Showing 15001 words to 18000 words out of 127932 words

Chapter 6 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6697

Allah nan da Karfe 5:30 mun iso,shiyyasa na kira ki fada ma ilya  yazo ya dauke ni na kira Yaya bai dauka"
"may be baya kusa ne" Ammy ta fada "to Ammy ki fada ma ilyan"
"yanzu kuwa Allah dai ya kawo ku lafiya"
"Ameen Ammy wallahi harna ƙosa na ganni kusa da ke" "Allah dai ya dawo da kai lafiya" ameen  ya fada,  kashe wayar tayi , mikewa tayi daga kan sallayar,parlor ta nufa a kan sofa ta zauna  , number ilya ta shiga nema cikin wayar ta sai ga fatima ta dawo  daga Islamiyya wurin Ammyn ta nufo tana cewa  "barka  da gida Ammy,  mikike yi zaune ke ka dai a parlor?"
ta fada yayin da take samun wuri kusa da Ammy ta zauna, amsa Ammy ta bata da "number ilya nake nema saboda  zai dauko mai babban suna"
"ya noor ya dawo ne" ta fada tana mikewa harzata nufi upstair Ammy tace " dawo uwar zumuɗi  cewa nayi zai dauko shi bawai ya dawo ba" dawowa tayi tana  turo baki gaba tana faɗin"to Ammy ƙarfe  nawa  zai dawo , Ammy tace"zuwa ƙarfe 5:00 in sha Allah jirgin su zai sauka,  shiyyasa yace a kira mashi ilya yaje ya dauko sa"
"Ammy dan Allah zanbi ilya in zai tafi"
cewa Ammy tayi" to shikenan maza kije " bata ma tsaya sauraron mi Ammy zata ce ba ta nufi dakin ta da sauri, wanka ta fara shiga bata jima ba ta fito sanye da bathrobe shaf shaf tashirya cikin doguwar riga abaya tayi rolling da gyelen  a kanta,  wayar ta kawai da jaka ta dauka ta fice daga dakin inda tabar Ammy nan ta sa meta,   ƙara sowa fatima tayi wurin ta tana fadi "yawwa Ammy na shirya, kin yi ma ilyan magana?"
"A'a bari nayi sai kin shirya tukunnan,ai a kwai sauran lokaci,duka  yanzu ƙarfe  4:00 kuma kinga cewa yayi sai 5:30 jirgin zai sauka"
"Ammy ai da kin yi mashi magana,kinsan fa a kwai nisa Airport din,zamu yi kusan 20 to 30 minutes bamu kai ba fah, kuma ga go slow" Ammy tace "haka ne nasha'afa ne shiyyasa,amma bari na kira ilyan ya fitar da mota sai ku tafi" ta fada yayin da take kiran ilya a waya yana picking  tace " ilya ka fitar da mota za ku je Airport kai da fatima domin dauko mai babban suna yana hanya"
"to Ammy in sha Allah yanzu kuwa zan fito da ita" ilya ya fada da yake shima Ammy yake cewa
"to shikenan ga fatimar nan fitowa" Ammy ta fada hadi da rejecting din kiran, mike wa Fatima tayi tana cema Ammy sai sun dawo
a dawo lafiya Ammy tayi mata sannan ta tashi ta nufi , kitchen innah Asabe ta samu a kitchen din tana gyarashi domin fara shirye shiryen dinner , Innah asabe na ganin ammy  tace " barka da fitowa hajiya, da yawwa Ammy ta amsa mata" kina bukatar wani abune ? Innah asabe ta fada saboda  ganin Ammyn da tayi a kitchen a wannan lokaci " eh kinsan mai babban suna na hanya to shine nake son a daura dinner tun yanzu , kuma shima shazim bai ci komai  ba ya fita ga fatima ita ma kuma,  kinga in aka gama da wuri zai fi ai" innah asabe tace"ah yaufa muna da babban bako,shiyyasa naga fatima ta wuce da gudu dan bata ma lura da niba" Ammy tace "kin san halin Fatima da zumuɗin,ai ina ce mata yana hanya duk tabi ta rude tana can tabi ilya Airport" dariya Innah Asabe tayi hadi dacewa" Allah dai ya kawo shi lafiya"ameen Ammy tace shirye shiryen daura dinner suka shi ga yi..

