Showing 9001 words to 12000 words out of 127932 words
shiga yi sai ga ya abdallah shima ya sauko jikin sa sanye da jallabiya,ƙarasowa yayi yana gaishe da abie da gajiyar tafiya, amsa mashi abie yayi tare da tambayar shi ya aiki,amsa ya bama abie da alhmdllh shima serving din sa Aaimah tayi , abinci su ka shiga ci ba magana sai dai karar spoon dake tashi, su Aairah su ka fara tashi
"ba dai har kun ta shi ba?" abie ya tambaya yana binsu da idanu
"eh abie,zamu je gidan granny ne shiyyasa kuma fa mun koshi"Aairah ta bashi amsa
"to shikenan sai kun dawo kar dai ayi dare , a dawo dawuri kun ji"
"In sha Allah abie baza mu kai ba"
Allah yasa, ameen suka fada su na nufar up stairs , abie su na gama cin abinci kan sofa su ka koma suna fira shi da ya abdallah ,mom kuma tattare dishes din da su kayi amfani dasu tayi ta nufi kitchen, baaba larai ce ta fito daga corridor din da da kinta yake wurin su abie ta nufo hadi da gaishe da abie tana tambayar shi ya gajiyar hanya amsa mata yayi da, "lafiya lau alhmdllh, ya gida ya kuma muka same ku"
"Alhmdllh mu ke, naga saƙo nagode,Allah ya saka da alkairi" ameen nagode bakomi abie ya bata amsa ( nasan masu karatu zasu ce godiyar mi baaba larai ke yi ma abie , kudi ya ba ma mom ta ba ma dukan hadiman gidan dama ya kan yi haka duk In zaiyi tafiya.) Kitchen ta nufa anan ta samu mom na wanke dishes din da suka ci abinci "ah hajiya dakin bari na zo na wanke ai, A'a bakomi baaba kema ki huta mom ta bata amsa, to shikenan bari mu yi tare" in ji baaba larai, "A'a da kin bar shi Allah, kinga na kusa gamawa ai"
" to shikenan" su Aairah ne su ka sauko sun sha jalbab har kasa sai bag kalar ta kalmin dake kafarsu,karasowa su kayi wurin su abie hadi da cewa sai mun dawo,abdallah ne ya ce" mudi na nan waje shi zai kai ku" to suka ce suna nufar kitchen wurin mom sun cewa sai mun dawo a dawo lafiya tayi masu , ficewa su ka yi zuwa harabar gidan, a nan suka samu mudi na jiran su , motar su ka nufa, shiga su kayi, key yayi ma motar suka fice da ga gidan dama me gadi ya bude masu gate labari kawai Aaimah da Aairah keyi shi dai mudi nashi saurare har suka isu gidan granny horn mudi yayi a bakin gate din gidan,bude masa gate din a kayi ya shiga daga ciki, ya na parking su ka fito gidane dan dai dai me kyau cikin gidan suka nufa wata kyakyawar tsohowa ce suka samu zaune a parlor tana kallon SUNNAH TV ( granny kenan mahaifiyar mom ce) sallama su ka yi da gudu suka nufi yar tsohuwar, granny tace "karku kuskura ku fado man,salon kawai ku ida kara sa man yan kafafun da nake fama dasu" Aaimah ce tace "haba granny daga munyi murnar ganin ki sai kice zamu ida karasa maki kafafun"ta fada tana turo baki, Aairah ce tace " shiyyasa yau zan zuga tsoho yayi maki kishiya tun da baki da kafafu" granny tace
"sai dai ke ayi maki kishiya, amma ba dai ni ba, saboda ni ba wacce zata iya kishi dani, in kuma kece kishiyar in ji tunwuri" dariya su ka kwashe da Ita su duka Aairah tace
"wah wai ni , ai kuwa da kin sha kwarkwasa da kisisina" murmushi kawai granny tayi hadi da fadin Allah ya shiryeki yan biyu ( dayake haka take ce masu ko kuma Hassana da hussainah) gaishe da Ita su kayi suna tambayar tsoho na nan, ( wato mijin granny) granny ce ta basu amsa da "yana parlor da yake ganin daliban sa, inajin ma karatu suke saboda yau juma'ah ( malamin addini ne shi duk da ya tsufa hakan bai hana shi koyar da daliban sa ba) Aaimah tace" to shikenan granny bari muje gidan aunty safiya mu dawo, kilan time din ya gama, to sai kun dawo ku gaishe man da ita" granny ta fada Aairah ce tace "za ta ji in sha Allah" fita su ka yi harabar gidan nan suka samu mudi zaune kan benchi suna fira da me gadin gidan, gannin sun fito ne yasa shi tasowa Aairah ce tace "kabar shi kawai ba nisa za muyi ba, gidan aunty safiya za muje"
