Showing 111001 words to 114000 words out of 153980 words

Chapter 38 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16342

nan bana son yayu so nake ayi aikin da zai ji baya kaunarta ya tsaneta bazai iya Aurenta ba Wanda da kanshi zaizo ya furta hakan" Yana buga kasa irin tasu ta y'an tsubbu ya ce "Wannan mai sauki ne saboda yaron bashi da wani karfin ibada sosai A yanzu ma za a iya Gamawa dashi amma ina Kara tunasar dake kinyi gaggawa zaki k'ara daukawa kanki zunubi ne a banza Bayan Abun daman bazaiyu ba Auren nan babushi na fad'a maki tun farkon zuwanki da maganar nan" eh Malam nidai ayi aikin hankalina zaifi kwanciya"Dubu Biyar din da saida ta sayar da fantekun ta na Aure ta bashi da niyyar idan Aiki yaci zata cika masa sauran "......yau ta kama Juma'a kuma yaune Ranar da za a fara Event din bikin Wanda yau walima kawai za ayi tunda Zarah ta tashi yau ta tashi da zazzabi mai zafin gaske da ciwon kai ga tashin zuciya Chuchu da Asmy kadai suka sani basu fad'awa kowa ba har Wajen 12:PM tayi Tana kwance jikin Chuchu jikinta yayi zafi rauu cike da damuwa Chuchu ta ce " Kinki a kaiki Asibiti momcy taya zaki zauna jikinki da zafi haka "Girgiza mata kai tayi ta ce " zanji sauki"Asmy data shigo da Ruwan tea a hannunta data had'o mata ta ce "Ki tashi kisha zakiji k'arfin jikinki Kinga ba abunda kika ci tun safe" Nanma girgiza mata kai tayi ta ce "Na koshi bana son Cin komai Asmy " Matsowa Inda take Asmy tayi tare da Aje cup din ta tallabota ta ce "Bazaiyu ba saikinsha wlh kinji na rantse " badan Zarah ta so ba saidan yanda Asmy ta rantse dole saita sha ya sanyata yunkurawa ta karba a hankali Tana rumtse idon kanta dake mata ciwo "Kurba d'aya Tayi taji Madarar ta taso mata Batasan sanda ta saki cup d'inba sakamakon aman da taji ya taho mata da gudu ta Ruga tayi waje kafin ma ta k'arasa makwararar gidansu ta fara sheka amai Kamar zata amayar da y'an cikinta dangin Baban ta da na Mama Rabi da suka zo Duk Kallonta suka tsayayi Yanda Take kwarara amai Chuchu ce ta biyo ta ganin ba Wanda yayi yunkurin taimaka mata ya sanyata d'aukar butar data gani a tsakar gidan ta cika ruwa tare da nufar Inda take ta fara jera mata Sannu a lokacin ko magana bata iyayi Asmy ma wajen tayo su Suka taimaka mata ta gyara jikinta Daya daga cikin K'annan babanta ta ce " Keko Zahra'u Me yake damunki Irin wannan aman"shiru tayi ta kasa magana.Mama Habi ta ce "Dake fa ake" Dagowa tayi ta Kalleta ta ce "Bakomai Mama" A a daga ganinki kaga marar lafiya ni sai yanzu ma na lura maza shirya na kaiki Asibiti anyi ciwo ba magani ciwon ma kuma na amarya"Hakanan Zarah taji gabanta ya fad'i "Chuchu ce ta ce " Mama Anjima basai a kaita ba yanzu tad'an huta "Mama Habi tace " to shikenan Sai Anjima idan ta tashi kizo ki fad'amun "To Chuchu ta fad'a daki suka koma Inda Asmy ta dirmiya duniyar tunani tsoro da fargaba cike da ranta tsoranta Allah tsoranta ace Zarah ciki ne da ita tasan shikenan tasu ta gama " Chuchu ko lallaba Zarah tayi harta samu tayi bacci sai sannan ta sauke ajiyar zuciya ta Kalli Asmy ta ce "waiko tana da typord ne " Girgiza mata kai tayi ta ce " a a a "Ikon Allah kuma take Amai haka to Allah ya bata lafiya Gaskiya ya kamata Aje asibitin Kar wuri ya K'ure amarya ba lafiya " Shiru Asmy ta dirmiya duniyar tunani ganin haka ya sanya Chuchu janyo wayarta ta fara chat sai wajen la'asr Zarah ta farka ta tashi jikin da sauki Saidai kasala da ciwon kan Kad'an nan suka shiga yi mata Sannu har khairat data shigo Inda taje ta fad'awa Mama Habi Ta tashi "Da Abinci a plate Mama Habi ta shigo d'akin Bayan ta zauna Kallon Zarah tayi ta ce " Anshi kici Nasan ba abunda kikaci"Dagowa tayi kamar zatayi kuka ta ce "Na koshi Mama" wani kallo tayi mata ta ce "Baki isa ba Anshi maza kici kar ranki ya baci" Zarah tana amsar abincin kafin ma takai Baki taji zuciyarta ta tashi amai na shirin zo mata "Cikin Sauri ta mik'e tare da rugawa tayi waje duk da kallon mamaki Mama Habi dake zaune ta tab'a hannu ta ce " me nake gani haka ni Habiba"batayi amai sosai ba saboda ba komai cikinta nan fa Mutane aka fara ido ido musamman dangin Mama Rabi ita ko "Fitowa tayi ta ce " Subhanalla Zarah me nake gani haka kiyi amai da safe yanzu ma haka lafiya kike saikace mai ciki"Kallon da Mama Habi tayi mata ne ya sanyata yin shiru tsaki taja tace Tashi Muje ki sanya hijab d'inki muje Asibiti "tab'e baki Mama Rabi tayi ta koma ciki ita da y'an uwanta suna cewa " shidai abun duniya baya rufuwa kome akayi sai anjishi ba wani boye boye "girgiza kai Kawai Mama Habi tayi Da taimakonta ta shiga toilet Dan tayi wanka Bayan ta fito D'akin da su Zarah take ta shigo shigarsu kenan Khairat ta shigo Tare da Kallon Mama Habi ta ce " Mama Baba yace wai kije keda su Mama Zainabu Yana dakinshi"To kice masa ina zuwa ta fad'a tare da mik'ewa kallon su Chuchu tayi ta ce "ta shirya kafin na dawo" yanayin yanda suka samu Baba ne hankalinsu saida ya tashi dafe da kanshi kallo d'aya zakayi mashi kasan yana cikin tsananin damuwa "dak'yal K'anwar tashi da Yayar tashi suka karasa " Mama Zainabu ta ce "Lafiya dai Malam" Sai sannan ya d'ago ya ce "da sauki Zainabu Yanzun nan shigowar da kikaga nayi dangin yaron Chan ne sukazo akan wai Yaron ya ce ya fasa sun kasa gane kanshi tun jiya gidansu ba irin Fafatun da ba ayi ba karya maidasu kananan mutane amma ya murje ido ya ce " ya fasa Auren kuma ma aka kuskura aka daura zai iya sakinta a ranar Dan haka shine sukazo suka bamu hakuri akan muyi hakuri a d'auki abun matsayin kaddara wlh hankali na matuk'ar tashe yake ina farincikin zan Aurar da Amanar Allah Murnata ta koma ciki wlh nayi mamakin yaron nan yanda lokaci guda zaice ya fasa saida ya bari ana gobe d'aurin Aure kafin a sanya Ranar Auren karkiga irin rawar k'afar da yake gaba d'aya hankali na ya tashi kaina ya kulle na rasa ta Inda ma zan fara"Cikin tsananin tashin hankali Suka rafka Salati Mama Habi ta mik'e ta ce "Allah ya kiyaye yaron nan ba yaudarar yarinyar nan yayi ba Yayi mata ciki yace ya fasa" ciki"Baba Da ?Mama Zainabu suka fad'a lokaci guda hankali tashe "Yo eh mana ciki inba ciki ba me zaisa yarinya tayi ta kwarara amai Tun safe sannan kuma yazo lokaci guda yace ya fasa ai wannan ba maganar d'auka bace da walaki Goro a miya" Girgixa kai