Showing 81001 words to 84000 words out of 127932 words

Chapter 28 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6717

tana son zama da ƴar uwarta ne har ta samu sauƙi "
"amma kuma bata ga abun da yayan yarinyar yayi ma yayan ta ba da zata wani bisu kamar wasu ƙannan uwar ta"
"kiyi haƙuri innah,shima luqman ɗin  yana da laifi "
"dama nasan bayan shi zaku bi"
gwaggo Uwani ce tace
" bansan mi yake nufi ba tafiya zai yi ba tare da yasa an saki luqman ɗin ba komi "
"ke bari kiga naje na  samu wannan mara mutuncin "
innah ta faɗa haɗi da miƙewa ta fice bayanta su gwaggo Uwani suka bi har da su Abba,  tana fita shazim na fitowa ɗauke da fatima a kafaɗar shi kamar wata gawa, noraiz da Abdallah na bayan shi sai sa'ada data fito hannun ta ɗauke da jakarta da jakar laptop ɗin fatima,drivern  Ambulance ɗinne ya buɗe mashi ƙofa  ya saka fatima, zama yayi kan wata ƴar chair dake cikin ambulance ɗin,ledar magungunan fatima ya amsa a hannun sa'ada  haɗi da maida ƙofar ya rufe,wani drip ɗin ya sake sama fatima sai da yaga komai na tafiya yanda ya kamata sannan ya fito,  motar mansoor ce ta shigo estate ɗin, gaba ɗaya hankalin su kan motar ya koma har yazo parking lot yayi parking buɗe motar yayi ya fito nufo su yayi luqman  ne ya fito jikin shi duk a sanyaye har ya ɗan faɗa dare ɗaya kawai, da sauri innah ta tare shi yana ganin ta shima da sauri yayi hugging ɗinta hawaye na bin idanuwan shi , su dady ma nufo su su kayi binsu yayi tayi ɗaya bayan ɗaya yana hugging ɗin sai kuka yake, dady ne yayi hugging ɗin shi yana lallashin shi,sa'ada ƙin zuwa tayi wurin luqman haushin shi take ji, mansoor ne  ya ƙaraso wurin su shazim, hugging ɗin shazim yayi "tnxs bro " ɗago da shi shazim yayi yana faɗin "godiyar ta isa haka, yaushe za ka zo "
"In sha Allah next week zan zo"
"to Allah ya kaimu " da ameen mansoor ya amsa, raba jikin su su kayi,
"ku kuzo mu wuce " shazim ya faɗa haɗi da nufar Ambulance ɗin  da fatima ke ciki zai shiga, gwaggo halima ce ta ƙaraso kusa da shi " shazim baza ka bari ko breakfast kuyi ba sannan ku tafi "
"ba komai Aunty, idan mun isa can za muyi "
"shikenan, Allah ya kai ku lafiya, ina gaishe da Ammyn ku sai na zo "
"za taji in sha Allah, sai kinzo "
"to shikenan " ta faɗa haɗi da ko mawa wurin su innah,mama Allah ya sauke su lafiya tayi masu,dady ma da Abba sai da suka yi masu Allah ya kiyaye haɗi da adu'ar Allah ya ba fatima lafiya, ƙin amsa masu shazim yayi dan duk haushin su yake ji musamman dady  kowa sai da yayi masu Allah tsare ban da mutum uku innah, gwaggo Uwani,sai momy dake part ɗin ta bata fito ba dan bama ta san luqman ya dawo ba, sai luqman ɗin dake tsoron yazo wurin saboda shazim, amma yaso ya ga ya jikin fatima yake,mota su ka shi ga, shazim na cikin ambulance   da fatima sai mansoor da noraiz Abdallah da sa'ada a motar mansoor , kairiyya taso ta bi su amma Abba yace ta bari sai za su je sai su tafi tare, feenah taci kuka kamar ranta zai fita haukace masu tayi ita a dole sai tabi shazim  tun ana lallashin ta kan ta bari sai su dady zasu har ta kai ga ba mutane haushi dady ya wanke mata fuska da mari, Allah ya ƙara kowa ke mata. Luqman ya so ya raka su airport amma dady yace a'a.

