Showing 36001 words to 39000 words out of 127932 words

Chapter 13 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

7911

mu goben zamu tafi in sha Allah" ammy tace "da ma dai ya fiye maku " ta faɗa haɗi da tashi ta nufi bedroom ɗin ta,  da idanu kawai suka bita, sai da su kaga shigewar ta ɗaki sannan su ka kalli juna noraiz ya ce "nifa gani nake kamar akwai abun da ke damun ammy, yan da tayi fushi akan tafiyar nan abun yayi yawa, kawai dai tana ɓoye mana ne, amma alamu suna nu na cewa tana cikin damuwa yan kwana kinnan, kuma nasan hakan da sa hannun innah" ɗan nisawa fatima tayi tana cewa "na daɗe da lura da hakan ya noor, kuma na tambayeta ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba tana ce man wai ba komi, abun da kawai ya ka mata shine mu shirya kawai gobe mu tafi, may be zata huce dan naga tayi fushi sosai"
"haka ne fatima, amma kinsan yaya baya son tafiyar nan"
fatima ta ce "amma dole yayi ta ya noor tun da ammy ta nuna ɓacin ranta, na san ko dan haka dole ya tafi " noraiz ya ce" haka ne dan bansan mi ya haɗa su ba naga tana fushi da shi kuma daga part ɗin sa ta ke "
"ina tunanin tayi mashi maganar tafiyar ne ya nuna bazai je ba "
noraiz ya ce "to ƙila, nima yanzu tashi zanyi naje na shiraya kayana, dan wallahi  nasan ta waiwaye  mu baza mu ji da daɗi ba yanda tayi fushin nan"
"dama ni ya noor tun da tayi magana nashirya kayan ganin ba'a yi tafiyar ba ne yasa na saka wasu daga cikin kayan da zani walimar school ɗin mu"
"ke daman murna kike da wannan tafiyar"
murmushi fatima tayi tana faɗin"ina son zuwa naga sa'ada da Aunty kairiyya ne kawai"
noraiz ya ce
"za kuma ki haɗu da innah guyaba ba" dariya fatima ta kwashe da ita, tashi yayi yana faɗin "bari  nima na tashi  yanzu na kammala shirya nawa kayan tun da ba inda zani" ya faɗa hadi da tashi ya nufi part ɗin su, tashi ita ma fatima tayi ta nufi nata bedroom ɗin....

