Showing 111001 words to 114000 words out of 127932 words
da bokan turai " wuri ya samu kan sofa kusa da ita ya zauna, mai akin ummy ce tace " ina wuni "
"lafiya lau "
ya amsa mata haɗin da kallon ummy yace
"ina wuni ummy, ya ƙafafun "
"da sauƙi ya aiki "
"Alhmdllh"
"ya fatima da jiki "
"Alhmdllh taji sauƙi sosai "
"to masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi "
"Ameen " sun ɗan jima suna taɓa fira da ummy kafin daga bisani ya nufi part ɗin malam
Samun shi yayi a kan carpet yana duba wani littafi,sallama yayi mashi haɗi da ƙarasawa ciki ya samu wuri ya zauna kan carpet ɗin, amsa sallamar malam yayi sannan yace
"daga ina haka da yamma "
"daga Abnoor nake, shine nace bari nazo na duba ku kai da ummy "
"ai kuwa ka kyauta,ina nuraddeen da fatima "
"Fatima dai na gida, noraiz kuwa yana mall kasan yanzu noraiz an daina zaman banza"
murmushi malam yayi yana faɗin " haka ne kam aboki na an girma yanzu ba'a zaman banza, to Allah ya taimaka"
"Ameen "
"fatima jiki yayi sauƙi ko "
"ta samu sauƙi ba inda bata zuwa yanzu "
"to Allah ya ƙara sauƙi"
"Ameen "
"yaushe zata fara zuwa makaranta? " malam ya tambaya
"in sha Allah nan da wani watan zasu fara karatu, da yake makarantar basu jima da bata addimisson ba "
"Ah abu yayi kyau Allah ya kaimu nan da wani wata "
" Ameen malam"
"ya wajen su kawun ka sun sake kiranka kuwa "
"A'a ba wanda ya kira ni cikin su " ya faɗi hakan kawai saboda bai son malam na mashi maganar yayi haƙuri ya ƙyale su
"shazim kenan, ina so kasa haƙuri a zuciyar ka, ko jiya Ahmad ya kirani yace suna nemaka ba su samun ka, abun da ya faru shazim yariga da ya faru tun da yaron nan yayi nadamar abun da yayi kayi haƙuri mana, yanke alaƙa da su bai da amfani su ɗin jinnin ka ne "
"amma ai malam su basu ganin haka"
"wayace maka basu gani sun sani kuma duk wani abu da kaga suna yi maka suna yi ne dan suna sonka a matsayin ka na ɗan ɗan uwan su "
"malam kai kaɗai kake fahimtar haka, amma su ba haka bane a ransu"
"idan zaka biye wannan tunanin naka bazaka taɓa fahimtar abun da nake so ka fahimta ba"
" malam na fahimce ka kuma nasan mi kake nufi"
"da ka fahimta da baka ɗauki wannan fushin da kake yi da su ba, ko ka manta lokacin da kana yaro miye wanda uba ke yima ƴaƴanshi wanda Ibrahim bai yi maku ba"
"malam baka san waye uncle Ibrahim ba shiyyasa kake cewa haka, kawai yayi ne saboda wani dalilin shi "
"hmmm lallai shazim,duk da ban zauna da Ibrahim ba sosai amma ina tabbatar maka da cewa mahaifiyar shi da yayan shi kaɗai za su nuna man sanin Ibrahim,suma sai dai su nuna man wani amma Ibrahim na san shi sani bana wasa ba, a halayen shi babu wanda ban sani ba, ko ƴan uwan nashi basu san shi da shi ba, tun da kaji nace kayi haƙuri ka maida komai ba komai ba kayi hakan kawai"
"shikenan malam, amma wane hali ne nashi wanda ka sani har kake cewa ƴan uwan shi basu san shi da shi ba?"
