Showing 99001 words to 102000 words out of 127932 words
gaisa saboda tun da abun ya faru ammy ta dai na fita tana part ɗin ta koda yaushe ita da ƴaƴan ta, ta ɗan samu natsuwa saboda kullum sai malam da ummy sun kira ta sun kwantar mata da hankali sun kuma faɗa mata sunan zuwa hakan yasa ta dai na damuwa sosai taci gaba da adu'a, kullum lawyern sadiq sai ya zo har aka tsai da ranar shiga court, ana gobe za'a shiga court malam da ummy suka zo amma basu sauka a estate ɗin ba sai suka sauka a gidan da sadiq ya fara zama , can ammy taje ta same su ita da su noraiz, anan suka kwana, washe gari da zasu tafi court gida aka bar su shazim tare da mai aikin ammy, suna isa court ba'a daɗe ba alƙali ya zo aka fara gaba tar da ƙara, da lawyer ya fara gabatar da ƙara abun yayi matuƙar ɗagama ammy hankali jin anƙara akan abun da efcc suka faɗa time ɗin da suka zo gida,an mai da zargin kan ana zargin sadiq da cinye hannun jarin abokanan kasuwan cin shi, sannan gomnati na zargin shi da satar maƙudan ƙuɗin da sunan aiki, an kuma kama container biyar da kayan maye da sa hannun shi, alƙali ya buƙaci ganin abokan kasuwan cin sadiq da wanda sune maƙa sudin shigar da ƙarar, abun yayi matuƙar ba ma ammy mamaki , saboda waɗan da suka shigar da ƙarar abokai ne ga sadiq na ƙut da ƙut wasu daga cikin su tun kafin ya shiga shiyasa yake tare da su, haka ƙara ta ciga ba da tafiya duk yan da lawyer sadiq ya so kare sadiq abun ya ci tura dan mutanen sun gabatar da hujuji masu ƙarfi, ammy na ji na gani aka ɓata sunan mijinta bayan ranshi kuma aminan shi,duk wani company na sadiq sai da kotu ta amshe har da wasu gidajen shi, a taƙaice daga gidan shi dake lagos sai estate ka ɗai kotu ta bari, rayuwa tayi ma ammy zafi, taci kuka kamar ranta zai fita, sai da malam da ummy suka yi ta bata haƙuri da nasiha, malam yace ta yita yi ma mijinta da ƴaƴenta adu'a,sun kwantar mata da hankali sun kuma nuna mata mahimmanci haƙuri da ƙaddara, hakan ya sa ta ɗanji sauki a ranta,amma abun na damun ta ba ita kaɗai ba har da malam da su uncle Ahmad dan sun san wannan duk sharri ne, innah kuwa kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha saboda tsabar jin daɗi an saki uncle Ibrahim,kwata kwata bata damu da halin da Ammy take ciki ba, yanke shawara ammy tayi idan su malam zasu koma lagos ƙafarta ƙafarsu kuma da ƴaƴen ta zata tafi komi innah zata ce sai dai tace dan a yan da take ji har kotu tana iya kai ta idan tace zata amshi ƴaƴen daga wurin ta,ko da ta faɗa ma su uncle Ibrahim shawarar data yanke, haƙuri suka shiga bata har da halimatu amma ina, sunyi sunyi amma taƙi haƙura, har zuwa su kayi wurin malam ko zai sa baki ta zauna amma sai yace shima yana buƙatar ta a kusa da shi, ya dai yi masu alƙawarin zata dunga ziyartar su in sha Allah ita da yaran,sun so ko noraiz a bar masu amma malam yace a'a,ba yanda suka iya haka suka haƙura, tsab ammy ta haɗa duk kayanta dana yaranta dake part ɗin su, duk wani abu da tasan tana so sai da ta ɗauka sannan ta fitar da wanda zai lalace taba ma'aikanta estate ɗin sannan ta kashe duk wani abu na wuta, har part ta samu innah tayi mata ban kwana tayi tunanin innah zata ce wani abu amma sai taga saɓanin haka, turai da asiya sun sha kuka da ammy zata tafi ,maƙalewa kairiyya tayi akan dole sai ta bi ammy, haƙuri ammy taita bata, mansoor ma sun shirya da shazim shima har da kukan shi innah har gida ta samu su malam tayi masu sallama, tun da safe suka kama hanyar lagos cike da kewar mutanan abuja.
