Showing 75001 words to 78000 words out of 127932 words

Chapter 26 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6708

zai ma luqman ne yasa ban sanar da shi ba "

"ai da ko mansoor ka fad'a mawa shi zai iya controling d'inshi ko halima, da sai su kai ta hospital adubata  ,amma yanazu ba k'aramin kuskure kayi ba na kin fad'a tun d'azu "

"ya salam amma yaya minene ma fita "

"mafita d'aya ce a sanar da shi halinda take ciki "
"amma yaya yana iya illata luqman da duka "

"to koma mi zai mashi ai shi ya ja tun da bashi da hankali ,kuma zamu k'i  fad'a ne saboda kar ya hukunta shi, kuma idan mu kayi haka ba muyima yarinyar nan adalci ba kamar yan da luqman yake a wurin haka take a wurin mu "

"hakane, bari na kira dr sai ta zo ta du bata " dady ya faɗa haɗi da ciro wayar shi daga aljihu yayi dialing number dr su.

_*✨SHAZIM✨*_

"Shazim ni ina mamkin in da fatima zata je ,ko ina a estate d'innan kun duba kuwa " a cewar Abdallah

d'agowa shazim yayi yana fad'in
"duk in da nake tunanin zata iya shiga mun duba amma ba  mu ganta ba"

"gaskiya abun nan da mamaki ,tun da dai ba inda zata je,nifa zargi nake tana cikin estate d'innan"

d'an nisawa shazim yayi had'i da cewa" nima zargina kenan,sai dai duk inda nake tunanin zata iya shiga ko za'a iya kaita sai da na duba,dan na daina tunanin wani wuri ta tafi yanzu nafi zargin sace ta akayi "

"abun da kawai ya kamata yanzu shine mu kira police kawai dan wannan zaman da muke bawai zai amfana ma wani abun arzik'i bane ,amma ya ka gani"

"gaskiya wannan itace mafita kawai "

Abdallah wayar sa daya d'aura kan hannun sofa ya d'auka ,number wani police abokin uncle ahmad yayi dialing
Mansoor ne ya shigo part ɗin wuri ya samu kan sofa kusa da Abdallah ya zauna, kallon shi Abdallah yayi yana faɗin " mansoor har yanzu ba wani labari "
"
"babu Abdallah,gashi tun ɗazu ya usman ya kira wani abokin shi  police amma har yanzu baizo ba, na rasa gane lamarin ƙasar nan "

"sai haƙuri, nima yanzu na kira wani abokin uncle na san shi insha Allah zai zo "

" Allah yasa " Mansoor ya faɗa, shazim dai na gefe yana jinsu baice ƙalaba wayar sa ce tayi ringing , dafe kai yana faɗin
" ya Allah, wallahi na rantse duk wanda na kama da sa hannun shi hmmm...  " kawai yace ba tare da ya ƙarasa ba, kiran ne ya sake shigowa wayar mansoor ne yace "idan bazaka ɗauka ba ka kawo na ɗauka, dan rashin ɗaukar ka shi zai ƙara jefa su cikin tashin hankali "

"idan na ɗauka mi zance masu mansoor?, idan har su ka sani hankalin su sai ya fi tashi akan wanda suke ciki yanzu saboda rashin ɗaukar kiran su da banyi ba "

"duk da haka shazim da ka ɗauka sai kace masu kun fasa dawowa ne yau,  amma hakan zai sa su cikin tashin hankali matuƙa "

