Showing 66001 words to 69000 words out of 127932 words

Chapter 23 - DOCTOR SHAZIM HAUSA NOVEL

01 Apr 2025

6710

kike shazim ba zai mare ku ba haka nan dole da abun da kuka yi mashi, kuma ma ko ba abun da kuka yi mashi ya mare ku yayi man dadai dan kun cancanci fiye da haka " jin abun da gwaggo Halima tace ne yasa feenah ƙara sautin muryar kukan da take, sai Aunty maryam ta faɗo parlorn kamar an jehu ta "mi nake ji, ba dai wannan mara mutuncin ba ne ya mare ku"
tsawa gwaggo Halima taa daka mata " ke maryam ki shiga cikin hankalin ki na ƙara jin kin faɗi wani abu a nan ranki zaiyi mumunnan ɓaci shashasha kawai kema"
turo baki maryam tayi tana faɗin
"haba Aunty mi yasa zaki ce haka, du ba fa kiga fuskar feenah duk sahun hannun shi, in ban da zalinci mi suka yi mashi har haka "
gwaggo Uwani ta fito tana faɗin "wallahi bai mari banza ba "
gwaggo Halima tace "yaya sai dai fa ki ga laifin shazim,  amma ko rantsuwa nayi bazan kaffara ba su ke da laifi "
"dama haka zaki ce  tunda da man ba son ganin laifin shi kike ba "
"Wai miyasa a kullum kike cewa, ina goyan bayan shi ne, ni ba goyan bayan shi nake ba kawai ina goyan bayan gaskiya"
" to ai sai ki ta goyan bayan gaskiyar, amma wallahi bai mari banza ba sai ya gane kuskuren shi "
"to shikenan in dai shazim ne ga kai ga fata "
"Wallahi Aunty laifin su " sa'ada ta faɗa wacce shigowar ta part ɗin keknan,juyawa su kayi su duka suna binta da idanu, gwaggo Uwani ce tace" munafuka ubanwa yasa bakin ki daga shigowar ki " turo baki sa'ada tayi " wallahi ba ƙarya nake ba,Aunty Ilham ce ta mari fatima kawai dan tayi magana bata jita ba, ita kuma Aunty Feenah tasa ɗan kwalinta ta shaƙe mata wuya bayan tasan tana da matsalar numfashi "
tafa hannu gwaggo Halima ta shiga yi tana salallami " yanzu da kashe ta ku ka so yi kenan, dan uban ku ku sau nawa mutum ke maku magana kunayin banza da shi bayan kuna jinshi , wallahi da ni na riƙa ku da sai kun yaba ma aya zaƙinta mutanen banza kawai "
gwaggo Uwani tace "ke yanzu kenan harkin yarda da maganar wannan shashasha yarinyar "
"dole na yarda da ita dan na san sa'ada bazata yi masu ƙarya ba"
Feenah tsagai tawa tayi da kukan da take ta kalli sa'ada tana faɗin "wallahi kika bari na kama ki sai kin gane baki da wayau " duka gwaggo Halima ta kaima feenah "dan ubnki idan kin kama ta kiyi mata bungun da zata kasa tashi mar mutunci, kuma wallahi daga ke har Ilham ɗin sai nasa Usman yayi maganin ku "
" a kan mi zaki haɗa su da shi, duk wannan marin da wannan mara mutuncin yayi masu bai isa ba "
"ai mai sauƙi yayi masu, gara nasa usman yayi masu dukan da ko wani su kaga zai dake ta sa hana, bari ma kiga yanzu zan kira shi "
"a'a sadiya kar ki kira shi a bar zancen kawai ya mutu "