"abun da ya wuce shazim ya riga da ya wuce sai dai kuma mu fuskanci gaba "
"Amma malam da ka sanar da ni "
"ka kwantar da hankalinka, idan akwai ƙaddarar ka sani zaka sani, amma karka sama ranka wani abu ba komai bane fatana kawai ka daina wannan fushin mara amfani da kake yi da su "
"shikenan malam in sha Allah zan dai na"
"kaji ɗan albarka ko kai fa " malam ya faɗa yana shafa kan sa, canza firar suka yi zuwa wata, ya jima sosai a gidan,sai bayan da yayi sallar magrib sannan yayima malam da ummy sallama ya kama hanyar gida,
yana shigowa layin su ya hangi wannan baƙar jeep ɗin tayi parking a ƙofar gidan su mai gadi na tsaye bakin motar da alama magana su ke da mai motar, ƙarasawa yayi bakin gate ɗin, mai gadin na ganin shi da sauri ya nufi gate ya buɗe mashi, ko kallon inda jeep ɗin nan take bai yiba ya shige ciki, yana shigewa mai gadi ya maida gate ɗin ya rufe, parking yayi a compound kashe motar kawai yayi ba tare da ya ɗauki kayan shi dake ciki ba ya fito ya nufi mai gadi dake ƙoƙarin ficewa zuwa wurin wannan mai jeep ɗin, da hannu ya dakatar da shi,alama yayi mashi da ya zo, da sauri mai gadin ya nufo shi,yana isowa yace " barka da dawowa ranaka ya daɗe "
ba tare da ya amsa mashi ba ya jifa mashi tambaya
"wanene a bakin gate da na ganku a tare? "
"wani mutumi ne"
"wani mutumi? kana nufin baka san shi ba"
"eh ranka ya daɗe "
"ok, maganar mi na hango ku kuna yi? "
"tambaya ta yake wai da yaushe zaka dawo gida, to shine sai gaka ka dawo "
"shine kawai abun da na hango ku kuna tattaunawa " da sauri mai gadin yace
"eh shine ranka ya daɗe"
"am wama kake da suna ina fatan kasan halina, ka faɗa man maganar da kuke tattaunawa da shi karka bari nayi bincike na gano gaskiya"
"yallaɓai dai Allah kayi haƙuri, wallahi ina tsoron matakin da zaka ɗauka a kaina, amma maganar gaskiya ya tambaye ni ne akan wai kai ke da asibitin abnoor, nace mashi eh naka ne to shine yace wai mahaifiyar shi ce bata da lafiya wai yaji ance a asibitin ka kuna duba marasa lafiya a kyauta wai bai san ta yanda zaiyi magana da kai ba shine yake so wai dan Allah na bashi wani haske ta yanda zai samu ayi ma mahaifiyar shi aiki"
"wane kalar haske kenan"
"wai so yake na haɗa shi da Ammy, to dana ji yace haka ne sai nace yaje asibitin ya kai ta za'a du bata ba dole sai Ammy ta sa baki ba, shine yace wai zai bani dubu ɗari dan na haɗa shi da Ammy "
"sai kace mashi mi kenan"
"zan bashi amsa ne sai gaka ka dawo"
"ok shine kawai abun da kuka tattauna"
"shine kawai ranka ya daɗe"
"to amma mi yasa naga kana ƙoƙarin komawa wurin shi "
"zan koma nace mashi ne idan da gaske yake ya zo ya sameka kuyi magana, "
"zaka iya tafiya, amma ba sai ka koma wurin shi ba "
"to shikenan nagode" mai gadin ya faɗa haɗi da komawa bakin ƙofar ɗakin shi ya zauna .