Baba yayi yana dafe saitin zuciyarsa da Yakejin wani irin zafi a dabarbarcewa ya ce "Ba haka bane Habiba na yarda da Zarah d'ari bisa d'ari bazatayi abunda bai dace ba na d'auki hakan a matsayin kaddara Da rubutun Allah ya rubuta ba mijin ta bane Dan haka ku hada lefensu ku mayar musu Har gida" Kallon Mama Zainabu Mama Habi tayi ta ce "Kije ke da su Kande ku mayar musu da kayansu ni kuma bari muje Asibiti wlh abunda nake zargi ya tabbata basu isa ba Saidai duniya ta zagemu amma bai isa yayi wannan yaudarar ba yaci bulus tana komawa d'akin ta samu Zara harta sanya hijab cikin muryar b'acin rai Dan ita daman zafi gareta ta ce " Wuce mu tafi "Asmy ce ta ce " Bari na rakaku Mama"Kallon Chuchu tayi ta ce "Ita kuma bakuwar ki barta ita kadai ki bari mu dawo A tare suka fita da Zarah hankalinta duk a tashe koda suka isa Asibiti Mama Habi cewa likitan yayi " Yi mata awon ciki"Gaban Zarah Ya bada daram Kallon Mama habi tayi tana so tayi magana taga yanda ta had'e fuska ya sanyata shiru Fitsarinta Dr ya d'auka Bayan yasa tayo a wata k'aramar kwalba ya tafi awo tagumi Zarah tayi Gabanta na tsananta fad'uwa ba ayi 20 minutes ba dr ya dawo Y'an rubuce rubuce yayi kafin ya d'ago ya kalli Mama Rabi ya mik'a mata takardar"Amsa tayi tace "Ba gane rubututtukan nan naku nake ba Dr fad'amun abunda ke damunta" Murmushi yayi ya ce "To shikenan Mama " Tana D'auke Da ciki ne Na wata Ukku da sati Ukku"Cikin tsananin tashin hankali Zarah ta d'ago ta kalli Dr Ta ce "Ciki kuma Dr" eh idan baki Yarda da result d'inmu ba zaki iya zuwa wani asibitin a aunaki amma Tabbas ciki ne dake na Wata hud'u ba Sati d'aya "Tashin hankali ne ya ziyarci zuciyar Zarah Wanda Bata tabajin irinshi ba a iya Rayuwarta ba " Batasan sanda Ta d'ora hannu aka ba Tana shirin kurma ihu cikin b'acin rai Mama Habi ta kwabe mata baki ta ce "Yiwa mutane shiru tashi muje" ta fad'a tana wartar hannunta "Sukayi waje kuka Zarah takeson tayi Amma tashin hankali yasa ta nemu kukan ta rasa Suna fita harabar asibitin Mama Habi ta ce " Tonon asiri ne zakiyi mana a Asibiti kowa ya fahimci halin da ake ciki ai ba yanzu ya kamata kiyi kuka ba yana nan gaba "Kuka Zarah ta fashe dashi Sosai ta ce " Wlh Mama karya yake bani da wani ciki sharri ne kawai zaiyi mini"d'auketa da Mari Mama Habi tayi cikin b'acin rai Ta ce "Yi mana tonon Asiri a titi Zakiyi bayani idan mukaje gida gaban mahaifinki bani ba " Tsaida mai napep sukayi suka shiga hade kai da gwuiwa Zarah tayi ta shiga rera kukan tausayin kanta Tabbas indai da gaske ciki ne da ita Musty ya cuceta ya gama da ita ya cuci rayuwarta "batasan sun isa gida ba Saiji tayi Mama Habi ta Ja hannunta bata dire ta ko ina ba sai d'akin Baba Kujerar Dake d'akin ta wullar da Ita tana huci ta ce " Kin cuce mu Zarah kin b'ata mana sunan zuri'a ana tunanin wuta a makera ashe a masak'a za'a sameta Kinban mamaki ko a mafarki ban tab'a tunanin zakiyi mana haka ba kin cuce mu kin cuci mahaifinki kin cuci mahaifiyarki dake k'asa sannan kin cuci kanki.........✍🏿

*domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*


1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨


_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: 🅿️...........*79 & 80*



Nuna kanshi da hannu MD yayi ce "Kina nufin ni zan shiga kitchen na girka maki abunda zakici" Tana binsa da harara ta ce "To kaid'in waye" Sosai Abun nata ya fara isar MD tsaki yaja yana maida hankalinshi ga aikin da yake ya ce "Baki da aikinyi shiyasa kike maganar nan ga abinci Chan a dining danayi order kala Ukku ne ciki ki zab'i Wanda zaiyi maki," Harara zahra ta banka masa tana kauda kai dajan tsaki ta ce "Bazanci ba Kuma wlh ka maidani gidan iyaye na na fad'a maka tun kafin nayi abunda baka tunani" Banza MD yayi mata kamar badashi take ba Sosai hakan ya bakanta mata dukda yunwar da take ji amma ta rantse bazataci na restaurant ba ciki ta koma Tare da hayewa Gado ta fashe da kuka MD ganin kusan har awa biyu da komawarta daki a tunaninshi ta fito taci abincin amma yaji shiru tunani yayi yarinyarfa yanzu ta tarki kafiya da zuciyar bala'i karfa wani abun ya samu cikinsa Dan yasan illace mace mai ciki na zama da yunwa Mikewa yayi Koda ya shiga daki kwance ya sameta tana hawaye yana ganinta yasan taci kuka gefenta ya zauna cikin sigar lallashi ya ce "Please Mamy ki daure kici abincin kar wani Abu ya sameki kinsan ban iya girki ba Sarai fa neman rigima ne" banza zahra tayi masa "Mamy ya k'ara kiranta Nanma shiru" Omg " ya fad'a a cikin ransa Kafin ya sake dauriyar cewa "Ko na kawo maki kici anan" Bazanci ba na k'oshi ta basa amsa kai tsaye"shiru MD yayi yana mamakin taurin kai irin nata Wanda da kwata kwata baiyi tunanin tana dashi ba shi damuwarshi bai wuce abunda ke cikinta ba da yakejin sonsa na daban yakejin zai iyayin komai indai zata Haifa masa cikin nan bashi da wani girman kai dole ya Aje ya ce "To ki fad'amun please me kike son ci " Na fasa bazanci komai ba "Cikin lallashi ya ce " na yarda zan girka maki din indai zakici "Sosai zahra tayi mamakin jin wai zai girka " shiru tayi masa "Kifadamun me kike so please" Saida taja mintuna kafin ta ce "jolloup d'in taliya da wake " Ajiyar zuciya MD ya sauke a boye ganin bata tsiro mai wahala ba Mikewa yayi ya ce "give me 30 minutes please kibar kukan nan" Shiru tayi harya fita kafin ta bisa da harara A waya MD yayi browsing Dan ko simple indomie bai iya girkawa ba tsawon rayuwarsa bai tab'a girki ba baima San ya ake ba dan ko school baiyi girki ba Saidai yaci na restaurant Saida ya kwabe manyan kayan jikinsa kafin ya shiga kitchen din waya na rik'e hannunsa daman video ne nan ya shiga Kalla ba laifi MD yayi trying sosai dukda yasha wahala Dan ji yake kamar an sanyashi aikin gini haka dai ya samu ya gama girkin Inda ya juye a plate sai shafce Zufa yake yana fitowa ma kai tsaye d'akin da take ya nufa Inda ya sameta tayi bacci Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Allah mai iko yau nine MD da shiga kitchen akan Aiken wannan y'ar kankanuwar yarinyar saikuma ya tuno da ai kome yayi saboda cikinsa yayi hakan ya sanyasa Aje warmers din tare da Fara kiran sunan da yake kiranta dashi watau Mamy saida ya kira sau Ukku kafin ta tashi Tana murza ido " ta ce "Meye " Abunda kika buk'ata"ya