Showing 93001 words to 96000 words out of 127932 words
da nuraddeen ya tashi tafiya maƙale mashi sadiq yayi akan sai ya bishi, zainab tasa ƙanwarta wacce suka zo tare da ga morocco ta haɗa ma sadiq kayan shi da zai bi nuraddeen...
Episode 50_51_
Koda nuraddeen ya koma da sadiq kurfi, bala'i maijidda ta tada akan dole sai sadiq ya dawo kurfi da zama tun da daman dan abdulƙadir bai da ɗa ko ƴa yasa aka bashi sadiq to tun da yan zu matarshi ta haihu sai sadiq ya dawo gida, sai da nuraddeen ya biyo mata ta bayan gida sannan ta kama kanta, sadiq bai gama hutun ba nuraddeen ya haɗa mashi kayan shi ya mai da shi lagos , a kwana a tashi asarar rai sadiq ya kammala secondry school lokacin aisha na da shekara bakwai a duniya,a lokacin tana primary 4, daya ke tun tana 4 year alhaji abdulƙadir ya sata makaranta, akwai soyayya da shaƙuwa tsakanin sadiq da aisha bacci kawai ke raba su, ko wane lokaci zaka same su suna tare da juna, musamman da yanzu sadiq yake zaune a gida yana hutu kafin ya fara zuwa jami'a, da sadiq zai tafi kurfi kuka aisha ta sa a dole sai ta bishi hajiya zainab da sadiq su kaita lallashinta sadiq yayi mata alƙawarin idan zai koma bikin su halimatu zai tafi da ita sannan ta haƙura,ko da sadiq yaje kurfi anan yake samun labarin rasuwar kakar shi wacce ta haifi ruma, yayi kuka sosai dan ba ƙaramin son tsohuwar ya ke ba saboda ita ma tana son shi,hutu na ƙarewa ya koma lagos , bai wani jima da dawowa ba ya fara zuwa school,kullum kafin ya tafi school sai ya fara ajiye aisha a school sannan yake wuce wa , da zai fara zuwa jami'a mota abdulƙadir ya siya mashi, idan an tashe su kuwa driver ke ɗauko ta ranar da bashi da lectures kuwa shi ke kaita ya ɗauko ta, haka rayuwa taci gaba da tafiya an tsaida ranar bikin su uwani ita da halimatu, bikin su na saura sati ɗaya sadiq ya shirya zai tafi kurfi maƙalewa aisha tayi sai ta bi shi, shirya mata kayanta hajiya zainab tayi suka tafi,suna isa kurfi da Ibrahim suka ci karo zaune ƙofar gida shida abokan shi, yana ganin su ya taso da fara'a a fuskar shi yana ma sadiq barka da zuwa yayin da yake amsar jakar kayan da ke hannun shi, gaishe da shi aisha tayi, ya amsa mata da fara'a yana ce ma sadiq su shiga ciki, gidan suka nufa, suna shiga halimatu na zaune kan kujera yar tsugunno tana wanke wanke, tasowa tayi da sauri tana ma su barka da zuwa suna nan tsaye maijidda ta fito daga kitchen hannun ta riƙe da kwano, wurin su ta ƙaraso tana bin aisha da ido, sadiq ya ce "ina wuni innah, mun same ku lafiya " daga mashi kai kawai tayi tana tambayar wannan fah, sadiq ya bata amsa da aisha ce ƙanwata, fuska a ya mutse tana kallon aisha ta ce"ba shakka, sannu ko " duƙara da kai aisha tayi tana cewa ina wuni da lafiya lau maijidda ta amsa sai kuma tace" yasu mamar ki kun baro su lafiya" da fara'a aisha tace" lafiya lau suke suna gaishe da ku"
"muna amsawa "maijidda ta faɗa sannan tace ma halimatu " ki kaita ɗakin ku, kunyi tsaye "tana gama faɗa ta juya ta nufi ɗakin ta, da kallo suka bita fuskar su da mamaki dan ba su taɓa tunanin zata yima aisha ko kallon arziƙi, kayan ta da ke hannun sadiq halimatu ta amsa haɗi da jan hannun ta suka nufi ɗakin su, sadiq ma ɗakin su suka nufa shida Ibrahim yana tambayar shi ina su baba da magaji
