Showing 75001 words to 78000 words out of 153980 words

Chapter 26 - AUREN WATA TARA COMPLETE HAUSA NOVEL

30 Sep 2024

16348

ban tab'a jiba"Nima a novels karanta wlh "ta fad'a tana y'ar Dariya " Tsaki Asmy taja tace keda kike karanta novels dinma har kika sani"Murmushi Chuchu tayi ta ce "Hmm ai wlh ina mamakinku da kikace wai baku karatun novels ai novels duniya ne musamman kika hadu da mai dadi duk wata damuwarki jinta zakiyi ta yaye novels yana yaye damuwa yanda baki tunani wlh Ga dadi jinki kike kamar kiyi tsuntsuwa ki koma duniyarsu" Dariya Asmy tayi ta ce "Haka dai kike cewa nikam gani nake bazan iya zaunawa na karanta ba gani nake bata lokaci ne kema Rashin aikinyi ne kawai" hmmmm bazaki gane bane Matar nan"To Ganar dani "Dariya chuchu tayi ta ce '" Ai tunda kince bazaki iya ba shikenan"a a yanzu dai Naji bani wani na karanta Page d'aya Naji yanda abun yake"okay bari na dubo maki *Ni da yaya Arman* da na karanta kwanaki tun lokacin da ake typing dinsa na saya littafin yayi dadi over yanda baki tunani anzuba zallar Soyayya a cikin book dinnan an zuba basira kede bari ki karanta saikin bani labari "okay ban page d'aya Na gani" Wayarta Chuchu ta bud'e ta shiga tare da mik'a mata "karanta Page d'aya ma kadai ki bani labari "Ansar wayar Asmy tayi ta fara karantawa Zarah dai na jinsu har ta gama salla girgiza kai tayi ta ce "Ana shirin exams kina shirin koya mata karatun Littafi" Dariya Chuchu tayi ta ce "Page d'aya ne fa zata karanta momcy kema ko zaki karanta" Girgiza.kai tayi ta ce "Bani da time d'in wannan Exams na gabatomu ina ni ina fara karatun Littafi " Asmy ita da zata karanta Page d'aya ai batasan ta zarce har page biyar ba saida Chuchu ta warce wayarta ta ce " Yadai naga kinjima bani wayata chat zanyi"Cikin doki asmy tace "wayyo ya zaki lasamun Zuma a baki kuma ki barni Dan Allah ki bani naci gaba please banso ko da second d'aya a wuceni" Dariya Chuchu ta kwashe da ita ta ce "Keda kikace bani da aikinyi ai bazaki cigaba page daya nace ki karanta" ai bansan haka abun yake ba shiyasa nace haka wlh book din tundaga fara karanta Page d'aya ya tafi da imani na tundaga farkon salon soyayyarsu ya burgeni ba k'aramar love za a zuba a book d'innan ba da na lura Dan Allah ki bani na ida please "Dariya Chuchu tayi tace bari dai na tura maki ba Dan halinki ba Ai baki fara komai chakwakiyar love sai nan gaba Ayra da Arman Ai duniya ne Bari dai karna baki labari ki karanta da kanki" Zarah ce ta ce "Ikon Allah to ga wayata nima turamun Idan mungama exams na samu na karanta"Duka ba haka za ayi ba ku bari zansaya muku complete document a wajen marubuciyar saina tura muku ta what's app wannan doc din free page ne kuma.lokacin da na karanta a paid grp dintane Kunga ba Tarawa zanyi ba " Cikin doki asmy ta ce "Nidai fara turamun wannan din Kafin taturo cmplt din wlh marubuciyar ta iya salon labari mai d'aukar hankali" Dariya Chuchu tayi ta ce "Kaji uwar azarzabi ki bari na saya muku mana " A a aban yarda ba please ni bani number marubuciyar ya sunanta na maza na saya kar a barni a baya"Dariya Chuchu ta dake ta ce "aifa inaga haka din zanyi chan ku karata rubuta mata number tayi ta ce " Kiyi save da Hajara L Sadeq ko miss hajo"girgiza kai Zarah tayi ta ce "Kinji uwar ujila nima bani numberta sanda Nasamu time naso karantawa saina tuntubeta" Itama Rubuta mata number tayi ta ce "Na tura miki free page din ta what's app" Okay Thnks daughter "Zarah ta fad'a sai yamma driver yazo daukarta suka wuce Gidan MD tana lissafin sauran lokacin da ya rage mata ya saketa kowa ya kama gabansa sosai ta maida hankalinta ga karatun ta dukda yawan baccin da take bai hanata raba dare tana karatu dukda MD baya barinta sakewa a dare saboda koda yaushe yana nanike ita itako ta rabu dashi ne kawai Dan tasan na bankwana ne yake nan da one months kowa ya kama gabansa da idonsa ma bazai ganta ba tsaye take tana soya awarar kwai a kitchen tunda taji karnin kwan taji zuciyarta na tashi Tun tana daurewa harta kasa da gudu ta fito tare da rugawa palour ta fad'a toilet a guje nan ta fara kwarara amai MD yana palour yana mamakin me ya sameta bai tashi ba ya bita haryaga Fitowarta tana maida numfashi " Sannu"ya furta a hankali ta gyad'a masa kai tare da bajewa kan kujera tana ci gaba da maida numfashi "Baki da lafiya ne" ya k'ara maimaitawa "Girgiza kai tayi tare da yatsine fuska ta ce.........โœ๐Ÿฟ

