Showing 105001 words to 108000 words out of 127932 words

Chapter 36 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6721

tayi sa'a samun abun hawa, lokacin da dr ya ƙara so bakin gate ɗin har mai adaidaitan daya ɗauke ta  yabar wurin, dafe kan shi yayi yana faɗin
" wai mi kike so ne hidaya? dan Allah kar ki zautar da ni " haka yayi ta sambatun shi shi ka ɗai a bakin gate da dai ya gaji, komawa yayi cikin hospital ɗin direct office ɗin su ya nufa, a bakin ƙofa ya samu maryam ta fito, tsaida ta yayi yana faɗin
"please maryam kayan hidaya za ki ɗauko man "
"dr lafiya dai, mi ya samu hidayar, yanzu muke tare da ita dr shazim ya kira ta  "
"ba komai ki kawo man ina office" yana faɗa ya wuce office ɗin shi 
ok kawai tace haɗi da komawa cikin office ta tattaro kayan hidaya ta nufi office ɗin dr kabir da wayarta a hannun tana dialing number hidaya amma bata shiga.
Tana yin nocking yana buɗe ƙofar, miƙa mashi jakar hidayar tayi tana faɗin " dr gashi, amma mi ya sameta ina ta kiran wayarta bata shiga "
Amsar jakar yayi yana faɗin " bata jin daɗi ne ta tafi gida"
"dr ai da kabari sai na tafi mata da kayan "
"A'a ki barshi kawai zan kai mata kafin na wuce gida "
"to shikenan Allah ya bata lafiya " da ameen ya amsa, wuce wa yayi ya barta anan tsaye sai mamaki take azuciyar ta tana faɗin
" mi ya samu hidaya yanzu yanzu, Allah dai yasa ba wani abu bane ya haɗa ta da dr shazim ba dan ta san abun da zai sa hidaya tafiya a wannan lokacin dole yana da alaƙa da shazim tun da shine ya kirata" 
A zahiri kuma tace "Allah dai yasa lafiya " office ɗin su ta koma tana cigaba da dialing number hidayar amma har yanzu bata shiga daga ƙarshe ma jin wayar tayi a kashe, hankalinta ya ɗan tashi jin wayar a kashe kuma
"tao wai mike faruwa da hidaya ne?, amma zanje gidan inji ko lafiya nake kiranta bata ɗauka" haka tai ta jefa ma kanta taambaya tana haɗa kayan ta ita ma.
Da ya bar hospital ɗin wani shopping mall ya nufa,parking yayi ba tare da ya shiga ba wayar ya fiddo yayi dialing wata number wanda ya kira na picking sallamar da yayi kawai ya amsa ma shi sannan yace
"ina waje "
shine kawai abunda   yace yayi rejecting kiran, bayan kamar 5 seconds sai ga wani matashi ya fito hannun shi ɗauke da wani madaidaicin kwali ya nufo motar dr kabir, yana iso wa dr kabir ya buɗe mashi gefan shi , saka kwalin yayi ya maida ƙofar ya rufe, zagayowa yayi wurin dr yace
"a sauka lafiya ranka ya daɗe"
da Ameen dr ya amsa haɗi da yima motar key ya bar harabar wurin.
A bakin gate ɗin gidan yayi parking, fitowa yayi haɗi da zagayawa, jakar  hidaya da kwalin daya amso ya ɗauka ya nufi gate ɗin, ƙofar da ke jikin gate ɗin yayi nocking, mai gadi ne ya buɗe ƙofar, kallon dr kabir yayi yana faɗin
" ranka ya daɗe barka da zuwa, an wuni lafiya, ai da kayi horn sai na buɗe maka "
"lafiya lau, kar ka damu wuce wa zanyi,  dan Allah wannan saƙon nake so ka ɗan miƙama hidaya"
"to shikenan yallaɓai,amma da ka shiga "
"karka damu , yanzu dai amshi kayan ka kaimata "
ya faɗa yana nuna ma maigadin jakar, amsa mai gadin yayi yana faɗin
"shikenan  ranka ya daɗe sai anjima" hannu yasa a aljihu ya ciro  5k ya miƙa ma mai gadin yana faɗin sai anjima, hannu mai gadin yasa ya amsa yana yi mashi godiya.

