Showing 117001 words to 120000 words out of 127932 words

Chapter 40 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6705

ina tana gida ne ko ta zo hospital ɗin"
"momy nima ban sani ba ko ta zo ba "
"ai kai kana hospital ɗin ko?"
"eh momy "
"to kaje ka du bata mana"
"to momy" ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran, ta shi yayi ya fice daga office ɗin ya nufi reception,gaishe da shi su maryam su ka shiga yi amsa masu yayi sannan yace
"maryam ina take,ko bata zo ba yau?" tun da ya faɗi haka maryam ta gane hidaya hake nufi
"tana office, a kira maka ita ne"
"a'a bari naje da kaina " ya faɗa haɗi da nufar office ɗin na su, binshi da kallo nurses ɗin su kayi kowa da gulma a bakin shi, maryam duk ya bata tausayi yana matuƙar son hidaya kuma shi ba ruwanshi ko a ina nu na sonta yake ba ruwan shi,jin nurses ɗin na ta ƙusƙus ne yasa maryam cewa " to uwayen gulma za ku fara, abun nema ya samu "
"daga faɗin alkairi sai abun ya zama gulma" wata ta faɗa
"eh, ai idan kayi maganar mutum ba tare da ya sani ba gulma ce"
"to munji ba sai kin yi mana wa'azi ba"
"ba ku son gaskiya na lura" maryam ta faɗa.
Yana zuwa bakin office ɗin  ya jiyo  muryar ta tana raira karatun alqur'an, ajiyar zuciga ya sauke yana faɗin
"ya Allah ka mallaka man wannan baiwar taka" ya faɗa haɗi da tura ƙofar da sallama a bakin sa,ɗagowa su victoria su kayi su ka kalle shi, abun ya basu mamaki mi ya kawo dr kabir office ɗin su, gaishe da shi su kayi,hannun ya ɗaga masu ba tare da ya amsa ba, jin suna gaishe da shi ne yasa hidaya ɗa gowa ta kalle shi, da sauri ta duƙar da kai, kallon su victoria yayi yana faɗin
"Please excuse us"
ta shi su kayi su ka fita, amma sai su ka laɓe bakin ƙofa dan son jin mi zai ce mata 
matsawa yayi ya samu wata kujera ya zauna kusa da wacce take zaune,binta kawai yake da kallon sai wasa take da ƴan yatsun hannun ta,  cikin ƙasa da murya ya fara magana
"beb wai mi nayi maki ne,Please idan da abun da nayi maki wanda baki so ki faɗa man kinji zan daina"
kanta na a duƙe tace "babu abun da kayi man"
"to amma mi yasa kike man wulaƙanci, ko dai baki sona har yanzu shazim kike so " girgiza mashi kai tayi
"magana nake so kiyi man, hidaya ki fahimce ni ina sonki tsakani na da Allah ne, ina son ki fahimce ni please"
har ga Allah bazata ce  dr kabir baya birgeta  ba, amma son da take ma shazim ne na daban ne wanda take jin bazata iya haƙura da shi ba har ta so waninsa ba,
"ya kabir maganar gaskiya bazan ce baka burge ni ba amma ina so ka fahimce ni ya shazi.... " tsawa ya daka mata yana faɗin
"dan Allah dakata man hidaya shazim ne dai ko to ga shazim nan" yana gama  faɗar haka ya tashi ya fice daga office ɗin,ya tsani maganar shazim da take yi mashi
duk sai taji ba daɗi amma ba zata iya haƙura da shazim ba, ta shi tayi ta bi bayan shi.

_*✨KATSINA✨*_

Su Aairah ne ke ta gyaran part ɗin da ke kusa da na Abie saboda zuwan su safwan, tun safe su ka tashi da shirye shiryen tarbar su Abie ma na gidan dadi saboda zuwa da za suyi su ɗauko su a airport shi da su uncle mustafa da Abdallah, mom da matar uncle Ahmad suna kitchen suna shirya masu abinci da ƙarfe huɗu na yamma jirgin su zai sauka.

