Showing 63001 words to 66000 words out of 127932 words
zuwa parlor ta wuce su mansoor zuwa ɗakin ta, shazim yana gama shan tea ɗin wayar sa ya saka cikin pocket ya nufi main parlor, kallo ɗaya yayi ma mansoor da Fiddausi dake parlorn, hararar shi mansoor yayi, ɗaga kafaɗa shazim yayi yana faɗin "aikin banza " haɗi da kama hanya ya fice daga part ɗin, yana fita a waje ya ci karo da uncle Ahmad zai shigo, gaishe da shi shazim yayi, amsa mashi yayi yana faɗin "wai ina kaje ne tun ɗazu bayan kasan yau su uwani zasu zo, ai ko ba komi da ka tsaya kun gaisa tukunnan " amsa shazim ya bashi da "naje wurin Abdallah ne saboda wani aiki da muke "
"Ok to kashiga part ɗin innah ku gaisa da su suna can " da to ya amsa haɗi da nufar part ɗin, ciki uncle ahmad ya shiga lokacin har mansoor ya koma part ɗin shi ita kuma Fiddausi tana ɗakin kairiyya a nan zata kwana, sama ya wuce zuwa nashi bedroom ɗin.
Shazim tsayawa yayi a bakin part ɗin Innah kamar zai shiga kamar bazai shiga ba daga bi sani dai ya shiga bakin shi da sallama ciki ciki, in ba ka kalli bakin shi ba baza ka taɓa cewa yayi sallama ba,gwaggo Halima ce da innah sai Aunty zainab da ke ba yaron ta abinci sai maryam a parlorn, amsa mashi sallamar da yayi Aunty zainab tayi, bawai dan taji sallamar da yayi ɗin ba sai dan sanin ba zai taɓa shiga wuri ba tare da yayi sallama ba, wuri ya samu kan sofa ya zauna, kallon gwaggo Halima yayi yace " ina wuni Aunty "da yake haka yake kiran ta
"lafiya lau shazim, ina ka shige tun ɗazu nake ta cigiyar ka "
"na je wani ɗan aiki ne "
"Agogo sarkin aiki, a nan ɗin ma baka huta ba" murmushi yayi ba tare da yace komi ba, Innah ce tace "da yake uwar ka kawai ka sani shiyyasa ka gaishe da ita "
"to idan ban fara gaishe da ita ba ke zan gaida "
"wah ni, ai ba jiran ta ka gaisuwar nake ba "
"Koma kina so ba wai zan gaishe da ke ɗin bane " harara maryam ta maka mashi jin yan da yake mai da ma innah magana yan da ran shi ya so
"bana ma so, gida cike yake da ƴaƴan albarka, kuma sun gaishe da ni, ba taka nake jira ba " har ya buɗe baki zai mai da mata martanin maganar da tayi, gwaggo Halima ta katse shi ta hanyar cewa " shazim ya su Ammyn ku da malam " tayi hakan ne dan ta hana shi ba innah amsar maganar da tayi dan tasan abun da zai fito daga bakin shi ba mai daɗi bane
"Ammy na lafiya haka ma malam "
"masha Allah "
Aunty Zainab ce tace "shazim ya kwana biyu, ya lagos "
"lafiya lau alhmdllh, ya gajiyar tafiya "
" ba gajiya" jan shi da fira gwaggo Halima tai ta yi har su ka ɗan ɗauki lokaci, tashi yayi zai tafi, da katar da shi gwaggo tayi ta hanyar cewa " ka jira yaya ta fito ku gaisa " kallon maryam tayi "maraya je ki kira ta su gaisa " tashi tayi ba tare da ce ƙala ba ta nufi bedroom ɗin innah, "zauna shazim kafin ta fito"
