Showing 96001 words to 99000 words out of 127932 words
lokacin daya zo yi mashi fatan alkairi daya ci zaɓe amma ƙiri ƙiri malam ya ƙi amincewa, baba ma da farko cewa yayi sadiq ya bar shi anan gidan shi amma sadiq ya ce a'a ya fi so ya zauna tare da shi yanda zai riƙa bashi shawara, sadiq ya fara mulkin shi cikin adalci mutane na jin daɗin mulkin shi,aiki ya nema ma Ibrahim da magaji dan tun dawowar shi abuja sadiq ya ne ma mashi admission ya jona karatu sai dai iya kar shi degree saɓanin Ibrahim da ke da master's ,business ɗin shi kuwa ya ɗaura wani aminin shi daya ke da amana, lokacin daya kusa gama zagayen farko na mulkin shi , Allah yayi ma nuraddeen rasuwa mutuwar da ta girgiza ahalin ga ba ɗaya musamman sadiq ya fi kowa fita hayyacin shi, sun shiga alhinin mutawar nuraddeen kamar mi, malam yaji mutawar aminin shi kamar mi, lokacin da aka yi adu'ar bakwai maijidda tace zata koma estate da zama wurin su magaji, ba yanda sadiq bai yi da ita ba amma ta ƙi zama ko da takaba ta gama amma ina ba dan ya so ba ya sa aka kaita, time ɗin da akayi arba'in ɗin nuraddeen matar Ibrahim ta sake haihuwa ta samu ɗiya mace kyakyawa mai suna hawa'u innah kenan suna kiranta da feenah,innah taji daɗi da Ibrahim yayi mata ta kwara ai kuwa ta ɗauki son duniya ta ɗaurawa feenah,bayan haihuwar feenah da sati biyu asiya ma ta haihu, ita ma ɗiya mace ta haifa mai suna kairiyya, watan nuraddeen tara da rasuwa za'a sake sabon zaɓe sadiq ya bar gidan gomnati ya koma gidan shi inda ya fara zama, awannan zaman ana saura sati ɗaya zaɓe Allah yayi mashi rasuwa, ta dalilin haɗarin mota, sunje wani ƙyauye ne a hanyar su ta dawowa su kayi haɗari wasu a nan take suka mutu sadiq kuma sai da yayi jinyar kwana biyu sannan Allah yayi mashi rasuwa ,mutawar sadiq ta girgiza dan gin shi kamar mi, aisha ta shiga tashin hankali mara misltowa da rasuwar sadiq hakama ƴaƴan ta sunci kuka kamar ransu zai fita duk da bawani wayaune da su ba sosai har dama dama shazim, kusan zaucewa aisha tayi, malam ma ya shiga alhini wanda ya fi na lokacin mutuwar nuraddeen , ummy taci kuka kamar mi dan ba ƙaramin son sadiq take ba tana mashi kallon babban ɗanta.