sai da yamma magaji suka dawo daga kasuwa shida nuraddeen, sosai magaji yaji daɗin ganin sadiq hakama nuraddeen yayi farin ciki sosai musamman da yaga aisha, kulawa sosai aisha ke samu wurin dangin sadiq mu samman halimatu dan ta ɗauki aisha kamar ƙanwarta, uwani ce kawai ba ruwan ta da aisha amma har maijidda na jan ta a jiki, abun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, ana gobe ɗaurin aure gida ya cika da baƙi alhaji abdulƙadir yazo shida hajiya zainab, tarba mai kyau suka samu wurin nuraddeen da maijidda, washe gari aka ɗaura aure aka kai amare gidajen mazajen su aisha gidan halimatu ta kwana, sai washe gari ta dawo gidan su sadiq saboda ranar zasu koma lagos harda sadiq, da zasu tafi kiran sadiq maijidda tayi ɗakin ta akan mizai hana su tafi tare da Ibrahim tun da ya kusa gama makaranta, haƙuri sadiq ya bata yana cewa ko jiya yayi ma baban su maganar yana so su tafi tare da Ibrahim amma yace bai amince ba, haushi kamar ya kashe maijidda, gani take nuraddeen baya son ƴaƴan ta sadiq kaɗai yake so, kwantar da murya tayi tana cewa "kana jina sadiq ka rabu da maganr baban ku, da kace ma alhaji abdulƙadir kana son tafiya da ɗan uwanka nasan zai amince "maganar nuraddeen suka ji daga bayan su yana cewa "to wallahi ban amince ba , idan har kana son zaman lafiya da ni kar na sake naji kayima abdulƙadir wannan maganar kaji na faɗa maka "maijidda ta ce" wai miyasa kake haka ne, yaro na son tafiya da ɗan uwan shi amma ka hana haba dan Allah "ko kallon inda take bai yi ba yace ma sadiq "kama hanya ka wuce suna waje suna jiran ka "da to sadiq ya amsa yana ma maijidda ban kwana, Allah ya tsare kawai tace tana bin nuraddeen da kallo da zai fita, har ƙofar gida nuraddeen ya samu su sadiq yayi ma abdulƙadir ban kwana dayi mashi godiya, da motar su zata bar anguwar Ibrahim harda kukan shi, sannu sannu bata hana kaiwa sai dai ajima ba'a kai ba magaji ma yayi aure lokacin halimatu da uwani na da ƴaƴa ɗai ɗai uwani na da namiji mai suna usman halimatu kuma mace sunan ta zainab.
soyayya ce ta ƙullu tsakanin sadiq da aisha hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma abdulƙadir da nuraddeen ba, dama basu da wani buri daya wuce haka, zainab abun yayi mata daɗi dan baƙaramin so take yima sadiq ba tamkar ɗan cikin ta haka take jinshi.
da sadiq ya kammala degree ɗinshi,kullum suna tare da aisha dan har binta yake makaranta, alhaji abdulƙadir ya ɗaura sadiq kan kasuwanci kafin ya fara aiki, sai da sadiq yayi kusan shekara ɗaya da rabi yana gudanar da kasuwanci sannan alhaji abdulƙadir ya sama mashi aiki a Abuja duk da sadiq ɗin yaso yayi a lagos saboda kwata kwata baya son abun da zai sa yayi nisa da aisha, da zai tafi kuwa aisha har da kuka abun ma mamaki ya ba ma hajiya zainab,sadiq bai daɗe da fara aiki ba nuraddeen da abdulƙadir suka tsaida ranar auren su da aisha akan da ta kammala makaranta za'a yi bikin, hakan ce ta faru aisha na kammala makaranta aka fara shirye shiryen biki,ana saura wata ɗaya ƙanwar zainab tazo daga Morocco ta tafi da aisha, chan za suyi mata gyaran jiki sai ana saura sati za su dawo da ita, ana saura sati ɗaya bikin Aisha ta dawo daga Morocco ita da yan uwan hajiya zainab , gida ya cika da baƙi aka fara shirye shirye an je anyi ma aisha jere gidan sadiq, shagali sosai alhaji abdulƙadir ya shirya haka ma nuraddeen ba'a barshi a baya ba, ana saura kwana uku yan kurfi suka zo part guda alhaji Abdulƙadir ya ware ma Nuraddeen ya ajiye duk wani baƙo daya zo mashi da yan uwan shi, maijidda kuwa ita da su uwani da yaran su suna part ɗin hajiya zainab , ranar juma'a aka ɗaura auren Abubakar Nuraddeen Ahamad Sharani da amaryar shi Aisha Abdulƙadir murna wurin ango da amarya ba'a cewa komai.
