Showing 150001 words to 153000 words out of 153980 words

Chapter 51 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16351

karfinta Sosai Itama Zahra kuka take Sosai taji wani irin tausayin Amera Ganin irin yanda numfashinta ya sauya da tarin da take ya sanya Zahra dauke little Dake kanta MD ko a matukar rude ya Fara girgizata Yana Amira Amira Mamanta ko wani irin kuka ne Mai karaji ta fashe dashi gaba daya hankalinsu ya tashi ganin irin yanda numfashinta ke Neman daukewa suna Ganin yanda bakinta yake motsi Amma Basu San me take cewaba a matukar rude hankalinta tashe MD ya fita ya Kira doctors likita hudu suka shigo bayan sun bada umarnin kowa ya fita MD kin fita yayi Zahra ko wake sukayi suna kuka Duk iya yanda likitoci suka so ceto rayuwar Amera abun ya gagara ba ayi 20 minutes ba komai na jikinta ya daina aiki Ganin likitocin na cire oxygen din da suka da Mata da kayan aikinsu ya sanya MD rikicewa a matukar tashin hankalin ya ce "Me kuke nufi Dr kardai kucemun ta mutu"Daya daga Cikin Dr din ya dafasa ya ce "Am so sorry Allah yayi Mata cikawa dukkan Mai Rai mamaci ne kowa jiran tashi ranar yake ta rigamu Gidan gaskiya saidai muyi addu'ar Allah ya jikanta ya rahamce ta mu Kuma ya bamu guzirin taddasu"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un MD ya fada kafin yaje ya rungumeta ya ce "Karkiyimun Haka amera me yasa Zaki tafi ki barni Amera kin mutu innalillahi wa Inna ilaihiraji'un yanzufa kike cewa jikin naki da sauki Dan Allah ki tashi saikuma ya fashe da kuka kamar mace Yana kan gawar Sosai likitocin suka tausaya Masa sunsan ba karamun shigarsa mutuwar tayiba maman Amira ko da aka fada Mata mutuwar Suma tayi Zahra ko Tasha kuka dakyal ta iya daukar waya ta sanar dasu ammy mutuwar Amera Sosai Suma hankalinsu yayi tsananin tashi MD ba karamun tashin hankalin ya shiga ba a mutuwar Amira yayi kukan da bai taba yin irinsa ba tunda yazo duniya A Haka dai aka Kai amera gidanta na aure Wanda Anan akayi Mata. Sutura Sosai wajen jana'izar Tata ta cika da mutane a makabartama MD Saida yasha kuka dashi aka sanyata ya jima Yana Mata addua da Neman Mata rahamar ubangiji Kira yake na yafe Miki Amira Baki mutu da hakkina ba komai kikamun a zamana Dake na yafe Miki Allah Miki rahama Allah yasa mutuwarki ta kasance hutu a gareki Allah yafe Miki mala'ikun rahama su amshi bakuncinki ya Allah Ka jikan Matata ka yafe Mata Sosai MD ya Sanya wasu daga Cikin Yan makabartama kuka kafin dakyal aka samu ya tashi dagakan kabarinta kafin kowa ya watse aka barta daga itasai halinta (😭😭Allahsarki Amera Allah jikanki) Koda Suka koma gida aka Fara zaman makoki MD baya iya cin komai kallo daya zakayi Masa kasan ba karamun shigarsa mutuwar tayi ba ko mahaifiyar Amira Bata Kai MD shiga wani hali ba Zahra ko itama Sosai ta damu idan Tana tuno da maganganun nasu da Amira na karshe dukda ba wani sabo sukayi da itaba Amma mutuwar ta shige ta Kuma ta karyar Mata da zuciya a Nan inda Amira ta yi rayuwar aurenta akayi zaman makoki su ammy da Yan uwa da kowa dasu Zahra da mahaifiyar Amira duk Nan suke kwana Yan uwan Zahra ma na wajen babanta sunzo motarsu guda sunyiwa MD gaisuwa sannan Bangaren Mamanta ma daga jigawa Suma da yawansu sunzo sunyi mashi gaisuwa Saida Akayi sati guda ana zaman makoki kafin ayi sadakar sati taro ya ragu ya rage Saina gida mahaifiyartama ta hakura tayi