A estate akayi zaman makokin shi har aka yi kwana bakwai, laulayin ciki Aisha ta fara na tsawan wata biyu sai bayan rasuwar sadiq cikin ya bayyana , ta sha kuka kamar ranta zai fita, tana tausayin abun da zata hai fa zai taso batare da ya san waye mahaifin shi ba, ko da maijidda taji labarin cikin aisha baƙin ciki kamar ya kashe ta, ta fara nuna ma aisha tsana da tsangwa ma, hakan ne ya sa aisha ta ce zata koma lagos da zama, amma si malam da ummy suka ce ta bari ta gama takaba sannan, haka ta haƙura har ta kammala takaba, amma da zata tafi sai Ibrahim da magaji suka roƙeta akan dan Allah ta zauna har sai ta haihu sannan saita koma lagos ɗin, hakanan ta haƙura ta zauna ba dan ta so ba, dan kwata kwata yanzu bata jin daɗin zama da innah, ta ware ta su asiya kawai take so su da ƴaƴan su ta ɗauki karan tsana ta ɗaurama su Shazim ba hali su shiga cikin ƴan uwan su ko su je part ɗin ta tafara kyarar su kenan da hantarar su, ta kuma sa su mansoor tsanar su babu hali su raɓu da juna, tun abun bai damun Aisha har ya koma yana damun ta, har ta kai da samun innah dan ta bata haƙuri ko tayi mata laifi ne batare da sanin ta ba , amma sai innah ta rufe ta da masifa wai tayi mata rashin kunya, haƙuri kawai aisha ta bata, lokaci ya shuɗe har cikin aisha ya shiga watan haihuwa, a lokacin ma ta so ta koma lagos ta haihu a chan amma ƙiri ƙiri innah ta ce bata isa ba sai dai ta tsaya ta haihu a nan in ya so daga baya bayan ta yaye abun da ta haifa sai ta tafi tabar masu ƴaƴan su, maganar innah ta girgiza Aisha ba kaɗan ba tun tana boye ma malam da ummy irin zaman da suke yi ita da innah har ta kasa haƙuri ta kira ummy tana kuka ta zayyane mata duk abun da ke faruwa tun daga mutuwar sadiq har zuwa yanzu, abun yayi matuƙar ba ma ummy mamaki dan ita bata san halin innah ba kallon mutuniyar kirki take mata ashe ba haka take ba, ko da ta sanar da malam shima abun ya bashi mamaki dan bai taɓa tuna nin haka daga wurin ta ba, haƙuri suka bata akan tabi komi a sannu in sha Allah komi zai wuce kuma baza su bari a rabata da ƴaƴan ta ba, Ibrahim yana bata kulawa sosai , hakan ya sa ta kwantar da hankalin ta taciga da kula da ƴaƴan ta , shazim tun da ya lura da innah bata son shi da mahaifiyar shi, kuma su mansoor ma basa son su yanzu sai kawai ya yanke shawarar fita harkar kowa dake estate ɗin , ko part ɗin su ya dai na zuwa, da tare su ke tafiya makaranta dasu mansoor amma ganin yan da suke takura mashi shi da noraiz ya sa ya dai na tafiya tare da su, yasa ammy ta ba ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan makullin motar ta yana kai su, abun yayi matuƙar bata ran innah, ta tasa aisha da bala'i tana son raba zumunci, ta kuma amshe makullin motar daga hannun drivern, ran shazim ya ɓaci da abun da innah tayi, ai kuwa har part ɗin ta yaje ya ɗauke key ɗin motar lokacin tana cikin toilet wanka su mansoor kuma na parlorn zaune dama cikin drawer ta sa shi,innah na fitowa feenah ta faɗa mata shazim ya shigo mata ɗaki kuma ya ɗauki key,mamaki abun ya ba innah ba shiri ta fice sai part ɗin Aisha tun daga bakin ƙofa ta fara masifa tana zage zage aisha na zaune kan kujera ita da mai aikin ta tana matsa mata ƙafafunta dake ciwo ta ji haya niyar innah, ta na shirin tashi innah ta shigo ta hau bala'i tana zagin ammy, haƙuri ammy ta shiga bata dan bata san mi tayi mata ba, suna nan sai ga shazim ya shigo innah na ganin shi ta shaƙo wuyan rigar shi tana faɗin
" ɓarawon banza ɓarawon wofi,bani key ɗin da ka ɗauko ɗaki na munafuki"
gaban ammy ne ya faɗin jin abun da innah tace, shazim kuwa cike da masifa ya ce
"wallahi ni ba ɓarawo bane, kuma key bazan ba da ba tun da ba naki bane "
suman tsaye ammy tayi jin rashin kunyar da shazim ke ma innah, mamaki da tsoro ne ya kama innah jin abun da shazim ya ce mata, yaron da ko yatsa kasa mashi a baki bazai tauna ba amma shine yau yake faɗa mata magana cike da rashin kunya, katse mata tunani yayi ta hanyar figewa daga riƙwan da tayi mashi ya nufi up stairs ya haye, bin shi kawai tayi da kallo har ya ɓace ma ganin ta, ammy tace
"dan Allah kiyi haƙuri innah zan amshi key ɗin na maido maki"
fashe wa da kuka innah tayi tana faɗin
"munafuka nasan ke zaki zuga shi yayi man rashin kunya, kuma wallahi ki sani dani kike magana"
tana gama faɗar haka ta fice daga part ɗin...