_Episode  62_63_

Hidaya lokacin da ta bi bayan dr kabir,ko da ta fita bata ganshi ba hakan yasa ta bi shi office ɗin shi, zaune ta same shi kan sofa ya ɗaura hannun shi na dama saman kai, idanuwan shi a lumshe  ya rasa mi ke mashi daɗi a  duniyar nan, ƙarasawa tayi wurin shi
"Dr are u ok" banza yayi da ita duk da ya gane ita ce tunaninta bai ji ta ba ne  hakan ya sa ta sake kiran sunan shi,
"Please hidaya leave me alone" ya faɗa da ɗan ɗaga murya
"kayi haƙuri, na san abun da nayi maka ne ya ɓata ranka,dan haka nake haɗa ka da Allah da kayi haƙuri "  hannun shi daya ɗaura saman kanshi ya cire duk a tunanin ta ya haƙura ne Amma sai ganin shi tayi ya kama hanyar ficewa daga office ɗin
"ba dan halina ba kar ka fita, idan nice baka son gani zan fita amma dan Allah karka fita" ta faɗa yayin da take miƙewa ta nufo ƙofar, tsayawa yayi cak shi bai fita sanna kuma bai dawo ba,zuwa tayi har gaban sa tana faɗin " ina so ka fahimce ni Please, duk abun da ka ga ina faɗa maka ina faɗa maka tsakani na da Allah ne"
"naji hidaya, ai na ce maki kije gaki ga shazim ba shikenan ba"
"amma dr.. "
"please ya isa haka bana son jin komai  daga bakin ki"
" saboda mi"
"saboda duk abun da zai fito daga bakin ki ba alkairi ba ne a wurina, dan haka ni kawai ki fita,ki barni da abun da ya ishe ni Please" ya ƙarasa maganar haɗi da haɗe hannuwan shi wuri ɗaya,kan sofa ya koma ya zauna
"shikenan zan fita na baka wuri" tana faɗa tabuɗe ƙofar office ɗin ta fice,  wurin su maryam ta nufa , tun kafin ta ƙara so  maryam ke jefan ta da harara
"lafiya wai ki ke hararata?" hidaya ta faɗa yayin da take samun wurin zama ku sa da maryam ɗin
"kinfi kowa sani"
"ni babu wani abu da na sani "
"yayi kyau " maryam ta faɗa, fira su ke ɗan taɓawa jefi jefi, suna nan zaune har aka fara kiran sallar zuhur, dr kabir ne ya fito daga office ɗin shi ya shiga na shazim, yana shiga ya same shi yana tattara files ɗin da ke kan table ɗin alamar ya tashi sai kuma wani lokacin.
Sallam kabir yayi mashi haɗi da shiga ciki, kallon shi shazim yayi yana amsa mashi sallamar
"Autan momy lafiya dai?" shazim ya faɗa dan ganin kabir da yayi duk sai a hankali ga idanuwan shi a kumbure kamar na wanda ya sha kuka
"lafiya lau,  mi ka gani?"
"bakomai" shazim ya bashi amsa
"mu tafi ko" shazim ya faɗa saboda ya gama haɗa duk wani kayan shi, gaba kabir yayi shi kuma ya bi bayan shi su ka nufi masallaci, da aka gama sallah shazim sallama yayi ma kabir saboda shi zai wuce Abnoor kabir ma cewa yayi shima da anyi sallar asr  gida zai tafi  hakan ce ta faru ana gama sallah bai daɗe  ba shima ya kama hanyar tafiya gida.