da to ya amsa haɗi da komawa kan sofa ya zauna yana amsar yaron Aunty zainab, tun da ya shigo yaron ke miƙo mashi hannu alamar ya ɗauke shi,amsar shi yayi haɗi da tambayar ya sunan shi "gaskiya shazim mutuncin ka ra gage ne yanzu bama ka san sunan shi ba kenan "
gwaggo Halima ta ce " a'a kar ki ga laifin shi,yaron da ba'a nan kika haife shi ba, kuma ma duka yaushe kika dawo ƙasar ne "
Aunty Zainab tace " haka ne, sunan shi Aayan "
" Allah ya raya " yace da Ameen Aunty zainab ta amsa,
Maryam samun gwaggo Uwani tayi kwance kan gadon innah amma ba bacci take ba, zama maryam tayi bakin bed ɗin tana faɗin "mamy wai shazim ne ya shigo, Aunty halima tace kizo ku gaisa "
"ɗan rainin hankali sai yanzu yayi lokacin zuwa kenan" maryam tace " ko dai aka ce ya zo ba "
"haka ne kuma yanzu haka wani cikin su yaya ne yace yazo ya gaishe da mu"
" ba ma mamaki " tashi gwaggo Uwani tayi tana faɗin "bari naje na same shi" ta faɗa haɗi da kama hanya ta fice, bin bayan ta maryam tayi.
firar suke cikin kwanciyar hankali shazim dai na sauraron ya ƙagara ta fito dan ya samu ya koma part ɗin su bacci ne cike da idanun shi.
gwaggo Uwani ce ta fito marya na bayan ta, a bakin ƙofar ɗakin innah ta tsaya tana faɗin " isashe ai nayi tunanin kafi ƙarfin gaishe da mutane "banza yayi da ita yana yi ma Aayan wasa duk da ya san da shi take ba tare da ya kalli in da take tsaye ba
"Eh dole kayi banza da ni saboda ga mahaukaciya sabon kamu na magana "ko kallon in da take yanzu ma bai yi ba,tsaki yaja a ranshi yana faɗin "da ya san masifa zatayi mashi da bai tsaya ba " masifa take ta in da take shiga ba tannan take fita ba, da dai ya gaji da jin banbamin da take, ajiye Aayan yayi kan sofa haɗi da kallon gwaggo halima yace "sai da safe "
"Allah ya tashe mu lafiya " da ameen ya amsa haɗi da kallon Aunty zainab yace "sai da safe "
" to Allah ya kaimu " ficewa yayi yana jiyo muryar gwaggo Uwani tana zazzaga masifa kamar ta ari baki " zanyi maganin abun da yake damun ka mara mutunci "
gwaggo Halima tace "gaskiya yaya kina abun da bai da cewa, yaron nan fa har ya tashi zai tafi na tsayar da shi dan ku gaisa amma kin fito kin rufe shi da faɗa mara tushe bare asali "
"Ok ni zaki ce ma haka saboda wannan yaron, ai da kin sani da baki tsayar da shi ba da kin bar shi yayi tafiyar shi "
"gaskiya yaya ki chanza, dan ko ɗazu banji daɗin abun kika yima Fatima ba, ya rinya ƙarama mi tasani game da abun da kike nufi "
"Wai sadiya magana kike son faɗa man saboda waɗannan yaran ko mi kike nufi "
"ni ba magana nake son faɗa maki ba kawai dai ina son ki san abun da kike aikatawa bai dace ba kwata kwata "