"idan har kinga zancen ya mutu to sai idan ita fatimar ce tace ta yafe masu "
"wallahi baza ki ja masu raini a wurin yarinya ba, tun da dai zancen ya wuce a barshi kawai "
" idan fa ba ita tace zancen ya wuce ba to fa bazai wuce ba, sa'ada kira man fatimar " da to sa'ada ta amsa haɗi da fita,ko da taje part ɗin shazim ta samu a parlor, gaishe da shi tayi, harta miƙe zata nufi ɗakin fatima yace mata bacci take saboda maganin da ya bata, koma wa tayi part ɗin Innah ,  ganin  ta dawo ita kaɗai ne yasa gwaggo halima tace " ina fatimar take "
"ya shazim na samu a parlor yace bata jin daɗi ya bata magani bacci take"
"to yaya kin dai ji ko, har sun kaita ga kwanciya, wallahi ko suje har part ɗin su bata haƙuri ko yanzu nasa Usman yayi maganin su "
"dan Allah dai ki ƙyale su,tun da harya bata magani zata ji sauƙi ne "
"sai fa sunje sun bata haƙuri, idan ba haka ba kuma tam"
"ba inda zasu, wai ke sadiya mi ke damun ki,  to kisa usman ɗin ya dake su " innah ta faɗa wacce shigowar ta kenan daga part ɗin uncle Ahmad
"mama dukan fatima  fa su kayi bayan sun san tana da matsala "
"koma mi su kayi mata baza su bata haƙuri ba "
"shikenan mama, amma bana jin daɗin abun da kuke yi "
"dallah ni yiman shiru tun da baki san ciwan ƴaƴan ki ba "
"Allah ya huci zuciyar ki " kawai gwaggo halima ta faɗa haɗi da tashi ta shiga kitchen, zama innah tayi kan sofa hannu ta miƙa ma feenah " zo nan ƴar albarka dai na kuka zai gane bai da wayau, yi shiru kinji " matsowa tayi kusa da innah ta ɗaura kanta saman kafaɗar ta "kar ki damu sai yayi dana sanin marin da yayi maki har ita munafukar fatimar,  Allah dai ya kaimu anjima" lallashin feenah innah tai tayi har sai da taga ta shiru.

✨SHAZIM✨

duk wani shiri da zai masu na tafiya yau ya kammala , shi ka ɗai yake kiɗan sa yake rawar sa, bayan mansoor ba wanda yasan da shirin shi na tafiya yau jira kawai yake su uncle su yi taron su da yamma su kuma su wuce, fatima ce ta fito daga ɗakin ta parlor ta nufo har kan sofar da take kwance, gaishe da shi tayi sannan tace mashi za ta je part ɗin uncle Ibrahim ta ɗauko kayanta,da to ya amsa mata haɗi da ce mata kar ta saki ta daɗe, to tace ta fice zuwa part ko da ta shiga ba kowa a parlor ɗakin sa'ada ta shiga samunta tayi zaune gaban dressing mirror tana shafa powder zama fatimar tayi kan gado tana kallon sa'ada da ke kallonta ta cikin mirrorn
"Wai lafiya sister kike kallo na kamar baki sanni ba "
"Fatima ai dole na kalle ki, wai daga bari ki ɗauko magani shikenan ko "
" wai dama dalilin da yasa kike man wannan kallon ne "
"Ok tambaya  ta ma kike "
ganin kamar ran sa'ada ya ɓaci ne yasa fatima cewa"sorry, ya shazim ne yace na kwana can "
"Ok ya jikin na ki "
"da sauƙi "
"Allah ya ƙara sauki, yau ɗin zaku tafi?"