   ✨SHAZIM✨

Zaune yake a office ɗin shi ya barbaza takardu kan table ɗin shi,zuba masu ido kawai yayi yana kallon da alama hankalin shi baya kansu, yayi zurfi cikin tunani ya ji ana nocking, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bada izinin shigowa, hidaya ce ta shigo hannun ta ɗauke da files, gaishe da shi tayi hannu kawai ya ɗaga mata, ganin hakan ne yasa hidaya fahimtar yau baya san magana, dan haka kawai ta matsa kusa da table ɗin ta ajiye mashi files, ɗago da kanshi yayi yana kallonta, fahimtar mi ya ke nufi ne yasa ta cewa "dama files ɗin patient ne dake waje" sai yanzu ya buɗe baki ya ce "kwashe su ki kaima dr kabir, bazan samu damar duba kowane patient ba  yau" daga yanayin yanda yake maganar zaka san cewa baya jin daɗin
"dr baka jin daɗin ne" hidaya ta tambaye shi, kai kawai ya ɗaga mata,ɗaukar files ɗin tayi ta fice, direct office ɗin dr kabir ta nufa, nocking tayi aka bata izinin shiga, shiga tayi bakinta ɗauke da sallama, zaune ta same shi yana aiki a laptop "good morning sir" hidaya ta faɗa, ɗago da kansa yayi yana amsa mata gaisuwar da tayi yana kallon files ɗin dake hannun ta "lafiya dai koh hidaya, ina zaki da wannan files ɗin?" amsa ta bashi da "dr Shazim ne yace na kawo maka, bazai samu damar duba patient ba yau"
"ok ajiye" ya faɗa yana maida kansa kan aikin da yake yi, hidaya tana ajiyewa ta fice daga office ɗin, saida ya gama aikin da yake yi sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, ya nufi office ɗin Shazim, shiga kawai yayi batare da yayi nocking ba, samun shi yayi zaune kan sofa dake office ɗin dafe da kanshi, jin alamar an buɗe ƙofa ne ya sa shi ɗago da kanshi yana kallon dr kabir da ya shigo, amsa mashi sallamar da yayi yayi, ƙarasawa dr kabir yayi haɗi da ne man wurin zama ya zauna kusa da shazim yana faɗin "hi dude, what's wrong with you, naga kasa nurse hidaya ta kai man file ɗin patient,lafiya dai ko" kallon shi Shazim yayi sannan ya ce "i'm not feeling better"
"ya salam,mike damun ka?" ɗan nisawa shazim yayi sannan ya ce "wallahi ammy ce wai dole sai na tafi abuja,  da na kawo mata excuse fushi ma tayi dani" kabir ya ce " to minene aciki da har zaka sama kanka damuwa irin haka, shawarar da zan baka anan kawai kashirya ka tafi, hakan ka ɗai zai sa ammy ta huce"
"baza ka gane ba kabir, kwata kwata bana son zuwa abujar nan"
"to ya za kayi haka nan zaka yi haƙuri ka tafi tun da ammy ta ce katafi,yaushe ne tace ka tafi"
"gobe fa" kabir ya ce "to Allah ya kaimu gobe, kai ka ɗai zaka tafi"
"a'a harda su noraiz"
"ok, Allah ya kaimu goben,  karka wani damu" shazim ya ce "ameen nagode"
"bakomai kar ka damu"
"ina ma tunanin tashi zanyi na tafi abnoor dan ban gaya ma majeed ba, sannan zan koma gida daga can"
Kabir ya ce "eh gaskiya ya kamata, da ƙarfe nawa zaku tafi ko dai sai munyi waya"
"ina tunanin da safe, dan wallahi ammy tayi fushi sosai"
"to Allah ya kaimu"
"ameen" Shazim ya faɗa hadi da tashi ya nufi table ɗin sa ya fara haɗa kayan shi yana maidawa cikin briefcase, yana gama haɗa kayan kabir ya taso domin yi mashi rakiya, su hiday na zaune a reception su ka zo suka wuce, suna wuce maryam tace "lafiya naga dr ya tashi lokacin tashin shi bai yiba" hidaya ta ce "baya jin daɗi ne, dan koda na kai masa files ɗin patient cewa yayi na kaima dr kabir, ina tuna nin ba zai iya zama ba shiyyasa zai tafi gida"
"Allah ya bashi lafiya" maryam ta faɗa da ameen hidaya ta amsa,can maryam tace"kinsan wane tuna nin nayi?" hidaya ta ce "a'a sai kin faɗa"
"kawo kunnan ki ki ji" matsawa hidaya tayi kusa da maryam, magana ta faɗa mata, sauran nurses ɗin dake wurin su ka ce "dan muna kusa shine abun harada su raɗa ko maryam" murmushi maryam tayi sannan ta ce "komai fa na son sirri, wannan magana ce tsaka ni na da ita" wata acikin nurses ɗin ce ta ce "in tayi wari maji" ƴar dariya maryam tayi haɗi da cewa "bama zata yi ba "