"uhmmm " kawai yace

suna nan zaune jigum sa'ada ta bankaɗo ƙofa  ta shigo har tana tuntuɓe tana shirin faɗuwa,sai haki take kamar wacce wani abun tsoro ya biyo, fuskar ta sharkaf da zufa  mansoor ne ya taso da sauri yana faɗin "wai miyasa ba zaki zauna wuri ɗaya bane sa'ada , ji yan da ki ka shigo kina shirin illata kanki, yanzu miya ya dawo da ke nan"

sai haki take maganar ta ma da kyar take fita "yaya dama.... " maganar ce ta sarƙe mata sai sauke numfashi take
"dan Allah ki kwantar da hankalin ki kiyi man baya nin abun da ke faruwa "
bata ba shi amsar tambayar sai ma nufar shazim da tayi da sauri, keys ɗin dake hannun ta miƙa mashi tana "ya shazim gashi "
ɗagowa yayi yana kallon ta "key ɗin ɗakin dady fatima na can " kamar saukar aradu haka su ka ji maganar ta mansoor da Abdallah da sauri suka nufe ta suna faɗin "da gaske kike sa'ada " ɗaga masu kai tayi tana faɗin " eh yaya da gaske nake tana can ita da ya luqman "
"luqman kuma?, kin tabbata sa'ada? "
"yaya fatima ce fa, wallahi tana can "
"ya Allah, amma mi ya kaita can mi ta ke yi tare da luqman a ɗakin uncle"
ƙarar rufe ƙofa su kaji da sauri ko wannen su ya kalli ƙofar basu ga kowa ba mansoor ne yace "shazim tashi mu je.... " bai ƙarasa ba ganin sofar wayam ba kowa, basu san lokacin da ya bar wurin ba sai yanzu su ka fahimci cewa ashe rufe ƙofar da suka ji shi ne ya fita, ba
yan sa suka bi da sauri ko da suka fita ko mai kama da shi basu gani ba a compound, zuciyar mansoor sai bugawa take yana tsoron abun da shazim  zai yima luqman,da sauri suka isa part ɗin direct sama suka nufa shazim har ya shige ya maida ƙofar da key ya rufe, bubbuga ƙofar su ka shiga yi suna kiran sunan shi amma ko motsin shi basu ji ba bare su sa ran zai buɗe masu, sai haɗa shi da Allah mansoor yake akan ya buɗe masu amma shiru.