Suna nan tsaye har motocin su suka bar estate ɗin, sai da suka ga fitar su sannan kowa ya koma part ɗin shi

Suna zuwa airport ba daɗewa lokacin tashin su yayi,har filin in da jirgi yake Ambulance ɗin ta shiga , shazim ne ya turo ɗan gadon da take kwance, da sauri  mansoor da Abdallah  suka fito daga cikin mota suka  shigar da ita cikin jirgin.

. Allah sarki fatima ta zo da ƙafar ta cikin ɗoki da nishaɗi amma zata koma cikin halin jinya, dama haka rayuwa ta gada in yau kai ne gobe ba kai bane, Allah ya baki lafiya mai amfani Ameen.

sa'ada da noraiz ma fitowa su kayi su ka shiga. 
Sallama mansoor yayi masu, da yake harda Abdallah zasu tafi.

Sai da jirgin su ya tashi sannan mansoor ya koma cikin motar ya bar airport  shi ka ɗai cike da kewar su.

Sai da suka isa lagos  sannan shazim ya kira malam ya sanar da shi sun dawo, faɗa sosai malam yayi mashi saboda ƙin ɗaukar wayar su da baiyi ba,duk ya bi ya tayar masu da hankali,haƙuri  ya shiga bashi ,ƙin haƙura malam yayi sai ma kashe wayar da yayi yana faɗin "zaka dawo ka same ni ne ai "
Tun kafin jirginsu ya tashi ya kira number majeed ya sanar da shi suna hanya ya turo mashi  da Ambulance suna tare da patient ne,  bai jira mi majeed zai ce ba yayi rejecting kiran yasan dole majeed zai tambaye shi waye bai da lafiya.

✨LAGOS✨

Kiran Ammy malam yayi ya sanar da ita su shazim na hanya
"amma shazim bai da hankali baba, yanzu da lafiyar su lau amma mu kai ta kiran shi baya ɗaga wa"

"Allah dai ka ɗan yasan dalilin da yasa bai ɗauka  ba"
"amma ko ma minene, ai ya ɗauki kiran mu idan baza su dawo a jiyan ba "
"yanzu dai sai sun shigo, kisa ilya yaje ya ɗauko su dan yace sun iso" da to Ammy ta amsa haɗi da yin rejecting, kiran ilya tayi ta sanar da shi su shazim na hanya yaje ya ɗauko su.
Suna gama waya da Ammy bai jira komai ba ya shirya ya nufi airport shi da ɗayan drivern gidan mai suna ɗan Auta, shi ba kasa fai ya cika driving ba yafi yawan zaman gida.

Ko da suka isa airport ɗin su majeed sun daɗe da zuwa da Ambulance tun da shazim yace mashi suna tafe da patient hankalin shi yaƙi kwaciya sai da ya zo dan yaga waye ba lafiya, basu wani jima ba  jirgin su shazim ya  ƙaraso.

hankalin majeed yayi matuƙar tashi da yaga fatima,bawan Allah ilya har da ƴar ƙwallar shi, shigar da ita su kayi cikin Ambulance ɗin , bai ma lura da Abdallah ba hankalin shi naga fatima,  har sai da shazim yace" wai lafiya Abdallah na maka magana hankalin ka na wani wajen baka ji " sai a lokacin ya lura da Abdallah dake mashi magana, gaisawa su kayi da shi.

Mota kowannan su ya shiga, yanzu ma shazim  Ambulance ya shiga shi da Abdallah sai  majeed  da man a nan yazo,majeed na gaba shida driver yayin da Abdallah ke kusa da fatima shi da shazim, ganin duk sun shige nan yasa noraiz da sa'ada nufar motar da ilya yazo ɗaukar su, ɗan auta kuwa empty ya koma ba kowa a motar da ya zo da ita,  Ambulance ɗin ke gaba su ilya na binsu a baya.

