Showing 69001 words to 72000 words out of 127932 words

Chapter 24 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6703

dalilin kukan ta bawai ki rufe ta da masifa ba, zo nan fatima " ta faɗa haɗi da miƙama fatima hannu ta zo kusa da ita, tashi fatima tayi ta nufe ta " yi shiru dai na kuka kinji, miyasa ki ke kuka baki son shi ne " carab innah tace " haba dai wane ita tace bata son shi, ta dai faɗi mi take ma kuka"
"dan Allah innah kiyi shiru, idan tace bata son shi ba wanda zai mata dole " acewar uncle ahmad
"idan tace bata son shi kenan biye mata za ku yi kenan, idan ba'ayi mata aure ba jiƙata za'ayi a sha " shazim dai na sauraron su dan yayi rantsuwa inda da ranshi babu wanda ya isa yayi mata auren dole kuma ma da wannan sakaran yaron
"shi na gani, wallahi ko tana so ko bata so sai ta aure shi tun ba jiƙata za'ayi ba...  " katse ta uncle ahmad yayi yana faɗin
"ke uwani kar na sake jin bakin ki a nan, kinji na faɗa maki "
" a kan mi zaka ce haka amadu, idan ba'ayi mata auran ba mi zata yi ma mutane " tashi fatima tayi ta fita da gudu tana kuka kamar ranta zai fita, tashi luqman yayi ya bi  bayan ta ba tare da kowa ya lura da shi ba
Shazim yace "idan bata da abun da zata yi maki ke, a kwai waɗan da suke da abunda za tayi ma su, kuma wallahi da raina da lafiya ta babu wanda ya isa yayi mata auren dole " gaban innah ne ya faɗi jin abun da shazim yace,fashewa da kuka innah tayi tana faɗin "ni kake ci ma mutunci a gaban ƴaƴana da jikoki na, saboda baka ganin darajata dan bani na haifi ubanka ba " gwaggo Halima ce tace "kiyi haƙuri mama ki daina kuka, taya zaki ce bai ganin mutunci ki saboda ba ke kika haifi mahaifin shi ba,kin kasa fahimtar shi ne amma..... " bata ƙarasa ba innah tace " yi man shiru ai duk abun da yake aikatawa na lura akwai sa hannunki mara mutunci"
uncle Ahmad ne yace " dan Allah innha kiyi haƙuri kiyi shiru "
"taya zanyi shiru kuna ganin yaro na ci man mutunci a gaban ku kun kasa ɗaukar mata ki "  
"Kiyi haƙuri dai dan Allah " ya faɗa haɗi da kallon shazim yace
"shazim mu ka ke faɗa ma haka koh, na lura ka raina innah ko,  kenan ba mu isa mu yanke hukuncin ba a kan ku kenan ba"
"uncle ba da ku nake ba, amma tun da ta nuna bata son shi a ƙyale ta kawai tun da bawai tayi girman da za'ace ta isa aure ta ƙiyi ba "
"ok kai zaka nuna mana abun da ya dace kenan ko " a cewar gwaggo Uwani,  banza shazim yayi da ita kamar ba da shi take magana ba, duk abun da ake uncle Ibrahim baice ƙala ba saboda a kan ƴaƴan shi ake magana,bazaka iya gane awane hali yake ciki ba jin su shazim sun nuna basu san ƴaƴan shi.