Lokacin da ya  shiga parlorn ba kowa hakan ya sa shi wu cewa bedroom ɗin dady tura ƙofar yayi ya shiga, kwance ya hangi fatima kamar matatta an rufe mata rabin jikinta da blanket, ƙara sawa yayi bakin gadon saitin in da fuskar ta take,sai fitar da numfashin wahala take kanta ko ɗan kwali babu sumar kanta duk a ya mutse   fuskara tayi fayau da ita bakin ta ya bushe ƙamas duk ya faffashe  goshinta ma a fashe yake da gefan bakin ta   fuskar ta tayi jawur , siraran hawaye ne ke fita daga gefen idanuwanta da suka kumbura su kayi suntum,wuyan ta da ƙirjinta duk sawun ya kushi, sai jan numfashi take da ƙyar tana fitarwa, wasu zafafan hawaye ne suka taru a idon shi zuciyar shi sai tafarfasa take, hannu biyu yasa zai ɗauke ta ƙarar buɗe ƙofa da yaji ne yasa shi juyawa dan ganin wanene ya shigo, ido biyu su kayi shida luqman da ke tsaye bakin ƙofar bathroom ɗin dady daga shi sai bathrobe, tun ɗazu yake cikin toilet ɗin jin motsin mutum ne yasa shi fitowa duk a tunanin shi dady ne, ai kuwa yayi daya sanin fitowa, wani mumunnan faɗi gaban shi yayi ganin wanda bai yi tsammani ba da sauri ya juya zai koma toilet ɗin sai kafin ya ja ƙofa ya rufe tuni shazim ya cimma sa, roƙwanshi ya fara akan dan Allah yayi mashi haƙuri wallahi ba da gangan yayi mata haka ba, kuma ba abun da yayi mata " sai magiya yake mashi amma ina shazim bai ma san yana yi ba,  buga mashi kai yayi da bango nan take goshin shi ya fashe ya fara zubar da jini, wani wahalallen ihu luqman ya saki yana cigaba da rokwan shi da yayi mashi afuwa bazai sake ba,naushi shazim ya kaima bakin shi da yake rokwan nashi,naushin shi ya shiga yi ta ko ina yana buga mashi kai da bango tun luqman na da bakin bashi haƙuri har ta kai muryar shi bata fita saboda azaba.
Su mansoor na bakin ƙofar part ɗin suna aiki bugawa da roƙon shazim akan karyayi ma luqman wani abu amma ko alamar yana jin su basu jiba, hankalin su duk ya tashi akan halin da luqman yake ciki, sa'ada sai kuka take tana kiran sunan luqman da fatima, momy ma sai kuka take tana ro kwan shazim karya kashe luqman, ganin da gaske shazim ba jinsu yake ba yasa momy fita da part ɗin a hargitse ta nufi part ɗin uncle Ahmad kamar an jeho ta haka ta faɗo cikin parlorn su mama da gwaggo Halima da ya usman da sauri suka miƙe cikin tashin hankali su ke tambayar ta lafiya, momy sai hawaye take tana nuna masu bayan ta bayan nata suka kalla su basu ga komai ba, sai da ƙyar ta samu kalmomin furta " sha... zi.. m... zai ka.. sh... e luqman " ta ƙarasa maganar a rarrabe,salati gwaggo halima ta rabka tana faɗin " na shiga uku ni halima, mi ya haɗa su kuma  Innalillahi "
da sauri su ya usman suka nufi part ɗin su momyn, bin bayan su su mama su kayi momy sai sharar hawaye take, a bakin ƙofar part ɗin suka tsaya suma su ka hau bubbuga ƙofar suna rokwan shazim da ya buɗe amma ina ya usman ne yace su sa ƙarfi kawai su ɓalla ƙofar kawai dan ko zasu kwana a nan shazim ba wai zai buɗe masu bane har sai ya fitar da luqman daga hayyacin sa, haka su kai ta ƙoƙarin ɓalla ƙofar, duk wanna budirin da ake dady da Abba suna garden jiran dr basu san mike wakana ba, ba irin ƙoƙarin da su mansoor basu yi ba ganin ƙofar ta buɗu amma ina, momy ce tace mahmud yaje ya kira su  dady a kwai key a jikin shi, da sauri luqman ya tafi kiran su, su kuma su mansoor na ta aikin ɓalla ƙofar yayin da Abdallah yake sake kiran number wannan police ɗin dan yaga sun jima basu zo ba gashi ana shirin kisan kai.
sai ga dady da Abbah sun shigo hankali a tashe da sauri dady ya nufi ƙofar yana ciro key ɗin dake aljihun shi matsawa su mansoor su kayi suna bashi wuri key ɗin yasa ya shiga kiciniyar buɗe ƙofar amma ina ta ƙi buɗuwa saboda key da shazim ya bari jikin ƙofar da ya shiga, kuma yayi hakan ne dan kar ma su samu sa'ar buɗer ƙofar

