Showing 54001 words to 57000 words out of 127932 words
masu ba"
"amma momy baki ji mi tace man ba "
"koma mi tace, ai ba ƙarya tayi ba, kin iya girkin ne " ran feenah in yai dubu to ya ɓaci jin momy ta goyi bayan sa'ada
"momy wai miyasa kike haka duk abun da sa'ada zata man idan na ce zan dake ta sai ki hana "
"dole na hana, saboda komi tai maki laifin ki yafi yawa "
"shikenan momy tun da haka ki kace " tana gama faɗa ta wuce fuuuuu kamar zata tashi sama, sa'ada tace azuciyar ta "nasan daga nan sai part ɗin innah"
babu wanda ya bi ta kan feenah daga momy har fatima, aikin dake gaban su suka kama, sai da suka kammala komi suka jera abincin kan dinning,Abdallah kuma cikin basket suka jera mashi shi da shazim, dama girkin saboda shi su kayi shi bayan sun gama su ka wuce bedroom ɗin sa'ada domin yin wanka, fatima ta fara shiga wanka sa'ada kuma ta ɗauko masu kayan da zasu sa, fatima na fitowa sa'ada ta shiga , shaf shaf suka shirya su ka fice zuwa kitchen, basket ɗin da suka jera ma Abdallah suka ɗauka, direct part ɗin su shazim suka nufa,tsit part ɗin kamar ba kowa, sama su ka wuce zuwa bedroom ɗin shazim, sa'ada ce tayi nocking shiru ba'a basu izinin shigaba sake nocking ɗin tayi still shiru, fatima tace "ko dai suna part ɗin uncle Ahmad "
"ba mamaki suna can "
fatima tace "amma bari nayi nocking ɗin ɗakin ya noor may be shi yana nan" juyawa tayi zuwa bedroom ɗin noraiz tun kafin tayi nocking a ka buɗe ƙofar , noraiz ne ya fito shi da mahmud da alama fita zasu yi, bim su da kallo su kayi noraiz yace "ku kuma lafiya ku kayi curko curko da basket a hannu "
fatima ce tace "daman su ya dr muka kawo ma abinci, munyi nocking shiru"
"to ku ajiye kan dinning mana"
"a'a gaskiya ya noor, idan kuma basu dawo part ɗin ba da wuri fa, zai iya yin sanyi "
"to tun da gudun yayi sanyi kuke mu sai ku bamu muci "
"a'a wallahi ya noor, ba fa naku bane, idan zaku ci yana can part ɗin momy" mahmud yace "mu da yake bamu da galihu ko "
"ni ba haka nake nufi ba" hannun noraiz ya ja "wuce mu tafi" ficewa su kayi su fatima su ka bi bayan su zuwa part ɗin uncle Ahmad,suna shiga part ɗin mansoor su ka nufa, nocking su kayi, izinin shiga aka basu, tura ƙofar su kayi suka shiga zaune su ka samu Abdallah da mansoor shazim na kwance kan three seater idanuwan shi a rufe da a lama bacci yake, sallam su kayi, amsa masu sallamar su kayi "ina wuni ya dr " fatima tace, gaishe da shi sa'ada tayi, amsa masu yayi cikin kulawa, sai sannan suka gaishe da mansoor ƙin amsawa yayi sai ma hararar su da yayi "ok sai yanzu kuka san da zamana ko " haɗa baki su kayi wurin faɗin
"a'a yaya "
"ba wani nan, ai na san zaman da nake da ku "
"a'a yaya "
"shikenan dai, mi aka dafa mana, naji tun da kuka shigo nake jin ƙamshi " fatima tace "abun daɗi, kuma na ya dr ne " zaro ido mansoor yayi "ai haka, abun ƴar wariyar launin fatace kenan dai " dariya fatima tayi
"wasa fa nake yaya, kaima kasan na ku ne" fatima sun shantake sai surutu su ke ganin boss na bacci,firar su kawai su ke, abun da basi sani ba idon shi biyu yana jin su banza kawai yayi da su, sai da yaji da gaske ba fita zasu yi ba sun samu wurin zama yasa shi buɗe ido yana faɗin "ke tashi ku ba mutane wuri " simi simi suka tashi su ka fice, mansoor ne yace "miye haka zaka wani kore su "
"an kore su ɗin " banza kawai mansoor yayi da shi bai sake cewa komi ba, tsaki Abdallah yaja yana faɗin "sai kace wani kafi rashin san surutu, zaka wani kore su " ta shi yayi ya nufi bedroom ɗin mansoor batare da yace masu ƙala ba, suma fita lamarin shi su kayi, mansoor ne yayi serving ɗin su basu jira fitowar shazim ba su ka kama cin abincin su, lokacin da zai fito har sun kusa kammalawa, zama yayi yana cema mansoor "nima sai ka zuba man ko"
"in dai ni zan zuba maka sai dai kar kaci ɗan rainin hankali " ɗaukar plate shazim yayi yana zuba abinci ba tare da ya sake ce ma mansoor ɗin komi ba.
