Showing 114001 words to 117000 words out of 127932 words

Chapter 39 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6725

ta nufa , ganin shirin ɗauko key take ta kai feenah da kanta yasa noraiz bin bayan ta yana faɗin
"dan Allah kiyi haƙuri zan kaita da kai na "  ko kallon shi bata yi ba ta shige bedroom ɗin , wardrobe ɗin ta ta nufa buɗewa tayi ta ɗauko hijab sannan ta koma wurin dressing mirror ɗinta locker dake jiki ta jawo key ɗin motar ta dake ciki ta ɗauka,
"Pls Ammy wallahi zan kai ta " roƙonta ya shiga yi sai da ƙyar ya samu ta bashi key ɗin , tana bashi ya fita a tsaye ya samu su fatima riƙe da feenahr sai ruri take tana kuka yan ƙarasowa wurin su yace
"Allah ko kiyi mana shiru ko wallahi na koma, ƴar rainin wayau kawai wani ya aike ki ɗakin shi da zaki ta wani cika ma mutane kunne " ya faɗa haɗi da nufar motar Ammy da ke parking lot, da harara feenah ta raka shi duk buguwar da tayi bai hanata rashin kunya ba, fito da motar yayi zuwa compound in da su ke tsaye sa'ada ce ta nufi motar ta buɗe ƙofar baya su Kairiyya su ka shigar da ita, kairiyya ce ta zauna a baya tare da feenah fatima kuma ta shiga gaba, sa'ada ta koma ciki dan ɗauko masu hijaban su saboda duk cikin su babu mai hijab sai fatima ita ma gama sallar ta kenan taji ihun feenah,bayan kamar 1 minutes sa'ada ta fito hannunta riƙe da hijab ɗin kairiyya da ta feenah,miƙa masu tayi su ka amsa sannan ta koma ɓangaren da feenah take ta shiga, zama tayi suka sa feenah a tsakiya ita kairiyya, reverse noraiz yayi ya nufi gate da tun fitowar shi ya sa mai gadi ya buɗe masu, ficewa yayi daga gidan hanyar Abnoor ya ɗauka idan su ka zo in da za su sha kwana da mugunta yake shan kwanar dan duk ya sha kwana sai fennah ta saki ƙara, sa'ada dariya kawai take kwasa a zuciyar ta tana faɗin

"Allah ya ƙara maganin mai shishigi kenan, mutum yace baya so to ina dalilin maƙale mashi, in dai ya shazim yanzu kika fara gani "
haka tai ta ma feenah dariya da Allah ya ƙara har su ka iso Abnoor, horn noraiz yayi mai gadi ya buɗe mashi ya shiga da motar ciki,parking yayi yana gama daidaita parking yace su sa'ada su kamata su shiga ciki, fitowa su kayi har da fatima su ka kamata sai ɗangesa ƙafa take har su ka shiga ciki yayin da shi kuma yake bayan su, sun shiga nurses ɗin dake night su ka amshe ta,noraiz ne yaje office ɗin majeed ya sanar da shi abun da ke faruwa da yake yau bai tashi da wuri ba,
"Ya salam " majeed ya furta haɗi da cewa " shazim baya gida ne?"
" yana nan baya jin daɗi ne shiyyasa bai duba ta ba"
"amma wane irin rashin jin daɗi ne wannan da har zai hana shi duba patient " abun da yasa majeed ke faɗin haka noraiz ce mashi yayi faɗowa tayi daga bene koma yana zargin ta karye shiyyasa duk hankalin majeed ya tashi.
"muje na ga jikin nata" majeed ya faɗa yayin da yake tashi daga kan kujerar da yake, fice wa yayi noraiz ya
biyo bayan shi har inda feenah take sai uban kuka take kamar yarinyar goye, nurses ɗin da ke wurin kamar su maketa haka su ke ji abunda kawai yasa su kayi shiru su ka ƙyaleta tana cika masu kunne saboda kawai sun ganta tare da masu asibiti amma da ta sha masifa
majeed na ƙarasowa tambayar ta ya shiga yi mike damun ta ina da ina ne ta bugu , bata bashi amsa ba sai sake ɓare baki da tayi tana wani kukan , noraiz ne yace
"dallah malama an magana, idan kuma ba inda ke maki ciwo mu tashi mu koma gida "
"da kata noraiz saboda mi zaka yi mata ihu bakaga sai kuka take ba dole akwai inda ke mata ciwo kuma ka ce faɗowa tayi daga bene ba "