*07026166536 domin magana da marubuciyar kai tsaye*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ


_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[10/3, 7:17 PM] Mother Mamy: ๐Ÿ…ฟ๏ธ.........*57 & 58*


Kwana biyu da komawar Zarah school MD ya rasa ta hanyar da zaije Zaria ga hankalinshi da ya tashi kiran da Hajiya tayi mishi tace ya saurari zuwanta karya zaci ta manta dukda Amera bata fiya damuwa da halin mijinta ke cikiba amma wannan Karin saida ta tambaya ta ce "Honey lafiya wai?Kallonta yayi ya ce " Me kika gani"Naga kamar akwai abunda ke damunka "Numfashi yaja ya ce " nothing kawai tafiya ce ta kamannine Germany to bana son na tafi na barki ne shiyasa saboda zanyi kewarki"murmushi Amera tayi cike da jin dadi ta ce "Kai honey saikace yau ka fara tafiye tafiye kayi tafiyarka wlh bakomai ni daman America nake son komawa na gaji da zaman Nigeria "da mamaki MD.yake kallonta a tunaninshi zatace Saidai su tafi tare ne ko ta kawo k'abli da ba Adi amma yaga cikin Sauk'i kamar ma.so take ya tafi girgiza kai kawai yayi ya ce " ko irin kewar nan tawa bakyajin zakiyi ko kamar ma.so kike na tafi'"Shigewa tayi jikinshi tace ba haka bane honey Kasan nafi kowa sonka da kaunarka da kuma kishinka kasan babu abunda zai hanani kewarka kawai dai Naji dad'in tafiyar taka ne saboda zaka bar k'asar nan ta sa ido y'an mata su daina kallemunkai shiyasa"Hmm Chan gemany din ba y'an mata kenan "Hade fuska tayi tamau tare da cewa " Aidai nasan yanda baka kula y'an mata anan ba Chan ma bazaka kuka su ba "zancen ki kenan Amera kullum magana d'aya yaci ace tsawon shekara goma kisan waye mijinki kinsan sarai babu macen da ta isa fa rud'e ni ke kad'aice tal daga ke ba k'ari to meye zaki dinga tada jijiyoyin wuya kullum magana d'aya kishiya kinsan da ina yi miki kishiya tsawon shekarun da mukayi dake da nayi ko kuma da kin taba samun labarin ina da y'an mata ko budurwa to why zaki dinga damun kanki " sosai Amera taji dad'in kalaman mijin nata da murmushi a fuskarta ta ce "Nasan da haka mijin da babu kamarsa ina son har kullum ka dinga rik'emun Amanata please MD wlh kasan bana son kishiya ina son kayimun alk'awarin bazaka tab'amun kishiya ba ko da Bayan rai nane please wlh Inajin da kayimun kishiya gwara ace ga ranar mutuwa ta tafiyumun sauki" ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka Rungumeta jikinshi MD yayi dukda ba Yau Amera ta saba irin wannan maganganun ba Amma yau d'innan ta karyar masa da zuciya yasan duk maganar dake fitowa bakinta da gaske take yasan ba karamun so amera take yi mishi ba Lallashinta ya shiga yi sosai Cikin kwantar da murya da kalamai masu dadi harya samu tayi shiru da dare koda yaga tayi bacci tashi yayi zaune ya kasa zaune ya kasa tsaye a ranshi ya ce "why Hajiya zakiyi mana haka me yasa kikeson ki ruguzamun farincikin mata,ina ruwanki da rashin haihuwa ta tunda ke kina da yaran meye ruwanki da nau,me yasa kike kokarin tarwatsa farincikina da na matata iska ya fezar me zafi zirga zirga ta fara a tsakiyar d'akin Tabbas dole ne ya samu mafita cikin Sauk'i ga yarinyar ma da jaber ya bada shawarar mafita da ita ba mafitar saima Kara rikita abubuwa da hakan yayi tsaki yaja a ranshi ya ce Tabbas dole ne yarinyar nan