Showing 33001 words to 36000 words out of 127932 words

Chapter 12 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6694

na ma su ammy ban kwana sai ya dawo,a dawo lafiya suka yi mashi, suna fita parking lot su ka nufa, mota suka shiga noraiz ke driving, suna tafe suna fira har suka kawo airport, sai da jirgin shazim ya ta shi noraiz ya bar airport ɗin ya wuce abnoor wurin majeed, acan ya wuni sai da yamma ya dawo gida.
kamar yanda shazim yace kwananshi biyar ya dawo daga jos, lokacin da ya dawo har ammy tasa fatima ta shirya kayanta.

Wannan kenan.

sanye yake da jeans da t_shirt, a hankali ya ke taka stairs, wurin ammy dake zaune kan sofa ya nufa, gaishe da ita yayi, cikin kulawa ta amsa mashi tana tambayar "yau batare za ku fita da noraiz ba ne?"
"tare zamu fita yana shiryawa ne" ko rufe baki bai yi ba sai ga noraiz ɗin ya sauko cikin sauri yana faɗin "yaya na shirya, ina kwana ammy"
"lafiya lau" ammy ta amsa, tashi su ka yi su ka fice suna faɗin sai mun dawo, adawo lafiya ammy tayi masu,fi cewa su ka yi zuwa parking lot,
wata sabuwar mota dake compound ɗin gidan su ka nufa,shazim na driving yayin da noraiz ke kusa da shi,buɗe masu gate mai gadi yayi su ka fice, 
sai da suka kawo kwanar da zata kaisu eko shazim ya ɗan kalli noraiz yana faɗin "yaushe za ka fara kula da business ɗin?"
"yaya duk lokacin da kace na fara, sai na fara"
"to shikenan, idan nagama kammala tsara komai zanyi maka magana sai ka fara"
"to shikenan yaya, Allah ya kaimu" da ameen shazim ya amsa  yayin da ya ke shiga cikin eko  ɗin, parking lot ya nufa yayi parking, fitowa su ka yi su ka shiga ciki, yana gaba Noraiz  na biye da shi, har zuwa office ɗin shi, key yasa ya buɗe,ciki suka shiga,
sofa noraiz ya nufa ya zauna, shi kuwa Shazim wurin zaman shi ya nufa  ya zauna, ba ɓata lokaci ya fara aiki, nocking ɗin kofar office ɗin aka yi , izini shazim ya bada , hidaya ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, amsa mata sallamar su ka yi, gaishe da su ta yi sannan ta ɗaura da cewa "doctor patient za su iya fara shigowa?" kai kawai shazim ya ɗaga mata alamar eh yayin da ya ke mayar da kansa kan laptop ɗinsa dake gaban sa ya cigaba da aikin da yake yi 
,ok ta ce haɗi da ficewa daga office ɗin....
  
      KATSINA

Su Aairah ne zaune parlorn mom suna kallo saboda yanzu ba school islamiya sai weekend ( saboda tunda suka gama hadda alaramma ya ware masu azuzuwan yara suna koyar wa su da abokan haddar su) mom ce ta fito daga bedroom ɗin ta, ta nufo parlorn tana cewa "kufa yanzu baku da aiki sai zaman gida" Aairah ta ce "mom ai na wani lokaci ne,da mun tafi school shikenan sai mun dawo"
"haka ne kuma" acewar mom Aaimah ce ta ce "mom wai har yanzu abie bai yanke shawarar school ɗin da zamu je ba" mom ta ce "har yanzu gaskiya banji yace komai ba shi da yayan ku, amma ina tunanin bai gama yanke shawarar in da za ku tafi ba " Aairah ta ce"mom dan Allah kisa baki ya bar mu muje wani gari muyi karatun Please" sai da mom ta ɗan nisa tukun tace "gaskiya bazan yi maku wannan alƙawarin ba, saboda ba shi ka ɗai ba nima kaina nafison kuyi karatu ku nan kusa da ni, hankali na sai yafi kwanciya" Aairah kamar za tayi ku ka tace
"haba mom yaza ki ce haka, duk inda muke Allah na nan zai tsare mu da tsarewar sa " kallon su kawai mom tayi amma bata ce komai ba, tasowa su ka yi daga inda su ke suka matso kusa da ita suna dafa ƙafarta suka ce "Please mom" har suna haɗa baki, sauke ajiyar zuciya mom tayi , sannan ta ce "shikenan zanyi mashi magana duk abun da yace bana da ja"
"yawwa mom, Allah yasa ya amince" mom tace "ameen" Aairah ta ce "mom yaushe abie ya ce zai dawo"
"to ya dai ce kwana biyar zai yi" Aaimah ta ce "Allah ya kaimu, ya dawo dashi lafiya"
amsawa su kayi da ameen....