✨ _SHAZIM_ ✨

 shigowa yayi main parlor bakinsa dauke da sallamada alama baya cikin gidan daga waje yake, su Ammy dake kitchen su ka amsa mashi sallamar, fitowa Ammy tayi daga kitchen din tana cewa
"kai ashe baka gidan, ka kuwa yi waya da ƙanin ka?  ya ce man ya kira wayarka baka dauka ba?"
"Eh na ɗan fita ne tun dazu har bedroom din ki nazo na same ki kina bacci, wayar na silent ne sai daga baya naga kiran sa,  yace man ai kunyi waya akan ki tura mashi ilya ya dauko shi"
eh Ammy ta fada tana komawa kitchen din shi kuma part dinsa ya nufa,bedroom dinsa ya wuce kayan jikin sa ya rage ya nufi toilet  bayan kamar  15 minutes sai gashi ya fito sanye da bathrobe dressing mirror dinsa ya nufa, zama yayi kan stool din dake gaban mirror din, ya jima yana yan shafe shafensa sannan ya nufi wardrobe , shiryawa yayi cikin kana nun kaya riga da wando,wandon baki ne iyakar sa gwiwarsa sai rigar fara mara nauyi mai gajeran hannu, wurin dressing mirror ya koma  feshe jikin sa yayi da turare sannan ya fita  daga bedroom din ya nufi  down stairs parlorn Ammy, dinning ya nufa  ya ga bakomi,  fita yayi daga parlorn ya nufi kitchen wurin su Ammy yana shiga yace "Ammy akwai abinci kuwa?, yunwa nake ji"
"gashi nan ana girkawa saura ka dan mukarsa" Ammy ta faɗa
"gaskiya  Ammy bazan iya jira ba, sosai nake jin yunwar babu wani abu ko da mara nauyi ne?"  Ya tambaya
Ammy ta ce" bari na yanka maka fruit" ta fada tana bude fridge ta dauko fruit ta wanke, yanka mashi tayi ƙanana  ta zuba mashi a ɗan bowl ta mika mashi amsa yayi yana faɗin "nagode sosai Ammy" ficewa yayi daga kitchen din,  main parlor ya koma TV ya kunna yana ɗaukar remote ya chanza channel zuwa TVC news,  zaman shi yayi kan sofa  yana shan fruit yana kallo