Episode 52_53_
Innah na fita ammy ta wuce bedroom ɗin ta, noraiz ne ya shigo yana kuka, har zai nufi ɗakin ammy sai ya fasa saboda maganar shazim daya ji yana ce mashi"lafiya kai kuma kake kuka, waya dake ka ? " cikin muryar kuka noraiz ya ce "su ya mansoor ne da luqman " balbale shi da masifa shazim yayi danmi zai tsaya luqman ya dake shi bayan ƙaninshi ne, shiru noraiz yayi, tsaki shazim ya ja haɗi da cewa "suna ina? " noraiz ya bashi amsa da "part ɗin uncle Ibrahim " shazim bai ce komi ba ya kama hanyar fita daga part ɗin ya fice, yana fita part ɗin uncle Ibrahim ɗin ya nufa, luqman da feenah ka ɗai ya samu zaune a parlor suna kallo, bai yi wata wata ba ya hau luqman da duka sai da yayi mashi jina jina sannan ya kyale shi yana kuka, feenah ce ta miƙe tana faɗin "ya shazim dan mi zaka dake shi" buge mata baki shazim yayi yana faɗin "rufe man baki koke ma na haɗa da ke " kuka ta kama yi tana faɗin Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na faɗa ma dady da innah"
kwata kwata feenah bata da kunya ko ko ko alama, kuma hakan ya samo asali daga wurin innah saboda mugun son feenah take kamar mi, ita ta shagwaɓata, ta kuma zugata akan duk wanda ya dake ta tace bata yafe ba idan bazata iya ramawa ba, hakan ya sa ta taso a sangarce ga rashin kunya iri iri feenah ta iya ta , abu ƙaɗan tace innah ko faɗa dadyn ta yayi mata tana kuku zata faɗa ma innah, ita kuma tai ta bala'i,saɓanin kairiyya da ba ruwanta, kuma tana son su noraiz dan kusan kullum tana part ɗin ammy,ita ba ruwanta shiru shiru ce, mari shazim ya kaimata ta ruga da gudu tana kuka ta shige bedroom ɗin momyn ta,yazo fita yaci karo da mansoor da faisal zasu shigo part ɗin, cakumo wuyan rigar mansoor yayi, faɗa sosai ya kyaure tsakanin su har sai da momy {turai} ta fito ta raba su, mansoor na kuka saboda ciwan da shazim ya ji mashi, wuce wa shazim yayi zuwa part ɗin su, yana tura ƙofa yaci karo da ammy tsaye , "daga ina kake? " shine abun da ammy tace, shiru yayi bai bata amsa ba,jin yayi shiru ne yasa ta sake mashi tambayar, shiru ya sake yi , saukar mari kawai yaji a kumatun shi, abun da ammy bata taɓayi mashi ba, rufe shi tayi da faɗa sosai,tana gamawa ta juya, yana dafe da kumatu yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri " wuce wa tayi batare da ta kalli inda yake tsaye ba, binta yayi har ɗaki yana bata haƙuri sai da ƙyar tace ta yafe mashi kuma ya ɗauko key ɗin daya ɗauko ɗakin innah ya kawo mata, da to ya amsa haɗi da ficewa ya bar ɗakin, key ɗin ya ɗauko ya bata, ƙarar buɗe main ƙofa sukaji da ƙarfi, sai kuma hayaniya, fita ammy tayi zuwa parlor, innah suka gani ruƙe da hannun feenah su luqman na bayanta tana ta zazzaga masifa, uncle Ibrahim ne ke bata haƙuri yana faɗin
" dan Allah innah kiyi haƙuri"
"wlh ba zan haƙura ba, yan da ya dake su wlh sai na rama masu "
ammy ce tace "mike faruwa ne? "
tun kafin ya bata amsa innah tayi saurin cewa " munafuka annamimiya, kina iya cewa baki san mi wannan fitsararen ɗan naki yayi ba, bayan ke kika sa shi munafuka kawai "