Wurin motar shi ya koma ya shiga,reverse yayi ya bar anguwar, a hankali yake tuƙi har ya kawo wani ƙaton gida yayi horn a bakin gate, maigadi ne ya leƙo yana ganin motar ya koma da gudu haɗi da buɗe mashi gate ɗin, ciki ya shiga da motar a compound yayi parking,yana gama parking ya fito ba tare da ya kashe motar ba a buɗe ya bar ƙofar haka ma key a jiki ya bar shi ya nufi main entrance ɗin gidan.

Gida ne bani da gida ba, babba ne sosai dan ya fi gidan su shazim girma nesa ba kusa ba, part part ne gasu nan bila adadin, tsayawa faɗa maku yana da gidan yake ɓata lokaci ne.
Ma aikatan gidan ne su ka shiga gaishe da shi, hannu kawai yake ɗaga masu, dan a yanayin da yake ciki ba zai iya magana ba.
Da sauri wani matashin saurayi ya nufi motar ya kashe  haɗi da buɗe back seat ya ciro mashi briefcase ɗin da laptop, key ɗin ya zare ya rufe motar da sauri ya bi bayan shi.
parlor ne ƙato da royel sofas a ƙalla za su kai set huɗu milk color.
Up stairs ya nufa  matashin saurayin nan na biye da shi da kayan shi da ya kwaso masu, suna zuwa wani ɗan corridor matashi saurayin ya ɗan da kata yana faɗin
" ranka ya daɗe ina zan kai maka kayan? " 
"main parlorn na" shine kawai abun da ya faɗa yayin da yake tura wata ƙofa da ke cikin corridor,juyawa saurayin yayi ya nufi wata ƙofa dake can ƙarshen corridor ya shiga wani parlor,ba laifi yana da girma kamar dai yanda main parlor yake,komai na cikin shi brown color ne, ya tsaru iya tsaruwa, kan tow seater saurayin ya ajiye mashi kayan ya fice.

Ƙaton parlor ne sosai dan da ƙaɗan parlorn da suka fara shigowa zai nuna mashi girma da tsaruwa, wata ƙofa dake facing ɗin shi ya nufa haɗi da tura ƙofar ya shiga,nan ma wani parlor ne ɗan madai daici, lab coat ɗin dake jikin shi ya cire ya yi wurgi da ita kan sofa sannan ya cire top ɗin da ke jikin shi ita ma yayi jifa da ita ya koma daga shi sai dogon wando da riga long sleeve, wani ta ƙofa ya nufa tura ta yayi ya shiga ciki, masha Allah nace da ganin wani danƙareren bedroom dake ɗauke da royel bed mai kyan gaske, komai na cikin bedroom ɗin white color ne, faɗawa yayi kan bed ɗin yayi kwanciyar rub da ciki, ya rasa mike mashi daɗi a duniyar  nan, gaba ɗaya ji yake ya tsani kan shi, magana ya shiga yi da zuciyar shi " miyasa hidaya zaki yi man haka,gaba ɗaya kin gama  zubar man da mutunci, dan mi zaki ƙi ƙarɓar soyayya ta kice wai  shazim kike  so, wai da mi shazim ɗinnan ya fini ne da har zata iya cewa tana son shi amma ni ta ƙi ƙarbar soyayya ta" haka ya cigaba da saƙawa yana kwance wa, daya juya ƙaɗan ya buga tsaki.
turo ƙofar bedroom ɗin akayi wata mata ta shigo, sanye take da less ɗin kin doguwar riga, hannun ta riƙe da kayan shi da ya zubar a parlor, bakin bed ɗin tazo ta tsaya
"Auta mike damun ka ne ka zubar da kaya a parlor sannan ka zo nan ka kwanta, lafiya dai ko?? "
shiru yayi bai ce komai ba, bai kuma juyo ba daga kwanciyar da yayi, kayan da ke hannun ta ta ajiye gefan bed ɗin, sannan ta hau kan bed ɗin, hannu tasa ta shiga shafa sumar kan shi, cikin lallashi ta fara magana