"haka ne faɗowa tayi " ya faɗa fuska a ɗaure shi a dole gaskiya ya faɗa, jin abun da yace ma majeed ne yasa feenah buɗe baki tace

"wurgi ya shazim yayi da ni har na faɗa kan table hannuna ya bugu da ƙuguna amma ba faɗuwa nayi ba "
norai a ranshi yace " shashasha ana so a rufa mata asiri amma da yake bata san ciwan kanta ba, take tona ma kanta asiri sai kace wani abun arziƙi ne dan ta sanar da ya majeed ya shazim ne ya ji mata ciwan"

tsaki yaja  sannan a zahiri  yace " ka rabu da ita kawai ya majeed ka duba ta ka gani ko ta samu karaya a ƙugunta dare yayi " ihu feenah ta sa jin noraiz na faɗin ko ta samu karaya, abun ma har so yayi ba majeed dariya, in ba sharri irin na noraiz ba yaushe daga wannan faɗuwar zata karye kuma a ƙugu

"ya isa haka dan Allah noraiz " nurses ɗin dake wurin yasa su ka kamata zuwa emergency room,cikin ƙanƙanin lokaci majeed ya shiga dubata daya kama hannunta sai ta fashe da kuka,hakan yasa ya gane cewa ta samu targaɗe ne a hannun,wurin gayran targaɗen sai da ta so ta tara mashi mutane, da dai ya gaji tsawa ya daka mata yana faɗin wallahi ko dai tayi shiru ko kuma ya ƙyaleta da ciwan,  nurses ɗin dake ciki suna taimaka mashi tsaki kawai su ka ja duk ta ba su haushi sai kace ba mace ba wata cewa tayi
" zanga ranar da ki ka zo haihuwa,ƙila ranar mutuwa zaki dinga yi kina dawowa"
"ai kam dai" harara kawai feenah ta maka ma su
"yo ashe abun iskanci ne tun da har kina da idon hararar  mutane "

"ya isa haka " majeed ya faɗa

Sai da ƙyar ya samu feenah ta tsaya ya gyara mata targaɗen sannan yayi mata allura,magunguna ya ɗauko mata a pharmacy  wanda zata sha  har da wanda zata shafa a fuskar ta da hannun ta  da na ɗigawa a ido saboda jinin daya kwanta mata  sannan ya sallame ta,

fitowa tayi sai ɗangesa ƙafa take hannu ya sha uban ɗauri, duk sai ta ba su fatima  tausayi idan ka cire sa'ada da noraiz dan su ko kaɗan ba su ji tausayin ta ba, sai ma Allah ya ƙara da su ke mata suna faɗin gobe ma idan halinta ne ta sake komawa part ɗin shi.

Godiya noraiz yayi ma majeed sannan suka nufi hanyar fita, tsaida fatima majeed yayi yana tambayar ta ya ƙarfin jiki da bata haƙuri na rashin zuwa kwana biyu da bai yiba ya duba ta
"babu komai ai ya majeed naji sauƙi sosai "
"to shikenan Allah ya ƙara sauƙi, amma duk da haka zan zo har gida na sake duba ki "
"to shikenan ya majeed sai na ganka "
"ok in sha Allah " ya faɗa
har in  da noraiz yayi parking su ka yayi mata rakiya lokacin da su ka iso har su Kairiyya sun shiga cikin motar ita kawai suke jira, sallama tayi ma majeed sannan ta shiga ciki, tsaye yayi har sai da ya ga ficewar su sannan ya koma ciki ya haɗa kayan shi ya bar asibitin.
Lokacin da suka iso gida tuni baccin wahala ya ɗauke feenah sai da kairiyya ta tashe ta tukun ta san sun iso gida, fitowa su kayi su ka shiga ciki a parlor su ka samu Ammy tana jiran dawowar su, wurin ta su ka ƙaraso,