tayi ciki ko tana so ko bata so Dan bazan tab'a jurar ganin Merah cikin wani hali ba kwata kwata kanshi ya kulle Ta ko ina ya hasaso saiyaji ba mafita dole dai yarinyar nan da jaber ya makala masa ita zai samu mafita ta hanyar ta Bai samu bacci ba sai Chan cikin dare Bayan ya gama nafilfilu da adduo'i akan Allah kawo masa mafita a cikin rayuwarsa washegari koda ya tashi asuba har lokacin da ya dawo daga masallaci Amera bacci take a hankali yahau tashinta taki tashi data tashi saita koma cikin y'ar daga murya ya ce " wai bazaki tashi kiyi sallah ba Amera kin sani sarai banason Sallar safen nan da kike "Cikin gigin bacci ta ce " Dan Allah ka rabu dani bana yi "Dukda yayi mamakin yaushe ta fara perioud saiyayi tunanin ko cikin dare yazo mata kyaleta yayi yashiga wanka Bayan ya fito ya shirya cikin shigarsa ta kasaitattun kayan da ya saba sai baza k'amshi yake Yana cikin duba wasu document akan makekekiyar kujerar dake d'akin yaga tashinta kallo d'aya yayi mata yaci gaba da abunda yake yana ganin sanda ta fito Bayan tayi wanka yana kallonta saida ta gama shirinta tsaf hada kwalliya sosai yayi mamakin Ganin ta d'auko hijab da darduma ta kabbara Salla yasan wannan ba shine karo na farko ba da take haka Amma ya rasa dalilin da yasa yanxu yake ganin dabi'un nata a wani kala tunowa yayi da Zarah yarinya k'arama amma bai tab'a ganin lokacin salla ya wuce ta ba shi har mamaki yake Yanda yarinya k'arama take da wannnan ibadar Dan wani time d'in yanajinta raba dare Take tana k'iyamul laili shi kanshi yasan duk kokarin shi na ibada yarinyar ta shanyesa ta damesa yana cikin wannan tunanin kuma sai ya tuno da kiriar d'ayar yarinyar da muryarta ta kasa barin kwalwarsa lumshe ido yayi Dan shi a rayuwar sa yana son yaga mace mai Ilimi musamman ta had'a biyun na addini da kuma na boko yasandai Amera bangare daya yayi sa a tana da ilimin boko da wayewar da duk taron da yaje da ita na manya da manya ko k'asashen k'etare bata basa ruwa tana fiddashi kunya Dan baya da shakkar ko ina yaje da ita Saidai Inda ta samu tangarda bangaren ilimin addini yana cikin wannan tunanin tajita gefenshi ta rungomasa ta ce "Sannu honey good morning" morning too dear how was your night "Fine " ta basa amsa "kamar bazai magana ba saikuma ya d'ago ya Kalleta ya ce " Amera me yasa kika raina addini haka ,sau nawa zanyi kokarin sauyaki daga kan wannan muguwar dabiar "tashi Amira tayi tare da Fara gunguni ta ce " wlh honey ka tarki y'ar cewa kwanannan Wanda da baka dashi abubuwan da baka magana akansu a da yanzu komai nayi saikace banyiba daidai bansan me zanyiba yayi daidai"ta fad'a tana ficewa daga d'akin da Kallo ya bita kafin ya maida idonsa ga aikin da yake yace "Allah shiryeki" (nikam nace Amen )ba ayi awa guda ba yaga shigowarta d'akin tare da akwati ya yafa beil din doguwar rigar aka Kallonshi tayi ta ce "Honey nafa shirya" ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Ina zuwa" America "ta basa amsa kai tsaye " Dukda mamakin abunda ta fad'a amma bai nuna mata ba "Allah ya kiyaye" ya bata amsa"Uhm to haka kawai zakace ba rakiya ba komai"Sai sannan ya d'ago ya Kalleta ya ce "Nida bansan da tafiyar taki yanzu ba Kuma bakiji addua nayi ba me kikeson nace " batare da ta