"yanzu ma kaya na nace mashi zan ɗauko"
"ok naso ace ya shazim ya bari ko da zuwa gobe ne "
"nima naso amma ya zanyi" fira su ka shiga yi duk akan tafiyar da su fatima za su yi sa'ada kamar zata yi kuka, anan fatima tayi wanka , bayan sun shirya ita da sa'ada sallah su kayi batan sun gama ne su ka nufi  ɗakin momy , da sallama su ka shiga momy na zaune kan carpet ta gama sallar, jiranta su kayi har ta kammala,  fatima tace "ina wuni momy"
"lafiya lau fatima, ya jikin ki "
"naji sauƙi"
"to Allah ya ƙara sauki, kiyi haƙuri kinji"
"bakomi momy"
"momy wai ya shazim yace zasu tafi, dan Allah kice ya bar fatima nan shi ya tafi "
"A'a gara dai su tafi, kuma ma fatimar ba makaranta zata fara zuwa ba "
"eh momy amma ai da sauran lokaci "
"duk da haka dai "
"momy baki son su tsaya ne "
"kinci gidan ku " turo baki sa'ada tayi tana faɗin "dan Allah idan kina so su tsaya ki roƙi ya shazim ɗin pls"
" sai kuma kiyi"
" shikenan momy tun da baza ki ba shi haƙuri ba bari na faɗama dady shi sai ya bashi, dama dady bai san zasu tafi yau ba " ( da yake suna gida shi da uncle Ahmad  ) ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi ƙofar fita
" kika saki ko ƙafar ki ta taka waje sai ranki ya ɓaci dan baki da hankali bai faɗama dadyn ku ba shine ke zakije ki faɗa mashi kin dawo kin zauna kafin ranki ya ɓaci "
da wowa tayi tana turo baki " momy to dan Allah ke ki bashi haƙuri ya barta "
"Kima daina yi man  magiya,gara su tafi ko itama ta huta "
ba yanda sa'ada bata yi ba amma momy tace bazata ce ma shazim ya bar fatima ba, har part ɗin uncle Ahmad su kaje nan ma sai da sa'ada ta roƙi mama kan tasa baki shazim ya bar fatima amma ita ma tace ba ruwan ta, tama fiso su tafi dan sarai tasan halin su gwaggo Uwani a ka bar fatima wahalar su kawai zata sha kafin su tafi.

Kamar yanda su uncle Ahmad su kace zasu yi meeting a yau, basu fasa ba yanzu ma haka sun hallara a babban parlorn da su ke meeting, Innah ce kawai sai su gwaggo da su uncle ba yaran, tattaunawa su ka fara daga bisani uncle Ahmad yace ayima Zainab magana tattaro kan ƙannanta, a waya gwaggo Halima ta kira ta, zaman jiran shigowar yaran su kayi,Aunty zainab ce ta fara shigowa sai Aunty maryam da Amina da Asma'u,Farida sai Fiddausi, kairiyya da su fatima ta shigo sa'ada na ɗauke da salma ƙanwar kairiyya ce,  feenah da Ilham suka shigo wuri guda matan su ka zauna sai mazan
ya usman tare ya shigo da su Anwar, Mahammad, mahmud, luqman, noraiz, faisal, mubarak, Umar, musa harda ƙananan Aliyu da Aminu duka mazan sun hallara mutum biyu ne babu shazim da mansoor, ganin babu su ne uncle Ahmad yace "usman ina sauran ƙannan naka"tun kafin yace wani abu   gwaggo Uwani tayi carabtace " na san dai mansoor zai shigo wannan mara mutunci sai dai wani daga cikin ku yaje ya kira shi amma bazai zo ba " gwaggo Halima tace " yaya baki ganin zarau sai kin tsinka, yanzu idan ya shigo ɗin batare da wani ya kira shinba fah "