har parking lot dr kabir ya raka shi,  saida dr kabir yaga tafiyar Shazim tukun ya koma cikin hospital ɗin, ya zo zai shiga office ɗin shi yaji maganr hidaya tana cewa"doctor " juyowa yayi yana kallonta sannan ya ce "na'am " duƙar da kanta tayi ganin ya kafe ta da idanu "lafiya dai koh hidaya,?   kin tsayar dani kin kuma yi shiru" magana ta fara yi ba tare da ta ɗago da kanta ba "dama dr tambayar ka zanyi mike damun dr ne?" kallon ta kawai dr kabir ke yi, sannan ya ce "baya faɗa maki baya jin daɗi ba"
"eh haka ne"
"to baya jin daɗi ne, gida ma ya tafi yanzu"
"ok, am dan Allah ko zaka bani number shi na kira shi nayi mashi ya jiki" magana take still kanta na ƙasa,  wani kalar kallo dr kabir ya shiga binta da shi, ita kuma jin baice komai ba yasa ta ɗago da kanta, tana ɗago wa idanun ta suka sauka cikin nashi daya kafe ta dasu, kusan 5 seconds bai ce komai ba, can ya ɗan nisa sannan ya ce "dama baki da number shi" girgiza mashi kanta tayi alamar eh, "ok shikenan ina wayar ki na sa maki number" hannu ta sa cikin aljihun rigar uniform ɗin ta ta ciro wayar ta ta miƙa masa,  amsa yayi ya sa mata number, miƙa mata wayar yayi tasa hannu ta karɓa tana faɗin "nagode" kallonta kawai yayi ba tare da ya ce  mata komai ba harta juya ta bar waje bai daina kallonta ba, sai da ya ga ta ɓace ma ganin sa tukun ya murɗa handle ɗin ƙofar office ɗin shi ya shiga.....

✨ Shazim ✨

yana barin eko direct abnoor ya nufa, yana parking ya fito ya nufi main entrance ɗin hopital ɗin ba tare da ya ɗauki briefcase  ɗin sa ba, yana shiga direct office ɗin dr majeed ya nufa
nocking yayi, daga ciki aka bashi izinin shiga, kama handle ɗin ƙofar yayi ya tura ya shiga, bakin sa ɗauke da sallama, zaune dr majeed yake yana duba files dake gaban shi, amsa mashi sallamar yayi, wuri shazim ya samu ya zauna, hannu ya miƙama dr majeed suka yi musabaha
"lafiya kuwa yau naganka a wannan lokacin?"
"lafiya lau majeed, maganar tafiya abuja nan ce ta taso, ammy tayi fushi dole sai mun tafi gobe" majeed ya ce "to fah, kwana nawa zaka yi"
"kai dai bari kawai wai sai nayi sati biyu  inji ammy"
majeed ya ce "shiyyasa fa tun time ɗin da kace tace ku tafi nace maka ka tafi kawai ni zan kula da komai, amma ka ƙi,yanzu ga irinta nan ta soke kwana biyar ɗin da tace"
"baza ka gane ba ne kawai majeed, wallahi bana son zuwa ko nan da can shiyyasa "
"to ya zaka yi zumunci ne dole ayi shi"
"haka ne"
"yanzun goben da ƙarfe nawa zaku tafi? "
"da safe" shazim ya bashi amsa "ok Allah ya kaimu" da ameen ya amsa,sun ɗan jima suna magana akan magunguna da allurai da zasu yi order, sai da shazim yayi sallamar asr bayan yaba ma majeed duk abun da zai bashi, sannan suka yi sallama ya nufi gida, tsit ya iske parlor alamar ba kowa, hakan yasa shi nufar bedroom ɗin ammy nan ma ba kowa, fita yayi ya nufi up stairs part ɗin noraiz ya shiga, samun shi yayi a parlor zaune kan sofa yana kallo cikin laptop, ɗagowa noraiz yayi jin anbuɗe ƙofa , yana ganin shazim ya miƙe yana faɗin "sannu da dawowa yaya" da yawwa shazim ya amsa yana cewa "ina ammy? , naga kamar bata gida kuma banga motarta a parking lot ba, nama yi tunanin ko kai ka fita da motar"
"tun da ka fita ta fita ko breakfast bata yi ba, na tambaye ta ina zata, sai cewa tayi yanzu zata dawo, amma haryan zu bata dawo ba" jinjina kai kawai shazim yayi haɗi da ficewa ya nufi part ɗin sa, yana shiga parlorn shi wayar shi dake cikin aljihun wandon shi ya ciro number ammy ya shiga kira, tana ringing amma ba'ayi picking ba harta katse ya sake kira sai da yayi mata 3 missed call amma bata ɗauka ba, fita yayi ya koma part ɗin noraiz, yana shiga yace "noraiz ina wayar ka?"
"gata nan yaya" noraiz ya bashi amsa "kira number ammy" da ok noraiz ya amsa, nan shima ya shiga kiran wayar amma ba'ayi picking ba, ƙofar parlorn su ka ji an buɗe fatima ce ta shigo da waya a hannun ta "yaya na shiga ɗakin ammy naji wayar ta na ringing, sai da na duba naga ashe kai ke kira" shazim bai ce komai ba ya fice daga part ya koma nashi, number malam yayi dialing, picking malam yayi haɗi da Sallama yana faɗin "likita bokan turai"
"ina wuni malam"
"lafiya lau, ya aiki"
"Alhmdllh "
"to masha Allah "
ɗan shiru Shazim yayi, jin yayi shiru ya sa malam ce wa "lafiya dai koh shazim? "
"lafiya lau malam, dama ammy ce" sai kuma yayi shiru,  malam "yace miya samu Aishar?"
"bakomai malam, tayi man magana ne akan zuwa abuja to nace mata ina da uziri wirin aiki, to sai bata sake maganar ba tun daga ranar, yau kawai " nan ya shiga  bashi labarin yan da suka yi da ammy yau , har fushin da tayi da kuma dawowa da yayi yanzu bata gida da kuma kiranta daya ke bata ɗauka, ɗan nisawa malam yayi sannan ya ce "ta faɗa man  komi da ya faru, gaskiya banji daɗi ba, baka kyau ta ba, shi zumunci Allah ne yace ayi sa, kuma komi ya faru tsakanin ka da su ai kai ne baka kyauta ba" sosai malam yayi mashi faɗa da nasiha, akan bai kyauta ba daya bari har sai da ran ammy ya ɓaci "ayi haƙuri malam in sha Allah hakan bazata sake faruwa "
"shikenan Allah ya kyauta gaba" da ameen malam ya amsa, sannan shazim ya ce "to malam ammy tana nan ne"
"eh tana nan" ajiyar zuciya shazim ya sauke, sannan suka yi sallama da malam, bedroom ɗin shi ya wuce, jefar da wayar shi yayi kan gado, kayan jikin shi ya cire daga shi sai boxer yanufi bathroom, kusan 15 minutes ya fito ƙugun shi ɗaure da towel, shiryawa  yayi ciki ash ɗin jallabiya wuri ya samu kan sofa ya zauna, laptop ɗinshi ya jawo yashiga dan dannawa....

