Showing 120001 words to 123000 words out of 127932 words

Chapter 41 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6695

jiki da shi ba har ta saki jiki su ka sha fira duk da firar ba wata bace tambayoyi ma da yake mata duk sunfi yawa.
Aunty Rabi ce ta kawo masu ruwa da lemu, sun jima a gidan sannan abie yace su tafi can gida amma sai wannan bawan Allah yace bazai je ba shi yana nan tare da mama, abie ne yace mashi ai idan sun je za su dawo,dadi ma tace zuwa za kuyi ku dawo sannan ya yarda ya bisu suka tafi.

Lokacin da suka isa gida su Aairah na nan zaune a main  parlor suna kallo, jin sallamar abie ne ya sa su tashi da sauri suka nufe su,  suna faɗin
"oyoyo ga abie"
haɗi da gaishe da su uncle Ahmad, ciki su Abie su ka shigo abie na faɗin
"ina su mom ɗin ku sai ku ka ɗai a parlor "
"yanzu su ka shiga ciki" Aaimah ta faɗa
Abie yace "ba kuga uncle sadiq ba" ya faɗa yana nuna wannan mutumin, da sauri su ka nufe shi suna faɗin
"uncle sannu da zuwa, ya gajiyar hanya "
"Alhmdllh, ya kuke "
"lafiya lau mu ke"
"masha Allah " ya faɗa
Wuri su ka samu kan sofa su ka zauna yana tambayar su Aairah ya sunan su, ɗaya bayan ɗaya suka shiga faɗa mashi sunayen su yan jinjina kai.
Ameera ce ta tashi ta tafi kiran su mom , ba ta daɗe da tafiya ba sai gata tare da su mom,ƙarasowa su kayi ciki, nan suka shiga gaishe gaishe, abie na nuna ma uncle su da sunayen su, sun jima anata fira har sai da aka fara kiraye kiyaren sallar magrib sannan su ka tashi su ka nufi masallaci, su mom ma da su Aairah ɗakunan su suka nufa domin gabatar da tasu sallar, bayan sun kammala ne mom tace su je su jera dinner kan dinning,tafiya su kayi su ka jera komai da ya kamata sannan suka koma kan sofa suna cigaba da kallon da suke ɗazu, su abie ba su dawo gidan ba sai bayan da su kayi sallar isha tukun su ka dawo,  suna shigowa dining su ka nufa,su Aairah mom tace suje suyi serving ɗin su,su kuma su kawo masu na su abicin nan kan carpet saboda dining ɗin da yayi masu ka ɗan.
bayan sun kammal serving ɗin su,kamar yan da mom tace kan carpet su ka kawo masu na su abicin su ka ci.
Bayan sun kammala dinner a nan mai parlor su ka zauna suna ɗan taɓa fira amma banda su Aairah da suka gama dinner bedroom ɗin su suka nufa, Abdallah ma da safwan part ɗin Abdallah su ka nufa su ka bar su Abie ka ɗai a parlor suna fira.
Sai wurin ten uncle mustafa ya tafi gida uncle Ahmad kuma ya tafi part ɗin da su ka sauka shi da ummah,abie kuma shi da uncle sadiq su ka tafi part ɗin shi.
bayan sun shiga part ɗin abie, wani bedroom abie ya kaisa wanda ke kusa da nashi, da suka shiga ciki pajamas abie  ya ɗauko mashi sannan ya nuna mashi wani corridor da wardrobe ce ciki yace ya shiga ya canza kayan jikin shi , bayan ya canza abie yace ya shiga toilet yayo alwala, da to ya amsa mashi haɗi da nufar toilet ɗin ɗakin bayan kamar 1 minute ya fito jikin shi da danshin ruwa.
Nuna mashi bed abie yayi yace ya zo ya kwanta, matsowa yayi ya hau gadon zaman abie yayi shima kusa da shi sannan yace" zan riƙa karanto maka adu'ar kwanciya bacci sai ka maimaita" to ya faɗa
nan abie ya shiga karanto mashi shi kuma yana maimaitawa har abie ya gama karanta mashi, sannan yace ya kwanta, kwanciya yayi abie yaja mashi blanket sannan yayi mashi sai da safe haɗi da nufar ƙofa ya kashe mashi light ɗin ɗakin tare da jawo mashi ƙofa, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba da shi..
_Episode  64_65_