🌹~ _KAINAAT_ ~ 🌹

_MURTALA MUHAMMAD INTERNATIONAL  AIRPORT

Mutane ne ke daban daban a cikin airport din wasu najiran time din da zasu hau jirgi yayi yayinda wasu kuma sun zo daukar yan uwan su ne, wasu na a parking lot cikin mota wasu na zaune akan chairs din da aka ta nada domin masu zama.
Motar su fatima ce ta kara so cikin airport din parking lot din dake wurin ilya  ya nufa parking yayi, fatima ce ta fara fitowa sannan shima ya fito, cikin airport din suka nufa in da mutane ke zaune fatima ta nufa, wuri ta samu ta zauna ,  wayar ta da ke cikin bag ce ta fara ringing fito da ita tayi "YA DR" shine sunnan daya bayyana akan screen din wayar, picking call din tayi hadi da sallama,on the other hand na cikin wayar ya amsa mata sallamar " ina wuni ya dr,ya gida ya kwana biyu?" "lafiya lau Alhmdllh Bintalo" turo baki Fatima tayi cikin shagwaba tace" haba Yaya nace fa bana son sunnan, amma ka ƙi ka daina ceman" ta fada tana dan bubuga kafafu, dariya na cikin wayar yayi, ai kuwa nan tashiga yi mashi kukan shagwaba tana cewa "dariya ma na baka koh"
"sorry fatimaaaaaa" ya fada yana jan sunan,Uhmmm kawai tace
sake magana nacikin wayar yayi "bana ce kiyi hakuri ba, ai duk laifin ki ne nace ki bar ceman ya dr nan da kika ƙware wurin kirana da shi, shiyyasa nima nace maki haka, kinga nima na rama kenan,amma kiyi hakuri bazan sake ba kin ji" "shikenan Yaya ya wuce"
"Yawwah koke fa, yasu Ammy kina ina ne haka naji hayaniyar mutane?
amsa ta bashi da " Ina airport,munzo daukar ya noor ne "
" ok yau zai dawo kenan, kice ina gaishe dashi ina mashi ya gajiyar tafiya "
" to zai ji In sha Allah yaya "
"ok take care of your self for me pls, bye" ya fada,itama bye masa hadi da rejecting  call  din, game ta shiga  bugawa a wayar tana a nan zaune aka fara sanar da iso war jirgin 5:30 tashi tayi ta koma inda mutane ke tsai tsaye domin tarbar yan uwan su passengers ne suka fara ɓullowa ta wata kofa da aka rubuta EXIST da manya harafi wacce domin su aka tana de ta,ta kai 5 minutes a nan tsaye, mutane da yawa na rugawa da gudu suna tarbar ƴan uwn su, ita dai sai zare idanu take so kawai take taga ta ina ya noor dinta  zai bullo.  Wani matashin saurayi ne ya ɓullo,sanye yake da ƙananun kaya jeans da T -shirt na company gucci,yana rataye da ɓaksr jaka a kafadar a jikinta anyi rubutu da manyan harrufa in da aka rubuta ADIDAS  da farin fenti, riƙe yake da trolleyn sa yana ja, P-cap ce a kansa sai face mask,Akallah zai kai kimanin shekaru 25 a duniya.
Fatima ce ta rugo da gudu tana fadin ya NOORRR tana nufar wannan saurayin, sakin trolley din dake hannun sa yayi, fa dawa tayi jikinsa tana dariya haɗi da cewa " shine kawani boye fuskanka dan kawai nasha wahala wurin gane ka koh" janye ta yayi daga jikinsa yana faɗin
"Autar Ammy ke dai har yau Allah baisa kinsan cewa kingirma ba koh" fatima tace "haba ya Noor haka ma za kace koh, shikenan tunda baka yi farin cikin ganina ba" ta faɗa tana juyawa zata bar wurin, hannun ta ya riko yana cewa "sorry my yar qanwerh, wasa fa nake maki, kema kin san nayi farin ciki ganin ki autar mu" ya fada yana jan kumatunta, dariya ta saki "koke fah " ya fada yana cire facemask din da ke fuskarshi MASHA ALLAH na fada daganin wannan kyakyawar fuskar ta Noraiz kamannin sa daya da fatima , dan dai shi namiji ne ita kuma mace.
ilya  ne ya karaso in da suke yana washe baki Noraiz  yace "kice tare kike da ilyan Ammy" ya fada yana mikama ilya  hannu domin su gaisa
"ina wuni,ya hanya, ya aka baro mutane turai " iliya ya faɗa,dariya fatima da Noraiz su kayi jin ilya yace wai ya aka baro mutanen turai, amsa mashi Noraiz yayi da
"Alhmdllh ilya,ya gida?" amsawa ilya yayi da "lafiya lau" ilya ya faɗa yana ɗaukar trolley din Noraiz suka bar wurin, parking lot su ka nufa booth ilya ya bude ya saka trolley da jakar Noraiz,shiga su kayi cikin motar Noraiz da ilya na gaba ita kuma fatima na baya, key ilya yayi ma motar su ka bar airport din, hanyar gida su ka nufa suna tafe suna fira Noraiz ne yace
"wai ina ya shazim fatima?" amsa ta bashi da "may be yana gida,dan ni ban jima da dawowa daga Islamiyya ba na biyo ilya"  ok kawai Noraiz yace,daga nan bai sake ce mata komai ba har su ka iso  anguwar su horn ilya yayi a bakin gate din gidan, megadi ne ya bude masu gate din, ciki ilya ya shiga, parking space ya nufa parking yayi, fitowa su ka yi daga motar suka nufi cikin gidan, ilya na biye da su a baya hannun sa dauke da trolley da bag din Noraiz.
Shiga su ka yi cikin gidan bakin su dauke da sallama
da sauri Noraiz ya nufi shazim dake zaune kan sofa, hugging din sa yayi yana faɗin "nayi missing ɗinka yaya sosai"
shafa kansa shazim yayi kamar wani karamin yaro yana cewa " to ai yanzu komai ya wuce tunda gaka ka dawo"
"haka ne kuwa yaya" Noraiz ya fada
Ammy ce ta fito daga kitchen ita da Innah Asabe wurin su su ka nufo Ammy na faɗin
"oyoyo mai babban suna" tashi Noraiz yayi ya nufi Ammy,hugging ɗinta yayi yana cewa "nayi kewar ki sosai Ammy nah"
"nima nayi kewar ka mai babban suna" Ammy ta fada,  Innah Asabe ce ta matso tana cewa "marhabun lale da babban mutum,ya hanya, ya kuma karatu??" Amsa ya bata da "Alhmdllh" ƴan gaishe gaishe suka shiga yi da firar yaushe gamo,sama ilya ya haurawa da kayan Noraiz zuwapart din sa,bai jima ba ya sauko yana sanar da Noraiz ya kai masa kayan part ɗinsa.
godiya Noraiz yayi mashi, ficewa ilya yayi ya koma bakin gate wurin mai gadi dama nan yake zama.
tashi Noraiz ɗin yayi yana faɗin"zan shiga na watsa ruwa na fito,naga time din sallah magrib ya kusa" ya faɗa yayi da yake haurawa upstairs.
Ammy ce tace  "shazim   abincin fa, ko ba yanzu ba?"
"A'a Ammy sai anjima in mun dawo sallar magrib"
"to shikenan" Ammy ta fada tashi yayi ya nufi upstairs shima
Ammy ma da Innah Asabe na su bedroom din suka nufa aka bar fatima ta gyara kitchen da jera abinchi kan dinning tana gama wa itama ta nufi nata bedroom ɗinta,wanka tashiga ( idan tana period takan yi wanka sau uku har huɗu a rana)