muryar shazim suka ji yana cewa "gaskiya innah ki dai na ce ma ammy na munafuka dan ba munafuncin da tayi maki, dukan noraiz su kayi ni kuma na rama mashi, kuma wlh suka ƙara dukan shi sai nayi masu mafiyin haka tun da ba jakin su bane "
tsawa uncle Ibrahim ya daka mashi yana cewa " kai baka da hankali ne shazim, innar kake faɗa ma wannan kalaman, kar na sake jin bakin ka "
innah tace "ai da ka barshi yayi man abun da uwar shi ta koya mashi, na san nan gaba har duka na tana iya sa shi tun da ba sona take ba"
uncle Ibrahim yace "kar Allah ya nuna mana hakan, dan Allah kiyi haƙuri ki koma part ɗin ki"
tasa ƙeyar su feenah tayi zuwa part ɗin ta tana tafiya tana zagin shazim,Aisha tayi tsaye ta kasa ko motsi,
uncle Ibrahim ne yace "dan kiyi haƙuri da halin innah, karki sa abun a zuciyar ki kinga dai halin da kike ciki,ce mashi ta bakomi nagode haɗi da nufar part ɗin ta, faɗa tayi ma shazim har da duka, tana faɗin saboda zuwa makaranta yayi abokai marasa kunya shine zai zo gida yana ma manya rashin kunya, ta kuma gargaɗe shi kar ta sake jin yayi faɗa da wani cikin estate ɗin,
cemata yayi to, bawai dan hakan ya shigeshi ba, ya zame ma yaran gidan abun tsoro dan ko kallon da bai yi mashi ba kayi mashi to zai hauka da duka ne ba ruwanshi, tun ammy na mashi faɗa har dai ta zuba mashi ido tana adu'a Allah ya shirya shi, dan komawa yayi mar kunyar ƙarfi da yaji har jira yake wani ya tsokane shi ko noraiz, dole tasa yaran tsoron shi.
Wata rana wasu mutane suka zo da ga hukumar efcc, har part ɗin ammy wai ana zargin marigayi Abubakar da satar kuɗin gomnati,dan haka ammy ta tattaro duk wani takardun dukiyar sadiq ta basu tun daga kan filaye har zuwa na company, abun yayi matuƙar bama ammy mamaki haka ma su uncle Ibrahim,ai kuwa kaca kaca ammy tayi masu ta kuma ce "babu wanda ya isa yasa ta bada koda allura ce daga cikin dukiyar sadiq, mutumin da yake hukunta duk wanda aka samu da laifin sata shine zaku ƙullama wannan sharrin , kuma abun ta kaici bayan ba ranshi, wallahi Allah bazai bar kuba"
wani daga cikin mutanen ne yace " hajiya ki kwantar da hankalin ki, mu bamu zo dan rigima ba aikin mu kawai muke yi, muna so ki fito mana da duk wani takarda daya shafi Abubakar in ba haka ba zamu sa jami'ai su duba mana"
ammy ta ce" sai dai kuyi duk abun da zaku yi amma ni bazan ba ku komai ba, tun da na san ƙarya kuke munafuncin ne kawai "
ganin dai da gaske bazata yi masu abun da suke so ba ya sa suka miƙe suna faɗin " to shikenan tun da haka kika ce, Ibrahim mu zamu wuce, amma bawai hakan na nufin baza mu sake dawowa ba " suna gama faɗar haka suka fice da harara ammy ta raka su, har inda suka yi parking Ibrahim ya raka su sannan ya dawo part ɗin ammy, magana ya fara yi ma ammy yana cewa "ina so ki fahimce ni "