ammy bata dawo gidan sai da yamma liƙis, ta shigo, gaishe da ita fatima da noraiz dake parlor zaune suka yi, amsa masu tayi tana samu wuri ta zauna kan sofa, hijab ɗin ta ta cire ta miƙa ma fatima tan cewa "kai man ɗaki" da to fatima ta amsa ta tashi ta kaima mata, tana fitowa ammy ta ce "ina innah asabe?" amsa ta ba ammy da "tana ɗakin ta"
"ok "
Noraiz ya ce "ammy wai ina ki ka je ne, yaya ya dawo tun ɗazu yana ta ne manki " fuska a ɗaure amma ta ce
"in da ya aike ni can na tafi"
noraiz ya ce "dan Allah ammy kiyi haƙuri ki dai na wannan fushin,goben zamu tafi kamar yanda kika ce"
"karma ku tafi" ammy ta ce, magana noraiz zai yi, ta ɗaga mashi hannu tana ce "ya isa haka kar ka takura man daga dawuwa ta" jin haka yasa dole noraiz ya kama baikin sa yayi shiru, saukowa shazim ya ke daga up stairs  ya nufo parlorn, hango ammy da yayi, yana isowa parlorn ammy ta miƙe ta nufi ɗakin ta, tsayawa yayi chak ganin tana ganin shi ta tashi, binta yayi har ɗakin, yana shiga ya ganta tsaye bakin dressing mirror, ta cikin mirror ta hange shi, yi tayi kamar ma bata san da shigowar sa ba, ƙarasowa yayi har gaban dressing mirror ɗin yana faɗin "ina wuni ammy" amsa mashi tayi  da  "lafiya " daga nan ta ɗauke kanta ta koma bakin gado ta zauna, binta yayi har bakin gadon, durƙusawa yayi yana dafa gwiwar ta, haƙuri ya shiga bata, da ƙyar ta haƙura, ganin ta haƙura yasa cewa "dan Allah ki rage satin da ki kace zanyi zuwa kwana biyar "
"idan har kana son zaman lafiya da ni to kawai kayi shiru,kayi abunda na ce" da to kawai ya amsa mata, sannan ya fice daga ɗakin ya koma part ɗin shi domin yin alawala saboda lokacin sallah da yayi,yana fita ita ma ammy tashi tayi ta nufi toilet domin alawa,  yana ko mawa   part ɗin shi  alawala kawai yayi ya fito suka wuce masallaci da noraiz dake parlor yana jiran shi yana saukowa suka wuce, anagama sallah suka wuce gidan malam  basu bane suka dawo gidan ba sai wurin ƙarfe 10 sannan suka dawo, koda suka dawo ammy da fatima har sunyi bacci, suma part ɗin su suka wuce kowa ya nemi makwancin shi..
Episode 20 _21