✨_NORAIZ_✨

Fitowa yayi daga bathroom sanye da bathrobe   (  part din sa shima ya hadu sai dai bai kai na shazim girma ba, amma dai masha Allah yayi kyau ) dressing mirror  ya nufa,mai kawai ya shafa ma jikin sa ya nufi clothes set dinsa,jallabiya ya dauko black color yasa, wurin kayan sa da ilya ya kawo masa ya nufa, turare ya dauko cikin jakar sa ya fesa ya mai
Ficewa yayi daga part din dama yayi alwala tun a toilet ,  part din shazim dake ku sa da na shi ya nufa.
yana shiga shazim din na fitowa daga bedroom
shi ma sanye yake da jallabiya.
Ficewa kawai su ka yi,masallachin dake can main gate din gidan su ka nufa, ba su ne suka dawo cikin gidan ba sai da su kayi har isha tukun su ka dawo
A parlorn Ammy su ka yada zango,fatima kaɗai su ka samu zaune a parlorn,su na  zama Ammy na fitowa, wuri ta samu ta zauna tana faɗin
"to a tashi ga abinci can najiran ku"  to su ka cemata su na tashi suka nufi dinning Fatima ce tayi serving din su.

✨ _KATSINA_ ✨

Zaune suke kan dinning suna dinner su duka gidan baka jin ƙarar komai sai na plate da spoon ɗin da su ke cin abincin
Su na gamawa abie  da  Abdallah da Mom suka koma kan sofa yayin da su Aairah ke gyara dinning din, suna gamawa wurin su abie su ka dawo,zama su ka yi abie  na tambayar su yaushe zasu fara exam din SSCE "saura 3 weeks abie " su ka bashi amsa "to Allah ya bada sa'a" da Ameen suka amsa  "abie  wace school  zaka kaimu  in mun gama" Aaimah  ta faɗa "ban gane inda zan kai ku ba,ku da ku ke da school a cikin grinku,ai ba sai kun je wani gari ba" abie  ya fada yana tsare su da idanu "A'a gaskiya abie,mu yi primary school da secondary school a nan sannan kuma ace munyi high school a nan, dan Allah abie a canza mana"
"to sai kun gama exam din tukunnan"
"to shikenan abei" chanza firar su kayi zuwa wata, sai kusan 9:30 sannan su Aairah su ka nufi dakinsu saboda sun fara karatun exam ga kuma zuwa school gobe
suna shiga bedroom din su wanka su kayi su ka sanya pajamas din su,books din su su ka ɗauka,sai a round 12:00 sannan su ka yi bacci.
9_10