fira mansoor da Abdallah su ke shazim kuma na cin abinci, da ya kammala fatima ya kira ta kwashe dishes ɗin,
sai da yamma liƙis Abdallah ya koma gidan uncle ahmad , fatima kamar tayi kuka, sai da yace mata zai dawo tukunnan ta haƙura, tare su ka tafi da shazim da mansoor a motar Abdallah, Abdallah ke driving mansoor na kusa da shi yayin da shazim ke baya, fira suke shazim na baya yana jin su amma bai sa masu baki ba har suka iso gidan uncle ahmad.
Episode 30_31
Horn Abdallah yayi a bakin gate ɗin gidan, ta ƙaramar ƙofa mai gadin gidan ya leƙo ganin motar Abdallah yasa ya koma da sauri ya buɗe mashi gate, ciki ya shiga da motar ya nufi parking lot yayi parking.
Kai masha Allah gidan ya haɗu ba'a cewa komi, part biyu ne gidan,ɗaya yafi ɗaya girma,ba laifi gidan yana da girma,
fitowa su kayi suka nufi ƙaramin part ɗin, ciki su ka shiga bakin su ɗauke da sallama, wata yar matashiyar budurwa su ka samu a parlor kwance kan sofa ta juya ma ƙofa baya, sallamar da suka yi ce ta sata tashi zaune haɗi da amsa masu sallamar,baza ta wuce shekara 19 zuwa 20 a duniya, sanye take da english wear's riga da skirt, cikin parlorn su ka shiga, haɗi da samun wuri kan sofa suka zauna, gaishe da su wannan budurwar tayi tana kallon Abdallah " yaya jiya muna ta jiran ka ka dawo baka dawo ba "
"yanzu ai gashi na dawo ko "
"amma sai da yamma, wai ma ina kaje"
"to uwar masu iya surutu, ban sani ba wuce ki kira mana ummah"
"yaya nice ma mai surutun ko"
"zaki wuce ko sai ranki ya ɓaci" barin wurin tayi tana turo baki, wata ƙofa ta nufa, ba nocking kawai ta buɗe ƙofar ta shige bayan kamar minti biyu sai ga wata kyakyawar mace ta fito daga ɗakin jikin ta sanye da gown ta material, a ƙallah zata yi kimanin shekara 40 a duniya, ba fara bace amma bazaka kira ta da baƙa ba chocolate ce kamar ɗiyar ta, ƙarasowa tayi cikin parlorn tana faɗin "Abdallah daga bari naje na dawo sai kwana " murmushi Abdallah yayi ba tare da yace komi ba, gaishe da ita su shazim su kayi,fuska ɗauke da fara'a ta amsa tana faɗin "daga ziyara sai ku riƙe mana shi harda kwana"
mansoor ne yace " ai gashi nan mun dawo da shi "
"ai duk da haka" murmushi kawai su ka yi
"Ya su umman fatan suna lafiya?"