_*FEENAH*_

zaune take bakin gado a ɗakin su ita da kairiyya, wayarta da ke kan bedside drawer ta ɗauka number innah ta shiga dialing bugu biyu innah ta ɗauka tana faɗin
"sai yau ki ka yi lokacina?"
"kai innah daga kiran ki zaki fara da complain"
" ni ki ke cema haka ko"
"innah ai ke ce daga kira sai ƙorafi"
"to naji , mi yasa ki ka kira ni dan na san ba dan Allah ki ka kira ni ba"
"haba dan Allah innah"
"ba wani haba, ƙarya na faɗa tun da nake da ke kin taɓa kirana haka nan kawai da sunan ki gaishe ni tun da kika kama ƙafa kika koma lagos da zama "
"naji ni dai innah, kima tsaya ki saurari mi ke damuna amma sai wani faɗa kike man"
"to naji, yanzu faɗa man mike damunki da yasa kika kirani "
"dama ba komai bane, yaushe su Abbah su ka tsaida ranar Auran mu da ya shazim, dan ni nagaji da wulaƙancin da yake man ga wannan munafukar kairiyya a gefe "
"wannan ko ƴar banzar yarinya, a nan ɗin ma sa maki ido take ke nan "
"Ai wallahi innah sai ma abun da ya cigaba jiya har da wani tsare ni zata yi man wa'azi saboda naje part ɗin ya shazim ya mare ni "
"mi?, mari fa kika ce?"
"eh kawai dan na taɓa shi, fuskata fa duk ya kumbura man ita, hannuna har da targaɗe kuma da Ammy tace ya duba ni ƙinyi yayi, shiyyasa na kira ki kisa su Abbah su tsai da ranar Auran mu nasan dai ya Aure ni ƙarya yake yace zai dake ni "
"amma kin bani haushi feenah, bana hanaki taɓa sa ba ke mi yasa baki jin magana ne, yanzu da ya illata ki da ya kenan, shi bai da asara saboda daman ba sonki yake ba"
"ai bazan ma ƙara ba, dan wallahi ba ƙaramar azaba na sha ba jiya da ana gyara man hannuna "
"to da dai ya fiye maki, dan shi ba ruwan shi dan ya yi maki illa"
"to innha yanzu yaushe zaki sa a sa ranar bikin mu "
"kar ki damu ki barni da su ni na san mi zanyi "
"yawwa innha ta shiyyasa nake sonki "
"kar ki ji komai, kawai ki bi abun da na ce maki "
"to insha Allah "
"sai anjima, na manta in faɗa maki mansoor na nan zai zo nace ya barki ya dawo da su sa'ada amma na san halin shi duk yanda zai yi karki saki ki biyo shi kinji na faɗa maki "
"in sha Allah innah bazan biyo shi ba"
"yawwa, sai anjima "
innah ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran
faɗawa tayi saman gado tana faɗin
"yawwa innah shiyyasa nafi kowa sonki don baki bari na zubar da hawaye "

✨KATSINA✨

Abdallah ne ya shigo wurin su mom dake  kitchen ita da ummah da baaba larai ya nufa, da sallama a bakin sa ya shiga kitchen ɗin, amsa mashi mom tayi tana faɗin
"wai da kai baka bi su abie ɗinka ba?"
"eh naje na dawo ɗaukar takardun su Aairah ne , makarantar ta fara ba da addimisson yanzu wani  abokin uncle Ahmad ya kira shi yake sanar da shi  Ameerah ta samu , shine uncle Ahmad yace na zo na ɗauki na su Aairah  na tura ma Abokin na shi wanda ya duba ma Ameerah sai suma ya duba masu suma"
"masha Allah kace ƴan biyu na sun kusa tafiya school hankali ya kwanta, kullum na huta da mom wai yaushe ya Abdallah yace za'a fara ba da addimisson kullum maganar su kenan"
Ummah tace "ai  gara su da Ameera, yanzu hankalina ya kwanta tunda Allah ya sa an samu addimisson yanzu hankalina zai kwanta "
"ai yaran nan idan ka bari su ka tasoka gaba kaga ta kanka" mom ta faɗa
Ummah tace " Allah dai ya shirye su " da Ameen su ka amsa Abdallah ya ce
"ni zan wuce"
Mom tace
"yaushe Abie ɗin naku yace za su iso"
"sai ɗan anjima ka ɗan yanzu ma ni su ke jira "
"Ok sai kun dawo, su kuma Allah ya kawo su lafiya"
"Ameen, sai na dawo" ya faɗa haɗi da ficewa ya bar kitchen ɗin.
Su Aairah ne su ka shigo da gudu daga garden  Ameera na riƙe da wayar Aairah, Aairah na biye da ita tana faɗin
"wallahi Ameera ki bani waya ta kafin ranki ya ɓaci "
"wallahi ban badawa kin bi duk kin ishi mutane,ban badawa idan kina da ƙarfi ki zo ki karɓa " Ameera ta faɗa tana ma Aairah gwalo, sai zagaye parlor su ke Aaimah na tsaye tana masu dariya tana faɗin
"wallahi karki bata "
"Aaimah ban san wulaƙanci dan mi zaki ce karta bani "
"ai wallahi ko bata ce haka ba bazan baki ba, dama kin daina bi na" Ameerah ta faɗa sai haki take, awannan yanayin ne Abdallah ya fito daga part ɗin shi ya gansu, tsawa ya daka masu yana faɗin
"wai ku wane kalar yara ne, kun girma amma kwata kwata baku san ciwan kanku ba, wallahi ko ku natsu ko ranku yayi mumunnan ɓaci sakarkaru kawai "
"yaya wayata fa ta amsa Aaimah na ce mata wai karta bani "Aairah ta faɗa tana turo baki
"na dai faɗa maku " Abdallah ya faɗa haɗi da ficewa ya bar parlorn , suna ganin ya fita kamar yace su cigaba sai kace ƙananan yara haka su kai ta zagaye parlor duk sun cika gidan da hayaniya.