"ya jikin feenah?" Ammy ta tambaye ta, amsa ta bata da
" da sauƙi Ammy "
"Allah ya ƙara sauƙi, ki tafi ɗaki ki kwanta " da to ta amsa haɗi da nufar ɗakin da suke kwana ita da kairiyya kusa da ɗakin fatima.
"noraiz mi majeed yace ya samu hannunta na ganshi a ɗaure?" Ammy ta tambaye shi
"targaɗe ne wai ashe,  dan ni har nayi tunanin karyewa tayi jin yanda take neman fasa ma mutane kunnne"
"ban san shashancin banza noraiz"
"to Ammy ga key ɗin ki nan sai da safe" ya faɗa haɗi da miƙama Ammy key ɗin motar ta ya nufi sama zuwa bedroom ɗin shi Ammy ma cewa tayi suma su fatima su wuce suje su kwanta dare yayi da to su ka amsa mata haɗi da wucewa ɗakunan su, kairiyya ɗakin su ita da feenah ta nufa da ledar magungunan feenah,tura ƙofar ɗakin tayi ta shiga ciki.
Masha Allah ɗakin ya haɗu sosai family bed ne acikin sa mai girma wanda mutum huɗu za su iya kwanciya ba tare da sun takura ba, dan gadon duk yafi na ɗakunan su Ammy girma da faɗi.
Zaune ta samu feenah kan gado sai zuba uban kuka take tsaki kairiyya taja dan   tun abun bai bata  haushi har abun ya fara bata haushi, ciki ta ƙarasa kan  dressing mirror ta ajiye ledar magungunan feenah ta nufi toilet, alwala ta ɗauro ta zo ta gabatar da sallar shafa'i da wutri da ta saba yi duk daren duniya, har ta kammala sallar ta canza kayanta zuwa na bacci feenah bata bar kuka ba,da abun ya ishe ta cewa tayi

"wannan kukan da kike yi ki sani bawani amfani da zai yi maki ba, dama kinyi shiru kin kwanata dan zai fiye maki, komai ma ya sameki feenah laifin ki ne kin san halin ya shazim sarai ba sai an baki labarin shi ba,tunda kika ga baya ra'ayin ki inaga da  haƙura kika yi da shi kika fita batun shi amma duk wannan shishige mashi da ki ke yi bazai amfana maki komai ba face ma kiyita shan wahalar sa,kina dai gani yau da da tsautsayi da tuni ya karya ki, shawa..... "

bata ƙarasa na feenah ta daka mata tsawa tana faɗin

"dallah dakata mana kairiyya, dama ba tun yau ba nasan cewa ke ƴar baƙin ciki ce , kina bakin ciki na samu ya shazim, to wallahi aniyar ki ta biki,dama sai da innah tace mana kema son shi ki ke damace kawai baki samu ba shiyyasa ki ke man baƙin ciki, to wallahi kiyi ki gama ni da ya shazim nan gani nan bari ɗumaman mayya ehe" ta ƙarasa maganar haɗi da dallama kairiyya harara kamar idanuwanta zasu zazzago ƙasa, abun yayi matukar ɗaure ma Kairiyya kai wai ita feenah ke ce ma tana mata baƙinci kuma wai innah da bakinta ta ke ce ma feenah wai tana mata baƙin ciki tun da take bata taɓa tunanin wani cikin su zaiyi tunani makamanci haka ba,
"Allah ya tsare ni feenah da yi maki baƙin ciki,gaskiya ce nake faɗa maki
"to bana so kitsaya a matsayin ki kawai ban son gaskiyar taki"
"haka kika ce?"
"eh haka nace, gaskiya ko in dai da ga wurin ki ne bana so na ya fe "
"shikenan wahalar ya shazim kuwa yanzu kika fara shanta" kairiyya ta faɗa haɗi  da jan blanket ta juya mata baya
ta rufe jikinta ruf, tana jin feenah na faɗin
" aniyar ki ta biki, ni da ya shazim sai alkairi duk baƙin cikin mutum wallahi sai dai ya mutu"
tana jin ta amma tayi banza da ita kamr ba da ita take magana ba, itama da ta gaji da banbotan kwanciya  tayi.