tawakkali MD ne dai abincima saidai idan ammy ta kirasa Tana Masa wa azi da nasiha Harta samu ya danci Kowa yazo sai yayi Masa nasiha Akan yayi hakuri ya bita da addua Wanda ya tafi baya dawowa a sati na biyu suka koma gidansu saboda Yan gaisuwa yanzu sai daidai tunda suka koma Zahra Bata gane kan MD hira ma basa zaunawa suyi kullum Saidai yayi shiru Yana tunani hirarta dashi saidai ta gaishesa ya amsa ko yanason wani abun tayi Masa yaransama idan ya daukesu baya musu wasa kamar da Sosai Zahra ta shiga damuwar da wannan halin da MD ke nuna Mata hankalinta duk ya tashi yau sati biyu kenan da dawowarsu gida Amma basa Zama suyi wata hira Kullum Cikin tunani yake ga abinci ma idan ta girka ba Ci yake Sosai ba baifi yayi spoon ukku ba ya tashi wani Karin ma bayaci "Zahra saidai taje daki Tasha kukanta Yauma ta na Cikin Shan kukanta taji wayarta tayi ringing Tana Ganin chuchu ce ta Dauka yanda ta amsa Mata sallamar ne ya Sanya chuchu ta gane akwai matsala cewa tayi "Lafiya Momcy naji kamar muryarki kinsha kuka"Kukan da take boyewa ne Zahra ya kubce Mata ta fashe dashi Saida ta tsagaita kukan kafin chuchu Cikin damuwa ta ce "Subhanallah Aunty me yake faruwa ne Wai"Cikin kuka ,Zahra ta Ce "Chuchu bansan me nayi Masa ba tunda akayi mutuwar Nan bayamun magana bayacin abincina Sosai gaba daya na rasa abuna ke mun Dadi zaman Gidan duk ya isheni kwata_kwata bani da walwala bansan me nayi Masa ba"Ta karasa fada Cikin kuka "Ammy Dake Jin Abunda Zahra ta fada kasancewar handsfree aka Sanya wayar Kuma suna kusa da juna amsar wayar tayi a hannun chuchu ta Kara a kunnanta ta ce Hello Zahra"Zahra Najin muryar Ammy gabanta ya fadi Allah yasa bataji ba saboda kartayi tunanin ko kararsa ne takawo saurin katse wayar tayi tare da yin Tagumi ta fashe da sabon kuka MD daga kofa zaishigo dakin yaji komai da irin yanda take kukan take fadawa chuchu batasan me tayi Masa ba Sosai yaji tausayinta ya kamasa Shi kanshi bayama sanin yamata Haka saboda kwata_kwata tunaninshi baya jikinshi Babban tashin hankalinshi da mutuwar Nan irin yanda ya banzatar da ita wata ukku bai taka inda take ba kota kirasa baya Dauka Shi yafi komai tsaye Masa arai na Ganin rashin kyautawar da yayi Mata karasowa dakin yayi tare Kama hannun Zahra ya tallabo fuskarta Dake kuka ya Ce "Kiyi hakuri Mamy bakiyimun komai ba Baki taba yimun laifi ba Dan Allah dalilin mutuwar Nan ne da Bata sakeni ba ya Sanya banason yin magana ko cin abinci Amma ba Wai Dan na musguna Miki ba Dan Allah kiyi hakuri ki yafemun"Lokacin guda Zahra ta dago saikuma ta sadda kanta kasa Tana hawaye rungumota yayi jikinsa ya ce "Baki hakura ba kenan"Girgiza Masa Kai tayi tana goge hawayenta ta ce "Dan Allah kayi hakuri Ka rage damuwar Nan a ranka Tana sakani Cikin wani Hali sainaga kamar ni nayi maka wani Laifin ne ita Kuma Aunty amera addu'ar ka take bukata a halin yanzu fiye da komai Allah ya jikanta"Yana goge Mata hawaye ya ce "Ameen my Mamy Insha Allahu Zan rage daga yau"wayarsa ce tayi ringing Yana Dauka daga Bangaren ammy ta ce "Babana lafiya meya hadaka da Zahra kake Mata gaba"Sorry ammy wlh ba abunda ya hadamu kawai fahimtata ce batayi ba har yanzu Mutuwar Amira ce ke tayarmun da hankali ammy musamman idan na tuna kyaketa din da nayi tsawon watanni fin ukku Ammy abun Nan Shi yafi damuna da tsayemun a Rai"Daga Bangaren ammy ta Ce "Ka daina damuwa