Kasa haƙuri majeed yayi har sai da ya  tambayi shazim mike damun fatima,  duk ya bi ya damu, abun har so yayi ya ba Abdallah haushi ganin yanda majeed ya ruɗe kan ciwan fatima, amsa  shazim ya bashi da  ciwan ta ne ya tashi, tambayar shi majeed yayi miye dalilin
"majeed ka kwantar da hankalin ka,  da sauƙi jikin ta"
tsaki Abdallah yaja,shi kuwa majeed hankalin shi naga fatima bai ma san Abdallah nayi ba, shazim kawai ya lura da shi, girgiza kai kawai yayi ba tare da ya ce ma kowa komi ba
"to amma hospital za'a nufa da ita " majeed ya faɗa, tsaki Abdallah ya sake ja yana faɗin "wai lafiya majeed ka bi duk ka tashi hankalin ka, ance maka jikin ta da sauƙi, amma sai tambaya kake "
"daga tambayar lafiyar ta zaka wani ce na damu mutane jiman ƙarfin hali"
" dan Allah ya isa haka,  gida za'a kaita duk wani abu da ya dace ayi mata zan iya yi mata shi a can ba dole  sai a hospital ba" shazim ya faɗa

Majeed yace "to shikenan , Allah ya bata lafiya "
"Ameen ya Allah " shazim ya amsa, babu wanda ya ƙara cewa komai cikin su har suka ƙara so  gida, horn su kayi da sauri mai gadi ya buɗe masu, ciki su ka shiga, a compound drivern yayi parking da Ambulance ɗin, jin jiniyar Ambulance ne yasa Ammy dake parlor zaune fitowa da sauri gaban ta na faɗuwa, tana fitowa su shazim na fito da fatima, da sauri ta ƙara so kusa da su dan taga waye kuma ba lafiya, ai ko da tayi arba da fatima kwance kamar matacciya,wani mummunan faɗuwa gaban ta yayi, jiri ne ya fara kwasarta  ta tafi luuu zata faɗi  babu wanda yalura da ita sai noraiz,da wani masifafen gudu  ya ƙaraso wurin ta yana kiran sunan ta cikin ƙaraji  ganin ta tafi luuu zata faɗi,ririƙeta yayi,ƙasa suka nufa shi da ita dan tuni har ta sume,  gaba ɗaya hankalin su shazim ya dawo kanta, shazim ma a tamanin ya ƙaraso wurin su  saura kaɗan ya faɗi..
Episode  _44_45_

tallabo kanta yayi  yana kiran sunan ta

"Ammy!  Ammy!!  pls ki tashi dan Allah " sai roƙwanta yake da ta tashi duk ya bi ya firgice sai jijjiga ta yake, noraiz ban da kuka babu abun da yake, ilya ne ya shiga ciki da sauri, ruwa ya ɗauko a kitchen da sauri ya fito ya dawo wurin su, Abdallah ne ya amsa ya nufi ammy da ke kwance a jikin shazim, da sauri ya kwance marfin robar ruwan ya shiga  yayyafa mata sai da ya yayyafa mata kusan sau ukku sannan ta ja wani dogon numfashi, Alhmdllh su ka shiga furtawa, hawaye ne suka taru idanuwanta
"mi ya faru da fatima??, kar ka saki kace man ta mutu  " tana faɗa hawayen da suka taru a idanuwan ta na zuba, abun tausayi su Abdallah ma sai da zuciyoyun su suka karaya ganin yanda Ammy ke zubar da ƙwalla
"ki kwantar da hankalin ki Ammy, ba wani abu bane ya same ta lafiyar ta lau "
"taya zaka ce man tana lafiya bayan na ganta a haka "