"lafiya lau su ke" fira suke da matar cikin nishaɗin amma ban da shazim, dan shi yama ƙosa su tashi, tashi tayi tana faɗin "sai fira muke ba'a kawo maku abinci da ruwa ba " mansoor ne yace "a'a ba komi yanzu zamu wuce "
"a'a gaskiya sai kunci ko da snacks ne, bari na sa Ameera ta kawo maku " tana faɗa ta koma ɗakin da ta fito ɗazu,shazim yace "ba sai ta kawo ba A hashim tafiya zamu yi " rai a ɓace
Abdallah yace "wallahi baku isa ba kuna nan har sai uncle ya dawo " ganin ranshi ya ɓaci ne yasa mansoor cewa su jira ɗin, fasa tafiyar su kayi, Ameera ce ta shigo parlorn hannunta ɗauke da tray ruwa ne da lemu, ajiye wa tayi a gaban su shazim, inda ta fito inda nake kyautata zatun kitchen ne can ta koma, sai gata ta fito hannunta ɗauke da snacks wata na biye da ita da bowl ɗin kayan marmari, a gaban su shazim ta sake ajiyewa, wacce suka fito tare ce ta gashe da su shazim, barin parlorn su kayi suka koma inda su ka fito, sai da Abdallah yayi da gaske sannan shazim yaci wani abu daga cikin abun sa aka kawo ma su, sun jima a gidan har sai da uncle Ahmad ya dawo suka gaisa, uncle ahmad yana matuƙar kama da abie sai dai abie ya fishi hasken fata,sun jima suna fira dashi, yanda ya sake masu kamar abokin su,da zasu tafi shida Abdallah su kayi nasu rakiya har parking lot.
lokacin da su ka koma estate lokacin kusan ƙarfe goma da rabi na dare, kowa ma kwancin shi ya nufa, alawala yayi ya kabbara sallah,daya gama adu'a kwai yayi ya kwanta.
Haka kwana ki su kai ta tafiya har
shazim sunyi tsawan sati ɗaya da kwana biyar da zuwa abuja,a cikin kwana kin nan kunsan kullum sai Abdallah yazo wurin su ko su suje, fatima ma da sa'ada zuwan su gidan uncle Ahmad biyu, har lokacin su uncle ahmad basu sanar da shi kiran da suke mashi ba, shi kuma bai tambayi kowa ba ya dai zuba masu ido idan har basu sanar da shiba, yayi alƙawarin bazai tambaye su ba zai haɗa kayan ahi ne kawai ya koma logas, ya gaji da zaman abuja, aikin shi ne kawai ke damun shi, shi da yazo da niyyar kwana biyar, ya kai wannan lokacin ne saboda Ammy, amma da ba dan haka ba da tuni ya daɗe da komawa,har ammy ya kira yace shi dai zai dawo, amma sai ta hana shi tace ta zauna har sai in sun sanar da shi kiran da suke mashi, ba dan yaso ba ya haƙura.
kullum idan mansoor zai tafi aiki tare suke tafiya.
kwance yake kan bed ringing ɗin wayar shi ne ya tashe shi,lalubo wayar, a hashim ne ke kira , picking call ɗin yayi haɗi da yin sallama sannan ya ɗaura da cewa"lafiya kira da sassafe haka? " banajin mai a hashim ke cewa, na dai ga shazim yayi murmushi da alama a hashim ya bashi amsar da ta dace da maganar da yayi,sannan ya ce "kar ka damu very soon" sun ɗan jima suna waya sannan suka yi sallama, tashi yayi ya nufi toilet, bayan kamar minti 5 sai gashi ya fito ƙugun shi ɗaure da farin towel,clothes set ɗin shi ya nufa cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin wani yadi fari da baƙi mai taushi da ɗaukar hankali, gaban dressing mirror ya nufa kwalbar turare ya ɗauka ya feshe jikin shi,wayar shi dake kan bed ya ɗauka sannan ya fice ya nufi hanyar fita tana zuba ƙamshi, part ɗin uncle ahmad ya nufa a bakin ƙofa yaci karo da mansoor, mansoor na ganin shi yace "dama wurin ka zani, naga har kusan 11 baka fito ba kana can kwance" ɗan ya tsine fuska yayi yana faɗin
"wallahi kuwa abun da ban taɓa yi ba kenan, amma yau ban san ya akai ba "hannun shi mansoor ya ja yana faɗin "mushiga ciki kayi breakfast may be gajiyan jiya ne "ciki suka shiga mama da kairiyya suka samu a parlor gaishe da mama yayi kairiyya ta gaishe da shi mama na faɗin "ga breakfast ɗin ku can kan dinning " tashi suka yi suka nufi dining ɗin, kairiyya tayi saving ɗin su tana kammalawa ta dawo kan sofa, mahmud ne yashigo shi da noraiz, wurin su shazim suka nufa suka gaishe da su, suma suka zauna domin yin breakfast ɗin.