"wane mai tsautsayin  ne  ya taɓa ɗan gidan momy yau ya kwana a kulle, faɗa man wanene yanzu na ɗau mataki a kan shi kaji ɗan gidan mama,ko na kira yayyen ka ne " shiru yayi nan ma baice mata komai ba

"yanzu Auta har  akwai ɓacin ran da zaka shiga kayi fushi da momyn ka tana magana kayi banza da ita" sai a lokacin ya ɗago da kanshi ya kalle ta ba tare da yace komai ba, murmushi tayi tana faɗin
"mike damun bugun zuciyata ne,faɗa man naji yanzu nayi maganin sa?"
hawaye ne suka kwararo daga idon shi, ɗuƙar da kai yayi ƙasa, da sauri ta sa hannu ta taro fuskar shi tana

" ya salam Auta mi zan gani haka, waye ya ɓata maka rai ne har haka yasa ka zubar da hawayen ka,  maza ka faɗa man ko waye yanzu na ɗau mataki saboda saman auta koka da yayi "  faɗawa yayi jikinta yayi hugging ɗinta so tightly, fashewa yayi da kuka kamar wani ƙaramin yaro, shafa bayan shi ta shiga yi

" dan Allah ka dai na wannan kukan ka faɗan man abun da ke damun ka, ko so kake nima ka sa ni kukan,kasan kukan ka tashin hankali ne a gare ni"
ajiyar zuciya ya shiga saukewa, cikin muryar kuka ya fara magana ba tare da ya raba jikinshi da nata ba
"momy ashe wahalar banza nake bani take so ba " yana faɗin haka ta fahimci akan hidaya yake magana dan komai na shi na rayuwa ta sani ko shawara zai yi da ita yake yi babu wani sirrin shi da bata sani ba, ba ya iya ɓoye mata komai.

"ban gane ba, itace tace maka bata sonka?"
raba jikin su yayi , komawa yayi ya kwanta ya ɗaura kanshi saman laps ɗinta, shafa sumar kanshi ta shiga yi
" ka kwantar da han kalinka babana nasan tana sonka, babu wata ƴa mace da zaka ce kana so a duniyar nan ta ƙi amincewa da kai,in sha Allahu hidaya matar ka ce bata da wani miji a duniyar nan bayan kai"

"to ai momy yau da kunne na naji bani take so ba "

"ba kai take so ba, to wa take so?"
"momy shazim wai take so bani ba "
"shazim dai "
"Eh momy, shi tace tana so "
"tofa ana wata ga wata, to shi shazim ɗin yana son ta ne"
"A'a momy, ai ya san ina sonta kuma ma anyi mashi mata a familyn su "

"to ai ta kwana gidan sauƙi tun da shi ɗin ba wai yana sonta bane kuma har kace an yi mashi mata "

"amma momy ta zubar man da mutunci, kullum faɗi nake tana da kamun kai tana da natsuwa amma ta buɗe baki tace ta son wani bani ba "

"kar ka damu ina tuna nin bata san kana sonta bane ai baka faɗa mata ba  "
"momy na faɗa mata kin manta ne "

"yanzu dai ka kwantar da hankalin ka, ni zan san yarda zanyi zan sanar da dadyn ku , in sha Allah za ka Aure ta kar ka damu kaji " ta faɗa tana share mashi hawayen da suka ɓata mashi fuska, murmushi tayi haɗi da jan gemun shi tace