ta buɗe baki kenan zata mai da ma gwaggo Halima amsa, sai ga mansoor ya shigo da sallama a bakin shi shazim na bayan shi, jikin shi sanye da baƙin wando cargo sai t_shirt fara, kallon gwaggo Uwani gwaggo Halima tayi tana faɗin "to yanzu gashi nan ya shigo " tsaki gwaggo Halima tayi batare da tace komi ba, wuri su shazim su ka samu kusa da su usman su ka zauna,uncle Ibrahim ne yace Faisal ya buɗe masu taro da adu'a, tashi Faisal yayi yayi adu'a bayan ya gama ya koma mazunin shi ya zauna,sallama  uncle Ahmad ya fara sannan ya ɗaura da nasiha , kowa ya baza kunne yana sauraron shi har ya gama nasihar da ya fara sannan yace " a taƙaice dai maƙasu dun wannan taro ba komi bane face a kan maganar  ranar da muka tsaida ce ta auran wasu daga cikin ku, tun tuni munso ace  an kammala komi ranar auran kawai muke jira, sai dai hakan bai samu ba dalilin wasu da basu shirya ba a cikin ku muka ɗaga masu ƙafa zuwa wani lokaci, wasu sun gabatar da waɗan da suke so wasun ku kuma har yanzu shiru, yanzu dai munyanke hukuncin tsaida rana ga duk kanku da wanda suka gabatar da wanda su ke so da wanda su kayi kunnan uwar shegu da maganar,dama ɗaya ce zan ba ma wanda basu gabatar da zaɓin su ba tuntuni shine yanzu su gabatar mana, idan ba haka ba zamu zaɓa masa duk wanda ko wacce ta dace "
ɗan nisawa uncle Ahmad yayi sannan ya ɗaura da cewa" shazim da mansoor sai faisal  ina magan ne a kan ku,tun a wancan lokaci na yi maku magan akan ku gabatar man da zaɓin ku amma shiru, abun da nake so na sani shine baku da raɓine ko kuwa wani abun kuke nufi na da ban, to kun daiji mi nace yanzu idan kuna da magana muna sauraron ku kafin mu zartar da hukuncin da muka yanke, muna sauraron ku " tun da uncle Ahmad ya fara magana su ka sadda kai ƙasa,  kowa dake parlorn zuba masu ido yayi domin yaji abun da zasu ce,faisal ne yace " ni ina da wacce nake so "
Uncle Ibrahim ne yace "to muna sauraron ka"
"uncle dama farida ce "  shiru su kayi basu ce komi ba,fiddausi kamar tayi kuka jin mansoor ya ƙicewa komai, shi kuwa mansoor so yake shazim ya gabatar da wacce yake so duk da yasan da wahala ,  uncle Ibrahim ne yace " muna sauraron ku kunyi shiru,ko kawai mu cigaba da abun da ya tara mu " da sauri Mansoor yace"uncle ni ina da wacce nake so" ajiyar zuciya ta sauke jin yace yana da wacce yake so
Uncle Ibrahim yace " to masha Allah kana iya faɗa mana wacece "
"dama uncle ba kowa bace Fiddausi ce " murna kamar ta kashe Fiddausi jin mansoor ya ambace ta
" to masha Allah"
Uncle Ahmad ne yace " to saura kai shazim muna sauraron ka "
ɗagowa yayi ya kalli uncle ahmad sai kuma ya sake mai da kanshi ƙasa, tsit kowa yayi jiran abun da shazim zai ce kawai su ke, tsawan 4 minutes shazim baice komi ba
"to idan na fahimta har yanzu baka fitar da zaɓin naka ba kenan"
sai a sannan ya buɗe baki yace "a'a uncle "
"to muna sauraron ka "
"ina so a ƙara man lokaci,bayan na su mansoor sai ayi nawa "
"wannan ne baka isa ba shazim,da cewa mu ƙara maka lokaci yau kusan shekara kenan, sai yanzu kuma ka sake cewa mu ƙara maka wani  lokacin abun da bazi yuwu ba kenan "
Uncle Ibrahim ne yace " to yanzu dai munji ra'ayin wasu daga cikin ku,mansoor ya gabatar da Fiddausi a matsayin zaɓin sa faisal farida, Muhammad dama tuntuni mun san ya gabatar mana da kairiyya a matsayin zaɓin sa, to sai wasu da suka nuna ra'ayin yin aure yanzu duk da munfiso mu fara gamawa da manyan su amma tun da sun nuna ra'ayin su na son yin auren yanzu insha Allah za mu yi masu yanda su ke so, kafin nan ina so na sanar da hukuncin da muka yanke akan ga duk wanda bai gabatar da zaɓin shi ba  "
Uncle Ahmad yace "shazim ina so ka sauraremu da kayau, tun da munce ka fitar da wacce kake so kaƙi, to mun yanke hukuncin haɗa ka aure da ƴar uwar ka hauwa'u "