suna kammalawa shazim da mansoor suka fice daga part suka nufi na uncle Ibrahim.
zaune take kan sofa ta juya ma ƙofa baya sallamar su ce tasa ta juyowa, fuskar ta da fara'a ta nufe tana gaishe da su, mansoor ne ya amsa amma shazim ɗaure fuska yayi kamar an aiko masa da saƙon mutuwa
"bro ana gaishe da kai "
"naji" shine kawai abun da yace,kuka ne ya ciyo feenah ta rasa mi tayi ma shazim yake wulaƙanta ta, ace ko gaisuwar ta baya iya amsawa, juyawa tayi da sauri ta nufi bedroom ɗin ta kukan na neman kufce mata
"gaskiya baka kyautawa, narasa miya sa ka tsani feenah kwata kwata baka son ta, in ta gaishe ka baka son amsawa wai miye duk hakan "
"ka gama"fuska da alamun ɓacin rai mansoor yace
"ok ni kake cema nagama ko yayi kyau"
riƙo hannun shi yayi yana faɗin"sorry bro kai." bai ƙarasa maganar ba saboda fisge hannun shi da mansoor yayi yana faɗin "rabu dani bana son jin komi daga gare ka" yana gama faɗa ya juya ya bi bayan feenah, ɗaga kafaɗa shazim yayi irin abun bai dame shi ba,sama ya nufa wurin uncle Ibrahim,yazo shiga kenan yaji yayi karo da mutum har sai da ya ɗan ja baya ,ɗagowa da kanshi yayi yana kallon luqman dake gaban shi tsaye yana liliya goshin shi da alama yaji zafin karon da suka yi, kallon shazim yayi yana faɗin "kayi hauka ne" tun kafin ya ƙarasa shazim ya ɗauke shi da wani mummunan mari har sai dai ya kusa faɗuwa, cikin azabar zafi ya ɗago yana faɗin "wannan wane irin zalunci ne azzalumi kawai mugu"sake wanka mashi mari shazim yayi har sai da ya duƙe kasa, amma duk da haka bai fasa ce mashi azzalumi ba,shaƙo wuyan rigar shi shazim yayi haɗi da kai mashi duka a baki, wahalalliyar ƙara luqman ya saki dan ba ƙaramin zafi yaji na har bakin shi ya fashe,uncle Ibrahim ne da ya fito sai ga mansoor da feenah har da momy sun nufo sama ta dalilin ƙarar da luqman ya saki,ganin yanda ya shaƙe mashi wuya ne yasa uncle Ibrahim cewa "shazim miye haka kashe shi za ka yi ne, wai ma miya haɗa ku ne kake mashi irin wannan dukan"
cikin kukan wahala luqman yace" ba abun da nayi mashi ya hau duka na, da yake azzalumi ne shi" wani sabon naushin ya sake kai ma luqman a baki, cikin sauri uncle Ibrahim ya ƙaraso kusa da su dan tun da ya fito yana tsaye ne a bakin ƙofa, hannun shazim ya fize daga riƙwan da yayi ma luqman yana faɗin "shazim baka da hankali ne illata shi kake son yi ne?" ran shazim ne ya ɓaci da maganar uncle Ibrahim, yasan cewa luqman bai da kunya kwata kwata kuma ya raina shi ya san dole sai da dalili zai mashi wannan dukan,amma da alama laifin shi yake gani, ce mashi yayi"eh, tun da shi bashi da hankali, bai san ina ke mashi ciwo ba"