fad'a yana hade fuska "Tura baki gaba tayi tare da mik'ewa taje toilet tayi brush tana dawowa ta iske harya zuba mata d'aukar plate din tayi ta na yatsine fuska kamar taga kashi ta nuna Alamun baiyi mata dadi ba nanko ba laifi saidai magi da yayi yawa kauda kai tayi ta ce "na koshi"murtuke fuska ,yayi ya ce "wlh kinji na rantse saikinci aini ba bawanki bane ki sani bakar wahala kuuma kiki ci abunda bazaiyu bane"bata tanka masa ba sai jujjuya spoon din take kafin ta dauka ta faraci MD na ganin ta fara ci har tayi rabi ya sanyashi sauke ajiyar zuciya Tare da ficewa daga d'akin da harara ta bisa sosai taci abincin Daren ranar zahra karfe d'aya ta tashi ta hau salla Sosai ta daga hannu tana rokon Allah ya kawo mata mafita hawaye na sauka daga idanunta ta ce '" ya Allah kaika jarabceni da duk wannan Abun kuma kana sane dani ya Allah ya kawomun mafita Ya Allah kasan banyi abunda zai tab'a mutuncina da na iyayena ba ya Allah ka fitar dani daga zargin da mutane ke yimun ya Allah ka wanke ni,ya Allah ina kamun kafa da masoyinka fiyayyan halitta Wanda babu kamarsa a duk duniya ya Allah ka bawa mahaifina lafiya Allah ka sanya cikin nan ya zube ta k'arasa fad'a cikin kuka gwanin ban tausayi sai wajen 2 ta ji bacci ya fara daukarta Kallon MD dake bacci kan gadon hankali kwance tayi Dan baya yarda ko daki daya Suki kwana Saboda baisan abunda zata kuma yiwa cikin ba Sosai takejin haushinsa kamar ta kashesa gefen gadon Chan karshe ta ja ta kwanta ba b'ata lokaci bacci yayi awon gaba da ita Cikin baccin ne tayi mafarki Gasu a wani tafkeken lambu Wanda ya cika da kayan marmari da alatu iya rayuwar zahra bata tab'a ganin irin wannan lambun ba waigawa ta dingayi taga ba kowa ba Tana cikin waigawa ta Hango wata mata na kusantowa Inda take fuskarta cike da murmushi da annuri tana sanye da fararan kaya kallonta zahra take har ta karaso Inda take sak Matar taga kamarsu d'aya rai da rai Kallon kanta tayi ta kalli Matar taga sak komai nasu iri daya Karasowa tayi tare da kama hannunta tanayi mata murmushi ta ce "bakisanni ba ko Zahra?Gyada mata kai tayi ta ce " Eh"Kama hannunta ta kumayi suka zauna kan wani lausassan waje da bata Tantance menene ba Matar ta ce "Ni ce Mahaifiyarki Zahra shine suna na nima" sosai zahra ta tsorata saikuma ta Rungumeta ta fashe da kuka ta ce "Ina kika shiga Mama kika barni ina ta shan wahala gashi yanzu ma bata rabu da ni ba Dan Allah Mama Karki k'ara tafiya ki barni ina matuk'ar buk'atar ki a rayuwata ina shan wahala a sanadin rashinki Mama Dan Allah ki daina tafiyar nan Mai nisa karki sake komawa ki zauna tare dani"sai taga hawaye na zuba daga Idanun mahaifiyartata tare da murmushi a fuskarta ta ce "Nasiha nake son nayi miki zahra rayuwa cike take da k'alubale da jarabawowi iri_iri a duk halin da kika tsinci kanki kiyi hakuri sannan ki k'ara kusanta kanki Da ubangijinki shine kawai Wanda zai yaye maki dukkanin damuwarki kiyi hakuri da jarabawa Allah yana jaraba bayinsa ne Dan yaga iya imaninsu karki karaya y'ata ki zama mai tawakkali da godewa Allah a duk halin da kika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login