"babana kafa girma ka rage wannan yarintar ko so kake ɗiyar tawa ta raina man kai ne " ta faɗa haɗi da   lakuce mashi hanci, murmushi yayi haɗi da cewa
"momy ai bazan yi a gabanta ba, ke kaɗai zan mawa tun da daman ke maganin kuka na ce"
"duk da haka dai, kar ka haifa man jikoki masu kukan banza kamar kai "
murmushi yayi
"momy har kin fara maganar jikoki, duk wanda ke a gaban ki "
"to babana idan ban yi maganr su ba maganar mi ka ke so nayi, jikoki kuma ai na babana na da ban ne  "
"haka ne my lovely mom"
" ta shi kaje ka watsa ruwa, abinci na nan kan dinning yana jiran ka "

"momy ni a nan zanyi" 

"to shikenan tashi kaje kayi, amma ka kusa daina shigar man toilet "

"kai momy, saboda mi?"
"saboda ka girma, ka kusa aje iyali "
ta bashi amsa haɗi da miƙewa ta bar bedroom ɗin, tana fita shima ya tashi ya nufi toilet ɗin, bayan kamar 15 minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe.
Ficew yayi daga bedroom din yanufi parlor ,zaune ya samu momy ita da su ya mustafa ( yayyan shi, su ba kwai  ne y'ay'an momy ,maza biyar mata biyu ,dr kabir shine karamin kanin su shi ka dai ne bai yi aure ba ,ya mustafa shine babba sai umar,khalid,aliyu,safeenah,
azeema sai dr kabir,duk acikin gidan  maza suke zaune da matan su   )
binshi da kallo su ka yi , ya mustafa ne yace " yau ina ganin ikwan Allah ,wai kai da man har yanzu baka girma ba ,wanka a bedroom din momy ko kunya "
  turo baki yayi gaba yana fadin
" wallahi da na san kuna nan da ban fito ba ,haka nan ku hana mutum saket "
rike baki ya umar yayi yana fadin " Allah ya shirye  ka junior"
( da yake haka su ke ce mashi  )
"Ameen" ya ce yana murguɗa ma ya umar baki kamar wata mace ,tsaki ya khalid ya ja ba tare da yace komai
ya aliyu kuwa cewa yayi "gaskiya ku kyale shi ya huta,idan bai ma momy da mu  ba wa zai mawa ,ku barshi ya shana wata rana sai labari"
Matsowa kabir yayi kusa da Aliyu yana fadin
"yawwa ya Aliyu shiyyasa nake sonka"
"mu kuma baka son mu ko saboda muna fada maka gaskiya  " ya khalid ya fada
Ya mustafa yace " ai shima jirgi daya ya kwaso su shi da Aliyu,dama ce kawai shima bai samu ba"
"fadi kanka tsaye ,da ace ni ne shi sai nayi abun da yafi wanda yake yi Allah" ya Aliyu ya fada ,momy dai na gefe sai murmushi take tana kallon su.
Ya Aliyu ne yace " kaji Autan momy ta shi kaje ka sa kaya ka dawo na san baka ci abinci ba ,kazo da kai na zan baka a baki "
"Allah dai wadaran naka ya  lalace ,yanzu wannan katon zaka ba abinci a baki amma dai gaskiya kaji kunya Aliyu "
"A'a ya khalid bari ,wane irin naji kunya ba wata kunya da naji kanina ne fa  ko ba haka ba momy " ya fada yana kallon momy dake bin su da ido
"rabu da shi Aliyu na lura adawa yake da babana"
"haba momy wane irin adawa ,wannan katon ne zai ba abinci a baki "
"Ai ba haramun ba ne ,idan kai bazaka bashi ba ,sai ka bar mai bashi ya bashi "
"Allah ma ya kiyaye na zauna ina ba junior abinci a baki sai kace ban da aikin yin "
"to ni zan bashi idan kai bazaka iya ba,je ka sa kaya kaji Autan momy  " ya Aliyu ya fada yana kallon dr kabir

gwalo dr kabir yayi ma ya khalid ,tsaki ya khalid din yaja yana fadin

" wallahi kaji kunya kato da kai kana abu sai kace wata mace "
Dariya su ya mustafa su kayi suna fadin

" da gaske dai adawa kake da shi "

Tsaki ya khalid yaja ba tare da yace masu komai ba ,kwata kwata baya son ganin kabir na taɓara  abun haushi yake bashi .