Abie ɗakin shi ya koma, shima alwala yayi sannan ya zo ya gabatar da safa'i da wutiri sannan ya kashe light ɗin ɗakin ya  kwanta, duniyar tunani ya shiga, yanzu baya da wani buri face yaga Allah ya toni asirin mutanen nan, ya jima a kwance yana saƙawa da kwancewa  batare da bacci ya ɗauke shi ba, sai da dare ya raba sosai sannan  bacci ya fara kama idon shi,ta shi yayi yaje ɗakin da uncle sadiq yake a bakin ƙofa ya tsaya, leƙashi yayi, hango shi yayi ta hanyar hasken bedside lamp dake kunne  yana ta sharar baccin shi  hankalin shi kwance, mai da mashi ƙofar abie yayi ya rufe, bedroom ɗin shi ya koma kwanciya yayi dan da nan bacci shima yayi awan gaba da shi..

_*WASHE GARI*_

Masallatai na fara ƙwala kiran sallar asuba abie ya farka,toilet ya nufa  ya ɗauro alwala sannan ya dawo ya canza kayan dake jikin shi zuwa jallabiya, fita yayi ya nufi ɗakin da uncle sadiq yake ciki, lokacin da ya tura ƙofar hango shi yayi a zaune a bakin gado da alama ma har alawala yayi saboda danshin ruwa dake jikin shi, da sallama Abie ya shiga , ɗagowa uncle sadiq yayi yana kallon abie, yace" yawwa harka tashi kenan"
"eh" uncle sadiq ya bashi amsa
"ta so to mu tafi masallaci " abie ya faɗa haɗi da kama hanyar fita, bin bayan shi uncle sadiq yayi, a main parlor su ka samu uncle Ahmad da su Abdallah,
ficewa su kayi zuwa masallaci,lokacin da su ka dawo abie da uncle sadiq a parlorn abie suka zauna abie na koya mashi karatun qur'ani mai girma, sun jima abie na koya mashi, har sai da gari ya waye sosai tukkun su ka ajiye karatun, uncle Ahmad ne ya shigo parlorn da sallama a bakin shi, amsa mashi sallamar su kayi, wuri ya samu kusa da abie ya zauna yana faɗin " ina kwana yaya, fatan an tashi lafiya " amsa mashi abie yayi da
"Lafiya lau Alhmdllh" sannan uncle Ahmad ya kallin uncle sadiq yana faɗin " ina kwana, an tashi lafiya"
"lafiya lau Alhmdllh " ya amsa shi ma kamar yanda yaji abie ya amsa, fira su ka ɗan shiga taɓawa,nocking ɗin ƙofar parlorn a ka yi abie ne ya  ba da izinin shigowa, turo ƙofar su Aairah su kayi su ka shigo bakunan su ɗauke da sallama hannun su ɗauke da manya tray da mom ta shirya ma su abie breakfast ɗin su, amsa ma su sallamar su abie su kayi, table ɗin da ke tsakiyar parlorn su ka nufa, trays ɗin su ka sauke su ka ɗaura kan table ɗin haɗi da gaishe da su,cikin kulawa su ka amasa ma su musamman uncle sadiq,tsayawa su kayi sai da su kayi serving ɗin su tukun su ka nufi hanyar fita, parlorn su ka nufa wurin su mom da ke zaune kan dinning suna breakfast, dinning ɗin su ka nufa har sun ja kujeru za su zauna mom tace " yayan ku fa, kun kai mashi abinci ne "
"mom bari mu kayi sai mungama, ba su isa tashi ba yanzu " Aairah ta faɗa
Carab Ameera ta ce " ba su tashi ba fa mom" daƙƙuwa ummah tayi ma Ameerah, mom na faɗin " kunfi kowa sanin halin Abdallah, kar Allah ya sa ku kai masa zai fito ne ya same ku "
"mom Allah ba isa tashi ba yanzu"
"ku dai kuka sani,amma ni ba ruwana ya fito ya same ku ba ku kai ma shi abinci ba"
Ameera cewa tayi " ni dai Aairah ta so muje mu kai masa wallahi ina tsoron abun da zai biyo baya "
"sai kin dawo, gaskiya ni yunwa nake ji"
"ok haka kika ce ko "
"eh" Aairah ta faɗa yayin da ta ke kai bread a bakin ta
hanyar kitchen Ameerah ta nufa tana faɗin

