie ya ƙi amincewa "
"yar baƙin ciki in sha Allah zai amince ne"
"bazai amince ba in sha Allah"
tashi safwan yayi yana faɗin
"Aairah ki kawo man tea please " turo baki tayi tana faɗin to, dama tun da ya zauna wurin bata sake cewa ƙala ba, haka nan ita fa shishige matan da yake yi ba burgeta yake ba,tashi tayi ta nufi kitchen ɗin shaf shaf ta haɗa mashi tea ta nufi part ɗin Abdallah, nocking tayi, da kanshi yazo ya buɗe mata ƙofar matsawa yayi gefe yana faɗin ki shigo ciki
" mom ke kirana " ta faɗa so kawai take ya amsa ta gudu, amsa yayi yana faɗin" to muje can main parlor sai na sha a can idan kin dawo daga wurin mom sai ki zo" to tace haɗi da yin gaba yana binta a baya har main parlor, kan table ta ajiye mashi ta nufi ɗakin
mom da Abdallah ta ci karo zai fito, yana ganin ta yace
"harkun biyo ni kenan"
"yaya ba kai na biyo ba wurin mom na zo "
" ba wani " ya faɗa haɗi da ficewa, ciki ta ƙarasa tana faɗin
" mom kinji dai ko abie bai amince ba"
"to ya za kuyi sai haƙuri "
" ya muka iya tunda bai amince ba " ta faɗa kamar zatayi kuka bed ɗin mom ta nufa ta kwanta, murmushi mom tayi " yanzu fa kina iya kuka "
" A'a mom ba kuka zanyi ba"
" ai nayi tunanin shi za kiyi, to wasa yake abie ɗin ku ya amince "
" dan Allah mom da gaske "
" A'a da ƙarya "
" sorry mom, farin ciki ne yasa nace haka, amma naji daɗi da abie ya amince " tana gama faɗa ta fice ta nufi parlor wurin su Aaimah, dariya ta fara yima Ameerah kafin ta sanar da su abie ya amince,ƙululun baƙin ciki kamar ya kashe Ameerah, saboda dariyar da Aairah ke yi mata.
Aaimah kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha da Aairah ta sanar da ita abie ya amince, haushi da takaici kuwa wurin Ameerah ba'a magana.
_Wannan kenan_
Lokacin da Ammy su ka gama waya da abie,parlor ta fito wurin su fatima take sanar da fatima zuwan Aairah, fatima kamar tayi hauka dan daɗi da ma ta jima tana son ganin su har cewa take idan su ka samu hutu sai taje katsina ko dan taga waɗannan yan biyun na su ya dr, yau gashi burin ta na ganin su zai ciki har ma za su zauna tsawan wa su shekaru,taji daɗi sosai da wannan labari da Ammy ta sanar da ita Ammy na barin wurin ta ɗauki wayar ta ta kira Abdallah dan sake ji daga bakin shi, ƙara tabbatar mata yayi da sunan zuwa nan da three weeks.
"ya dr dan Allah su zo next week, wallahi na ƙosa na gan su "
"one week da three weeks ai duk ɗaya fatima, in dai da rai da lafiya za ki gansu har ma sai kin gaji "
"duk da haka dai ya dr"
"to ni dai babu ruwana hukuncin abie ne wannan "
"shikenan Allah ya kaimu, ka basu wayar to mu gaisa "
"sai dai na tura maki number Aairah ko ta Aaimah"
"kai ya dr, to naji ka tura man duka "
"to shikenan zan tura maki "
"yawwa ya dr nagode bye "
"Wait naga sai wani rawar ƙafa kike, karfa su zo ni ki share ni kuma dan saboda ke nasa abie ya amince za su zo dan nima na samu damar ganinki" ya faɗa yana ɗan murmushi, rufe ido fatima tayi ita a dole kunyar zancen shi taji
"kinyi shiru idan haka ne gara tun wuri na sani "
"haba ya dr dan Allah ka daina faɗar haka, kaima ka san babu abun da zan samu da zai ɗuke man hankali har na share ka "
"na sani, nima wasa nake maki, naga dai kina ta rawar ƙafa ne "
"na ƙosa na gansu ne"
"very soon zaki gan su "
"to shikenan, katuro man number" to ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran, bayan kamar minti ɗaya sai ga number ya turo mata duk da ta Aairah da Aaimah,ko kiran shi tace taga number bata yi ba saboda zumuɗi, number Aairah tayi dialing, da sallama Aairah a bakinta tayi picking kiran, a hanzar ce fatima ta amsa mata sallamar tana faɗin
"sister ya kike, ya gida "
"lafiya lau, pls wake magana " Aairah ta faɗa, murmushi fatima tayi sannan tace " na san bazaki gane ni ba, fatima ƙanwar ya shazim abokin ya Abdallah"
"ooo Allah sarki, ya kike ya su Ammy "
"lafiya lau su ke, yanzu take faɗa man zaku zo lagos ke da Aaimah"
"Eh"
"dan Allah kuce ma abie ya barku ku zo next week ba dole sai nan da sati ukku ba pls "
abun mamaki ma ya ba Aairah ganin yarda fatima ke zumuɗin zuwan su duk da ba su san juna ba a zahiri, hakanan taji fatima ta kwanta mata arai ita ma taji ta ƙagu da taganta
" shikenan in sha Allah zan roƙe shi ni da Aaimah "
"yawwa nagode sosai, ina Aaimah take?"