  Lagos....

Hidaya ce zaune a reception ita da maryam suna magana, maryam ce ta ce
"gaskiya ya kamata ace zuwa yanzu komai ya wuce" hidaya ta ce "baza ki gane bane maryam, abun da wahala "
"haba dai hidaya miye abun wahala a ciki" hidaya ta ɗan nisa sannan ta ce"baza ki gane ba ne maryam, wallahi dana ganshi sai na rasa duk wani ƙwarin gwiwar da nake dashi"
Maryam tace "gaskiya daurewa za ki yi, dama ace na samo number sa ne to da ko a waya ne sai ki faɗa masa, duk da gaskiya zai fi kyau ace face to face ki ka faɗa masa, ko ya ki ka gani "
"haka ne, matsalar bazan iya ba, kuma ina tsoron ya wulaƙanta ni"
Maryam tace "ki cire duk wannan tunanin na cewa wai zai wulaƙanta ki, saboda gaskiya doctor bai yi kama da wanda zai yi hakan ba"
ɗan ajiyar zuciya hidaya ta sauke, sannan ta ce "shikenan, amma dan Allah ki samo man number kawai "
Maryam tace "shikenan zanyi ƙoƙarin hakan, amma mi zai hana ke ki tambayi dr kabir nasan ma zai baki"
hidaya ta ce "kai gaskiya bazan iya tambayar shi ba "
"saboda mi baza ki iya tambayar shi ba?" maryam ta faɗa tana kallon hidaya "kin san muddin na tambaye shi sai yaji ba'asin mi zanyi da number shi,ba wannan ba ma gaskiya bazan ma iya tambayar shi ba"
"haka ne kuma, amma ga shawara mi zai hana ki rubuta mashi sai ki ajiye mashi a office kan table ɗin sa, nasan dole zai gani kuma zai karanta"
"haka ne kuma maryam kin kawo shawara, hakan kawai za'a yi "
"sai kiyi ƙoƙari wurin ganin kin tsara mashi kalamai wanda zasu tafi da imanin shi" maryam ta faɗa tana yar dariya ita ma hidaya dariyar tayi,  wata nurse ce ta nufo wurin su tana faɗin "mi ake tattaunawa ne, naga kuna ta dariya?" juyawa maryam tayi tana kallon wacce tayi magan tana faɗin "sirri ne sister Aisha" gyaɗa kai Aisha tayi  tana faɗin "ah bari na zauna nima ayi da ni" murmushi hidaya tayi, maryam ce tace mata "zauna kuwa kisha sirri" dariya su ka yi su dukan su,fira suka shiga yi akan aikin su,suna nan sai ga victoria da destiny sun fito daga office ɗin da su ke zama, wani kallon banza victoria ta bisu da shi, tsaki maryam taja haɗi da cewa "aikin banza aikin wofi, haka dai zaki ƙare yar wahala kawai" a harzuƙe victoria ta nufo wurin su tana nuna maryam da yatsa tana faɗin "ke maryam kar ki kuskura kice zaki gaya man magana,ki bari sai nayi lokacin ki tukunnan" tashi maryam tayi daga zaunan da take tana kallon victoria tun daga ƙasa har sama, sannan ta ce "idan aka faɗa maki maganar miza kiyi" girgiza kai victoria tayi tana faɗin "wallahi da sai kin gane baki da wayau, dan zan nuna maki cewa ni ba sa'ar yin ki bace " dariya maryam ta kwashe da ita tana ce ma victoria "wallahi  ni har mamaki kike bani wahalalliya kawai" a masife victoria tace "kinga wahalalliya nan bayan ki" ta faɗa tana nuna hidaya dake zaune wacce tayi kamar ma bata san da zaman victoria awurin ba, maryam tace "wallahi kin dai san ko wacece wahalalliya, waye a hopital ɗinnan baisan cewa ke yar wahala bace" a harzuƙe victoria ta matso tana shirin kaima maryam duka dan ba ƙara min haushi maganar maryam ta bata ba, riƙe ta destiny tayi tana faɗin "lafiyar ki kuwa, duka fa ki ke shirin kai mata" victoria ta shiga kiciniyar ƙwace kanta daga riƙwan da destiny tayi mata tana faɗin "rabu dani na koya mata hankali" tana huci, ita kuwa maryam cewa take "dan Allah ki ƙyaleta destiny ta dake ni" fizgewa victoria tayi daga riƙwan da destiny tayi mata sosai ta kaima maryam duka, ramawa maryam tayi ita ma,  sosai faɗa ya kaure tsakaninsu abu kamar wasa, hidaya ce ta riƙe maryam tana faɗin "dan Allah maryam kiyi haƙuri ki ƙyale ta Please"
"haba yaza kice in ƙyale ta baki ganin cin mutuncin da take man ne,duka fa ta kaiman,  ki barni kawai na nuna mata cewa bafa wai ana tsoronta bane" destiny ce tace "please maryam kiyi haƙuri" jan hannun victoria tayi suka bar wurin, saida suka shiga wani corridor sannan destiny ta saki hanun victoria tana faɗin "wai miki damun ki ne victoria, nace ki fita daga harkar su, ki fuskanci abunda ke gaban ki, kin dai san mi gurutu ya ce mana, amma kin zo kina sakarci" ajiyar zuciya victoria ta sauke tana faɗin "wallahi idan naga yarinyar ne sai kawai naji wani baƙin ciki ya turniƙe ni"
"hmmm koma mi kike ji game da ita bai kamata ki bari yayi ta siri ba tunda dai kinsan mi gurutu ya ce"
"shikenan zan kiyaye "
"da dai ya fi maki"destiny ta faɗa haɗi da barin wurin, bin bayan ta victoria tayi...