da wannan Babana kayiwa Amira gatan da babu namijin da zaiyiwa matarsa Haka sannan ka godewa Allah da saida kayi jinyarta kukayi bankwana kuka yafi juna kafin Allah yayi Mata cikawa inason ka cire damuwar mutuwa a ranka ka dinga binta da addua muma muna Mata Allah yayi Mata rahama nasan kana da ilimi Kuma kasan dukkan Mai Rai mamaci ne kowa jiran nasa lokacin yake"Nasiha Sosai ammy tayi Masa kafin tace ya bawa Zahra wayar itama nasihar tayi Mata ta ce "aikinkine Zahra ke Zaki kula da mijinki har ki mantar dashi wata damuwa ke matarsa ce ke kikasan duk wata hanyar da zakibi wajen basa farinciki Kiyi iya kokarinki nasan Kuma kinayi Allah yayi Miki albarka ga driver Nan zanturo ya kawo mun yaran suyini"To Ammy nagode Insha Allah Zahra ta fada..tun daga ranar Zahra tafara bakin kokarinta wajen Ganin ta dawo da farinciki rayuwar mijin Nata duk wani da hirarraki masu dadi Shi take Masa a hankali a hankali ya dinga sabawa da rashin Amira harya dawo normanl saidai addua da yake Mata da sadakoki har masallaci ya Sanya a Gina Mata kamar yanda ya ginawa mahaifinsa da Kuma mahaifiyartama Zahra Wanda ko ita Zahra Bata sani ba Akan Allah yakai musu ladar rayuwarsu taci gaba da wakana Cikin farinciki da kaunar juna MD ya dawo asalin MD Mai nuna kulawa da soyayyar ga matar tasa itama Zahra Tana Nata bakin kokarin wajen Ganin faranta Masa an Sanya ranar Auren chuchu da Adil Wanda aka had'e Dana Asmy da Jabir wata hudu masu zuwa Yau Zahra na kwance Baba ya kirata bayan sun gaisa yake cewa ta Mika Masa sakon godiya wajen MD Sosai tayi mamakin yanda baba yake kwaraawa me addua tare da gode Masa ita dai Zahra murmushi tayi Bata tambayi baba abunda yayi musu ba baba na katsewa maman Asmy ta kirata itama godiyarce take ta surfawa hada kukan farinciki ta ce 'Allah yayi Miki albarka Zahra sanadinki Zan take kasar da bantaba tunanin zuwa ba sanadinki Zan sauke farali Allah yayi Miki albarka Zahra Yasa a gama lafiya ya Raya muku zuriarku godiya Sosai mama ta dingayi sai sannan Zahra ta fahimta kenan aikin hajji MD ya biyawa su baba Sosai taji Dadi Kuma tayi farinciki Koda ya dawo Tana Fara Masa gdy ya Girgiza Mata Kai ta Ce "Sun chanchanci fiye da haka Mamy kome.nayi akanki ban fad'i ba ke Kika Fara bani farincikin da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwa kingako dole wani ma Wanda ya shafeki na basa farinciki kafin ya ce Abunda yasa Baza a tafi Dake ba saboda su Akhbar Dole.saidai next year sannan kin yayesu kin Kuma haifamun wasu triple din"murmushi Zahra tayi tare da rufe fuska "Bayan su baba sundawo daga aikin hajji Wanda hada maman Asmy da babanta da bappa aka biyawa Zahra ta shirya domin taje tayi musu sannu da zuwa Sosai tayi mamakin Ganin yanda aka gyara gidansu da na su Asmy dakyal ta iya gane gidansu Dan har bene aka Dora musu Koda ta shiga ciki ma Saida tayi mamakin irin kayana alatun da aka zuba Baba ko hada kukan farinciki yake Yana godewa Allah na mallaka Masa Zahra a matsayin y'a itadai Zahra saidai tayi murmushi inda yayi Mata addu'a ta amsa da amen MD ko yasha ruwan addua Bayan ta huta gidansu dukda tayi mamakin rashin Ganin mama rabi a Gidan ta wuce gidansu Asmy nanma Tasha godiya da sa albarka Kukan farinciki ko maman su Asmy ta Shashi Bayan sun gama gaisawa Zahra tayi musu sannu da zuwa sai sannan ta samu Daman tambayar maman su Asmy ta ce mama Wai Ina