Tunda suka koma lagos malam da ummy suke bama ammy kulawa ta musamman dan ganin ta kwantar da hankalin ta,hakan baƙaramin kwantar da hankalin ammyn yayi ba ta rungumi ƙaddarar ta, kullum cikin yima mijinta adu'a take da ƴaƴen ta, malam ya saka shazim da noraiz makarantar boko da islamiya,shazim na jss one noraiz kuma primary two, makarantar su ɗaya, su noraiz ƙarfe 12 ake tashin su amma noraiz baya komawa gida sai an tashi su shazim 2:30 pm sannan su tafi tare, da sun dawo wanka suke su ci abinci sai su wuce islamiya, malam ya tsaya tsayin daka akan rayuwar su duk wani abu na rayuwa wanda uba kema ƴaƴen shi malam na masu shi,hakama ummy babu abun da ba ta masu, uncle Ibrahim da uncle Ahmad ma suna matuƙar ƙoƙari akan su sosai su ke basu kulawa duk da basa a tare da su, kuma lokacin bayan lokacin uncle Ibrahim yana kawo masu ziyara har lagos, haka suka taso cikin soyayyar kakannin su da mahaifiyar su,
malam ya so ammy ta ƙara wani auren musamman da uncle Ibrahim ya nuna yana ra'ayin aurenta, malam ya so tayi ko da ba uncle Ibrahim ɗin ba,mutane sun sha zuwa suna nu na ra'ayin aurenta amma tace a'a tafi son ta zauna tare da su malam da ƴaƴen ta, ƙyaleta malam yayi sai ma nema mata aiki da yayi, da farko ƙin amincewa tayi da aikin sai da malam ya zaunar da ita yanuna mata amfanin yin aikin sannan ta amince tafara aikin.
haka rayuwa ta cigaba da tafiya ammy na zuminci sosai da su asiya, suna waya time to time, lokacin da turai da asiya suka haihuwa har abuja taje ita da fatima bata tafi da su shazim ba saboda makaranta.
Akwana a tashi shazim harya kammala secondry school lokacin noraiz na jss one fatima kuma na nursery one, uncle Ibrahim yazo lagos ya roƙi ammy da ta bashi shazim yayi karatu a hannun shi tare da su mansoor, ƙin amincewa ammy tayi da zaman shazim a abuja saboda innah, tana tsoron zaman su tare saboda ta lura kwata kwata innah bata ƙaunar shazim, da kuma shi kan shi shazim ɗin ta san bazai taɓa raga ma innah ba tana tsoron abun da zai biyo baya, babu yan da uncle Ibrahim bai yiba amma tace a'a,ganin bazata amince bane yasa ya sanar da malam da ummy, faɗa malam yayi ma ammy dan mi zatace a'a, Ibrahim ba uba ne a wurin shazim ba yana da ikwan da zai iya mai da shi wurin shi da zama bama karatu ba, ba dan ammy ta so ba ta haƙura,sosai uncle Ibrahim yaji daɗi da ta amince kafin ya tafi sai da ya amshi takardun shazim duka, ko da ya koma abuja addimission ya nema ma shazim da mansoor cikin ikwan Allah suka samu,
kiran ammy uncle yayi ya sanar da ita ya kuma faɗa mata time ɗin da zasu fara lectures, malam ta samu ta sanar da shi yaji daɗi ya kuma kira uncle Ibrahim yayi mashi godiya, ya kuma ce mashi in sha Allah ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim zai zo,hakan ce ta faru ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim ya shirya ya tafi abuja, da zai tafi noraiz harda kukan shi, ko da ya isa abuja mansoor ne yazo har airport shi da driver ɗaukar shi, farin ciki sosai mansoor ya nuna na zuwan shazim ɗin da kuma kasancewa da zasuyi a tare,ko da suka isa estate ɗin tarba ta musamman shazim ya samu daga wurin uncle's ɗin shi da matan su, sosai suka nuna farin cikin zuwan shi har da yaran su, feenah ce dai da innah sai luqman ko a jikin su, lura da hakan da shazim yayi ne yasa ya ɗauke kan shi daga innahr yayi kamar ma bai san da zamanta a estate ɗin ba, feenah kuwa ko kallon banza bata ishe shi ba daga ita har luqman ɗin dama ba son rainin wayau yake ba kuma ita da ma yar rainin wayau ce ga rashin kunya, da zasu fara zuwa makaranta uncle Ibrahim ya sai masu motoci masu kyan gaske, sunyi farin ciki sosai, da farko shi da mansoor kowa tafiyar shi yake shi ɗaya har da haɗi da ba department ɗin su daya ba shazim na karantar medicine and surgery mansoor kuma yana karantar medicine,abokin shazim ɗaya a department mai suna A hashim,shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A hashim, mansoor kuwa yana da abokai ba laifi , sai daga baya mansoor ya ce mizai hana su dinga tafiya tare, da ƙyar shazim ya