" a'a maganar dai kike son faɗa man a kan yaran da ban sani miye haɗin ki da su ba "
"Amma nayi mamaki yaya da ilimin ki kike faɗin haka,bayan kin san jinin da ke yawo a jikin ki shike yawo ajikin su amma kike faɗin haka "
"jinin da dai ke yawo a jikin ki amma ba jiki na ba "
"Ai kuwa ko kin ƙi ko kin so jinin da ke gudana ajikin ki shi ne dai ajikin su"
"Wa ni Allah ya tsari gatari da saran suka, ni bani da wata alaƙa da su "
"Ke kuwa ke da alaƙa da su, saboda uban su da kika haɗa uba da shi "
"dan na haɗa uba da uban su ba ahi ke nuna cewa sun zama jinina ba"
"Wannan kuma kin faɗi san ranki ne "
"Wai sadiya miye ribar ki idan kin goyi bayan yarannan ne, wata riba gare ki "
"ni kuwa ke da riba, saboda zumunci Allah ne yace ayi shi kuma na riƙe shi da hannu bibiyu "
"wahalar banza kike, yau da ace uban nasu kafin ya bar duniya ya bar wani abun arziƙi to da nace kina yi ne dan ki samu wani abu a wurin su "
"ko mi nake inayi ne dan Allah, kuma maganar mahaifin su dake, ina tuna nin ko bai bar komi ba da zai rasu ina tananin sai da ya rufa maki asiri ke da ƴaƴan ki da ƴan uwanki kafin ya bar duniyar"
"Wai dakata sadiya, gori kike son yi man kan abun da sadiq yayi man "
"Ni ba gori nake maki ba saboda ba ni nayi maki ba, ina tuna maki ne da abun kika manta "
"gorin dai kike man sadiya kuma na gode "
"duk yan da kika ɗauka yaya, Allah dai yasan mi nake nufi " Innah tace "wallahi kin bani mamaki sadiya, ƴar uwar ki kike ma gori akan abun da wani yayi mata, miye dan gan takar ki da shi da har zaki ba ɗe baki kiyi ma ƴar uwar ki ta jini gori "
"mama sai dai ku ƙi fahimta ta amma ni ba gori nike mata ba, kuma innah ki dai na cewa ba ni da alaƙa da su, duk duniya basu da wasu da zasu nuna a matsayin dangin uban su bayan mu, muma haka kamar yan da zamu nuna su mansoor a matsayin ƴaƴan yan uwan mu haka suma dole mu nuna su a matsayin haka"
gwaggo Uwani tayi cab tace" ki dai nuna su amma ba dai ni ba, bari kiji sadiya na san ko mi yasa kike wannan faɗe faɗen "
Aunty Zainab ce tace " dan Allah mama Aunty kuyi haƙu ku dai na wannan gan ganun ba dan ni ba "
"taya zaki ce haka zainab, gara dai ta ƙarasa yi man gorin da ta fara "
"Ni dai ko mi ki kace naji, kamar yan da muke zuminci lokacin da yake raye yanzu ma bazan fasa ba "
maryam tace " haba mama dan Allah karku zama ƙana nan yara a gaban mu, mu ya kama ta ace munyi haka kunyi mana faɗa amma ba wai ku ba" ta shi gwaggo Halima tayi ta fice daga part ɗin zuwa na uncle ahmad, bedroom ɗin mama ta nufa, tsit ta same shi ba kowa mama na ɗakin abba, hasken ɗakin ta kashe haɗi da hawa kan bede ta kwanta zuciyar ta duk ba daɗi.