da yamma Alhaji abdulƙadir da nuraddeen suka haɗa aisha da sadiq su kayi masu nasiha,sannan suka je wurin hajiya zainab,nasiha sosai tayi masu da fatan alkairi, aisha na kuka ƙannan hajiya zainab suka yi mata rakiya zuwa gidan mijinta, ranar lahadi yan uwa da abokan arziƙi suka fara tafiya , ƴan kurfi kuma washe gari zasu tafi litinin kenan , da yamma maijidda tasa aka kira mata sadiq ta sake mashi maganar Ibrahim, cemata sadiq yayi "innah baba ya hana, ina kuma tsoron abun da zai biyo baya idan nace dole sai Ibrahim ya tsaya"bal bale shi da masifa maijidda tayi, wai bai son zumunci dan yaga Allah ya ɗaukaka shi shine zai fara ƙyamar ɗan uwan shi,abun yayi mugun bama sadiq mamaki, bai taɓa tuna nin Innah za tace mashi haka ba arayuwa, haƙuri kawai ya bata, washe gari da safe sadiq yaje gidan alhaji abdulƙadir domin gaisawa da su ya kuma yima su nuraddeen rakiya saboda da safen zasu tafi, koda ya gaishe da nuraddeen bai san miya faru kawai nuraddeen ya rufe shi da faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yana cewa "kenan ni ban isa na hana ka abu ka hanu ba ko "
haƙuri sadiq ya shiga bashi batare da yasan miya aikata ma mahaifin nashi ba, sai da zasu tafi halimatu ke bashi haƙuri haɗi da faɗa mashi abun da ya faru, wai ashe lokacin da ya bar ɗakin da maijidda ta sauka, fita tayi daga ɗakin taje har ɗakin hajiya zainab ta roƙe ta akan dan Allah tunda sadiq da aisha basu gidan yanzu za su ji duk ba daɗi mizai hana Ibrahim ya dawo gidan da zama,shine hajiya zainab ta sami alhaji abdulƙadir da maganar shiku ya samu nuraddeen akan dan Allah ya bar mashi Ibrahim ɗin, nuraddeen yayi tuna nin sadiq ne ya faɗama abdulƙadir ɗin shine ya rufe shi da faɗa, koda halimatu tagama faɗama sadiq bai ji daɗin abunda Innah tayi ba yaso ace ta bari ya lallaɓa baban nasu harya amince, amma ta ɓata mashi komai gashi baban yayi fushi da shi, kafin su wuce sai da sadiq ya sake bama nuraddeen haƙuri,ya haƙura amma akan da Ibrahim zasu tafi daga baya sai ya dawo amma ina abdulƙadir yaƙi amincewa , ba yanda nuraddeen ya iya dole ya bar Ibrahim, maijidda daɗi kamar ya kashe ta, nuraddeen na lure da ita bai dai ce komai ba,sai da suka isa kurfi yayi mata tatas dan ya san ita zata sa sadiq duk shirin ta ne, nunawa tayi ko a jikin ta burinta dama Ibrahim ya zauna a lagos to burinta ya cika komi zai ce bawai zai dameta bane, watan sadiq da aisha ɗaya dayin aure suka wuce abuja aka bar Ibrahim a lagos saboda makaranta da ya ke zuwa, cikin ƙan ƙanin lokaci Ibrahim ya goge ya zama ɗan gayu,saboda ba ƙarmin kulawa yake samu daga wurin su hajiya zainab ba,sadiq watan su bakwai a abuja ya nema aisha admission ta fara zuwa makaranta, idan zai tafi aiki tare suke fita ya ajiyeta a makaranta ranar da take da lectures ɗin yamma kuma ya ɗauko ta, mota ya siya mata ranar da take ra'ayin driving da kanta sai taje da kanta ta dawo da kanta , akwana a tashi aisha har ta kai aji uku a jami'a matar magaji ta haihu ta haifi ɗa namiji kyakyawan gaske sunan yaron mansoor lokacin Aisha tana ɗuke da ciki