to ya fada yana komawa kan benchi ya zauna,su ku ma fita su kayi daga gidan, tafiya su kayi a kafa ba mai nisa ba su ka iso gidan, tura yar kofar dake gefen gate su kayi su ka shiga gidan, gida ne mai girma ba laifi dan har ya kusa girman gidan su, part din masu gidan suka nufa da sallama a bakin su suka shiga parlorn, yan yara su ka samu na wasa a parlorn mace da namiji a kalla za suyi kimanin shekaru 10, suna jin sallamar su suka nufo su da gudu suna masu "oyoyo aunties ya gida, ya mom" su Aaimah su ka ce "lafiya lau hisham sai ku ka dai a parlor kai da hibba" wata matashiya ce ta leko daga up stairs jin hayaniyar yaran zata yi sa'anni dasu Aaimah tana ganin su Ita ma da gudu ta sauko tana fadi "oyoyo lovely sister, da ku ka ce kun fasa zuwa" Aairah ce tace "ke dai bari najma, dafa har mun fasa saboda abie zai dawo yau, to da muka koma gida daga school mom take ce ma ai yama kusa isowa, to shine fa muka shirya yana dawowa muka ta ho" najma tace "gaskiya naji dadi, da Allah har nayi fushi"
Aaimah tace "yanzu dai ba wannan ba naji banji mutsin Ummah ba ( Aunty SAFIYA suke cema Ummah saboda su najma ) ko bata nan ne , tana dakin Abba najma ta bata amsa hadi da jan hannun su tana cewa "mu tafi part din Abban daga nan sai ku gaisa da shi ko"
"ok muje" part din abban su ka nufa, sallama su ka yi yayin da suke shiga cikin parlorn zaune suka same su kan sofa, amsa masu sallamar su ka yi aunty safiya tace "ah lallai yau ina da manyan baki" abba yace " lallai kam yau muna da man yan baki, ya mom din ku da abie ya kuma school, alhmdllh abba suka amsa mashi, to masha Allah abba ya fada najma ce tace " to ku tashi mutafi daki, da to suka amsa mata hadi da mikewa suka fice direct bedroom din najma suka nufa suna shiga suka yada zango akan bed din ta Aairah ce tace " wai nikam ina Yaya mus'af ne najma" wani kallo Aaimah tayi mata
"uhmm dama nasan hali,har ni za kiyi ma bariki wai ziyara za mu zo bayan nasan ƙarya ne"
"eh din naji komi za kice kice Aairah ta fada tana murguda ma Aaimah baki ,najma ce tace" ya Isa haka in kuka fara sai ku ba mutun haushi wallahi, ya mus'af ne dai ko, to yana part dinsa bari nakira maki shi a waya ko ke ki kira shi ba shikenan ba" Aaimah tace "aikin san wasa nake maki ko rabin rai"
niban wani sani ba Aairah ta fada, to yanzu kinsani shikenan ko ta wuce, bari ni na kira maki shi da kaina a cewar Aaimah hadi da ciro wayarta tayi dealing number sa kiran na shiga ta mikama Aairah wayar picking call din yayi hadi da ce " Assalamu Alaikum"
"Waalaikassalam" ta amsa mashi sallama da ya yi
cewa yayi" Aaimah ya ki ke,ya gida yasu mom da ya Abdallah,ina kuma sweetie nah take" bubbuga kafafu ta shiga yi tana turo baki hadi dacewa" haba Qalbei nice kenan ma baka gane ba"su najma mi za suyi inba dariya ba,suna cewa "ashe soyayyar bata kaiba da har ake kasa gane muryar juna" fashewa tayi da kukan shagwaba tana faɗin"ka gani koh Aaimah da najma nayi man dariya, on the other hand yace " sorry sweet heart nayi tuna nin Aaimah ce, kinga ai numberta ce amma kiyi hakuri kinji my, najma na gidan kune?"