Sanye suke da uniform din su na school, ko wacce rataye da school bag din ta,  ficewa su kayi daga bedroom din su ka nufi main parlor ,su Mom suka samu kan dinning  suma basu jima da zuwa dinning area ba, gaishe dasu su kayi hadi da samun wuri kan dinning din suka zauna,  abie  ne yace " yau yan biyu an shirya dawuri kenan " amsa suka bashi da " eh abie  "
"to Allah ya taimaka ya ba da sa'a"
da ameen suka amsa, mom  ta miko masu tea  data hada masu godiya su ka mata suna sa hannu suka Karba, basu fi minti 10 ba su ka tashi suna goge bakin su da tissue paper,sallama su ka yi masu, a dawo lafiya su ka yi masu, fice wa su ka yi suna fadin Allah yasa.

Suna ficewa daga gidan school bus ɗin su na shigo anguwar,har bakin gate in da su ke tsaye Bus ɗin ta zo tayi parking, kofar bus dince ta bude shiga su kayi daga ciki su ka nemi wuri suka zauna kusa da wannan friend din ta su Aeesha
Aeesha tace "twin friends yau wace rana kun fito da wuri, kun samu bus first round " ta fada  da  murmushi a fuskar ta " ke dai bari kawai Aeesha sa'a ce kawi yau " Aairah ta fada Aaimah kuwa cewa tayi
"sai kace kema kullum da wuri ki ke zuwa Aeesha " dariya Aeeshar tayi tana faɗin "ai wlh duk da haka gara ni dai "
"bawani nan, wlh kema muguwar let comer ce " Aaimah ta fada lokacin da bus din ke shiga cikin School ɗin,
bus stop bus din tanu fa parking tayi aka bude kofar student nata fita suna nufar assembly ground
Inda ss 3 ke tsayawa nan su Aairah suka nufa annan suka samu sauran yan class din su wanda su ka zo dawuri, gaisawa suka shiga yi.
bayan 30 minutes aka gama assembly kowa ya nufi class din su

✨SHAZIM✨

Saukowa suke daga upstairs shi da Noraiz parlor Ammy su ka nufa,a dinning suka same ta ,  gaishe da ita su kayi Noraiz yace  "ammy ina fatima, naganki ke kaɗai a dinning?"amsa  ta bashi da
"Fatima ai ta wuce school"
"kai!,na manta fah, amma Ammy yaushe take gama wa ne"
" tace man dai next month zasu fara exam,  daga wannan week din ma ta gama zuwa school sai kuma exam"
"Allah ya taimaka ya bada sa'a, yaya" Noraiz ya kira Shazim dake zaune yana sauraron su, da na'am ya amsa mashi  , Noraiz yace "amma dai yaya  fatima a abuja za tayi  university kamar yanda take buƙata idan ta gama secondary school " sai da yayi kusan 5 seconds sannan yace "A'a a nan za tayi  school kusa dabammy" ya fada fuskar sa babu a lamun wasa, hankan yasa dole Noraiz ya kama bakin sa yayi shiru,amma baiji dadin shawarar da yayan nasu ya yanke ba,  saboda  fatima ta ƙwallafa rai akan zuwa abuja saboda sa'ada
"Allah ya taimaka " kawai yace yaci gaba da breakfast din sa,  Ammy duk da  ta fison fatimar  tayi karatu kusa da ita amma sai tace "wai shazim mi yasa ka ke haka ne, tun da kai ka janye jiki da abuja, mi yasa suma ka ke son dole sai sun janye jiki da abuja ne wai, miye ai bun dan tayi karatu a can, duk da ni ma nafi son tayi kusa da ni amma zamanta can zai ƙara maku kusanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login