na tsawan wata biyar, sosai take samun kulawa daga mijin ta da cikin ya isa haihuwa lokacin suna hutu zasu shiga aji huɗu, hakan ya sa sadiq ya ɗauki hutu wurin aiki suka tafi lagos dan ta haihu a can, cikin yardar ubangiji da komawar su ba da jimawa ba Allah ya sauketa ta samu ɗa namiji kyakyawan gaske mai matuƙar kama da ita, murna wurin sadiq ba'a cewa komai, hakama iyayen aisha da ƴan kurfi sunyi matuƙar farin ciki, da sati ya zagayo, yaro ya ci sunan Alhaji Abdulƙadir suna kiran shi da {shazim} malam yayi matuƙar farin ciki da wannan takwara da sadiq yayi mashi,haka ma aisha taji daɗi sosai,kulawa sosai take samu wurin ummy, da tayi arba'in suka tafi kurfi ita da sadiq,Ibrahim ya so su tafi tare da shi amma makaranta ta hana saboda yana shekarar ƙarshe a jami'a, sun samu tarba ta musamman daga wurin maijidda haka ma magaji da nuraddeen hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma sadiq ba, matar magaji kuwa komawa su kayi tamkar ƙawaye ita da aisha, yaron ta mansoor shekarar shi ɗaya da rabi a duniya, kafin su ka koma lagos Aisha sai da ta zaga gidajen ƴan uwan sadiq, ta kuma je gidan uwani da halimatu, suna komawa lagos basu jima ba suka wuce abuja , haka rayuwa ta cigaba da tafiya Ibrahim ya gama makaranta, sadiq yace ya dawo abuja yayi masters, shazim ya taso cikin kulawa da soyayyar iyayen shi da dangin shi musamman Ibrahim duk abunda ya siya zai ce na Shazim ne, haka ya taso cikin kulawa da gata,da shazim ya isa yaye lagos suka kai shi wurin ummy, har sai da yayi shekara ɗaya a lagos lokacin yayi wayau sosai, ya iya tafiya ga surutu, haka zaka same shi ya tasa hajiya zainab gaba da surutu abu kaɗan yace ummy { da yake shima haka yake kiran ta saboda yaji ammyn shi na kiran ta da haka}
*_WANNAN KENAN_*
Ibrahim ya fara zuwa makaranta Aisha kuma na shekarar ƙarshe, shazim nada shekara uku a duniya sadiq ya ajiye aiki ya kama kasuwanci gadan gadan riba sosai yake samu, cikin ƙanƙanin lokaci ya zama attajirin gaske ya buɗe katafaren company da yake sarrafa kayan masarufi musamman shinka fa, kasuwancin shi na ta haɓaka , ɗaura Ibrahim yayi kan wasu harkokin kasuwancin yana kula mashi da su, gida ya gina mai girman gaske ya kuma biya ma baba, innah, malam, ummy makka , sai shi da aisha, farin ciki wurin su ba'a cewa komai ya sha adu'a wurin su, kafin ya tafi ya tare a sabon gidan da ya gina, da zasu tafi ya ce ma magaji ya dawo Abuja da zama shida matar shi da ƴaƴan shi , da ma gidan da ya gina yayi shine saboda su, magaji yayi godiya sosai ya kuma tattara komai nashi dake kurfi suka dawo abuja shi da matar shi asiya, sunje sun sauke farali, a abuja su ka sauka da ma ta nan suka tafi, sai da malam su kayi sati shi da ummy sannan suka wuce lagos, baba kuwa da innah nan zasu zauna part ɗin su da ban, har da ibrahim da baiyi aure ba part ɗinsa da ban , innah sai nan nan take da sadiq ta ɗauki son duniya ta ɗaura mashi tun bai sakin jiki da kulawar da take nuna mashi har ya fara sakin jiki, abun ba ƙaramin ba nuraddeen mamaki yake ba, yan da ta sauya.