"wallahi idan baki zo mun tafi ba saina cema ya Abdallah ke akace ki kawo masu ki kace baki zowa "
ɗan ɗaga murya Aairah tayi tana faɗin
"idan kin fasa, uwar yan jan sharri " daga kitchen Ameerah tace
"wallahi zaki san ni kike cema uwar ƴan jan sharri "
"eh ɗin in sani, ai na san dalilin da yasa kike son jaman sharri kuma ko mi zakiyi bazan ba da ba ehe " ɗaga murya Ameerah  tayi yan da Aairah zata jita sosai tace
" wannan kuma ke kika sani kar Allah yasa ki bada ƴar rainin hankali " gwalo Aairah tayi mata sai kace tana gaban ta tace
"oho dai, ban ba dawa " Ameerah na jin ta amma tayi bazan da ita,
Aaimah dai na jin su bata ce ƙala ba, sai zuba ma cikin ta abinci kawai take, Ameerah ce ta fito hannun ta ɗauke da trayn da ta shirya masu breakfast, zata wuce kenan Aaimah ta dakatar da ita tana faɗin  
" kawo na ɗaukar maki naga kamar kayan sun yi maki yawa, ke kuma wallahi Aairah sai kin gane baki da wayau "
"dan Allah ku rabu da ni, zuwa dai ne nace bazanyi ba koma mi zaki faɗa kin daɗe"
"haka kika ce " Aaimah ta faɗa, amsa Aairah ta bata da
" sosai ma kuwa, duk abun da zaku faɗa mashi kun daɗe " ta ƙarasa maganar tana murguɗa ma Aaimah baki
"haba yarinya kamar a gabansa kika yi haka"
"dan Allah ya isa haka, ke Aairah tashi ku tafi ko gaisawa ai kunyi da safwan"
"mom zanje idan na gama " Aairah ta faɗa, kallon su Aaimah mom tayi tana faɗin " to ke wuce ku tafi ba dole sai kunyi zuga ba, ke da Ameerah ma ai ya isa "
"mom ai ta je ta gaishe da ya safwan ko "
"za taje ai tace idan ta gama, maza ku wuce ku" da to su ka amsa haɗi da nufar part ɗin, suna tafe suna surutun da suka saba amma fa acewar Abdallah, suna isowa bakin part ɗin Ameerah ce tayi nocking har ta ɗaga hannu zata sake wani nocking sai gashi an buɗe ƙofar, safwan ne tsaye jikin shi sanye da ɓakar jallabiya, da fara'a a fuskar Ameerah tace
"ya safwan ina kwana, fatan an tashi lafiya" fuskar shi shima da fara'a yace "lafiya lau,ina su ummah"
"suna main parlor suna breakfast, ga naku nan kai ma mun kawo maku kai da ya Abdallah " murmushi yayi a zuciyar shi yace " Ameerah ba dai surutu ba,  Aaimah ce tayi gyaran murya tana faɗin
"to ni dai a bani wuri na wuce dan na gaji da tsuyuwa" girgiza kai safwan yayi da murmushi a fuskar shi yace
"Aairah uwayen ƙorafi, zo ki wuce kar ki faɗin ƙasa " ya faɗa haɗi da matsa mata hanya, ciki ta shige tana faɗin " wai dan Allah mi yasa ya safwan kake ce man Aairah ne, ba fa ita bace wannan Aaimah ce " ta faɗa yayin da take ajiye tray ɗin kan carpet, Ameerah ma bayanta ta bi ita ma ta ajiye wanda yake hannun ta
"to naji ina ita Aairah take na ganku ku ka ɗai, ita bata zuwa a gaisa" 