Uncle Ahmad ne yace "to naji ba da mu kake ba,sai ka faɗa man da wanda kake " shiru yayi baice ƙala ba ganin bazai ce komai bane yasa uncle ahmad ɗin cewa " kace babu wanda ya ida yayi mata auren dole,mi kake nufi?" yanzu ma shiru yayi baice komi ba, ɗan nisawa uncle Ahmad yayi yace "to bari kaji hukuncin munriga da munyanke aure babu fashi "
"Uncle wannan yarinyar da kuka haɗa ni da ita bana son ta,a yana yin kukan da fatima keyi alama ce ta bata son shi,   idan kuka tursasa dole sai mun bi umarnin ku komai zai iya faruwa " yana gama faɗa ya tashi ya bar parlorn, da idanu kowa dake parlorn ya bishi,tashi feenah tayi zata bi bayan shi sai a lokacin uncle Ibrahim yasa baki tsawa ya daka ma feenah yana faɗin "dawo ki zauna, shashasha banza " innah ta nufa ta faɗa kan jikinta  fashewa tayi da wani mahaukacin kuka  sai ihu take kamar wacce uwarta ko ubanta ya mutu basu taɓa tunanin shazim zai iya shuka masu rashin mutunci ba irin wannan musamman uncle Ibrahim da ya kasance ƴaƴan shi ne na cikin shi, tashi uncle Ibrahim yayi ya nufi feenah dake jikin innah ya ɗauke ta da wani mumunnan mari haɗi da jan  hannun ta ya bar parlorn, bin bayan su innah tayi tana mashi masifa dan mi zai mareta, yarinya na son shi yace bai son ta ya barta da baƙin cikin da ya ƙunsa mata..

gwaggo Uwani ce tace "yaya yanzu kenan haka za'a zuba ma wannan yaron ido yana cima ma mutane mutunci  kuma baka ce komai ba  "
gwaggo Halima tace " mi kike so yace, tunda yace bai sonta a ƙyale shi kowa Allah ya haɗa shi da rabon shi "
"dallah sadiya kiyi ma mutane shiru ke dama tuntuni nasan cewa baki tare da mu, hada ke cikin masu zuga wannan yaron "
"ni dai komi za kice kice,goyan bayan gaskiya nake, kuma tun da ya nun..... " bata ƙarasa ba uncle Ahmad yace"  dan Allah ya isa haka, kowa zai iya tashi ya tafi na sallami kowa " ɗaya bayan ɗaya yaran suka fara ta shi suna fita wasu naji haushin shazim da fatima wasu kuma na ganin yana da gaskiya duba da rashin tarbiya da feenah ke da shi, uncle Ahmad ka ɗai aka bari a parlorn yayi shiru damuwa ƙarara a fuskar shi.

_*✨SHAZIM✨*_

Tun da ya bar parlorn part ɗin su ya nufa, bedroom ɗin shi ya shiga trollyn shi da ke bakin gadon shi ya jawo ya kai shi parlor wayar shi ya ciro ya kira noraiz bugu ɗaya noraiz ya ɗauka tunkafin yace wani abu shazim yace ka same ni a ɗaki ƙit ya kashe wayar, bayan kamar 10  seconds noraiz ya shigo da sallama, ko sallamar da yayi shazim bai amsa ba yace "wuce ka ɗauko kayan ka " kwata kwata babu sauƙi a fuskar shazim, da to noraiz ya amsa haɗi da ficewa ya nufi bedroom ɗin shi ya fito da trollyn shi zuwa parking lot da mansoor yaci karo zai shigo part ɗin, ba wanda yace ma ɗan uwan shi wani abu, ciki mansoor ya shiga zuwa ɗakin shazim yana shiga shazim na fitowa hannun shi riƙe da jakar laptop ɗin shi, kayan da ke jikin shi ne ɗazo a jikin shi sai p cap da yasa yanzu da baƙin glass, tsaye mansoor yayi yana kallon shi..
Episode 38_39_

Ƙarasa wa ciki mansoor yayi yana kallon shazim sama da ƙasa sanna ya fara magana
"shazim ka bani mamaki matuƙa, ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba "
"mamaki na baka ko?"
"tambayata kake ma "
"mansoor idan har baka ga laifin abun da akai man ba bai kamata ni kaga laifina ba "
"dole naga laifin ka, a gaban mu fa kake faɗa masu magan son ranka "
"sai dai kai ta ganin laifi na amma bazan zauna a tauye man haƙƙina inaji ina gani ba, mi fatima tayi da za'a yanke mata wannan  hukuncin kuma su rasa dawa zasu haɗa ta sai wannan ɗan iskan "
"ko da yace yana sonta kaji sun ce zasu aura mata shi ne?"
