Showing 108001 words to 111000 words out of 127932 words
zai zame maki masifa a rayuwa, miyasa bazaki rabu da shi ki kama wanda ke sonki naga dai ba wani abu da dr shazim zai nuna ma dr kabir, kuma tun da ki kaga kina roƙon Allah a amma kuma baki samu abun da kike so ba, ki haƙura mana inaga haka shine mafi alkairi a rayuwar ki "
"maryam amma kin fi kowa sanin yanda nake son dr, mi zai sa kice in rabu dashi "
"idan baki rabu da shi ba ya zakiyi hidaya, bafa a so dole kin sani, tun da ki ka ga ya nuna baya ra'ayin ki ki haƙura mana ko dan ki samama kanki sauƙi"
"ni dai shawarar da zan baki shine ki fitar da shi a zuciyar ki,ki roƙi Allah idan har dr kabir alkairine a rayuwar ki Allah ya tabbatar maki amma idan kinji "
"maganar gaskiya ina son dr so mai ƙarfi wanda nake jin bazan iya daina son shi ba "
"to aikuwa kina da aiki mai girma a gaban ki"
"ba wani aiki,in sha zan cigaba da roƙon Allah wataran na san zai so ni "
"gaskiya hidaya baki cikin hankalin ki, naga Allah kika roƙa akan idan shi ba alkairi bane a rayuwar ki ya sauya maki da alkairi, yanzu ga alkairin ya zo amma kin kasa fuskantar gaskiya "
"bazan ɓoye maki ba maryam wallahi bana son dr kabir idan nace na amince da soyayyar sa zan cutar da kaina ne kawai tunda bana son shi "
"ba cewa nayi ki amince da shi ba, A'a ina son ki fitar da tunanin dr shazim a zuciyar ki ki roƙi Allah idan har dr kabir alkairine Allah ya tabbatar maki, amma kina ɓata lokacin ki ne akan shazim "
"bazaki gane yanda nake jinshi bane a raina maryam"
"bazan gane ba ko dai bazaki gane ba "
Haka suka cigaba da magana a tsakanin su kowa so yake ɗan uwan shi ya fahince shi har dai ummah ta shigo ta same su, tana shigowa su kayi shiru binsu da idanu tayi daga baya tace,
"maryam ɗan bamu minti biyu babanta na san magana da ita " da to maryam ta amsa, kallon hidaya ummah tayi tace
"ta shi ki wuce Abban ku na kira" gabanta ne ya faɗi , yanzu idan Abba ya tambayeta mike damun ta mi zata ce mashi
"ummah nace maki fa kaina ne kawai yake ciwo "
"zaki tashi ki wuce ko kuwa " tashi tayi ta nufi ƙofa ta fice zuwa parlorn Abban ta zaune ta same shi kan carpet yana duba jarida, sallama tayi ta shiga ciki, amsa mata sallamar yayi yana nuna mata wurin zama, zama tayi inda ya nuna mata kusa da shi, gaishe da shi tafa ra daga bisani tace "Abbah gani ummah tace kana kira na"
"miyasa kika dawo gida yau da wuri, sannan mi ya sameki a wurin aikin na ku da har yasa kika dawo gida kina kuka, sannan miye haɗin ki da kabiru ɗan gidan minister mai wada daya kawo maki jakar ki sannan wannan kwalin na minene ??? " ya faɗa yana nuna mata jakarta da wani ƙaton kwali da ke gefan shi.