✨Shazim  ✨

Kayan shi dake kan table ɗin shi ya shi ga tattarawa yana zubawa cikin briefcase ɗin shi yana cema noraiz "tashi to kai,time ɗin sallah yayi"
ok kawai noraiz ya ce, haɗi da miƙewa amsar briefcase ɗin yayi daga hannun  shazim, ficewa suka yi daga office ɗin suka nufi masallaci koda aka gama sallah abnoor suka wuce, suna shiga a compound  ɗin hospital ɗin suka ci karo da majeed wanda dawowar sa kenan daga sallah asr hango sabuwar mota ne yasa shi tunanin koh  shazim ne, tsayawa yayi, sai da Shazim ya gama dai daita parking sannan su ka fito shi da noraiz, ƙarasowa majeed yayi wurin su, gaisawa suka yi majeed na faɗin "noraiz kenan ɗan gidan  yayan sa, ai dama karatun doctor kayi, kaga ni kullum kuna tare  duk da ma yanzu haka ne" ɗan sosa kai noraiz yayi yana kallon shazim can kuma sai ya mai da kallon shi wurin majeed yana faɗin "wallahi kuwa ya majeed abun da naso kenan amma yaya yaƙi yarda" Shazim ne yace "to parrots zaku fara naku surutun koh, to ni kun ga tafiya ta" ya faɗa yana nufara entrance ɗin hospital, bin bayan sa suka yi suna cigaba da firar su har suka iso office ɗin Shazim, sun ɗan jima a abnoor dan sosai shazim ya duba patient anan sai da suka yi sallah magrib da isha  sannan suka nufi gida, koda suka isa gida gaishe da ammy kawai shazim yayi ya nufi part ɗin sa domin ba ƙaramin gajiya yayi ba dinner ɗin sa ma sai dai fatima ta kawo masa nan part ɗin sa, wanka yayi ya shirya cikin kayan bacci  white color, parlor ya dawo akan center table ya samu dinner ɗin sa da fatima ta kawo masa, serving ɗin kansa ya shiga yi yana kammala dinner ya wuce bedroom ɗin sa toilet ya wuce baifi five minutes ba ya fito jikinsa na danshin ruwa alama alwala yayi da brush, wurin wardrobe   ya nufa ya fito da sallaya shimfi ɗawa yayi, shafa'i da wutiri yayi, ya ɗan jima yana adu'a, sannan  ya tashi ya nufi bed ɗinsa ya hau adu'a yayi sannan ya kashe bulb ya kunna bedside lamp..
Episode 18  _19