_WASHE GARI_

zaune su ke kan dinning suna breakfast, kowa nacin abinci amma ban da feenah da bata iya ko da ɗaga hannunta balle ta samu taci lura da hakan ne yasa Ammy cewa

" feenah lafiya kowa yana breakfast amma banda ke "
Kwalla ce ta taru a idanuwan ta tace "Ammy bazan iya ci ba saboda hannun" ta faɗa hawayen da ke idanunta na zubowa
Sai da ta faɗi haka sannan Ammy ta tuna da cewa tayi fa targaɗe a hannunta,
"taso ki dawo kusa da ni sai na baki, ke sa'ada koma in da ta taso " Ammy ta faɗa, turo baki gaba sa'ada tayi tana faɗin
"Ammy tana fa iya ci da kanta"
"kinci gidan ku zaki tashi ko sai naci mutuncin ki, wai ku wane irin mutane ne wai" miƙewa sa'ada tayi haɗi da ɗaukar plate ɗin da take cin abinci  ta koma in da feenahr ta tashi
"wallahi Ammy ke ki ke ƙara biye mata wani bata iyaci da kanta sai kace wacce ta karye, ai da karyewa ki ka yi ƙila komai sai anyi maki k....... "
kasa ƙara sawa yayi ya duƙe ƙasan table da sauri sakamakon jifar shi da Ammy tayi da spoon, dariya ce ta kubce ma fatima dama haushin abun da yake ma feenah tun jiya ta keji , yana a ƙasan table bai ɗago ba yace
"na rantse da Allah na kamaki fatima sai ranki ya ɓaci zaki san ni ki ke ma dariya "
hannu ta sa ta toshe bakin ta tana faɗin
"A fuwan ya noor bazan sake ba "
"kima sake yarinya , dan Allah Ammy kiyi haƙuri "
Ya faɗa ba tare da ya ɗago ba, tsoro yake ya ɗago Ammy ta sake jifan shi
"Ammy kinyi shiru baki ce kinyi haƙuri ba " sai kace wani yaro
"Sai baƙin tsoro ga jan faɗa " Ammy ta faɗa, jin tace haka ne yasa shi  fahimtar  cewa ta haƙura, ɗagowa yayi yana zuba ma fatima harara, tsit wurin yayi baka jin motsin su sai na cokulan da suke cin abinci, shazim ne ya shigo daga motsa jiki,wurin su ya ƙara so Ammy kawai ya gaida ya nufi sama daman tun da su feenah su ka zo ya daina breakfast a dinning dama can ba gwanin zama dinning  ba ne, suna kammalawa fatima ta shirya mashi na shi a tray da zata kai mashi noraiz cewa yayi mi zai hana ta ba feenah ta kai mashi, cika feenah tayi ganin da gaske noraiz bazai barta ta zauna lafiya ba shikenan ya samu abun da zai riƙa tsokanan ta.
Shazim bayan fatima ta kai masa breakfast ɗin shi yaci shirya wa yayi ya wuce EKO.