Shekarar shazim 5 sadiq ya sa shi makaranta shi da mansoor aisha ta sake haihuwar ɗa namijin mai matuƙar kama da sadiq, sosai sadiq ya yi murna haɗi da gode ma Allah da kyautar daya bashi, ranar suna yaro yaci sunan baba watau nuraddeen suna kiran shi da { noraiz} baba yaji daɗi,satin noraiz uku da haihuwa asiya ta haihu ita ma ɗa namiji sunan shi mahmud, Ibrahim ya samu mata yayi aure sunan matar turai, yar kano ce amma iyayen ta anan abuja suke da zama, shekarar ta ɗaya ta haifi ɗa namiji mai suna luqman lokacin noraiz da mahmund nada shekara ɗaya da kusan rabi, shazim shidda mansoor bakwai faisala ukku ƙanin mansoor, wani abun mamaki tun da matar Ibrahim ta haihu innah ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa aisha da asiya kamar sunyi mata wani laifi, duk da wannan chanji da take nuna masu hakan bai hana su kyautata mata ba, kuma kan su haɗe yake dan matar Ibrahim ba ruwanta hakama yaran su kansu haɗe yake ko wane lokaci suna tare da juna musamman shazim da mansoor dan ko school tare zaka gansu da ƙanansu faisal da yake ansa shi makaranta shi ma , noraiz ne dai da luqman sai mahmud ba'a kai da sa su ba , sai daga baya aka sa noraiz , luqman da mahmud makaranta, shazim da mansoor kullum sun part ɗin baba kakansu wani lokacin har da su noraiz kullum haka suke in basu part ɗin baba suna part ɗin papah { sadiq} ko hutu shazim zai je lagos tare suke zuwa shida su mansoor luqman ne dai bai taɓa zuwa ba.
_*WANNAN KENAN*_.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau daɗi gobe akasin haka
sadiq ganin duk abokan shi sun tsunduma a cikin siyasa ne ya shi samu baba da batun yana so ya shiga shiyasa ƙin amincewa baba yayi hakan yasa abokan sadiq su kayi zuga suka zo wurin baba dan su roƙe shi akan ya bar sadiq, ai kuwa faɗa sosai baba yayi ma sadiq ya ce kenan dama su suka hure mashi kunne ya ke son shiga shiyasa,dole ta sa sadiq haƙura ganin baba yayi fushi sosai, lagos yaje ya sanar da malam abun da ke faruwa, hakan ya sa malam wanke ƙafa yazo har abuja wurin nuraddeen, tattaunawa suka yi malam kuma ya roƙe shi akan ya bar sadiq ɗin, ba dan hakan ya kwanta ma baba arai ba ya amince,sosai sadiq yaji daɗi, da matakin ɗan majalissa ya fara ,cikin ikwan Allah ya samu,shekarar su uku da fara mulki ya ida ginin estate ɗin daya fara opposite da gidan shi, suna gab da sauka daga mulki da jam'iyar su zata tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa suka tsaida shi, ƙin amincewa yayi dan shi baya da burin yin muƙami mai girma irin wannan,matsa mashi suka yi ba dan ya so ba yace "to shikenan, amma sai yayi shawara da iyayen shi, duk abun da suka ce da shi zaiyi amfani ", ko da ya samu malam da baba da maganar cewa suka yi yayi haƙuri ya yi, ai abu ne mai kyau in sha Allah zasu taya shi da adu'a, yaji daɗin hakan da suka ce ya kuma samu ƙwarin gwiwa, cikin ikwan Allah ana zaɓe sadiq ya samu,daya ci zaɓe sai Ibrahim da magaji suka koma estate da zama,sadiq ya so malam ya dawo abuja da zama