gabanta ne yayi wani mumunnan faɗuwa jikake daram, a zuciyar sai faɗin " mi ya kawo dr gidan nan sannan wannan kwalin na minene " katse mata tunani yayi ta hanyar cewa
"da ke nake magana kinyi man shiru "
"Abbah bana jin daɗi ne kaina na ciwo shine na dawo gida"
"to shi wannan kwalin na minene??, hidaya kin san dai bana wasa da ke ko? "
_lokacin da dr kabir ya zo ashe Abba na bayan shi harya bada jakar da kwalin, da ya tafi ne ya tambayi mai gadi kayan miye kabir ya bashi, a nan ya sanar dashi cewa hidaya yace a ba_
"Eh Abbah da gaske nake maka bana lafiya ne shine ya ɗauko man jakata wannan kayan kuma na maryam ne "
"Yau kika fara rashin lafiya ne da zaki kama kuka " shiru tayi
"idan kika bari na bincika na gano ta ƙamaimai abun da ke damunki baza kiji da daɗi ba "
" da gaske nake Abbah "
" shikenan ɗauki jakar ki da kwalin ki wuce"
da to ta amsa haɗi da ɗaukar jakarta da kwalin ta fice, da ummah taci karo zata shiga part ɗin Abbah , fuskarta a ɗaure babu alamun sassauci, fasa shiga tayi tace " biyo ni ina son magana dake " kawai ta faɗa, ajiye kwalin tayi a main parlor ta bi bayan ummah har bedroom ɗin ta, tsaye ta samu ummah a bakin gado, kallon ta ummah tayi tace.
" hidaya miye haɗin ki da kabir yaron mai wada?"
" ummah ba komai "
" kar kiyi man ƙarya hidaya, maryam ta sanar dani duk abun da ke faruwa"
"ummah maryam ƙarya take"
"ƙarya? , maryam ɗin ce zata yi maki ƙarya "
"A'a ummah"
"ki shiga hankalin ki dani hidaya kinji na faɗa maki "
"to ummah "
"tafi amma ba wai mun gama maganar bane kina jina ko "
"eh ummah " ta faɗa haɗi da kama hanya ta fice, da idanu ummah ta bita hara ta fice.
ɗaukar kwalin tayi da jakar ta ta wuce ɗakin ta, zaune ta samu maryam kamar yanda ta bar ta ɗazu, mai da ƙofar ɗakin tayi ta rufe, tana zuwa tsakiyar ɗakin tayi jifa da kwalin harda jakar ta, da sauri maryam ta kalleta tana faɗin
" ke kuma lafiya miya same ki ki ke jifa da kaya"
"Ki barni kawai maryam, wai ashe dr gidannan ya zo har Abba ya ganshi " wani wawan tsaki maryam ta ja tana faɗin
"aikin banza da wofi, shine zaki shigo kina wannan jifar da kaya, wai dan Allah miye laifin wanda yace yana sonka ne, kuma kema kin sani in ban da so na so ba wallahi bazai ce yana sonki ba dan kin fi kowa sanin shi ba sa'anki ba ne,kawai dan Allah ya jarabce shi da son ki shine zaki riƙa yi mashi wannan wulaƙan cin"
"maryam na lura bazaki taɓa fahimta ta ba "
"in dai akan wannan haukan da kike yi ne bazan taɓa fahitarki ba, kuma ki sani zan sanar da ummah duk abun da ke faruwa tsakanin ki da dr shazim kin dai san abun da zai biyo baya idan taji kin buɗe baki kince kina son wani ɗa namiji "
" maryam bana son irin wannan wasan, ke yanzu sai ki faɗa mata "
"kina wasa ne ki cigaba da wulaƙanta dr ki gani idan ban faɗa mata ba, ke har ma abun da bakiyi ba sai nace kinyi wallahi"
"komai zakice sai dai kice, amma maganar gaskiya bana jin son dr a zuciya ta "
"zaki ma koya ne malama, kwalin minene wannan da ki ka jefar " maryam ta faɗa yayin da take nufar kwalin da ke ƙasa yashe, ɗaukar shi tayi ta buɗe, wani kyakyawan teddy bear ne pink sai heart fari a gaban cikin shi an rubuta am sorry dear da baƙin fenti, kwashewa maryam tayi da dariya tana faɗin
" soyayya ruwan zuma, lallai dr " ta fa ɗa haɗi da sake buɗe kwalin ta fito da sauran kayan da ke ciki, sweet ne da uban chocolate masu ɗauke da sorry a jikin ledojin su, ba maryam ba har ita kanta hidayar sai data dara.