Lokacin da ya bar part ɗin innah part ɗin su ya nufa, a main parlor ya zauna kan sofa, gaba ɗaya ji yake zaman abujar nan kamar yana kan ƙaya yanke shawara yayi gobe ko da da yamma ne sai ya bar abuja ya koma lagos, ya ɗan jima zaune sannan ya tashi zai nufi sama zuwa bedroom ɗin shi, karab idanun shi suka sauka kan mutum dake zaune kan dinning ya duƙar da kai kan table , tashin farko bai gane ko waye ba sai da ya matsa dinning area sannan yaga ashe macece kuma fatima, ƙara sa wa yayi haɗi da kiran sunan ta amma ko motsi bata yi ba, bubbuga table ɗin yayi still bata motsa ba abun ya ɗaure mashi kai wane irin bacci ne take yi haka har bata ji kiran da yayi mata ba, gaskiya ba lafiya, hannu yasa ya ɗago da kanta, ya salam ya furta ganin ko numfashi bata yi, ruwan da ke kan dinning ɗin ya ɗauka buɗe marfin jirkar yayi ya ɗan zuba a hannun shi shafa mata yayi a fuska amma bata motsa ba, sai da yayi haka kusan sau uku sannan ta ja wani dogon numfashi "mi ke damun ki? " ya jefa mata tambaya, biji biji take kallon shi saboda nauyin da idanun ta su ka yi mata, sake jefa mata tambayar yayi, ware idanun ta tayi a kan fuskar shi, "da ke nake magana, mike damun ki "
da ƙyar ta iya furta "babu komi yaya, nayi dinner ne shine bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba "
"ok da man a nan kike dinner "
"a'a yau ne nayi a nan "
"Zaki faɗa man mike damun ki ko sai na ɓata maki "
"da gaske nake yaya ba komi " tsawa ya daka mata yana faɗin "ina wasa da ke ne, zaki faɗa man ko sai na ci mutuncin ki " fashewa tayi da kuka " Aunty Ilham ce ta mare ni "
"ta mare ki da kika yi mata mi keken "
"Wai dan momy tace na kira su su zo su ciki abinci, to shine sai tayi magana ni kuma ban ji ta ba, dan kawai nace banji ta ba shine ta mare ni Aunty feenah ta shaƙe man wuya "
"Ok shine kika zo nan kina kuka har sai da numfashin ki ya ɗauke ko "
"ba kuka nayi ba, bacci ne ya ɗauke ne "
"ok yayi, kinsha magani "
"Eh sa'ada ta kawo man "
" to yayi, ina so gobe tun da safe ki haɗa duk wani kayn ki dake can part ɗin gobe zamu koma lagos ina fatan kin ji ni"
"Eh yaya naji "
"ta shi ki wuce kije ki kwanta " da to ta amsa haɗi da nufar ƙofa zata fita " ina za ki "
"zanje na kwanta ne "
"Ok shine kika kama hanyar fita "
"Zanje ɗakin sa'ada ne "
" ba can zaki ba, ɗakin ki zaki wuce " da to amsa haɗi da nufar sama ta shiga ɗakin ta bata taɓa kwana a cikin shi ba, tashi shima yayi ya nufi na shi bedroom ɗin,a jiye wayar shi yayi kan bed ya shiga toilet ta ɗauro alwala, carpet ya shimfiɗa ya shiga gaba tar da nafilfilo da yake yi duk dare, bayan ya gama light ɗin ɗakin ya kashe haɗi da hawa gadon shi ya kwanta, bacci ya ɗauke shi cikin ƙan ƙanin lokaci
*WASHE GARI *
Bayan ya dawo daga masallaci ɗakin fatima ya fara liƙawa dan ganin a wane hali take ciki, zaune ya same ta kan carpet ta gama sallar subhi, gaishe da shi tayi, amsa mata yayi yana faɗin "ya kike jin jikin ki yanzu "
"lafiya lau"
"to masha Allah, ki ƙara shan maganin ki " da to ta amsa mashi, ta shi yayi ya bar ɗakin ya nufi nashi, wayar shi ya ɗauka ya kira ammay ya sanar da ita yau zasu dawo, cewa tayi sai dai shi ya dawo yau amma ban da fatima,bai faɗa mata cewa fatimar bata jin daɗi ba ya dai roƙi ta bar su su dawo yau amma tace a'a, ganin bazata haƙura bane ya sa shi yi mata sallama, mai da akalar kiran yayi ga malam bugu ɗaya malam ya ɗaga yana faɗin "likita bokan turai ka shige abuja ba a ko jin ɗuriyar ka "
"ai insha Allah ina nan dawowa yau "
"Allah ya nuna mana "da ameen ya amsa yana faɗin "na kira ammy na faɗa mata yau zamu dawo ta ƙi amincewa wai sai dai ni na dawo ni kaɗai "
"To ai ba wani abu bane dan ka baro su can, sai su dawo da kan su "
"ba wai barin su bane matsala malam, su gwaggo Uwani suna kuma kasan halin ta da ya ranta shiyyasa bana son su zauna musamman fatima, dan ko jiya ban san mi ya haɗa suba har sai da su ka yi sana din tashin ciwan ta"
"Subahanalilahi, yanzu ya jikin nata "
"taji sauƙi, ina tsoron abun da zai biyo baya ne yasa nake son mh dawo tare "
"E gaskiya ya kamata ku dawo tare, ku shirya ku tahu zanyi magana da Aishar "
"To shikenan malam mun gode, sai mun dawo " Allah yasa malam ya faɗi sallama suka yi, kiran noraiz yayi awaya yace ya same shi a ɗaki, ko da yazo ce mashi yayi ya haɗa kayan shi yau zasu koma lagos, da fara ko uziri noraiz yafa kawo mashi akan ya bari sai gobe ko monday, ganin babu wasa a fuskar shazim ne yasa shi kama bakin shi yayi shiru.