tuna ni shazim ya shiga shin wai wacece hauwa'u cikin yaran dan bai ma san wacece mai wannan sunan ba
Uncle Ahmad ne ya katse mashi tunanin da yake ta hanyar cewa " kayi shiru banji kace komi ba " carab innah tace "yo mi zai ce, daga ma anyi mashi gata "
"duk da haka innah muna son jin ta bakin shi, ina jinka shazim " shiru kamar bazaice komi ba can dai yace
"Uncle bangane wacece kake magana a kanta ba "
riƙe haɓa innah tayi tana faɗin "lallai ɗan iskan gaye wato hauwa'un ce baka sani ba saboda ka raina ma mutane wayau ko, to ba kowa bace face takwara ta feenah ince ita ka santa " wani mumunnan faɗuwa gaban shazim yayi,a zuciyar shi yake faɗin " amma an raina mashi wayau arasa da wacce za'a haɗa shi sai wannan daƙiƙiyar yarinyar, lallai sun shiraya ganin ɓacin ranshi kenan" uncle ahmad ne yace "to ka dai ji ko wacece, mi kace a game da hukuncin " banza shazim yayi da shi kamar ma ba da shi yake magana ba, har sai da mansoor ya zungure shi yace "bro ana magana kayi shiru " ɗago da kanshi yayi idanun shi sun kaɗa sunyi jawur tsantsar ɓacin rai ne a cikin su ya wurga ma mansoor wata mummunanar harara wacce tasa mansoor kauda kai dan bai taɓa ganin ɓacin rai a fuskar shazim ba irin na yau,   mai da kanshi yayi ya  ɗuƙar, gwaggo Uwani tace "yau ga rainin wayau, yan isaka ka ɗauke mu ana magana kayi shiru "wani ɗan iskan kallo ya  jefeta da shihar sai da gabanta ya faɗi  innah tace " kayi fiye da haka ma mara mutunci, aure ne dai sai kayi " feenah dai sai zare ido take tsoron ta kar shazim yace bai son ta
ganin ya mai da su mahaukata ne yasa uncle Ahmad girgiza kai ya cigaba da faɗin"waɗan suka buƙaci a sa ranar da su "
ban da murmushi babu abun da ke fita daga fuskar luqman tun kafin ma a kira sunan shi
Uncle Ahmad yace "luqman da mahmud muna sauraron ku ku gabatar da zaɓin naku muna ji " jin uncle ya ambace su ne yasa farin cikin luqman ƙaruwa, sai da uncle ya sake magana tukunnan mahmud yace "Ilham itace zaɓin da na kawo maku "
"to masha Allah Ilham muna so muji daga bakin ki kinji abun da ɗan uwan ki yace  " duƙar da kai Ilham tayi cike da kunya  tace " uncle na amince "
"masha Allah, Allah ya nuna man lokaci " da ameen kowa ya amsa, sannan uncle ahmad yace "to kai luqman mauna sauraron ka " gyara zama luqman yayi yana kallon Innah da wani munafukin murmushi a fuskar shi yace " uncle ni ba kowa bace zaɓi na face fatima " kamar saukar aradu haka fatima taji maganar luqman, ita yaushe harma su ka samu jituwa da zai ce wai yana sonta anya ba kunnuwanta  bane suka jiyo mata ba dai dai ba, shazim mamaki abun ya bashi dan shi bai san da wani zacen soyayya ba tsakanin luqman da fatima ba kuma da ace ya sani da tuni yayi ma tufkar hanci amma ko yanzu bawai lokaci ya ƙure bane in dai da ranshi da lafiayar shi zai ga wanda zai masu auren dole, watau meeting ɗin nasu ne ma kenan  dan su aka tara wannan taron kenan maganar uncle Ahmad ce ta dawo da su cikin hayyacin su " to fatima kinji abun da yayan ki yace miye ra'ayin ki " kasa cewa komi fatima tayi sai ma kuka da ta fashe da shi " yau ga iskanci, daga tambaya sai kuka, zaki buɗe baki ki ba mutane amsar tambayar da aka yi maki ko kuwa " gwaggo Uwani ce ta faɗi haka cike da masifa, sake fashewa da kuka Fataim tayi " haba yaya kamata yayi kiji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login