"Koma dai mi ne ne, bazan taɓa bari a ci zalinta ba, kuma ni kaga tafiya ta "yana gama faɗa yaja trollyn shi ya bar mansoor tsaye yana kallon shi, bin bayan shi mansoor yayi a bakin ɗakin fatima shazim ya tsaya tura ƙofar ya shiga tsit ya samu ɗaki alamar ba mutum a ciki, tunani yayi ko ta fita tare da noraiz, fita yayi mansoor na tsaye "wai shazim fushi kake dani ko mi " banza shazim yayi da shi ya nufi stairs case janye da trollyn shi, sake magana mansoor "magana nake maka shazim "
"inajin ka, mikake so nace maka ne "
"ok haka kace " a taƙaice yace eh, fita su kayi zuwa parking lot aminu ne ya amshi trollyn da ke hannun shazim ya sa a booth, dawowa yayi ya buɗe mashi bayan motar ya shiga rufe ƙofar aminu yayi, mansoor na tsaye bakin part ɗin yana kallon su, noraiz ne ya ƙaraso parking lot ɗin shi da mahmud, tambayar shi shazim yayi ina fatima "tana ɗakin ta "
"bata can " noraiz yace " kila tana part ɗin uncle Ibrahim "
"mi take a can kuma?" shazim ya tambaya "nima ban sani ba "
"to kaje ka kira ta " da to noraiz ya amsa haɗi da juyawa ya nufi part ɗin uncle Ibrahim shi da mahmud,da sallama su ka shiga part tsit main parlorn babu kowa, bedroom ɗin sa'ada suka a bakin ƙofar ɗakin suka tsaya mahmud ne yayi nocking, zaune take bakin bed tana kuka taji ana nocking, tashi tayi ta nufi ƙofar ta buɗe mahmud ne yace " sa'ada kice ma fatima ta fito su tafi "
cikin muryar kuka sa'ada tace "ai bata nan, ina tunanin tana ɗakinta " noraiz yace "bata can " maimaita maganar sa'ada tayi "bata can yaya, to ina ta tafi?"
"shine ba mu sani ba, mun ma yi tunanin kuna tare "
"ai tun da ta fita a parlor na biyo bayan ta ban san ina ta shiga ba da na zo ɗaki banganta ba  sai nayi tunanin ko tana ɗakin ta , to ko dai tana tare da Aunty kairiyya " sa'ada ta faɗa, fita su kayi zuwa part ɗin uncle Ahmad mahmud da sa'ada ne suka shiga part noraiz wurin shazim ya nufa, yana isowa shazim yace "wai ina fatimar ne kasan ƙarfe nawa yanzu "
"yaya gata nan zuwa, bata tare da sa'ada ne " ok kawai yace, gaba kusa da driver noraiz ya buɗe ya shiga, mahmud ne ya fito shi da sa'ada wurin su suka nufo tun kafin su ƙara so noraiz yace "tana ina "
sa'ada ce tace "can ma bata nan " shazim yace "bata nan" ɗaga mashi kai sa'ada tayi alamar eh, wayar shi ya ciro ya shiga dialing number ta tana ringing amma ba'a ɗauka ba, tsaki shazim yaja yana faɗin "amma sai na ci mutuncin yarinyar nan" sai da yayi mata kusan 5 missed call bata ɗauka ba, ganin dai da gaske fatima ba ɗaga wayar zata yi ba ne yasa shazim cewa "noraiz ku shiga ciki ku duba ta ko tana ɗakin ammy, ko ina dai ku duba ta " da to suka amsa noraiz ya fito su ka nufi part ɗin su, ba inda basu duba har bedroom ɗin shazim dana noraiz ɗin amma ba fatima ba dalilin ta,ne man fatima har part ɗin innah da na su Aunty zainab,su da zasu bi jirgin ƙarfe biyar na yamma sune har aka yi sallar magrib ba su tafi ba suna neman fatima,abun da ya ɗaga masu hankali ganin wayar ta da suke ta faman kira a main parlorn part  ɗin uncle Ibrahim kan sofa  sa'ada har ta fara kuka, hankalin shazim yayi ƙololuwar tashi, ina fatima taje.