Episode 58_59_
"Amma fa dr na matuƙar son ki hidaya " maryam ta faɗa yayin da take buɗe wani chocolate ta kai baki, taɓe baki hidaya tayi
"ke ki kaga haka "
"wai ke haryanzu kina a kan bakanki na baki son shi "
Kwanciya tayi haɗi da juya mata baya batare da tace komai ba, binta da ido maryam tayi tana faɗin
"karki fasa zaki sha mamakin abun da zanyi maki kuwa "
"ke maryam kin daɗe ko mi za kiyi ana so dole ne "
"haka ki kace? "
"eh haka nace "
tashi maryam tayi zata fice, da sauri hidaya ta riƙota
"wai ke ƴanzu ko kunya bakiji sai kije ki faɗama ummah "
"sakar ni" maryam ɗin ta faɗa taba fisgewa daga riƙon da hidayar tayi mata ta nufi ƙofa, a sukwane hidayar ta rigata isa bakin ƙofar, abun ma dariya ya so ba maryam amma sai ta ɗaure fuska bata yi ba tace " ki matsa man a gabana "
"wallahi bazan matsaba tun da ke baki san wasa ba "
"wasa ko zakiga wasa " maryam ɗin ta faɗa tana ƙoƙarin janye hidaya
"dan Allah maryam kiyi haƙuri wasa fa nake "
"Ina ruwana da wasanki ni bani hanya na wuce " haka su kai ta jayayya har ummah tayi nocking ta hidaya sai roƙon maryam take akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, gajiya ummah tayi ta sake wani nocking ɗin tana faɗin
"wai lafiya kuke da baza ku buɗe man ba " da sauri hidaya tasa hannu ta buɗe tana yima maryam alama da da ido akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, ummah na shigowa kallon su tayi tana faɗin "ku lafiya naga duk kunyi wani tsaye cirko cirko " hidaya ce tayi carb tace
" ba komai ummah magana muke"
"maganar ce har sai kun zo bakin ƙofa? "
maryam tace " tafiya zanyi ne daman"
"tun yanzu zaki tafi maryam?, ga abinci can a dinning, ki bari sai kinci sai ki wuce gida "
" naci abinci ummah kafin na fito daga gida daman saboda naga ta dawo ne da wuri kuma ina kiranta bata ɗauka ba yasa nayi tunanin ko lafiya "
"to shikenan, ki gaishe da mamar ku "
"za taji insha Allah " jinjina kai ummah tayi haɗi da ficewa ta ba ɗakin
"shine zaki wani ce zaki tafi "
"idan ban tafi ba mizan yi maki ne, ko so kike na zauna ki cigaba da ɓata man rai "
"haba dan Allah wane irin ɓacin rai kuma "
"koma dai minene ni tafiya zanyi "
"Amma ai kin tsaya na baki wancan kayan "
"bana so" shine kawai abun da maryam ta faɗa ƙofar ta nufa ta buɗe bin bayan ta hidaya tayi tana bata haƙuri amma taƙi sauraronta,ba yanda ta iya haka maryam ta tafi ba tare da ta amshi chocolate ɗin ba ko ban kwannan arziƙi ba su yi ba, juyawa tayi ta koma ciki dinning ta nufa wurin ummah .
_*✨KATSINA✨*_
Abie ne da uncle Ahmad da uncle mustafa zaune a parlorn suna magana
Uncle mustafa ne yace
" yaya yanzu yaushe zaka tafi kenan"
Amsa Abie ya bashi da
"da wannan week ɗin nace amma yanzu ina jin sai wani week ɗin saboda safwan da za su zo gobe "
"to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen abie ya amsa,
uncle Ahmad ne yace
" wai yaya idan sun zo su safwan ɗin anan za su zauna?"