Ciki shazim ya shiga,ba kowa a main parlorn , sama ya nufa zuwa part ɗin shi, yana tura ƙofar ya shiga wani ƙamshi ne ya bigi hancin shi,ba irin wanda ya saba ji a ɗakin , wani irin ƙamshi ne gashinan dai, bin ko ina na ɗakin ya shiga yi da kallo sai gani yayi kamar an canza mashi fasali , azuciyar shi yace
"wannan wane irin ƙamshi ne haka" ya faɗa haɗi da nufar bedroom ɗin shi nan ma ƙamshin yaji irin na parlorn, mai da ƙofar ɗakin yayi ya rufe , gaba ɗaya ƙamshin ya addabe sa dressing mirror ɗin shi ya nufa inda yake ajiye room fresheners ya jawo ƴar locker room fresheners ne iri iri a cikin locker, daya daga cikin su ne ya ɗauka haɗi da maida locker ya rufe, fesa room freshener ya shiga yi sai da ya tabbatar ya canza ma ɗakin iskar shaƙa tukun ya maida turaren wurin zaman shi, kayan jikin shi ya shiga ragewa, toilet ya nufa bayan minti biyar ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani a hannun shi yana goge kanshi, ajiye towel ɗin yayi daya gama guge kansa,zama yayi kan kujerar dake bakin dressing mirror ɗin nan ya shiga shafe shafen shi sai da ya ɗauki kusan minti biyar zaune yana abu guda daga baya ya nufi corridor da wardrobe ɗin sa take,ash ɗin jallabiya ya ɗauko ya sa, komawa yayi bakin dressing mirror ya feshe jikin shi da turare, yana shirin barin wurin yaji anturo ƙofar bedroom ta ciki mirror ya zuba ido dan ganin wanene wannan da ya fi ƙarfin yi mashi nocking, a iya sanin shi dai ko Ammy bata shigar mashi ɗaki babu nocking, turo ƙofar tayi ta shigo hannunta ɗauke da tray data shirya mashi abinci, zuba mata ido yayi yana kallonta ta cikin mirror har ta gama shigowa ta nufi ɗan table ɗin dake tsakiyar ɗakin ta ajiye mashi juyowa tayi tace " dinner ne na kawo maka " banza yayi da ita kamar ma bai san da zamanta a ɗakin ba, matsowa tayi kusa da shi kamar zata shige jikinsa tana faɗin " ya shazim wai minene matsalar, ina sonka kuma kaima nasan kana sona,so banga wani abu aciki ba da zaka rinƙa wulaƙanta ni " baƙaramin ɓaci ranshi yayi ba wai yau wannan yarinyar ce ta samu power har ta iya tsayawa a gabanshi tana faɗa mashi waɗannan maganganun, bai gama fita daga mamaki ba yaji ta kai mashi runguma ta baya.
Episode _60_61
"Please duk ka ajiye wani fushi a gefe da kake yi dani,abun da ya wuce ai ya riga da ya wuce " ta faɗa tana wani ƙara manne mashi ajiki haɗi da zagayo da hannunta tana shafa ƙirjinsa,wani irin mumunnan ɓacin rai ne ya rufeshi har bai san lokacin da yayi wurigi da ita ba, bata faɗa kan komai ba sai kan table ɗin dake tsakiyar ɗakin gaba ɗaya ta kifa kan tray da tashigo da shi,kafa abinci ya zube ajikinta, azabar zafin abincin da taji ne yasa ta fasa wata uwa ƙara gashi hannunta ya bugu sosai, bata gama dawowa hayyacin ta ba ya ɗago da ita wanke ta yayi da lafiyayyun maruka har sau huɗu tangal tangal ta shiga yi juwa ta kwashe ta sai ƙasa jikake tim ta faɗi ba ƙaramin buguwa ƙugunta yayi ba, fashewa tayi da wani matsannancin kuka tana faɗin " wayyo Allah nah momy zai kashe ni, na bani innah ki zo ki taimake ni ya ɓallaman ƙugu "
tsawa ya daka mata yana faɗin " tashi ki fita ki bani wuri kafin ranki ya ɓaci" wani kukan ta sake fashewa da shi dan bazata iya tashi ba dan ba ƙaramin azaba take ji a ƙugunta ba gashi idanuwan ta bata wani gani sosai saboda marukan da yayi mata har jini ya kwanta gefan indonta na hagu,ganin bata da niyyar tashine yasa shi jan hannunta data bugu ƙiyyy ya jata har bakin ƙofa yana zuwa yayi wurgi da ita wani ihu ta kwala zaiyi wuya ace su Ammy basu ji ta ba, dan kware baki tayi sai ihu take tana ta bani ta lalace hannunta ƙugunta,maida ƙofar bedroom ɗinshi yayi ya rufe nan ya barta sai kuka take tana kiran su Kairiyya su zo su kawo mata ɗauki.