" tana wurin mom "
" ok dan Allah ki bata mugaisa harda mom ɗin "
" to shikenan, kashe idan naje wurin su sai na kiraki "
" to " fatima ta faɗa haɗi da kashe wayar.
Wani wawan tsaki feenah taja, dama tun da taji Ammy ta faɗin zuwan su Aairah taji ranta ya ɓaci hakanan taji ta tsane su duk da bata san su ba amma taji bata ƙaunar su zo
" haba ya feenah miye abun tsaki kuma?"
" dole nayi tsaki, saboda ke shashasha ce baki san mutane ba amma dagaji za su zo sai wani zumuɗi kike "
" bangane bata san su ba, ke dai idan baki san su ba to kiyi shiru amma ita ta san su ko nima nan da kike gani na san su " sa'ada ta faɗa tana hararar feenah
"ƙannan uwarki ne su da zaki ce kin san su,kuma wallahi na kama ki zaki san ni kike harara"
" ba ƙannan uwata ba ne, amma ai su muslmai ne kuma muslmi ɗan uwan muslmi ne, to wai ma ina ruwanki idan sun zo ke dai ba a kanki za su zauna ba kuma ai dai inji nan ba gidan dady bane bare har sai kin zaɓi wanda zaizo kema kara ki akayi " sa'ada ta faɗa tana miƙewa tsaye dan ta san abun da zai biyo baya tsakanin ta da feenah ba mai kyauba ne, tashi feenah ita ma tayi ai tana gani haka ta kwasa da gudu sai ɗakin Ammy tana faɗin " Allah yasa idan su ka zo su koya maki hankali, tunda ta ƙamarki yi ma mutane wulaƙanci sai kace ma nan ɗin gidan ku ne "
"ai da kin tsaya inji uban da kike faɗa ma wannan maganganun " gwalo sa'ada tayi mata tana faɗin
"da karyeyyen hanun " ta faɗa tana langabar da hannun ta irin ciwannan taji tana faɗin " wayyo Ammy wurgi ya shazim yayi da ni "
A harzuƙe feenah ta bi bayan ta, da gudu sa'ada ta shige ɗakin Ammy jikake garam ta banko ƙofa ta rufe da key, bubbuga ƙofar feenah ta shiga yi tana faɗin
"wallahi sai na ci ubanki na kamaki "
daga cikin ɗakin sa'ada tace
" ki kashe ni idan kin tashi "
" zaki san da ni kike magana feenah ta faɗa haɗi da barin bakin ƙofar, ta koma cikin parlor, samun fatima tayi tana waya da mom da Aaimah, haushi kamar ya kashe feenah, ta shima tayi ta nufi bedroom ɗin ta da take kwana, wayarta ta ɗauka tayi dialing number Innah, tana picking ko sallama bata ti ba ta zayyane mata komai dan gane da zuwan su Aairah har da ƙari
Baƙin ciki da takaici ne ya cika Innah ƙala bata ce ba ta kashe wayar, haushi kamar ya kashe feenah jin innah bata ce komai ba.
Shazim da ya dawo gida Ammy ke sanar da shi zuwan na su, Allah ya kawo su shine kawai abunda yace.
A kwana a tashi babu wuya wurin ubangiji yau ya rage saura kwana biyu su Aairah su zo lagos, duk wani shiri da za suyi sun kammala, ranar da zasu tafi kawai su ke jira, Abdallah ne zai kai su, sai ya gama su komai a school sannan zai dawo.
Ameera sun koma Abuja tun last week, ta sha kuka kamar mi bata yanda zata yi dole ta haƙura, taci ƙurin suyi school tare amma bai nufa ba.
Washe gari ranar da za su tafi har gida su ka je su ka yi ma dadi sallama, sannan su ka je gidan granny da gidan Aunty safiya, najma ma kamar ta haɗiye zuciya dan baƙin ciki za su tafi su barta, saboda ita dadyn ta a nan ya samar mata da school, sai da dare sannan su ka koma gida...