Cikin parlorn su ka shigo hannun su ɗauke da basket, dinning area suka nufa, feenah ce ta fito da flaks ɗin abinci tana jerawa kan dinning
Jin motsin mutum ne yasa fatima fitowa parlorn, ganin su feenah yasa ta tsayawa a bakin ƙofar ɗakin ta, Ilham ce tace" ke zo nan " banza tayi da ita " ke bada ke nake magana ba " banza fatima ta sake yi da ita ganin bazata zo bane yasa Ilham tashi ta nufe ta " ke har ni zan kira ki kiyi banza da ni " da buɗar bakin fatima sai cewa tayi " eh nayi banza da ke ɗin sai aka yi mi " da sauri feenah ta ƙara so tana faɗin "lallai wuyan ki ya isa yanka " hannu Ilham tasa zata ɗauke fatima da mari bata kai da kai mata marin ba taji saukar lafiyyen mari a fuskarta har sau biyu, ɗago da fuskar ta tayi tana kallon shazim da ke tsaye gaban su, feenah zata buɗe baki tayi magana kenan ya ɗauke ta itama da wani a zabeben mari har saida ta dafe ƙarfen bene dan ba ƙaramin maruwa suka yi ba" ya shazim mi mukayi ka ma... " bata ƙarasa ba yasake ɗauke da mari ganin haka ne yasa Ilham watsawa da gudu ta nemi hanyar fita , magana ya fara cikin kakkausar murya "wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da wata banza a cikin ku zata sake ɗaga hannu ta daki fatima" yana gama faɗa ya wuce ta nan tsaye dafe da kumatu tana kuka, fatima ɗakin ta ta shige ta turo ƙofa, Ilham ce ta dawo ganin shazim ya fita ta kama hannun feenah suka bar part ɗin..
Episode 36_37_
Ilham ce ta dawo ganin shazim ya fita, ta kama hannun feenah suka bar part ɗin zuwa part ɗin Innah, feenah sai kuka take kamar wata ƙaramar yarinya, gwaggo Halima su ka samu akan sofa a parlor da cup a hannun ta tana shan kunun gyaɗa, da sauri ta juyo tana kallon feenah da ke ta kuka kamar wata ƙaramar yarinya "ku kuma lafiya daga ina haka?"
basu bata amsar tambayar da tayi masu ba, sai ma neman wurin zama da su kayi kan sofa, feenah har wani ƙara ɗaga murya take duk dan innah da gwaggo uwani su ji su fito
"wai ku ba da ku nake magana ba,ke kuma ko ki man shiru ko wallahi na make maki baki, sakar yar banza kawai" Ilham tace " mama ya shazim ne fa ya same mu yayi ta marin mu baji ba gani "
"wani iskancin kuka yi mashi ko "
"ba abun da muka yi mashi, abinci kawai muka je kai mashi shine ya haumu da mari "
"ke Ilham ƙarya