"da gaske nake Ammy, ki kwantar da hankalin ki " ya faɗa haɗi da kallon su majeed yace " majeed ku shiga ciki da ita " da to majeed ya amsa, shi da Abdallah su ka shiga da fatima, da sauri Ammy ta tashi ta bi bayan su, bin bayan ta noraiz yayi ya na  share hawaye , shazim kallon sa'ada da ke gefe rakuɓe sai hawaye take  yayi yace " shiga ciki mana " da to ta amsa haɗi da bin bayan su noraiz ta shiga ciki,komawa yayi cikin Ambulance ɗin ledar magungunan fatima ya ɗauka sannan yayi ma drivern sallama, bai  shiga ciki ba   waya ya ciro daga aljihun wandon shi, dialing ɗin wata number yayi,wanda ya kira na ɗagawa bai ko amsa mashi sallamar da yake yi ba yace " kayi sauri ka  kawo man na dawo " yana gama faɗa yayi rejecting kiran, ciki ya nufa, bai same su a main parlor ba hakan yasa shi nufar medical room ɗin su dake kusa da part ɗin shi, tura ƙofar yayi ya shiga ciki, tsai tsaye ya same su fatima kuma na kwance kan gadon marasa lafiya gaban gadon ya ƙarasa haɗi da ajiye ledar da ke hannun shi kan ɗan table ɗin dake gefan gadon wani drip ya sake fiddowa daga cikin ledar haɗa shi yayi duk su Ammy na nan sun zuba mashi ido harya gama haɗa shi ya sama fatima, sai da ya gama daidata komai sannan ya kalle su yace "mu fita mu bata wuri "
ficewa su kayi zuwa waje, ban da Ammy matsawa ma tayi kusa da gadon ta zauna kan wata kujer ta roba  dake gefan gadon
"Ammy mu fita bata son kowa kusa da ita yanzu " shazim ya faɗa
"babu inda zani, ina nan har sai ta farfaɗo ta faɗa man abun da ya same ta " lallashin ta ya shiga yi akan ta tashi su fita amma ƙiri ƙiri tace bata fita, saima tsare shi tayi akan dole saiya faɗa mata abun da ke damun fatima shiru yayi yana kallon Ammy ba tare da yace mata komai ba
"magana nake maka shazim mike damun fatima ka wani tsare ni da idanuwa kana kallo na" Ammy ta faɗa da damuwa a fuskar ta, duk ta damu da son jin miya samu ɗiyarta
"kiyi haƙuri Ammy kamar yan da nace maki ciwanta ne ya tashi "
"haba shazim sai kace dai ban san yanda ciwan nata yake ba, kuma yaushe rabon da ya tashi ina tuna nin tun tana ƙarama kuma  kai da kanka kace man ta samu sauƙi idan ba abu yayi tsanani ba ba lallai bane ciwan ya tashi"
"haka ne Ammy, amma ai bai zama dole sai abun yayi tsanani ba"
"shazim!  shazim! !  shazim!!!,  sau nawa na kira sunan ka "
"sau uku Ammy "
"to ka faɗa man mike damun ɗiyata mi ya haddasa mata wannan ciwan tun kafin ranka ya ɓaci, idan ma laifi tayi maka ka dake ta ka faɗa man dan na fara zargin laifinka ne ciwan ta  "
"Ammy kema kin sani bazan taɓa sa  sannu na daki fatima ba duk kuwa abunda tayi man"
"to naji faɗa man mi yasa same ta " baya son ya faɗa mata ne dan kar ta tashi hankalin ta sosai,
"kayi shiru?"
"zan faɗa maki Ammy, amma yanzu ina so na ɗan watsa ruwa, zan zo part ɗin ki na same ki "
"na lura dai faɗaman ne baka son yi "
"ba haka bane Ammy zan faɗa maki amma yanzu ki bari na watsa ruwan, ko fa breakfast ba muyi ba mu ka taho" jin yace ko breakfast basu yi bane yasa tace " to shikenan na ji zan koma part ɗina, amma kar ka shanya ni, zan sa Innah Asabe ta shirya maku breakfast a dinning "
"in sha Allah da na shirya zan shigo "
"to shikenan "
fita su kayi daga ɗakin, bin bayan Ammy noraiz  da sa'ada su ka yi , a parlornta ta zauna kan sofa,  kusa da ita noraiz yazo ya  zauna, sa'ada kuma kan sofa ta zauna tana faɗin " ina kwana Ammy " kwata kwata Ammy bata san da sa'ada aka zo ba sai yanzu da ta gaishe da ita sannan ta san da ita su ka zo " lafiya lau sa'ada  tare ku ke kenan "
" eh Ammy, ya gida "
" Alhmdllh, ya su momyn ku "
"suna lafiya "
"Masha Allah "Ammy ta faɗa
Innah Asabe ce ta shigo parlorn, gaishe da ita noraiz da sa'ada su kayi, cikin kulawa ta amsa tana tambayar ya mutanen abuja.