"tana parlor wurin su mom " Aaimah ta faɗa yayin da take nufar ƙofa
"to ki kira man ita Please" da to Aaimah ta amsa haɗi da nufar ƙofar fita su ka fice,  tana zuwa wurin su mom tace "Aairah ki je ya safwan yana kira" ɗagowa Aairah tayi tana faɗin ni kuma
"A'a ba ke ba ni " Aaimah ta faɗa yayin da take jan kujera ta zauna
"dallah daga tambaya zaki wani mai da man da baƙar magana "
"an mai da maki, dallah malam idan zaki tashi kije ki tashi idan kuma bazaki tashi ba kiyi ta zama ƴar rainin wayau, wai ke A'a ni " Aaimah ta faɗa tana kwai kwayon yanda Aairah tayi magana,
Aairah tace " mom kina jinta ko,daga maganar ariziƙi sai ta tsiya "
dafe kai mom tayi tana faɗin
"ya Allah, ke Aaimah kar na sake jin bakin ki ke kuma Aairah tashi kije kira da yake maki " 
tashi Aairah tayi tana hararar Aaimah, taɓe baki Aaimah tayi tana faɗin
"inga sun zazzago ƙasa  sannan zan san kina harara"tsaki Aairah taja haɗi da wuce wa ta nufi  part ɗin Abdallah, girgiza kai ka wai mom tayi ba tare da tace ma su komai ba.
Nocking tayi, izinin shiga aka bata, tura ƙofar tayi ta shiga, zaune yake kan sofa  kamar yanda su Aaimah su ka barshi hannun shi ruƙe da cup ɗin tea sai turiri yake,yayin da Abdallah ke zaune kan carpet yana haɗa breakfast fitowar shi kenan daga bedroom ya samu an kawo masu breakfast, safwan  ɗago da fuskar shi yayi ya zuba mata ido haɗi da amsa mata sallamar da tayi, gaishe da su tayi tana faɗin " ya safwan gani,Aaimah tace wai kana kira na " amasa mata gaisuwar yayi yana faɗin
"dama ba wani abu bane, kawai naga baki zo bane shine na ce su kira man ke mu gaisa tunda ke baki zo ba "
"zan zo ya safwan breakfast nake ne shiyyasa "
" ok yayi kyau, kin tashi lafiya"
" lafiya lau "
" masha Allah "
" ina iya tafiya " ta faɗa dan duk ta gaji da tsayuwa da kuma kallon da yake mata
" eh kina iya tafiya dama kiran kenan "
"to sai anjima " ta faɗa haɗi da ju yawa zata wuce Abdallah ne yace " ki dawo anjima ki kwashe wannan kayan " ya faɗa yana nuna mata kayan breakfast ɗin da ke gaban sa, da to ta amsa haɗi da kama hanyar ficewa, idanu safwan zuba mata har sai da ta ɓace ma ganin sa tukun ya janye idon sa, karb su ka haɗa ido da Abdallah, hararar shi yayi yana faɗin
" lafiya da wannan kallon malam " taɓe baki Abdallah yayi yana faɗin
" aiki ya zo ga ma iya "
" ƴan sa ido ba " safwan ya faɗa
" mi zan sa ma ido a nan, Allah ya kiyaye " Abdallah ya faɗa yana mai da kanshi kan breakfast ɗin da yake yi
"Ohon maka kuma  wannan " safwan ya faɗa shima yana kai cup ɗin tea dake hannun shi baki, babu wanda ya sake cewa komai cikin su.