_*✨Airport✨*_


motar su Abie ce ta shigo cikin Airport ɗin Abdallah ke driving motar da su Abie suke ciki yayin da uncle mustafa  ke driving motar shi, parking lot su ka nufa haɗi da yin parking su ka shiga fitowa,  Abie da uncle Ahmad  ne su ka fara fitowa sai uncle mustafa  sai ya Abdallah, cikin Airport ɗin su ka nufa abie da su uncle Ahmad suna ɗan fira sama sama, wani ƙyatattce wuri su ka nufa, zama su kayi kan chair's ɗin da ke wurin , su abie kaɗai ne su ka zauna ya Abdallah kuma can gefan su ya samu wuri ya zauna wayar shi ya ciro yayi dialing number fatima,bakin ta ɗauke da sallama tayi picking call ɗin tana faɗin
"ni nayi fushi,sai yanzu daga bari na dawo "
"da ya dr ki ka yi fushi?" ya faɗa cikin sigar tamabaya
"ai duk laifin shi ne, ya bar ƙanwar shi tana ta jiran shi" a shagwaɓe tayi maganar
"kin san dai idan ba wani abu ya tsare ya dr ba bazai bar ƙanwar shi tana jiran shi ba ko?"
"shikenan tun da haka kace "
"haka ne fah ba wai nace ba "
"kana ina yanzu?" fatima ta tambaya
"ina airport"
"ya dr ba dai wani wuri zaka je ba?"
"zanyi tafiya ne, kina so na zo maki da wani abu ne"
nan take yana yin muryarta ya canza, rai a ɓace tace 
"bana so, sai ka dawo"  ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran, murmushi ne ya suɓuce mashi yana faɗin
"fatima manya" tashi yayi daga inda yake zaune ganin su Abie sun ta shi,bin bayan su yayi.
Wani kyakyawan matashin saurayi  ne ke saukowa daga mata ƙalar benen jirgin da ya sauka, fari tas da shi  hannun shi ɗauke da madai daicin trolly sanye yake da baƙin cargo trouser  sai t_shirt wacce ita ma ta kasan ce baƙa da p_cap red color da ɓakin glass, ba ƙaramin fito da kyawun shi da na fatarshi kayan su kayi ba,saukowa yake cikin natsuwa   yayin da wani dattijon mutum ke bayan sa  jikin sa sanye da kayan mu na hausawa riga da wando na yadi mai taushi.
shima fari tas kyakyawan gaske za su yi sa'annin juna da uncle Mustafa duk da yawan shekarun shi haka bai hana kyauwun shi fitowa ba, tafiya su ke shi da matashin har su ka iso inda mutane ke tsaitsaye.