_*✨SHAZIM✨*_

A bakin part ɗin shi ya sami su Abdallah sun yi  tsaye, kowa da abun da ke damun shi majeed gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake burin shi ɗaya su keɓe da shazim yaji miye ke damun ta yayin da Abdallah ke gefe guda sai cika yake yana batsewa duk dan saboda majeed dan duk ya lura da take taken shi, da kallon shazim ya bi su,  murmushin gefen baki yayi
yana faɗin "lafiya dai dakarun yaƙi, duk kun wani yi ma mutane cirko cirko sai kace wasu body guard "
majeed ne yace " dan Allah ka ajiye  wannan wasan a gefe,  ka ƙi ka faɗa man mi ke damun fatima dan na daɗe ban ganta aciki irin wannan halin ba " 
 Abdallah ne yayi saurin cewa
"wai kai dan Allah wannan damuwar ta micece ne, duk ka wani bi ka damu mutune da mike da munta sai kace in an faɗa maka ɗauke mata ciwan zaka yi " wani ɗan iskan kallo majeed ya bi Abdallah da shi can kuma sai yace
"ina abun da ya dame ka ne wai da tambayar da nake tun da ba kai nai mawa ba, wai ma miye naka a ciki ne  ina ruwan ka da ni ne ma"
"wannan kuma matsalar kace" Abdallah ya faɗa haɗi da jan tsaki ya shige part ɗin shazim, shazim dai na tsaye yana bin su da idanuwa  dariya ce ke cinsa amma sai ya ɗaure fuska bai yi ba amma a zuciyar shi dariya kawai yake masu.

Majeed ne yace " ni wallahi abun a hashim ma mamki yake bani, dan na tambayi abun da ke damun ta laifi nayi ne zai wani dage shi a dole kar a tambayi mike damun ta sai kace wani mugun abu "

Shazim ne yace " kar ka damu ranshi ne kawai a ɓace ba wani abu ba "
"dan ranshi na a ɓace shine zai ta wannan ƙarfin halin"
" ya isa dai yanzu kayi haƙuri, komai ya wuce  "
hmmm kawai majeed yace dan ba ƙaramin ɓaci ranshi yayi ba da abun da Abdallah yayi mashi,
"kayi tsaye mu shiga ciki " shazim ya faɗa, ok kawai majeed yace haɗi da bin bayan shazim su ka shiga ciki, zaune su ka samu Abdallah kan sofa ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya jin alamar shigowar su ne yasa shi zaro wayar shi da ke cikin aljihun shi yayi dialing number Abie, yana picking ya tashi ya fita zuwa waje, a bakin ƙofar part ɗin ya tsaya amsa sallamar da abie yayi yayi sannan yace " ina kwana abie, ya su mom "
"lafiya lau, ya su shazim ɗin ya kuma jikin ƙanwar tasa "
" lafiya lau abie, jikin ta da sauƙi "
" to Allah ya ƙara sauƙi, shazim ɗin na kusa "
" eh bari na bashi "
" to " abie ya faɗa, ƙofar ɗakin ya tura ya shiga ciki, zaune majeed yake yayin da shazim ke tsaye bakin fridge, ƙarasawa Abdallah yayi kusa da shi miƙa mashi wayar yayi yana faɗin  " abie ne ke magana" ok shazim yace haɗi da amsar wayar ya kara akunnen shi " ina kwana abie "
"lafiya lau shazim, ya kwana biyu, ka yada mu ko " murmushi yayi yana cewa "ba haka bane abie, ya mom "
"haka ne mana shazim,ban taɓa ganin ƙafar ka a katsina ba  idan ba abuja kaje ba nima 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login