Su hidaya ya samu zaune a reception, gaishe da shi suka yi amma ba wacce ya amsa mawa acikin su gaba yayi abun shi, victoria ce ta taɓo destiny tana nuna mata hidaya kwashewa su kayi da dariya ashe duk abun da ya faru tsakanin ta da shazim sun sani wani munafukin aka samu ya sanar da su shiyyasa yau suka zauna a reception kawai dan su sa mata ido, abu kaɗan su saki dariya, tun hidayar bata gane da ita su ke ba har ta fahimci cewa ita su ke ma dariya, gajiya tayi da dariyar da su ke yimata tashi tayi ta nufi office ɗin da suke zama,wata dariyar shaƙiyyanci suka ƙara kwashewa da ita, abun yayi matuƙar ɓata ran maryam aikuwa ta tashi tana faɗin
"Amma dai wallahi wasu anyi dabobi,ku wani tasa mutane kuna yi masu dariya sai kace wasu mahaukata,Allah dai wadaran wanda bai san ciwan kanshi ba " nurses ɗin da ke wurin har haɗa baki su ke wurin faɗin " ke dai bari maryam wasu mutanen dai basu san ciwan kan su ba" tsarguwa su ka yi ganin kowa sai faɗin abun da yazo bakin sa yake yasa victoria miƙewa tan faɗin
"kushiga hankalin ku dan naga take taken ku, dan duk wacce tace zata zage mu sai ta gane bata da wayau"
"wai dakata victoria ki ke ko wa, wai ma wakike faɗa ma wannan maganganun "
"da uban da ya tsargu nake "
"ai fa kaji matsalar bamuguje" maryam ta faɗa haɗi da kwashe da dariya dan ta san victoria bata san mi kalmar bamaguje take nufi ba sauran ma dariyar su ka kwashe da ita, haka su kayi ta jefa ma victoria baƙaƙen magamganu da hausa ganin bata fahimtar mi suke cewa, baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshi nan ta shiga zunduma masu zagi da yaren su, banza su kayi da ita kowa ya kama harkar gaban sa su ka barta ita kaɗai sai ɓaɓatu take kamar wata mahaukaciya,  destiny ce tace "haba victoria sun maida ke mahaukaciya,amma baki gane ba sai wani gazi ki ke "  da yaren su tayi maganar dan kar su maryam su fahimci mi take faɗa mata amma abun da bata sani ba daga yana yin yanda victoria tayi shiru su ka fahimci cewa wani abun ta faɗa mata, jan hannun ta destiny tayi suka bar wurin zuwa office ɗin su da suke zama samun hidaya su kayi tana karatun alqur'ani mai girma,zama su kayi suna sauraron ta  wani abu na Allah kamar tace su zauna suyi shiru, haka suka zauna sai satar kallon ta su ke bata ma san da zuwan su ba, karatun ta kawai take, wayar ta ce dake cikin jaka ta fara ringing,sai da ta kai aya tukun ta buɗe jakar ta ciro wayar duba mai kiran tayi , dr kabir shi ne mai kiranta, latse wayar tayi ta sata a silent  ta cigaba da karatun ta, haka yayi ta kira ba tare da tayi picking ba.
Zaune yake a office ɗin shi abun duniya duk yabi ya ishe shi sai kiranta yake Amma taƙi ɗauka kuma ya san taga kiran shi ɗauka ne kawai ba zata yi ba,sai dai daya juya yace "wai hidaya kashe ni kike sonyi ne, mi nayi maki ne dan Allah da ki ka zaɓi ki azabtar da ni" haka yake ta sambatu bawan Allah duk ya zama abun tausayi ƙarshe dai kiran Momy yayi tana picking ya fashe da kuka yace "momy so take sai zuciyata ta buga momy bata sona ban san mi nayi mata ba "
"ya Allah Auta ba dai acikin hospital ɗin kake man wannan kukan ba "
"momy a nan ne mana gaba ɗaya so take ta zautar da ni ban san mi nayi mata ba"
"yanzu dai daina wannan kukan da kake yi kamar wani yaron goye"
"to momy na dai na, amma dai yau dady zaije wurin baban ta ko"
"eh yau zai je in sha Allah ka kwantar da hankalin ka, idan kana saurin karaya bazaka iya shawo kanta ba, ka daina saurin karaya ka sama ranka ƙwarin gwiwa, ka nuna mata soyayya na san zata so ka my Auta"
"to shikenan momy na dai na "
"yawwa, yanzu tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login