Shazim  sai da yayi mashi lilis duk ya farfasa mashi goshi da bakin shi shaƙe mashi wuya yayi har sai da yaga baya motsi ko ɗan yatsa baya iya motsawa tukun ya sake shi ya faɗi ƙasa yarab ba numfashi, bai bi ta kanshi ba ya nufi gadon da fatima take hannu biyu yasa ya ɗauke ta irin ɗaukar da ake yima jarirai ya fice  da ita yana zuwa bakin ƙofar su mansoor na samun nasarar  ɓalleta suka shigo da sauri  ganin shi da fatimar ne yasa suka nufe shi sa'ada da sauri da shigo tana kuka haɗi da cewa "ƴar uwata miya same ki, ya shazim naga kamar bata numfashi " sai tambayar shi suke wane hali take ciki dan ganin fatima sun ma manta da luqman da ke can yashe a bedroom ɗin dady, dadyn kawai ya nufi bedroom ɗin da sauri har sai da gabanshi ya faɗi da yayi arba da luqman yashe  a ƙasa babu alamar ma yana numfashi, bayan shi Abba ya biyo da sauri shima ya ja burki ya tsaya yana bin luqman da ke kwance ƙasa,  kuka ne ya kubce ma dady yana faɗin "luqman dan Allah ka tashi kar ka mutum, dan Allah na roƙe ka katashi " sai jijjiga shi dady yake yana roƙwanshi da ya tashi amma ina ko motsi wannan bai yi ba Abba ne ya ƙaraso kusa da su dafa kafaɗar dady yayi " Ibrahim ai suma yayi " sai a lokacin dady ya lura da cewa suma luqman ɗin yayi.
barin wurinAbba yayi ya nufi toilet ya ɗebo ruwa yazo ya yayyafa ma shi a fuska a firgice luqman ya farka sai sambatu yake yana faɗin "dan Allah ya shazim kayi haƙuri wallahi babu abun da nayi mata, dan Allah kar ka kashe ni wallahi bazan sake ba plea.... "  da sauri dady ya kira sunan shi, zambur luqman ya miƙe zai nufi toilet dan duk a tunanin shi shazim ne tashin farko bai gane muryar dady bace sai da Abba yace "dawo luqman ina zaka ba shazim ba ne mune " sannan luqman ya tsaya yana sauke numfashi da sauri ya nufi dady yayi hugging ɗinsa fashewa yayi da kuka kamar wani ƙaramin yaro
"dady ya shazim kashe ni yaso yi, baya ƙaunata sai ce mashi nake ba abun da nayi mata amma sai da ya dake ni , miyasa ka bar shi ya shi go "

dady yace "luqman duk laifin ka ne, yanzu ai kaga irin abun da nake guje maka ko "
"dady wallahi ban yi mata komai ba, Allah bazan sake ba, dan Allah kar ka bari ya raba ni da ita wallahi ina son ta "
"kama daina faɗar haka luqman dan yanzu ko mutuwa za ka yi shazim bazai taɓa bari ka aureta ba,ba shi kaɗai ba har ita kanta fatimar da su Aisha "
"dan Allah dady"
Uncle Ahmad ne yace "ya isa haka, zo muje mansoor ya duba ka ko mu tafi asibiti goshin ka da bakin ka sai zubar da jini su ke "

"Abba banzan iya zuwa wurin ya mansoor ba nasan shima fushi yake da ni  kuma ina tsoron na fita mu sake haɗuwa da ya shazim, momy dai  ta zo nan ta duba ni " hannun shi Abba ya jawo
"zo mutafi ba abun da zai sake yi maka ai ina tare da kai "
"ni dai momy nake so ta duba ni"

"to shikenan zo mu tafi "

duk da yace haka ƙin binshi luqman yayi sai da dady yace "nima ina nan ba abun da zai maka kaji " sannan ya bi bayan su suna gaba yana baya sai zare ido yake har suka shigo main   parlor ba kowa duk su mansoor sun fita sai momy dake zaune kan sofa ta buga uban tagumi, tana ganin su da sauri ta taso tana "luqman yanzu kaga irin ta ko "
da sauri ya nufeta ya yayi hugging ɗinta " momy wallahi bazan sake ba Allah "
Abba ne yace "turai kiyi mashi dressing ɗin wannan ciwukan"
sai a lokacin momy ta lura da ciwukan da ke jikinshi,medical room ɗin su ta nufa da sauri zama su kayi kan sofa suna jiran ta fito, kamar daga sama suka ji ƙarar jiniyar motan ƴan sanda

Abba ne yace "Innalillahi ba dai usman sai da ya kira ƴan sandan nan ba, ya Allah  "
da sauri  luqman ya tashi  yana zazzare ido " na shiga uku dady ni su ka zo kamawa ya shazim ne ya kira su" dafe kai dady yayi
"shazim wai wane irin yaro ne yaya, yanzu duk wannan dukan da yayi mashi bai isa ba sai ya haɗa shi da ƴan sanda " shi dai Abba yayi shiru baice komi ba

"dady dan Allah kar ka bari su tafi da ni, dan Allah ba dan ni ba dady" duk ya bi ya ruɗe jikin shi sai rawa yake
dafa shi dady yayi "kwantar da hankalin ka ba abun da zasu yi maka kaji... "

ko rufe baki bai yi ba a ka turo ƙofar parlorn aka shigo ƴan sanda ne su uku suka shigo, da gudu luqman ya boye bayan dady, Abba ne ya nufe su da sauri yana faɗin " yallaɓai lafiya?"

babban cikin su ne yace " munzo ne da sammacin kama luqman Ibrahim Nuraddeen "
Abba yace " wa ya baku izini ke nan?"