mama rabi tunda nazo banganta ba "Girgiza Kai Mamansu Asmy tayi ta Ce "Ina ko zakiga rabi Ai tuni Malam ya saketa yaran Nan biyun dukansu sukayi ciki lokacin Yana batsari baisan wainar da ake toyawa ba Saida ya dawo Shima saidaga baya Anje cirewa Salamatu Cikin Rai yayi halin sa to kinsan dai maganar garin Nan magana ba boyuwa take ba asirinta ya tonu Wanda Malam ya saketa yace bazai iya Zama da ita ba "Salati Zahra tayi ta Ce "Wayyo Allah Salamatu ta mutu kenan bantaba sani ba Allah ya jikanta to Ina habibar ita ta haihu ne"Eh ta haihu d'an Wai ya mutu waya sani ma ko kashe shege sukayi"Sosai Zahra taji wani iri a ranta ta Ce "yanzu mama Suna wani Gida"Wama ya sane Mata Kullum Tana zarya Tana kuka Tana rokon Malam akan ya yafemata tayi nadama ya mayar da ita ya kiya yo me zaiyi da rabi matar da ta wulakantaki taso taga kin tozarta sai gashi kaikayi ya koma kan mashekiya Abu ya koma kan y'ay'anta shiyasa ba ason bin mutum da mugun nufi Shi shairi kwikuiyo ne Mai Shi yake dawowa"Sosai Zahra tayi sanyi ta ce "Mama Dan Allah tunda tayi nadama kusa Baki baba ya maida ita Dan Allah tunda tayi nadama kodan saboda su khairat Dan Allah mama "wani banzan kallo mama tayi Mata ta Ce "Amma bantaba sanin Baki da hankali ba Zahra sai yau matar da ta wulakantaki itace kike maganar ta dawo taci arzikinki ke wata irin zuciya ce Dake maimaikon kiyi farinciki mahaifin ki ya rabu da muguwar Mata shine kike kokarin ki Kara lakaba Masa"Ba Haka bane mama saboda su khairat za a duba"Barmun maganar Nan Zahra a Kama wata"da dare Zahra tajewa baba da maganar Akan ya mayar da mama rabi furtumarta yayi ya dinga Mata fada Akan Bata da hankali Sosai Zahra ta kafe hada kukanta Tana bawa baba hakuri akan Dan Allah ya dubi su khairat ya maidota idan ta sake wani abun saiya saketa dakyal ta samu ta shawo kan baba ya yarda Zai maidota Amma da sharadin saidai habiba ta koma wajen dangin babanta dan bazata shafawa ya'ayanshi kashin kaji ba ajiyar zuciya Zahra ta sauke ta ce ta yarda Koda baba ya maido mama rabi Bayan yayi Mata kashe sannan ya Dora da cewa arzikin Zahra ne taci harya maidota mama rabi kukan nadama hada durkusawa kamar zatayiwa Zahra sujjada Tana Mata godiya ta ce 'Har kunyar had'a Ido nake Dake Zahra ki yafemun irin zalincin da nadinga maki Shiyasa akace duk yanda ya rike Allah shiya rike Babban bango na tsaneki na tsangwameki naso ki wulakanta ki kaskanta saigashi Allah ya d'aukakaki d'aukakawar da bakowa Zai samu irinta ba Zahra a yanzu kina daya Daga Cikin macen da za ayi alfahari da ita a duniya ki yafemun Zahra nayi nadama har kunyar had'a Ido nake Dake gashinan muna Cikin cin arzikinki Shiyasa akace kaji tsoron mutumin daka wulakanta"Murmushi kawai Zahra tayi ta Ce "Allah yafe Mana tare mama"Kwana biyu Zahra tayi Wanda Cikin kwana Biyun mama rabi kamar ta goyata abinci ma saita tambayeta irin Wanda takeso Dan tunda mama rabi tasan cewar Zahra MD take aure ta sadakas tasan Zahra tayi daukakar da babu mahalukin da ya Isa yayi kasa da ita gwarama tayi hakuri ta dangwali arziki Rayuwar su Zahra na tafiya yanda ya kamata a Haka har lokacin bikinsu Chuchu ya gabato anfara shiryen shirye ta ko Ina Bangaren Zahra da MD ma Sosai suke Shirin bikinnan a Haka har lokacin bikinsu yayi Zahra hankalinta duk ya kasu biyu ga Gidan ammy Bangaren chuchu ga chan funtua Bangaren Asmy tunda aka