"Aa fa, kai da na zo dan nayi surprise din ka, amma sai ka bata komai baka gane ni ba" Aairah ta fada"sorry kinji tawan faɗa man kina ina kin ji" turo baki gaba tayi hadi da cewa " Ina bedroom din najma"
"am coming sweetheart" ya fada hadi da kashe wayar,ajiye wayar tayi Ita ma tana yima su najma gwalo "oho dai ke da ba'agane ba najma ta fada su na tafawa ita da Aaimah" nocking su ka ji ana yi da sauri Aairah ta nufi kofar ta bude,wani matashin saurayi ne tsaye jikin sa sanye da jeans da T-shirt na kamfanin Gucci kyakyawa ne ba laifi a kalla zai yi kimanin shekaru 20 a duniya murmushi Aairah ta sakar mashi shima martanin murmushi ya mayar mata, gaishe da shi Aaimah tayi, ficewa su kayi daga bedroom din, su Aaimah kuwa fira kawai suke har aka kira sallar asr, sallah su ka tashi su kayi a lokacin Aairah itama ta shigo domin yin sallar Aaimah na ce mata "ai nayi tunanin nisa ku kayi da naga kun fita ashe kuna kusa" banza Aairah tayi da ita ta nufi bathroom domin yin alwala, basu ne suka bar gidan ba sai wajen 5:00 sannan suka koma gidan granny najma da Aaimah na gaba yayin da Aairah da mus'af ke bayan su , suna shiga gidan granny tace "ashe za ku dawo harna yi tunanin kun wuce gida, ashe kuna nan" kallon mus'af tayi tana fadin "kai kuma lafiya kayi man tseye a kai , aure ne dai bana yi ehe" dariya mus'af yayi yana faɗin "sai mi, dama ni yarinya nake so me jini a jika ba tsohuwa ba" dariya su ka kwashe da Ita su duka, "haba kai dai kawai dan ba za ka samu bane , ya safiyar take ina su Hibbatu da hisham"
"lafiya lau suke granny" fira su ka shiga yi da granny tana tsokanar su a nan tsoho ya same su, gaishe da shi suka yi , dashi suka taru suna ta firar ba su ne suka bar gidan ba sai kusan 5:50 sannan mudi ya mayar da su gida duk da mus'af ya so mai da su, amma suka ce ya barshi tun da da driver su ka zo ,da shigar su gida bedroom suka nufa domin time din sallar magrib ya kusa kayan jikin su suka cire suka sanya ma rasa nauyi, saukowa su kayi down stairs direct kitchen suka nufa wurin mom da baaba larai dake shirya dinner , kama masu aikin su kayi har suka kammala kowa ya nufi bedroom dinsa domin gabatar da sallar magrib wacce ake kira.
KAINAAT
_Lagos....._
Innah asabe ce a kitchen ita da fatima suna girki kiran sallar da a ke yine yasa fatima cewa "Innah kije kiyi sallah zan karasa aikin, to amma kefa, karki damu Innah kitafi kawai ( da yake tana fashin sallah ne) To shikenan, fita tayi daga kitchen din ta nufi dakin ta, shazim ne ya shigo cikin gidan jikin sa sanye da farar jallabiya da alama daga masallachi yake parlorn Ammy ya nufa bai isketa ba sai ya wuce bedroom din ta, nan ma bata nan fitowa yayi daga part din ya nufi main parlor fatima ya gani ta fito daga kitchen hannun ta rike da food flask " Ammy bata dawo bane,eh bata dawo ba , ok ya fada hadi da komawa part din sa, lokacin da Innah asabe zata koma kitchen har fatima ta gama komai da yake sai da ta jira aka kira sallah isha tayi, kama mata kawai tayi suka gyara kitchen din, falo fatima ta fita kiran daya daga cikin ma aikatan gidan tayi a waya domin yazo ya daukar masu a binchin su, sallama a kayi daga kofar falon haɗi da turo ƙofar, fateemah ce tace yawwa ilya tana shiga kitchen,fitowa tayi hannun ta ɗauke da food flask din masu aikin mika mashi tayi , part dinsu ita da Ammy ta nufa bedroom din ta ta shige kayan jikinta tacire towel ta daura bathroom ta wuce domin yin wanka 10 minutes ta fito daga bathroom din dressing mirror ta nufa mai kawai ta shafa ta nufi clothes set dinta, dama ta sanya pad tun a toilet shiryawa tayi cikin pajamas lemon green ta yafa mayafi white mai dan girma feshe jikinta tayi da turare mai dadin kamshi fita tayi daga bedroom din a falon Ammy ta zauna kan sofa wayarta dake charge tacire ta shiga chatting wurin 9:00 sai ga Ammy wacce shazim ya dauko falo ta tsaya shi kuwa up stairs ya haura sai 9:30 fatima da Ammy su kayi dinner dan shi shazim cewa yayi takai masa part din sa,suna kammalaawa fatima ta kwashe kayan da su ka yi amfani dasu ta kai kitchen nan falo ta zauna suna fira da Ammy sai wuri 10:00 su katashi kowa ya shige bedroom dinsa
zaune yake kan sofa dake bakin bed dinsa yana aiki a laptop dinsa sai wurin 12:00 ya rufe laptop din toilet ya nufa bayan 5 minutes yafito jikin sa da damshin ruwa da alama alwala yayi, wardrobe dinsa ya nufa sallaya ya fito da Ita ya shimfida shafa'i da wutiri yayi,ya jima kan sallayar yana adu'oi sannan ya niketa ya maida ta cikin wardrobe, bed dinsa ya nufa hadi da kashe bulbs din dakin ya kunna bedside lamp, zama yayi daga bakin bed din adu'a yayi ya shafa a fuskar sa sannan ya ida hawa kan bed din kwanciya yayi hadi da jan blanket yarufe iya kugunsa.