_*✨LAGOS✨*_

Zaune yake a office ɗin shi yana aiki, files ne gaban shi na patient yana duba wa, wayar shi ce ta fara ringing, hannu ya sa ya ɗauko ta, du ba mai kiran shi yayi, privet number shine abun da ya gani, tsaki ya ja haɗi da yin rejecting kiran ya cigaba da abun da ke gaban shi, wani kiran ne ya sake shigowa, ko kallon inda wayar take bai yi ba haka taita ruri har ta gaji tayi shiru alamar mai kiran ya gaji
sai ga message ya  shigo, ɗaukar wayar yayi dan ganin wanene ya turo mashi message, baƙuwar number ce ya gani kuma da alama bata nigeria ba ce, buɗe message ɗin yayi ya fara karan tawa kamar haka

_DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN,manya yan aji bakwai ba'a ɗaukar baƙuwar number,ganinka  kuma sai an cika form,wow i like your style  keep it up na san nan gaba zai yi maka amfani, ba komai bane ya sa nake neman ka ba face ina so na sanar da kai illar dake cikin yaƙin da kake son  jefa kanka aciki,manyanka ma sunyi ba suci riba bare kai ƙaramin alhaki, ko da yake hausawa na cewa barewa baza tai gudu ɗan ta yayi rarrafe ba malam Abdulƙadir o afuwan dr Abdulƙadir, kar kace na mai da kai malamin makaranta 😊, ya ta kwaranka kuma kakan ka,mun kwana biyu ba mu gaisa ba amma da alama yanzu na lura  kana so mu dawo da zumunci dake tsakanin mu , fatan yana lafiya shi da hajiya zainab ina nufin ummy????, 
Abdulƙadir ina mai baka shawara idan har kana son zamanka lafiya a duniyar nan to ka tsame hannuka daga abun da kake shirin aikatawa gudun aikata abun da zai jefa ka cikin matsala kai da iyalanka, fatan zaka ɗauki shawarata duk da na san kai mai taurin kai ne, amma ina mai baka shawara._

Wani wawan tsaki shazim ya ja lokacin da ya kawo ƙarshen message ɗin yana faɗin " aikin banza matsoracin banza da wofi kawai, mu zuba mu gani ni da kai da duk wani mai hali irinka shege ka fasa " ya faɗa yana
maida kanshi yayi kan abun da yake, wani tsakin ya sake ja yana sake faɗin " aikin banza matsoracin banza da wofi kawai "

Ƙofar office ɗin yaji an turo an shigo, majeed ne ya shigo a uzirce kamar wanda aka jeho, wurin shazim ɗin ya matsa yana faɗin " amshi shazim ka gani " ya faɗa yana miƙa ma shazim wayar shi, amsar wayar shazim yayi yana duba abun da majeed ɗin ke nuna mashi, text message ne shima aka turo mashi da irin number da aka turo ma shazim yanzu, karanta message ɗin shazim ya shiga yi

_ABDULMAJEED MA'ARUF WAKILI,na san za kayi mamakin wanene ni da kuma sunan ka da na ambata, kar kayi mamaki yanyi ne ya zo da haka.
a taƙaice dai abun da ke tafe da ni,  ba wani abu bane face ina so na ja maka kunne kai da  abokinka, ku rufa ma kanku asiri ku fitar da kanku acikin yaƙin da  iyayen ku su ka kasa,idan kuma ba haka ba zaku sa kanku cikin bala'in da ba kuyi tsammani ba ku da iyalanku, shawara ce idan kun  ɗauka  ku zata yima amfani idan kuma kun ƙi to duk abun da ya biyo baya  kuyi kuka da kanku._

Tsaki shazim yaja yana miƙa ma majeed wayar shi, amsa majeed yayi yana faɗin
" ni dai shazim a ganina mu fitar da kan mu a wannan matsalar ko dan su Ammy "
" tsoro kaji ne wai majeed?"
" dole naji tsoro shazim, barazana fa yake mana, ni abun da nake ganin zai fi shine kawai kayan nan mu miƙa ma hukuma su "
" to dan yana mana barazana sai mi, ya isa yayi mana abun da Allah bai nufa ba ne, sannan kaya da kake cewa mu miƙa ma hukuma su tamkar munji tsoron ne, kuma Allah zai kama mu da laifi duk wanda ya cutu a kan kayan "
" bai 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login