Noraiz ne ya shigo a sukwane jin ihun mutum, bai ɗauki murya ba ya dai ji ihu da koke koke sunyi yawa kuma a part ɗin yayan shi, hakan ne yasa shi shigowa a guje,a nan durƙushe ya sameta sai kuka take
"wai wacece ke wannan ihun lafiya?,mi ya sameki?" bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba sai ma sake fashewa da wani kukan da tayi, su fatima ne suka banko ƙofar ɗakin har rigen rigen shigowa suke Ammy na bayan su, noraiz sai magana yake mata, amma taƙi shiru gashi bai gane ko wacece a cikin su ba bare ma ya san minene ke damun ta, sai da ya ga shigowar su kairiyya sannan ya fahimci cewa ita ce,tsaki yaja haɗi da cewa
"yo wai ashe ke ce ki ka wani addabi mutane da ihu, ai ba wani ya aiko ki part ɗin nasa ba koma mi yayi maki wallahi Allah ya ƙara " abun da yasa ya faɗi haka yasan dole ita da shazim ne wani abun tayi mashi har yayi mata
"wane irin sakarci ne wannan noraiz, bakaga halin da take ciki ba kake mata Allah ya ƙara,kenan ma kasan abun da ya sameta?" Ammy ta faɗa yayin da take matsawa wurin feenah da kairiyya ke ta ƙoƙarin ɗagawa amma ta kasa saboda data ɗagota take komawa saboda bata iya tashi
"yana wuce wani abu tayi ma ya shazim, tun da daman ya hanata shigo mashi part, amma da yake ba jin magana take ba ai gata nan ta shigo "
noraiz ya faɗa yayin da yake ƙoƙarin juyawa ya nufi ƙofa, da katar da shi Ammy tayi ta hanyar cewa
"na ga kana shirin fita ina zaka ko bakaga halin da take ciki ba ne,kuma yaushe shazim ɗin ya shigo gidan "
"na gani Ammy mi zan yi mata?"
"tambayata kake?"
"A'a Ammy mi zan yi mata to"
"kira man shi yayan naka da ya yi mata hakan, ai sai ya zo ya san yanda zaiyi da ita idan ma hospital zai kaita"
"
to noraiz yace haɗi da nufar ƙofar bedroom ɗin shazim ɗin yayi nocking shiru ba'a bashi izinin shigaba ba kuma a buɗe ƙofar ba,Ammy tace
"lafiya?"
"da alama dai baya ciki, dan ban ji motsin shi ba "
kallon feenah Ammy tayi tana faɗin " wai ma mi ya sameki, da nayi tunanin ko ke da shazim ne?"
"Ammy shi ne ya mare ni ya kuma haɗa ni da table ɗin bedroom ɗin shi ko nan shine ya jeho ni "
sai da tayi magana tukun Ammy ta lura da jinin daya kwanta a gefan idon ta, ga sawun hannuwan shi nan a fuskar ta raɗau, mi noraiz zai in ba dariya ba jin tace wai ya jehota, sa'ada ma ɓoyewa tayi bayan fatima tana dariya, daƙuwwa Ammy tayima noraiz tana faɗin
"ya jeho ki dai ?, sai kace wasu kayan wanki " wata dariyar noraiz ya sake kwashewa da ita yana faɗin " kayan wanki fa ki ka ce Ammy " wani ƙululun baƙin ciki ne ya tukare feenah ganin yan da noraiz ya dage sai kwasar dariya yake yana mata Allah ya ƙara
"Noraiz wallahi zanci mutuncin ka kai da sa'ada, ku wane irin mutanene wai, tana wani hali kuna mata dariya saboda rashin tausayi "
"Ammy kina ji fa tace a bedroom ɗin shi ya mareta, in ba tsabar iskanci irin nata mi ya haɗata da bedroom ɗin shi" noraiz ya faɗa
tsaki Ammy taja haɗi da nufar bakin ƙofar bedroom ɗin shazim, nocking ta shigayi tana kwala mashi kira amma babu alamun ma yana ɗakin,