"nine" ya ji an faɗa daga bayan su matsawa yan san da suka yi a dai dai lokacin momy ta fito hannunta riƙe da first aid box
Abdallah ne tsaye bayan su ya harɗe hannuwa a ƙirji
da mugun mamaki su dady ke kallon shi Abba ne yayi ƙarfin halin cewa "a kan wane dalili kenan, duk dukan da shazim yayi mashi bai isa ba"
Abdallah yace "pls Abba kayi haƙuri" ya faɗa haɗi da kallon jami'an tsaron da ke tsayae yace " yallaɓai kuyi aikin da ya kawo ku "
matsowa dady yayi ganin ya matsa ne yasa luqman da sauri ya nufi sama   
"dan Allah yallaɓai ku dakata dan Allah "
tsayawa su kayi suna sauraron mi dady zaice kamar daga sama suka ji ihun luqman yana kiran sunan dady a tamanin suka juya suna kallon sama, shazim ne su ka hango ya damƙi wuyan luqman ya nufo parlorn da shi ba wanda yaga san da ya shigo  part ɗin, ya gaji da jiran police ɗin ne su fito da luqman ganin sun jima ne yasa shi ya shigo shine yaji dady nacewa su dakata ya kuma hangi luqman zai shige part ɗin dady, har wurin su ya ƙara so da luqman ya miƙama ɗaya daga cikin police yace "arrest him" kama hannun luqman police ɗin yayi ya sa mashi handcuff ya fice da shi,kan sofa dady ya zube, Abba ne yace " why shazim why, yanzu duk dukan da kayi mashi bai isa ba, shima fa ɗan uwan ka ne kamar fatimar " kallon Abba  shazim yayi da idanun shi da suka kaɗa su kayi jawur tsantsanr ɓacin rai da masifa ce a cikin su hannu kawai  ya haɗa ma Abba  alamar haƙuri ba tare da yace komai ba ya fice daga part ɗin sai a lokacin momy ta fashe da kuka.
ciki mota su ka sa luqman suka tafi da shi sai ihu luqman yake yana kiran sunan dady.
Episode 42_43_

Sai ihu luqman yake yana kiran sunan dady.
Shazim ba irin haƙurin da su ya usman da su mahmud, faisal mama,gwaggo halima, har da su Asma'u da kairiyya basu bashi ba amma ko kallon in da suke bai ma yi ba sai ma kama hanya da yayi ya bar part ɗin

tare shi mansoor yayi yana faɗin " haba shazim miyasa zaka yi haka duk haƙurin da ake baka yaci ace ka haƙura,  dan Allah kar ka bari su tafi da shi, a nan ma zaka iya hukunta shi, please "
ya ƙara sa magana cikin sigar roƙo, amma ina ko kallon shi shazim bai yi ba sai ma bi ta gefan shi da yayi ya wuce, bin bayan shi mansoor yayi yana ci gaba da roƙonkwan shi amma kwata kwata babu alamar ma zai saurare shi, ko mawa yayi kan Abdallah yana faɗin " haba Abdallah miyasa zaka kira su tun da har shazim ya ɗauki doka a hannu ai da an barshi yaji da iya wannan "
"mansoor kafi kowa sanin halin luqman tun da kai ke tare da shi, ji irin abun da yayi ma fatima ace ma bai mata komai ba, halin ciwan da ya sata ya kyauta kenan "
"na san bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login