duk wannan bidir da suke na ne manta babu wanda su ka faɗa ma suna ne manta, zaune suka yi a main parlorn part ɗin su shazim kowa yayi ta gumi tunanin kawai suke ina fatima ta shiga, sa'ada kuwa sai kuka take mahmud na lallashin ta,har aka yi sallar isha basu san in da ta shiga ba, tashi su kayi su ka nufi masallaci, sa'ada kuwa part ɗin su ta nufa wurin momy , ko da ta shiga samun momy tayi zaune bakin gado tayi tagumi, damuwa ce ƙarara a fuskar ta,da gudu ta faɗa saman jikin ta tana kuka, ɗago da ita momy tayi tana faɗin "lafiya ke kuma daga ina haka, mi ki ke ma kuka kuma " cikin shashekar kuka tace "momy ba'aga fatima ba " da sauri momy ta ɗago da fuskar ta tana faɗin "ban gane ba, ina ta je "
"momy tun ɗazu muke nemanta ni da su ya shazim ba mu ganta ba, muna ta kiran wayar ta ashe tana a nan parlor ta barta "  dafe kai momy tayi tana faɗin "ya salam, ina taje , kun du ba har part ɗin su innah da na su Auntyn ku?"
"eh momy babu inda bamu duba ba amma bata nan"
"har ɗakin feenah kin duba "
"a'a momy ban duba ba "
"to ta shi muje mu duba " ta shi su kayi zuwa ɗakin feenah babu in da basu duba har cikin toilet sai da su ka duba babu almun ta,ɗaya bayan ɗaya duk wani ɗaki da ke part ɗin sai da suka duba amma bata ba alamar ta, dafe kai momy tayi kamar mai tunanin,girgiza kai ta shiga yi tana faɗin " ba gaskiya bane , hakan ma bazata taɓa faruwa ba, idan ko haka ne na shiga uku ni turai "
"momy miya faru, miye kuma ba gaskiya ba?" sa'ada ta jefa mata tambayar haɗi da tsare ta da idanu
"bakomi sa'ada,kije part ɗin su Kairiyya ku sake duba ta " momy ta faɗa tana nufar  part ɗin dady,fita tayi zuwa part ɗin su shazim yan da ta bar su ɗazu zazzaune kan sofa yanzu ma haka ta same su amma ban da shazim
"ya noraiz an ganta " girgiza mata kai kawai yayi, fashewa tayi da kuka sai kace ƙaramar yarinya, mahmud ne yace" dan Allah sa'ada kiyi mana shiru, ba ɓacewa tayi ba za'a ganta"
ficewa tayi daga part ɗin.

Su Asma'u ne zaune a main parlorn part ɗin uncle Ahmad, fira su ke duk a kan meeting ɗin ɗazu da abun da shazim yayi, kowace na tofa albarkacin bakin sa, kairiyya ce ta saukko daga sama part ɗin mansoor  hannun ta ɗauke da tray da alama dinner ta kai masa ta shigowa parlor sa'ada na banko ƙofa kamar zata ɓallata ta shigo fuskarta jage jage da hawaye,da sauri su ka juyo suna binta da idanu gaban su sai faɗuwa yake jira kawai suke su ji tace ga wanda ya rasu dan duk a tunanin su mutuwa akayi , sai kuka take ta kasa cewa komi,magana su ka shiga yi mata "ke wai mi akayi ne kike kuka, wani ne ya rasu " sai jefa mata tambayoyi suke amma ta ƙice masu ga abun da take ma kuka, karshe ma part ɗin mansoor ta nufa da gudu, ta shi su kayi suna binta da idanu har ta haye sama, kallon kallo su ka shiga yi ma juna, fitowar shi kenan daga bedroom ɗin shi  yaji an banko ƙofar parlor  ɗin shi kamar za'a ballata har sai da ya ɗan tsorata da ganin sa'ada idanunta sunyi luhu luhu "ke lafiya daga ina haka " bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba sai ma ƙara sautin kukan da tayi,  har sai da mansoor ya kwatsa mata tsawa yana faɗin "ke lafiya kike wannan kukan mi a kayi maki " cikin shashekar kuka tace "fatima ce..... " bata ƙarasa ba mansoor ya katse da "fatima ce tayi mi, kiyi magana mi ya samu fatimar " fashewa tayi da kuka tana faɗin