Fara bikin take Shan gayu da wankan gwala_gwalai Sosai suke Shan masifar kyau ita da yaranta da suka Fara tafiya gwanin sha'awa duk inda suka gitta sai anyi sha'awarsu ana gobe daurin aure ta samu damar zuwa funtuaa Wanda motoci takwas sukayi Mata rakiya tare da security yanda kasan matar shugaban kasa ita kanta Zahra ta kalli wanna daukakar da Allah yayi Mata har hawayen farinciki take Wai itace Zahra da da ba abakin komai take ba yanzu ta daukaku har Haka Koda ta Isa Unguwarsu duk manyan motocin sun cika wajen kowa sai daukin su gaisa da ita ake Saida ta gaishe da tsaffin layinsu Bayan tayi musu alkhairi kafin ta shiga gidansu Asmy dakyal ta samu ta shawo kan mutuniyar Tata Akan tayi fushi sai yanzu take zuwa dakyal ta fahimta bayaninta na cewar hidimar gidansu mijintace ta hanata sakat Yauma dakyal suka barta ta taho Nan aka cigaba da shagali da Zahra da dare gidansu taje Dan ta kwana zo kuga murna wajen mama rabi Kira ta ce "lale marhaban ga y'ar arzikin tazo Yar albarka sannu da zuwa jikokina sannunku ta fada Tana yin sama da little itadai Zahra murmushi kawai take Bayan ta Gaisheta Nan khairat ta ruga da gudu Tana murnar Ganin Yar uwartata Haka safiya da yanzu itama ta Zama budurwa Mama rabi kusan raba dare tayi tana goye da little dakyal Zahra ta samu ta saukota Tana mama zata gajiyar Dake Kira take ba komai Yar Nan barni in Goya abuna washegari aka daura Auren *Jabir & Asmy* tare da *Chuchu & Adil* na Asmy a funtua aka daura na chuchu Kuma a kd kasancewar an hade dinner ya Sanya aka Kai amarya da wuri Gidan ammy aka sauketa karfe goma na dare aka Tafi dinner Wanda Zahra da MD su suka shirya dinner Sosai wajen yayi masifar kyau da tsaruwa amarenma sunyi anko suma angwayen sunsha kyau iyayen gayya kuwa MD da Zahra ba a magana sunyi masifar kyau duk inda suke suna like da juna Excord dinsu na take musu baya tare da yaransu Dake tsalle tsallensu gwanin ban burgewa Sosai cemarori ke yawo Akan Zahra da MD yanda kasan sune amaren Zahra ko an kame girma ana zaune ita ta bada tarihin amaren MD Kuma ya nada na angwayen taro ya tashi Lafiya washegari aka wuce da kowacce gidanta chuchu Abuja Asmy Kuma Nan kd grab Dan gida daya ne tsakanin gidanta da Zahra..


*After 3 years*

Fitowarsu kenan daga tafkeken shopping mall din MD Dake Abuja waiwaye ta dingayi inda zataga Akhbar Dan tunda suka fito Bata ganshi ba Sosai Naga ta Kara kyau da wayewa Tana sanye da bak'ar doguwar riga Abaya Mai shegen tsada tayi roalling gyalen Sosai tayi masifar kyau ga fuskarnan Tata kallo daya zakayi Mata kasan Tana samun hutu da Jin Dadi juyawa tayi Tana kallon MD dake rike da karamar y'arsu Wadda taci sunan Amira halimatus sadiya ana kiranta da amera itama watanta biyar da haihuwa kamarta daya da Zahra Rai da Rai ta ce "Sweetheart Wai Ina Akhbar tunfa da muka fito bangansa ba "Cike da damuwa MD ya ce "to ko yayi wani wajen Nan "Kafin ya kalli Amar dake wasa da katuwar bindigar wasa ya ce My boy Ina Dan uwanka ya shiga ba tare kuke ba "Dad Nima bangansa ba "Innalillahi MD ya fada ya ce ki duba sa farfajiyar Nan Ni Kuma Bari nayi maza na duba sa ciki ya fad'a Yana komawa hankali tashe Zahra ta rike Amar ta dinga dubawa duk yaron data gani saita dubasa gaba daya
hankalinta duk ya tashi chan ta hangoshi gaban wasu Cikin sauri ta nufi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login