amince da su rika tafiya tare, ta dalilin haka shaƙuwa sosai ta shiga tsakanin su kowane lokaci suna tare da juna ko a school ko a gida, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma uncle's ɗin shi ba dan dama burin su yaran su haɗa kan su, innah ce kwata kwata hakan bai mata daɗi ba dan ba haka taso ba, har kiran mansoor tayi tana mashi faɗa dan mi zai shige ma shazim, shazim ɗin da ba son su yake ba san da suna yara, shikuma ya ce mata ko ada laifin su ne , su suka nuna ba ss son shi shiyyasa shima ya nuna bai son su, ba ƙaramin haushi maganar mansoor ta ba innah ba hakan yasa ta ƙara jin ta tsani shazim musamman ma yanda yayi fatali da ita a estate ɗin, dan sai ayi sati bata sa shi a ido ba kuma kullum sai mansoor ya zo gaishe da ita da safe amma bata taɓa ganin shazim ba, har ƙararshi ta kai wurin uncle ahmad akan bai zuwa yana gaishe ta, kiran shi uncle ahmad yayi yayi mashi faɗa da nuna mashi hakan bai dace ba, haƙuri ya bashi ya kuma yi alƙawarin gyarawa, tun daga ranar kullum da safe idan mansoor zai je gaishe da ita tare suke zuwa, kullum kuma yaje gaishe da ita ta rinƙa faɗa mashi baƙaƙen maganganu kenan, in tana yi yi yake kamar ma bai san mitake yi ba, hakan kuwa ba ƙaramin haushi yake bata ba, sai daga baya daya lura abun nata ba mai ƙarewa bane yasa in tace mashi A to sai ya kai mata har Z, bata yi mamaki ba tun da daman tasan halin shi tun yana yaro ba ragamata yake ba, wata rana suna dawowa daga makaranta mansoor ya ce suje su gaishe da ita ko da suka je gaishe da ita basu same ta ba tana part ɗin uncle Ibrahim sai su feenah da kairiyya suka samu a part ɗin suna kallo, gaishe da su kairiyya tayi amma feenah mansoor ka ɗai ta gaida, dama tun da shazim ya zo kowa na gaishe da shi amma banda ita, lura da bata gaishe da shi ba ne yasa mansoor rufe ta da faɗa maimakon ta gaishe shi sai tashi tayi tafice tana ƙunƙunai, a kwai wata rana da uncle Ibrahim ya kira shazim part ɗin shi daya je part ɗin ba kowa a parlor sai ita kaɗai da yayi sallama ta ƙi amsawa sai ma ɗago da kai tayi ta kalle shi ta kauda kai tana jan tsaki , abun yayi matuƙar bata ran shi ya tsani rainin wayau da rashin kunya hakan yasa ya ɗauke ta da mari har sau biyu har sai da ta duƙe saboda zafin da taji ai kuwa ba shiri ta nufi ɗakin momyn ta tana kuka, da ta shiga ko da ta sanar da momyn ta taso ƙeyarta tayi har parlorn ta bashi haƙuri, dan dole ta bashi haƙuri tun da ga ranar kuwa ta dai na yi mashi koda kallon banza bare aje ga tsaki.
Lokacin da su shazim su kayi hutu da zai tafi lagos tare suka tafi da mansoor har hutun su ya ƙare suka dawo, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A hashim dan A hashim yana yawan zuwa lagos wurin shazim hakan ne yasa kowa ya sanshi tare da shazim musamman fatima ba ƙaramin son a hashim take ba idan ya zo lagos to tana nan maƙale da shi, tun wata rana da noraiz ya ji ciwo yayi mashi alura shine ta tambaye shi daman ya iya alura kamar ya shazim sai yace mata eh ai su doctors ne tunga ranar ne ta sa mashi suna ya dr.
Cikin ikwan Allah sun kammala degree za suyi joining masters,maganar aure su uncle ahmad suka yi masu amma sai suka ce su ba yanzu ba sai sun kammala masters sun fara aiki tukunnan, ko da suka ce haka su uncle ahmad sunyi na'am da hakan, tunga time ɗin basu sake masu maganar auren ba sun barashi a sai sun fara aikin,business malam yace shazim ya fara kafin su fara masters, da zai fara malam ya bashi jarii, cikin ikwan Allah lokacin da za su tafi business ya haɓaka Allah ya sa ma abun albarka,da zasu tafi malam ya samo wani yaro mai gaskiya da ruƙwan amana ya ɗaura shi akan business ɗin kafin shazim ɗin ya kammala karatu,cikin ƙanƙanin lokaci business ɗin ya ƙara haɓaka,saboda yaron na kula da business ɗin shazim cikin aminci ga gaskiya da ruƙwan amana,
lokacin da suka kammala master business ɗin shazim ya haɓaka sosai dan malam na kula da komai ga kuma hameed hakan yasa business ɗin haɓaka.
lokacin da suka kammala masters lokacin su noraiz shi da mahmud da luqman suna aji biyu a jami'a.