kallon feenah tayi tace " ko fita yayi? " girgiza mata kai feenah tayi tana faɗin " yana nan ciki, daya jeho ni waje mai da ƙofar yayi ya rufe " dariyace ta kusa kufce ma noraiz jin ta sake cewa ya jehota, da sauri ya sa hannu ya tushe bakin sa haɗi da sadda kai ƙasa
"shazim kana jina shine kayi banza dani ko saboda tsabagen rainin wayau" Ammy ta faɗa yayin da take sake nocking ɗin ƙofar still shiru babu alamun zai zo ya buɗe mata, ganin dai da gaske ba zuwa zai yi ba ya buɗe mata ba ne yasa tace su Kairiyya su kama feenah, haka su ka talallabata kamar kayan wanki da take faɗa su ka fice noraiz na bayan su yana dariya mara sauti dan gudun kar Ammy ta ji shi, haka su ka saukko da ita daga saman stairs un expected su ka hangi shazim kwance saman sofa three seater ya ɗaura hannun shi na dama saman kanshi yayin da hannun shi na hagu yake saman cikinsa da alama ma bacci yake jallabiyar da yasa ce ɗazo a jikin shi , abun har so yayi ya ba feenah tsoro tun da ita dai ta san lokacin da ya fito da ita bedroom ɗin shi ya koma abun mamaki kuma gashi a parlorn Ammy, Noraiz ne yayi surin cewa "to ga ya shazim a parlor kin gani kenan ƙarya take da tace shine ya mare ta Ammy " zuba shazim ido Ammy tayi baccin shi kawai yake kwasa abun shi hankali kwance,zama kusa da shi Ammy tayi tana kiran sunan shi haɗi da bubbuga hannun sofar, duk abun da ke faruwa idon shi biyu yana jin su, sai da Ammy ta sake kiran sunan shi tukun ya buɗe ido yana kallon ceiling sai da ya ɗauki sakanni sannan ya mai da duban shi ga Ammy
"lafiya na ganka nan kwance?" Ammy ta jefa mashi tambayar, ɗan ya tsine fuska yayi haɗi da yun ƙurawa ya tashi zaune
"kai na ne keman ciwo shine na sha magani na kwanta "
"Amma shazim mi feenah tayi kayi mata haka?"
"wacece kuma feenah?" ji wani tambayar rainin wayo nan wurin shazim
"ok baka ma santa ba "
"Ammy naji kina wata magana ne bayan ni tun da na dawo ina nan kuma ni banga kowa ba, shiyyasa na tambaye ki " fashewa feenah tayi da kuka tana faɗin
"wallahi ya shazim mun haɗu ba dinner naje kai maka ba kuma ma ai tray yana bedroom ɗinka" hannu Ammy ta ɗaga ma feenah tana faɗin "ya isa haka feenah, yanzu kai ai sai kaje da ita medical room ka du ba hannun ta"
tashi yayi yana faɗin "Ammy cewa fa nayi kaina ke man ciwo, bazan iya duba kowa ba a yanayin da nakeji kai na, noraiz ya kaita asibiti " yana gama faɗa ya kama hanyar barin parlorn
"tafiya ma kake?,ka yima yarinyar mugunta sannan kace baza ka duba ta ba "
waigowa yayi yana faɗin "bana jin daɗi ne Ammy kuma ni ban ma san akan mi kike magana ba" yana gama faɗa ya haye sama, da kallo kawai Ammy ta bisa tasan ƙarya yake shine ya dake ta amma zai ce wai bai ma san akan mi take magana ba
"Kairiyya ku ka mata zuwa waje noraiz ya kaita asibiti, kai kuma maza ka ɗauko key ka kaita asibiti " ammy ta faɗa tana kallon noraiz da ke tsaye, turo baki yayi yana faɗin
"Ammy ni bacci nake ji " ko kallon shi Ammy bata yiba tace "ku fita da ita kunji, gani nan zuwa"
da to su ka amsa haɗi da nufar waje da ita, Ammy kuma bedroom ɗinta