A kwana a tashi babu wuya wurin ubangiji, har an ciye sati da wasu yan kwana ki da maganar tafiyar su shazim abuja, kullum da kalar excuses ɗin da zai ba ma ammy har  dai suka yi wannan kwana kin basu tafi ba, a gefe kuma innah ta addabi ammy kullum cikin kira take akan miyasa ba su zoba har yanzu sai dai ammy ta bata haƙuri, yau ma tun da sassafe ta kirata, tun da ammy taga kiran innah sai da gabanta ya faɗi tasan da tace mata ba yau ba zata rufe ta da cin mutunci ne, haka nan ta ɗaga wayar kamar yanda ammy tayi zargi hakan ce ta faru dan sosai innah ta cima ammy mutuncin san ranta, baiwar Allah ammy harda kukan ta, tashi tayi daga bakin gado da take zaune ta nufi part ɗin Shazim, bata same shi a parlorn ba hakan ne ya sata nufar bedroom ɗin sa tayi nocking buɗe ƙofar yayi,sanye yake scrub suit da'alama ma ya gama shirin tafiya hospital ne, ganin ammy tsaye bakin ƙofar bedroom ɗin sa yasa shi mamakin ko lafiya ta zo da kanta maimakon tasa fatima ko noraiz ya kirasa, gaishe da ita yayi, amsa mashi tayi da lafiya, daga yana yin da ta amsa mashi yasan cewa gaskiya ba lafiya, domin tun da yake da ammy bai taɓa ganin ta cikin irin wannan yana yin da ya ganta ciki ba yanzu, kafin ya sake cewa wani abu ya ji tace "wai ni kam shazim yaushe ka zama mara jin magana ne, wai har ace nizan saka abu amma kafi ƙarfin kayi abun da nake so koh" kallon yayi ammy yayi da mamaki jin abun da  tace danshi a iya sanin shi baisan mi take nufi ba dan shi harga Allah ya manta sunyi wata magana ta zuwa abuja "ammy dan Allah kiyi haƙuri wallahi ban san akan mi kike magana ba" wani irin kallon ammy ta bishi da shi tana cewa"watau saboda kagama rainani shiyyasa ka manta da maganar da mu kayi da kai koh, wai nikam Shazim wane irin yaro ne kai maganar zuwa abujar ce ka manta saboda ka raina mutane koh" sai yanzu ya ma tuna da wata maganar tafiya dan shi duk a tunaninshi ammy ta bar maganar ganin ta kwana biyu bata sake yi mashi maganar ba "dan Allah ammy ki daina cewa haka ta yaya zan raina ki,dan Allah kiyi haƙuri wallahi yana yin aiki.... " bai ƙarasa faɗar maganar da zai faɗa ba ammy ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu tana cewa "da kata man bana son jin wani excuse naka, umarni nake baka ba shawara ba kashirya gobe tun da safe ku tafi " cikin rashin jin daɗin  hukuncin da ta yanke yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri sai jibi " tsawa ammy ta daka mashi tana faɗin "wallahi kaji na rantse gobe za ku tafi in dai na isa da kai,sannan kamar yanda su fatima za su yi sati biyu kaima sai kayi shi ,  in kuma ban isa ba zaka iya yin duk yanda ka ga dama" tana gama faɗar haka ta juya tafice daga part ɗin, komawa Shazim yayi cikin bedroom ɗin shi ya zauna bakin bed yana dafe kansa dan harga Allah baya son tafiyar nan gashi ammy tayi fushi, bashi da wani zaɓi banda ya shirya kawai gobe su tafi ko hakan zai sa ta sauko daga fushin da tayi dashi, ammy na fita daga part ɗin shi main parlorn ta nufa, noraiz da fatima ta samu kan dinning suna breakfast gaishe da ita su kayi, amsa masu tayi tana tambayar su "kun shirya kayan ku da nace ku shirya? "fatima tace "eh ammy saura kaɗan ingama shiryawa yawale nake jira ya kawo kayan guga sai na gama" ammy ta ce "ok anjima zai kawo daya kawo kishirya su yau" da to fatima ta amsa,  mai da kallon ta tayi kan noraiz tana faɗin "kai fah ka shirya naka "
"a'a ammy, wai ba anfasa tafiyar ba " kallon shi kawai ammy tayi bata ce komai ba, "wallahi ni ammy da kin haƙura da maganar tafiyar nan, dan ni wallahi bana son zuwa ko dan saboda wannan tsohuwar, tayi ta zagin mutum bayan ba wani abu mutum yayi mata ba, tana faɗin wai dama ba sonta kike ba shiyyasa muma bamu sonta, wai da papah na raye bamu isa muyi nesa da ita ba " katse shi ammy tayi ta hanyar ɗaga mashi hannu tana cewa
"ya isa haka,  kar in ƙara jin kace wani abu inba so kake yanzu nan ranka ya ɓaci ba" shiru noraiz yayi ganin kamar ran ammy ya ɓaci.