"ina sau raron ka "ɗan nisawa yayi sannan ya ce " ina so ki gane cewa tun da ki kaga an turo su to daga hukumar su ne, kuma ba sharri zasu yi ma yaya ba dole akwai abun da mu ba mu sani ba, amma ina so kiyi haƙuri mu bi komi a sannu ko dan halin da kike ciki, in sha Allah komi zai dai dai ta " ko mi akayi sai yace saboda halin da take ciki bai da wata magana bayan wannan
"to shikenan Allah ya shige mana gaba kuma zan yi magana da lawyern sadiq, tun da a high court yake aiki " uncle Ibrahim ya ce "hakane ni da kaina zanyi magana da barrister, ba sai kin kira shi ba " sun ɗan jima suna tattaunawa ta yan da zasu ɓulloma al'amarin, uncle Ibrahim na barin part ɗin ya kira barristern sadiq ya faɗa mashi duk abun da ke faruwa,sannan ya samu uncle Ahmad ya faɗa mashi lokacin da suka zo baya gida, ammy ma ta kira su malam ta sanar da su,lallashinta su kayi,ko da su uncle Ibrahim suka sanar da innah abun da ke faruwa cewa tayi to sai mi su ɗauki haƙƙin mutane su ba su mana , sadiq ɗin waliyyi ne shi da bazai iya satar ƙuɗin mutane ba , abun yayi matuƙar basu mamaki dan basuyi tsammanin jin haka daga wurin ta ba, kwana uku da zuwan efcc ammy ta haihu ta haifi ɗiya mace kyakyawa mai matuƙar kama da noraiz, farin ciki wurin ammy ba'a cewa komai dan tana matuƙar san ɗiya mace,kwanan ammy biyu da haihuwa turai ita ma ta haifi ɗiya mace kyakyawa, farin ciki wurin uncle Ibrahim ba'a cewa komai, duk wani abu da uba zai yima ɗiyar shi sai da yayima babyn ammy da tashi,da ranar suna ta zagayo aka sama babyn ammy fatima babyn turai kuma sa'adatu suna kiranta da sa'ada.
Shiru har tsawan wata uku efcc basu dawo ba kuma basu shigar da ƙara ba.
watan fatima da sa'ada biyar da haihuwa kwatsam sai ga sammaci kama uncle Ibrahim da ga court efcc sun shigar da ƙara, hankalin kowa yayi matuƙar tashi musamman uncle Ibrahim da akayi arresting, Innah sai kuka take tana ma ammy masifa uncle Ahmad na bata haƙuri akan tayi shiru , amma ina sai zagin ammy take tana cewa
mijinta yaje yayi sata shine zata liƙama ɗan ta, wallahi duk abun da ya samu Ibrahim sai ta gane bata da wayau
Allah sarki ammy ban da kuka babu abun da take,noraiz ma sai kuka yake ganin mahaifiyar shi na kuka shazim kuwa in ban da haɗiyar zuciya babu abun da yake, zazzaɓi ne ya rufe ammy bayan ta shiga part ɗin ta,wayar ta shazim ta ɗauka ya kira malam ya faɗa mashi abun da ke faruwa, hankalin malam yayi matuƙar ta shi sosai, ya kuma cema shazim in sha Allah suna nan zuwa shi da ummy.
innah taci kuka kamar ranta zai fita ta tsine ma ammy yafi aƙira akan laifin da bana ta ba, takuma ƙara jin tsanar ta, turai ma sosai taji zafin ammy in ta tuna saboda laifin sadiq aka kama mijin ta duk da bata nuna mata a zahiri ba,kwana biyu da kama uncle Ibrahim uwani da halimatu suka zo daga kurfi su da ƴaƴan su , har suka yi kwana ɗaya da zuwa ammy bata san sun zo ba, dama halimatu ce mai zuwa wurinta to innah ta hana, sai washe gari da safe ta shigo part ɗin ammy suka gaisa, sai a sannan ammy ta san da zuwan su, daga ranar kullum sai halimatu ta shigo sun