Shaf shaf ya sa kaya ya dawo parlorn samun su yayi zaune a dinning su duka har da dady wanda shigowar shi kenan ,kusa da dady yaje ya zauna ,shafa kanshi dady yayi yana fadin
"likita bokan turai yau da wuri aka dawo kenan? "
"Eh dady"
"sannu to ,ya aikin?"
"Alhmdllh dady"
"to masha Allah" dadyn ya fad'a
"juyo na baka abincin kar ya khalid yaji dadi"
ya Aliyu ya fada yayin da yake d'ebo abincin a spoon ,bude baki  kabir yayi ya Aliyu na ba shi a baki dady ma na bashi sai murmushi yake yana ma ya khalid dake jifan shi da harara  gwalo ,karshe dai daya gaji da ganin abun kunya  jifan shi yayi da spoon da sauri ya duke yana fadin " wayyo Allah dady zai cire man ido "
"wallahi zan sa k'afar wando d'aya da kai khalid idan baka fita harkar junior ba "
"haba dady baka ga yanda ya  k'ara sangar cewa ba kuma fa duk dan kuna goya mashi baya ne "

"An goya mashi bayan " momy ta fad'a ,shiru khalid yayi bai sake cewa komai ba, dr kuwa sai murmushi yake  kamar wani zautacce

Haka suka cigaba da lunch suna fira cikin ni sha di ,da suka gama ma kan sofa su ka koma momy ke sanar da dady maganar hidaya, haƙuri ya ba dr ya kuma ce in sha Allah zaiyi iya bakin ƙoƙarin shi ganin ya amsar mashi auren hidaya, da dady ya faɗi haka da sauri ya rungume shi yana faɗin
"na gode sosai dady " saboda sangarta da rashin kunya har da su rawa.
Su ya mustafa nayi mashi dariya, ya khalid kuwa ban da tsaki babu abun da yake.

Wannan ahali akwai nisha ɗi a tattare da rayuwar su, Allah ya dawwamar da farin cikin a gare su, hidaya ina taya ki murna idan kika shigo wanna ahali mata ga junior ɗan gata momy da dady da su ya khalid 😜.
Haka suka cigaba da fira cikin nishaɗi sai da lokacin sallah yayi tukun suka nufi masallaci.

_*✨HIDAYA✨*_

"Wai hidaya zaki buɗe ƙofar nan ne ko sai ranki ya ɓaci"

zuwa tayi ta buɗe ƙofar idanuwan ta duk a kumbure alamar taci kuka, tana buɗe ƙofar ta koma ciki, bin bayan ta ummah tayi tana faɗin
"yanzu abun da ki ka yi kina ganin shi ne dai dai ko, wai zaki faɗa man abunda ke damunki ko sai na kira Abban ku"

"Ummah kai na ne ke man ciwo "

"Ƙarya kike hidaya,har ni zaki ɓoye ma damuwar ki  "

"umma ki yarda da ni kaina ke man ciwo "
Shikenan shine abun da ummah ta faɗa
"kije to ki watsa ruwa kizo ki ci abinci ki sha magani " ummah na gama faɗa ta fice ta bar bedroom ɗin, komawa tayi ta kwanta a rigingine kanta na kallon ceiling , tayi shiru gaba ɗaya ta rasa mike damunta, dagaske dr kabir yake anyi ma shazim mata a familyn su,hawaye ne suka gangaro mata daga cikin idanuwanta, hannu tasa ta share
turo ƙofar ɗakin akayi, tsaye tayi tana binta da kallon daga baya ta shigo, zama tayi kan bed ɗin, ta dai ji almar shigowar mutum amma bata san waye ba duk a tunanin ta umma ce, sai da taji shiru ne yasa ta tashi daga kwanciyar, zuba mata ido maryam tayi tana kallon ta
"lafiya kike man wannan kallon " ta faɗa cikin kasalalliyar murya
"idan ma da akwai abun da yafi kallo kin cancanta hidaya,yanzu kan dr kike son sama kanki ciwan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login