shazim ne ya sauko daga part ɗin sa ya nufo main parlorn, fuskar shi cike da damuwa,  zuwa yayi wurin  ammy ya durƙusa gaban ta yana faɗin "dan Allah ammy kiyi haƙuri " kau da kai tayi kamar ma bata son ganin shi tayi banza da shi, haƙuri ya shiga bata amma ko ta ɗaga kai ta kalle sa, tashi  yayi daga durƙuson da yana faɗin"dan Allah kiyi haƙuri, na wuce office" ko yanzu bata ɗaga kai ta kallesa ba, noraiz ne yace "yaya bazaka yi breakfast ba" ganin shazim ɗin ya nufi hanyar fita batare da ya kalli dinning ba "na ƙoshi" shine kawai abun da ya cema noraiz, ficewa yayi daga parlorn ko da ya shiga motar shi ya daɗe bai tada motar ba gaba ɗaya baya jin daɗin fushin da ammy ta ɗauka da shi, sai da ya kusan 15 minutes a motar bai tafi ba sannan yayi mata key ya bar gidan ko gaisuwar da megadi keyi mashi shi da ilya bai amsa ba ɗaga masu hannu kawai yayi ya fice..
a parlorn kuwa noraiz ne ya taso daga kan dinning ya dawo kan sofa kusa da ammy yana faɗin "ammy wai mike faruwa, naga kamar kina fushi da yaya lafiya?" amsa ammy ta bashi da "ba komai tafiya ce bai so kuma dole sai kun yi ta" noraiz ya ce "dan Allah ammy ki janye maganar tafiyar nan, ni ban san miyasa ki ke son sai munyi wannan tafiyar ba,kinsan halin innah bawani son mu take yi ba kema kin sani,su uncles ne kawai suka damu da rayuwar mu lokacin da muke buƙatar  kulawar su" ammy tace "ya isa haka,dama kai da shazim na lura halin ku ɗaya, to tafiyace sai kunyi ta gobe ma bawai jibi ba kunji na faɗa maku"
"ammy gobe fa ki ka ce"
"ƙwarai kuwa gobe nace, idan kuma ban isa ba sai inji "noraiz ya ce "kin isa ammy, Allah ya huci zuciyar  ki , in sha Allah ba zamu sake cewa komai ba game da wannan tafiyar,yanzu zamu fara shirya kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login