Abie ne ya ƙara so da sauri wurin su  fuskar shi ɗauke da tsantsar farin ciki,su uncle mustafa na bayan shi, yana ƙarasowa yayi hugging ɗin wannan dattijon yana faɗin " masha Allah, barkan ka da zuwa ƙasar ka,  barka da  dawowa " murmushi shima dattijon yayi yana faɗin "nagode" raba jikinsu su kayi su uncle Ahmad ma matsowa su kayi kusa da shi, hannu suka miƙa mashi su ka yi musabaha, suna mashi barka da zuwa, ya Abdallah matsawa yayi wurin wannan matashin yana faɗin
"safwan manyan ƙasa yau dai gaka a nigeria,ina tsoron naka ya tafi"  
murmushi safwan yayi haɗi da cire glass ɗin dake idon shi yace
"Abdallah ka raina ni, wani ya ce maka ina tsorone"
"sosai ma kuwa tsoro kake, in ba tsoro ba mi ya hanaka zuwa tun tuni sai yanzu"
"saboda kai ma baka zuwa "
"ba wani nan tsoro ne ya hanaka zuwa " 
"haka ka ce "
"eh haka na ce "
"zamu gani ai ni da kai wake tsoron" safwan ɗin ya faɗa haɗi da matsawa wurin Abie ya shiga gaishe da su.

Ɗunguma su kayi zuwa parking lot in da su kayi parking ɗin motocin su, safwan shi da Abdallah su ka shiga motar shi yayin da Abie da uncle Ahmad  su ka shiga motar uncle mustafa, barin airport ɗin su kayi ba su nufi ko ina ba sai gidan Dadi.
Horn su kayi a bakin gate ɗin gidan dadi, mai gadi ne ya buɗe masu ciki su ka shiga,parking lot su ka nufa haɗin da yin parking, fitowa su ka shiga yi ɗaya bayan ɗaya bayan sun gama fitowa ciki su ka nufa, abie gaba ɗaya a cikin farin ciki yake da zuwan wannan bawan Allah, da sallama a bakunan su suka shiga ciki, parlorn tsit yake kamar ba kowa, Aunty Rabi ce zaune kan sofa tana karatun qur'ani mai girma,sai da ta kai aya sannan ta tsaya haɗi da  amsa masu sallamar da su kayi, ciki su ka ƙara sa haɗi da samun wurin zama kan sofa's su ka zauna, gaishe da wannan dattijon ta  yi tare da yi mashi barka da zuwa ,cikin kulawa ya amsa mata, da fara'a a fuskar safwan ya gaishe da ita, amsa mashi tayi tana faɗin "safwan yau dai gaka a nigeria,ya gajiyar hanya "
"lafiya lau Alhmdllhl" safwan ya faɗa
"masha Allah , ya ka baro momyn ka "
"tana lafiya tace a gaishe da ku"
"muna amsawa"
abie ne yace  " ina mama, ko tana ɗaki?"
"eh yanzu ta shiga bari naje nayi mata magana"  ta faɗa haɗi da tashi ta nufi ɗakin dadi,wannan dattijon ne ya kalli abie  yace
"sai dai ban gane nan ina ne ba?"
"nan gidan mama mahaifiyar mu"
"oho Allah sarki " mutumin ya faɗa
Aunty Rabi ce ta fito ita da dadi,ƙarasowa wurin su su kayi wuri dadi ta samu kan sofa ta zauna tana kallon wannan mutumin, ta sowa yayi ya dawo kusa da ita yana faɗin " mama ina wuni " wani iri dadi taji jin ya kirata da mama, duk sai ya bata tausayi, shikenan waɗannan mutanen sun cuce shi yanzu baya iya tuna komai da ya shafi rayuwar shi,ya manta ko shi wanene ya manta iyalan shi da ƴan uwan shi.
Kallon Abie yayi yace "naji tayi shiru ko ba ita bace mamar ba?"
"ita ce bata ji ka bane" abie ya faɗa
"lafiya lau nake, ya hanya" dadi ta faɗa fuskar ta da ɗan murmushi wanda da ka ganshi kasan na dole ne
"Alhmdllh " mutumin ya faɗa, fira suka shiga taɓawa shi da dadi kamar ɗan da ta haifa da cikinta, tun bata saki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login