"tun ɗazu muke nemanta ba mu ganta ba" tsaki mansoor ya ja yana faɗin "ina fatimar zata je, ki je dai ki sake du bata "
"wallahi yaya ba inda ba mu  duba ta ba amma ba mu  ganta ba ni da su ya shazim  " ya salam mansoor ya furta yana faɗin "an kira wayar ta kuwa "
"bata tare da wayar"  ok bari na zo mansoor ya faɗa haɗi da nufar bedroom ɗin shi  da sauri ya tura ƙofar ya shiga, wayar shi da ke kan sofa ya nufa ɗauka yayi ya shiga dialing number fatima tana ringing amma ba'a ɗauka ba kamar yan da sa'ada ta faɗa mashi kusan 5 missed call, ɗan dafe kanshi yayi yana furta "ya Allah " fita yayi daga bedroom ɗin in da ya bar  sa'ada a nan ya same ta ƙofar fita parlorn ya nufa bin bayan shi sa'ada tayi, su Asma'u har yanzu suna nan tsaye hankalin su duk a tashe, ganin ya mansoor da sa'ada da sauri kairiyya ta nu fi mansoor tana faɗin "yaya wai mike faruwa ne " ficewa yayi batare da ya bata amsa tambayar da tayi mashi ba ganin haka ne yasa ta jawo hannun  sa'ada tana faɗin " sa'ada wai mike faruwa ne "
"Aunty kairiyya fatima ce ake nema ba'a ganta ba " dafe ƙirji kairiyya tayi tana faɗin "ba'a ganta ba "
"Eh, tun ɗazu muke nemanta ni da su ya mahmud amma bamu ganta ba, ko ɗazu da na shigo nan ita muke ne ma"
Asma'u da Amina har haɗa baki su ke wurin jan tsaki da faɗin "aikin banza kawai saboda kawai ba'a ganta ba zaki wani shigo ma mutane kamar wacce wani nata ya rasu " mtsww su ka sake jan tsaki, kairiyya ce tace " amma nayi mamakin abun da ya fito daga bakin ku wallahi, haba Aunty Asma'u cewa tayi fa tun ɗazu ake nemanta ba'a ganta ba "
Amina ce tace "ke kairiyya ki kam kan ki, ko cewa tayi ta mutu ina ruwan mu "
kairiyya tace "wallahi ku dai canza dan wannan ba rayuwa ba ce "
hayayyaƙo mata su kayi da masifa Fiddausi tace "gaskiya fa ta faɗa ko da ace ba ƴar uwar ku ba ai ita muslma ce bare jinin ku ɗaya da ita, gaskiya ku gyara "
kallon juna su kayi suna faɗin "yau ga ƴan iskan yara wa'azi za ku yi mana " kairiyya tace " ba wa'azi za muyi maku ba gaskiya ce muke faɗa maku "
"to ba mu so " a cewar Amina, jan hannun sa'ada kairiyya tayi su ka bar part ɗin zuwa part ɗin innah wurin gwaggo Halima, ita ka ɗai suka samu a  part ɗin gwaggo Uwani da innah ba su nan, suna asibiti wurin feenah data yanke jiki ta suma lokacin da uncle Ibrahim ya fitar da ita daga parlorn da suka yi meeting ɗazu,   abun dake faruwa su ka faɗa mata,sosai hankalin ta ya tashi, wayar ta ta ɗauka ta shiga dialing number uncle Ahmad da yake shima bai nan yana tare da su innah , korma uncle Ahmad bayani tayi akan abun da yake faruwa, sosai ya nuna tashin hankalin shi, tamabayar gwaggo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login