"eh mana Ahmad idan ba nan ba ina zasu zauna "
"a gaskiya yaya da zaka ji shawara ta da ba su zauna anan ba "
"saboda mi? "
"yaya bawan Allah rayuwar shi tana cikin hatsari, sai nake ganin zaman shi a nan kamar akwai gangance "
"Ahmad bawani gangance nasan da lilin da yasa nace ya zauna nan "
"to shikenan yaya,bawani abu Allah ya bashi lafiya "
"Ameen shi ne kawai, yaushe zaka koma Abuja ne " abie ya tambaya
"tunani nake ranar friday zan tafi "
"ok Allah ya kaimu, wai addimisson ɗin su Aaimah shiru "
Uncle Ahmad yace
"Inajin fa basu fara ba dawa ba kuma kaga late aka nemar masu addimisson ɗin Amma na san bazai wuce wannan week ɗin ba tun da makarantar next month su ke fara lectures "
"to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen su ka amsa su duka, dadi ce ta fito ta zo wurin su ta zauna kan sofa gaishe da ita su kayi, amsa wa tayi da kulawa a fuskar sannan tace
" mi ake tattaunawa ne tun ɗazu? "
uncle Ahmad ne yace " magana muke ta yanda zamu nemo maki yaron ki "
"mai makon naji kunce kun nemo shi sai kuce magana ku ke ta yanda zaku nemo shi, na lura so kuke mu sa ƙafar wando ɗaya da ku kafin ku nemo shi "
Abie ne yace
"ba sai an kai ga haka ba"
"to yauahe zaku kawo man shi gidannan? "
"in sha Allahu nan bada jimawaba, da wannan satin zan tafi kadunar to amma saboda zuwan su safwan yasa na fasa sai wani satin"
"Allah sarki gobe ne kenan zasu zo, to Allah ya kawo su lafiya "
"Ameen " su ka amsa su duka, fira suka shiga yi cikin nisha ɗin har sai da lokacin sallar zuhur yayi sannan suka nufi masallaci dadi kuma ta nufi ɗakin ta.
_*✨SHAZIM✨*_
Lokacin da hidaya ta fita daga office ɗin shi bai wani jima ba shima ya nufi Abnoor
Aiki yayi sosai sai daga baya yanufi office ɗin majeed,bai same shi a ciki ba hakan yasa yayi tunanin ko yana duba patient ne zama yayi kan sofa yana jiran ya dawo, wayar shi dake ringing ya jawo duba mai kiran yayi, Mansoor ne, picking kiran yayi sallama yayi, amsawa mansoor ɗin yayi yana faɗin
"kai dai babu ruwanka da neman mutane, idan mutum bai nemeka ba shikenan kai ba ruwan ka da shi "
ɗan yatsine fuska yayi yace
"kai ai na lura neman mutanen kake yi "
"gashi kuwa na neme ka "
"to naji, yaushe ne ma kace zaka zo "
"ok ka ma manta yaushe nace zan zo, nalura kamar baka son zuwana saboda zan zo na ɗauke maka habibtyn ka "
"wait mansoor idan ba so kake nayi maka rashin mutunci ba to ka daina haɗa ni da wannan sakaryar yarinyar"
"lallaima shazim sakaryar kace?"
"ƙwarai kuwa ba sakayar bace, ni da zaka taimaka wallahi da zuwa kayi yau ka tattarata ka mai da ma iyayenta ita dan nagaji da zama da muke yi a gida ɗaya "
"Amma nayi mamaki shazim ko da ace yau baka san taba ai baka faɗi haka ba, bare ma tana ƴar uwar ka "
"ni dai da zaka taimaka da kazo gobe ka tafi da ita "
"bazan zo ba ɗan rainin wayau, idan da gaske ne ka gaji da zama da ita ka dawo da ita da kan ka"
"bana da wannan lokacin kuma "
"to nima bana da shi "
"Alright haka kace "
"Kwarai ma kuwa " yana faɗar haka yayi rejecting kiran, murmushi gefan baki yayi haɗi da cire wayar daga kunnan shi, kwanciya yayi kan sofar latsar wayar shi ya shiga yi, anan majeed ya shigo ya same shi, zama yayi yana faɗin
" yaushe ka shigo?"