Basu jima da kammala masters ba suka samu aiki su duka,har da A hashim, uncle Ibrahim ya so shazim yayi aiki a abuja amma yace ya fi son lagos saboda business ɗin daya ke hakan yasa uncle Ibrahim haƙura,shazim yana aiki awata babbar asibiti dake nan garin lagos, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shazim yana aiki hameed na kula mashi da business,yanke shawarar yin phd yayi, ko da ya sanar da uncles ɗin shi da malam goya mashi baya su kayi ,amma sai malam ya bashi shawarar yin phd ɗin ta online, sosai hakan yayi mashi daɗi ko ba komi zai samu ya dinga zuwa aiki wani lokacin yana kuma kula da business ɗin shi,cikin ikwan Allah yana kula da aikin shi da business ɗin shi ya kammala phd,ƙarin girma ya samu a wurin aikin shi bayan nan kuma yana visiting wasu hospital ɗin,ganin komai na tafiyar mashi dai dai yasa ya yanke shawarar buɗe privet hopital, daya samu malam da maganar , sosai ya bashi goyan baya, ya kuma taimaka mashi da wani abun wurin gina hospital ɗin, cikin ikwan Allah aka gama gina hospital ɗin , ammy ma ta tai maka mashi da wani abun da zai zuba kayan aiki, sosai yaji daɗi ya kuma yi ma ammy godiya,kayan aiki masu inganci ya zuba, sai da komi ya kammala sannan ya ɗauki ma'ikata,ya kuma ɗaura wani abokin shi mai suna majeed wan da su kayi islamiya ɗaya,daman yayi karatu a harkar lafiya hakan yasa shazim ya ɗauke shi aiki ya kuma ɗaura shi a matsiyin MD na Hospital ɗin,shi ke kula da komai ko da shazim ɗin na nan...
Episode 54_55_
Uncle Ibrahim da uncle ahmad tasa shazim da mansoor gaba suka yi akan su fito da mata suyi aure, amma sai su kace ba yan zu ba, faɗa suka yi masu sosai suka kuma ce sun basu nan da wata huɗu ko dai su fito da mata ko kuma su zaɓa masu da kansu
ganin haka ne yasa mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru ta business ɗin shi kawai yake dan ya ma manta da wata magana ta aure.
ganin mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru yasa uncle Ibrahim shiryawa yaje har lagos ya samu malam da batun, ya kuma sanar da shi sun yanke shawara ko dai ya fito da mata yayi aure ko kuma su aura mashi duk wacce suka ga dama, malam bai bada goyan baya ba akan hukuncin da suka yanke yace su bar shi da shazim ɗin shi da kansa zai sa ya fito da matar , kwata kwata ba haka uncle Ibrahim ya so ba yaso ace malam ya goyi da bayan su, ba dan ya so ba ya amince ya koma abuja, koda ya koma ya sanar da uncle ahmad yan da suka yi da malam faɗa ya kama yana cewa kenan malam ke goya mashi baya shiyyasa da suka yi mashi magana yayi kunnen uwarshegu da su, ya kuma yanke hukuncin dole tare za su yi mashi aure shi da mansoor da su feenah dake shirin kammala makaranta, {su noraiz su gama masters kawai suke jira} ko yana so ko baya so, sosai uncle Ibrahim da innah suka amince da hukuncin da uncle ahmad ya yanke, uncle ahmad da kan shi yakira malam ya sanar da shi cewa sun ƙarama shazim ɗin wata biyu kacal ko dai ya fito da mata ko kuma su aura mashi duk wacce ransu ya so,abun yayi matuƙar ba malam mamaki yan da suka ɗau abun da zafi sosai har haka, shima yana so yaga shazim ɗin yayi aure amma ya fiso abi komi a sannu gudun dana sani.
Ammy da ummy malam ya kira ya sanar da su abun da uncle ahmad ya ce, suma basu ji daɗin hukuncin da suka yanke da zafi haka ba,suma babu abun da suke buri sama da shazim ɗin yayi aure.
Kiran shazim malam yayi ya sanar da shi hukuncin da uncle ahmad ya yanke,sannan yace mashi komi yake ya fito da mata suma sun fi son yayi auren tunda dai dai dai gwargwado Allah ya bashi rufin asiri, to sai ya godema Allah shima yayi aure ya tara nashi iyalin, cewa yayi in sha zaiyi ƙoƙari ganin ya fitar da mata yayi auren, malam yaji daɗi da ya amince zai yi auren ya kuma yi mashi adu'a Allah ya zaɓa mashi mata tagari.
Tun ranar da su kayi magana da malam har tsawan wata biyu shazim bai kawo matar ba bai kuma sake maganar ba, tun su uncle ahmad nasa