Washe gari...

Iliya ne ke  saka trolleys ɗin su fatima a booth ɗin  mota da zai kaisu airport,
ammy da fatima da noraiz sai Shazim zaune suke kan sofa a main parlor, ammy nayi masu nasiha sai da ta gama faɗa masu duk abun da zata faɗa masu sannan suka tashi suka kama hanyar fita daga parlorn, fatima da noraiz harsun fice ammy ta tsaida shazim, tana faɗin "dan Allah shazim kar naji kar na gani dan Allah, kayi haƙuri da komi zaka gani har Allah yayi maku dawowa "
"to ammy in sha Allah" fitowa su ka yi ammy ta raka su har parking lot su ka shiga mota, tana masu Allah ya tsare hanya da ameen suka amsa mata, sannan ilya yaja motar su ka fice daga gidan ammy na ɗaga masu hannu, saida taga mai gadi ya rufe gate sannan ta juya ta koma ciki,  cike da kewarsu yanzu sai ita kaɗai cikin gidan, fatan Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya.
suna fita daga gidan direct gidan malam su ka wuce dan suyi mashi ban kwana, sosai malam yayi masu nasiha da  fatan isa lafiya, suna fita ilya ya kama hanyar airport,ko da ya kaisu sai da ya jira har jirgin su ya tashi sannan ya dawo gida...

✨Abuja✨

Airport, passengers ne su ka fara fitowa ta ƙofar da aka rubuta exist wacce aka tana da domin passenger, su shazim ne suka ɓullo ta wannan ƙofar yana gaba fatima da noraiz na biye da shi abaya da trollys ɗinsu a hannu, wata kyakyawar matashiya ce wacce zasu yi sa'anni da fatima, fara ce sai dai ba ta kai fatima haske ba,   da gudu ta nufo fatima tayi hugging ɗinta tana faɗin "oyoyo sister" fatima da fara'a a fuskar ta tace "ya ki ke sa'ada?" wacce aka kira da sa'ada, tayi murmushi tana faɗin "lafiya lau ya hanya" sannan ta juyo tana cewa" ya "Shazim ina wuni" amsa mata yayi da "lafiya lau" sannan ta juya tana gaishe da noraiz, da fara'a a fuskar shi yace "ai nayi tunani fatima ka ɗai ki ka gani" da murmushi a fuskarta tace "a'a ya noraiz kuma ai na gan ku" suna a nan tsaye wasu ƴan mata  kyawawa su biyu su ka iso fararene sai dai ɗaya tafi ɗaya haske, mai hasken sosai tana kama da  sa'ada sai dai ita daka ganta zaka san tana ƙarawa dana kanti,jikinsu sanye da ɓakar jallabiya sunyi rolling da gyelen jallabiyar,  wurin su su ka nufo,  mai kama da sa'ada  cike da yanga take  faɗin "hi ya shazim" haɗi da nufar Shazim da nufin tayi hugging ɗin shi, kasa ƙarasawa tayi ganin wani mumunnan kallo daya bita da shi fuskar shi a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, kwal kwal tayi da ido kwalla na taruwa ciki tace " haba ya shazim miyasa ka ke haka,daga na  nuna farin cikin ganinka"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login