hannu ya miƙa mashi su kayi musabaha
" tun ɗan ɗazu na shigo "
"Ok naje duba patient ne, lafiya dai ko"
" lafiya, maganar waɗan nan kayance nake so muyi "
" ok , wanda ke hannun mu ko wanda kace a tura "
" eh wanda nace ku aika "
"anyi kamar yanda kace"
"yawwa nagode sosai "
"Amma shazim baka gani gara mu miƙa kayan nan hannun ƙungiyar drugs Abuse"
"a'a majeed, idan mu kayi haka kamar mun ba masu kayan kayan su ne, kasan yanda cin hanci yayi yawa a ƙasar nan muna bada kayan nan masu su za su fito ne su bada cin hanci su amshi kayan su "
"haka ne, amma to idan mun bar su nan mi za muyi da su"
"ba abun da za muyi da su, kawai ina son yin amfani da su ne wajen gane mai kayan daga nan sai na ɗauki matakin da ya dace akan shi "
"to shikenan, amma a canza masu wurin zama daga store "
"ka jika da wata magana, idan ba nan ba ina zamu kai su, a nan zamu bar su har Allah ya toni asirin masu su"
"shikenan " majeed ya faɗa canza firar su kayi zuwa wata, ana kiran sallar asr su ka fita su ka nufi masallaci, da suka gama sallah majeed office ɗin shi ya koma shazim kuma yace mashi briefcase ɗin shi kawai zai ɗauka gida yake son ya koma saboda fatima, sallama su kayi majeed na faɗin yana gaishe da fatimar.
Yana shiga office ɗin kamar yanda yace briefcase ɗin kawai ya ɗauka ya rufe office ɗin, motar shi da yayi parking a parking lot ya nufa, shiga yayi yayi mata key haɗin da yin reverse ya nufi gate , mai gadi na ganin shi da sauri ya tashi ya buɗe mashi gate ɗin , yana ɗaga mashi hannu har ya bar hopital ɗin.
yana fita wata ɓakar jeep ta fito daga bayan Abnoor, ta mirror ya hange ta abun yaso ya bashi mamaki saboda ya san bawani titi ko wani gida da mota zata iya fitowa daga wurin, tuƙi yake yana kallon motar da farko yayi tunanin hanya ce ta biyo da ita may be ko matsala ta samu ne yasa ta tsaya a bayan Abnoor ɗin, sai da yaga ya bar titin abnoor ɗin ya hau wanda zai kai shi gida yaga motar tana nan tana binshi, tafiya ya fariyi a slowly abun mamaki sai kawai yaga mai motar yayi parking,murmushi ne ya so kufce mashi dan abun yayi matuƙar bashi mamaki, key yayi ma motar ya cigaba da tafiya, shima mai jeep ɗin key yayi mata ganin haka ne yasa shi yin kwana ya sauka daga titin da zai kaishi gida, shima mai motar canza hanya yayi zuwa wacce shazim ɗin ya bi, yanke shawara kawai shazim yayi daya tsaya ya ga ko waye ke binsa a baya, gangarawa yayi bakin hanya yayi parking kashe motar yayi ta zare key ɗin motar ya fito, mai motar na ganin ya fito da sauri yayi reverse ya a wani irin masifan gudu ya shiga wata kwana, jinjina kai yayi yana faɗin "ƙaramin ɗan iska ai da ka tsaya sai naji dalilin bin nawa da kake " komawa yayi cikin motar ya kama hanyar gidan malam, yana isowa horn yayi mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga , parking yayi sannan ya fito ya shiga ciki, parlorn ummy ya fara zuwa zaune ya sameta ita da mai aikinta tana ɗan daddana mata ƙafa saboda fama takeyi da su kwana biyu, ƙarasawa yayi ciki bakin shi ɗauke da sallama
Amsa sallamar da yayi ummy tayi tana faɗin " lale marhabun