"shazim ni kake faɗa ma haka?" banza yayi da uncle Ibrahim sai ma kama hanyar fita yayi, riƙo shi mansoor yayi yana faɗin "baka ji ana maka magana za ka fice" cikin tsantsar l ɓacin rai shazim ya ce "sakar man hannu na mansoor" ƙin sakar mashi hannu mansoor yayi, ganin bazai sakar mai hannu bane yasa shi fizge hannun shi ya fice daga part ɗin bin bayan shi mansoor yayi yana ƙwala mashi kira ,da kallo uncle Ibrahim ya bi su har suka bar part ɗin ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli luqman yana faɗin"maganin ka kenan luqman, tun yaushe nake maka faɗa akan ka daina shiga harkar shi amma baka ji, yanzu da bama kusa Allah ka ɗai yasan irin illar dazai yi maka "cikin kuka luqman yace"yanzu dady goyan bayan shi kake, duk irin wannan dukan da ya yi man"
"dole na goyi bayan shi dan na san halinka da rashin kunya, kuma haka nan bazai rufe ka da duka ba batare da kayi mashi komi ba "cikin ɓacin rai luqman yace "tun da haka ne dady, wallahi sai na rama bazai dake ni a banza ba wallahi"juyawa yayi zai bar wurin da sauri uncle Ibrahim ya jawo hannun shi yayi yana faɗin "ashe baka da hankali ban sani ba,dallah wuce ciki sakarai kawai " ya faɗa haɗi da janshi suka shiga parlorn shi aka bar momy da feenah tsaye, feenah ce tace "wai miyasa ya shazim ya tsane mu ne, ji dukan da yayi ma ya luqman dan Allah" ɗan nisawa momy tayi sannan tace "idan har da laifin shazim to na innah yafi yawa dan ita ta haddasa komi, ita tasa luqman bai ganin shazim da mutunci"
"haba momy yaza kice haka,ba ruwan innah, dama chan ba son mu yake ba"
"nace hakan,duk ba ita ta haddasa komi ba tasa kuka tsane su ku ke mashi rashin kunya,ke ma duka yaushe kika dai na raina shi, dalla wuce ki bani wuri" wucewa feenah tayi tana turo baki ta nufi ƙofar fita zuwa part ɗin innah, a bedroom ta same ta mai aikin ta na shirya mata kaya a wardrobe, kallon mai aikin feenah tayi tana faɗin "ke tashi ki bamu wuri"ta shi talatu tayi ta fice, kallon feenah innah tayi tana faɗin "ke kuma lafiya kika korar man mai aiki? " zama tayi bakin bed ɗin tana cewa "tacika sa ido ne da gulmar tsiya"
"to aikuwa ke zaki ƙara sa man tun da har kika kore ta "ɗan ya tsine fuska feenah tayi tana faɗin "ai yanzu zan tashi sai ta zo ta ida maki"sannan ta ɗaura da cewa "innah kin san mi ya faru kuwa?"gyara zama innah tayi tana faɗin "a'a sai kin faɗa,mi ya faru"
"hmm ya shazim ne yayi ma ya luqman dukan tsiya har da fasa mashi baki"zaro ido innah tayi haɗi da rike haɓa tana faɗin "wallahi bazai yiwu ba, shikuma sai luqman ɗin ya tsaya kamar wani sakarai har ya zubar mashi da jini"
"to kema innah in ban da abunki ina ya shazim ina ya luqman "miƙewa innah tayi tana cewa "to wallahi bai daki banza, ka gaman azzalumi yaro"ficewa tayi daga bedroom ɗin tana masifa ta nufi part ɗin uncle Ibrahim, momy da ke zaune kan sofa tun daga waje ta fara jiyo masifar innah, sai gata ta shigo, tana ganin momy tace "ina Ibrahim ɗin yake? " sama momy ta nuna mata da hannu, fuuuu innah ta wuce zuwa sama tana ta zazzaga masifa,tana shiga parlorn ta samu