Washe gari.......
Zaune Ammy da fatima suke kan dinning suna breakfast, shazim ne ya shigo jikin sa sanye da jogging suit black color sai p-cap white hannun sa rike da water bottle wurin su Ammy ya nufa " ina kwana Ammy fatan kin tashi lafiya ya fada Ammy tace "lafiya lau alhmdllh, yau baka zuwa abnoor ne, amsa ya bata da " A'a Ammy zanje, ok naga har 10:30 tayi Ammy ta fada , " eh wallahi nayi late wurin tashi daga bacci,amma yanzu zan shiga ciki nashirya In sha Allah"
"to shikenan sai ka shirya ga breakfast dinka nan na jiran ka a dinning, to Ammy ya fada hadi da nufar part din sa.
✨ _Victoria_ . ✨
Anguwace ta christianity irin ta masu kara min Karfi, destiny naga ni ta fito da ga wani gida ta nufi wan da ke opposite din in da ta fito jikin ta sanye da gown iya gwiwarta purple color kanta da kitson kalaba na attachment ka farta sanye da flat shoe, gidan dan karami ne, ko ina ya sha cement dakuna biyu ne a gidan nufar daya daga cikin kofofin tayi knocking tayi hadi da cewa" excuse" daga cikin dakin naji ance "come in" tura kofar tayi hadi da shiga Victoria ce acikin
dakin tana ta faman jan straight gown taki shigar ta destiny ce tace " lallai Victoria a she bakima shirya ba, kin kuwa san nisan da wurin ya ke da shi,sai fa mun fita Lagos kuma fa kinsan yau ana zuwa church da yamma, sorry destiny yanzu zan shirya mu tafi, abun da yasa ma nayi late bari nayi sai momy ( mahaifiyar ta ) ta tafi market sannan domin in tasan inda zamu ba zata bari mu tafi"
"Ok kiyi sauri gaskiya" Victoria na ga ma shiryawa su ka fita gidan tafiya su kayi sai da suka hau kan titi tukun suka tsai da mai mashin suka hau, tafiya su kayi mai dan nisa sannan suka kawo wani dan karamin kyauye duk duwatsu suna kawowa inda mashin bai wuce wa suka sauka, kudin sa suka bashi su kuma suka cigaba da tafiya nanma sai da su kayi tafiya ba laifi tukun suka kawo wata yar bukka ita kadai a wurin sai mutane dake a jere a bakin bukkar, suna karasowa suma suka bi layi, sun jima a tsaye layi bai zo kansu ba, victoria harta gaji da tsayuwa ta duƙa, lokacin da layi ya zo kansu shiga su kayi tare cikin bukkar,wani mutum ne zaune, gaban sa wasu irin ƙahuna ne sai ƙoƙunnan kan mutane,jikin sa sanye yake da jajayen kaya fuskar sa duk ta sha ɗiɗɗige ɗiɗɗigen fari idanun sa a kewaye su ke da bakin fenti,gaishe dashi su kayi da wani irin yare mara dadin ji, kwashewa yayi dawata irin dariya mai firgitarwa sannan ya tambaye su meke tafe dasu, destiny ce ta kora masa bayani a kan abun da yake tafe dasu, dariya ya sake kwashe wa da Ita sannan yayi yan surkullen shi wani magani ya dauko cikin wani bakin tulu ya ba destiny tasa hannu ta karba ita kuwa Victoria sai zare idanu take kudi suka dauka masu yawan gaske suka ajiye a gaban bokan sannan suka fice daga bukkar ta hanyar da suka biyo ta nan suka bi sai da suka kawo cikin kyauyen tukun suka samu wani mashindin ya dawo dasu gida, gidan su destiny suka wuce dan lokacin kafe 4:15 dakin destiny suka nufa zama su kayi suna huce gajiyar tafiya destiny ce tace" ina zuwa" tana fada ta fice daga dakin, ba tafi 1 minute ba ta dawo da kwano a hannun ajiye shi tayi gaban Victoria fita ta sake yi sai gata ta sake shigowa hannun ta rike da pure water guda biyu zama tayi,bude kwanon ta yi sakwara ce da miyar okra ( kubewa) suna cikin ci saiga wani saurayi ya shigo dakin sanye ya ke da crazy jeans sai singlet gashin kansa kuwa yasha dada ( yanda yan iska keyima gashin su ya koma kamar lagwani ) kallo ɗaya zaka masa ka san a buge yake, ya na ganin Victoria ya kama washe baki daure fuska Victoria tayi tana ganinsa , kusa da Ita ya matso kamar zai yi hugging din ta ba shiri ta mike tsaye hadi da daka mashi tsawa tana cewa
"which kind of this nonsense samuel"
"bangane wulakanci ba Victoria,you