k'ara cewa komai ba taje tayi hug dinsa tare bashi peck a kumatu ta ce "Bye honey sai munyi waya" tana gama fad'ar hakan tabar d'akin tana Sauri "Sai Bayan fitarta da awa Ukku sannan MD ya fita Escord dinsa suka biyo sa daga musu hannu yayi " Motarshi da ba kowa ya sansa da ita ba mai tinted ya hau Kafinma yayi horn security sun bud'e masa get yayiwa motarsa key sai Zaria koda ya isa gidansa ya nufa dukda. Yaga gidan yana buk'atar shara da mopping Dan ya fara kura tunani ya dingayi yanda zai hadu da yarinyar Dan yana tsananin buk'atarta wani tunani ne ya fad'o masa me zai hana yayi irin waccen dabarar da yayi na kiran Malam Umar ya ce a kira masa Zarah Yusuf Dan ya rik'e sunanta radam cikin ikon Allah yasan ta saikuma ya tuna kar Mlm din yayi zargin akwai abunda ke tsakaninsa da yarinyar Dan ya lura da irin kallon da yake masa tsaki yaja ya ce laifinane da ban Anshi number ta ba wani tunani ne ya fad'o masa kiran driver da ya d'aukar mata Wanda zai dinga kaita sch yayi Bayan ya d'auka ya amsa gaisuwarta a takaice ya ce "Da Allah ka rik'e yarinyar nan da kake daukowa daga makaranta" daga bangaren driver d'in ya ce "Eh ranka ya dad'e " okay gobe ina son kaje sch din lokacin tashinsu daga lectures kace ni na aikoka ka daukota"To shikenan ranka ya dad'e a Angama"daman Dan Zaria ne kuma baisan MD ba a fuska amma yasansa a baki washegari Zarah fitowarsu daga lectures kenan sun fito harabar da zasu wuce hostel taji ance "Hajiya " Bata amsa ba saboda batayi tunanin da ita ake ba cigaba da tafiya sukayi Ganin hakan ya sanya driver d'in binsu ya ce "Ranki ya dad'e ina yini" Yusuf ne ya Kalleta ya ce "da ke fa yake Daugher" Kallonsa tayi saita kalli driver dukda da farko bata Ganesa sosai ba Ta ce "Lafiya " Cikin girmamawa ya ce "Lafiya qlau Hajiya daman Alhaji ne ya turoni ya ce na daukoki nace maki shi ya Aiko ni" Numfashi Zarah taja tare da sauke ajiyar zuciya irin andameta ta ce "Ka ce masa nace bazanzo ba" Cikin girmamawa ya ce "Umarnine ya bani Hajiya Dan Allah ki daure kishigo "nima sako na baka ka kai masa ta fad'a tana yin gaba Hango su Chuchu da tayi Yusuf dai tsaye yayi yana mamakin me hakan ke nufi Kallon driver da yayi tsaye yayi ya ce " lafiya dai ko Malam "Lafiya " ya basa amsa daidai lokacin da wayarsa tayi ringing "dubawa yayi yaga oga ne Sosai hankalinsa ya tashi a sanyaye ga d'aga Daga bangaren MD ya ce " basu tashi ba ne"a sanyaye driver ya labartawa md yanda sukayi da ita"tsaki daga bangaren MD yaja ya ce "Ka bata wayar" ranka ya dad'e tabar wajen fa"ba ta yanda za ayi a bita da wayar"Kallon Yusuf yayi ya ce "Eh to ga wani nan Wanda na gansu tare kilan shi zai iya sanin yanda yayi ya kai mata wayar " saida MD yaja numfashi kafin ya ce "zankira nan da 5 minutse ka tabbatar an kai Mata wayar" yana fad'ar haka ya katse kiran kallon Yusuf yayi dake shirin barin Wajen ya ce "dan Allah Abokina ko zakayimun wani taimako ka mik'awa yarinyar da tabar wajen nan. Wayar" shiru Yusuf yayi Dan maza basa shiga hostel din mata kuma yaga harta shige hostel Hango su Asmy a wajen da yayi ya sanyashi amsa ya ce "badamuwa bari na ba y'an uwanta su kai mata" Yawwa Abokina na gode "su Asmy na karasowa yusuf ya mik'awa Asmy wayar ya ce " Dan Allah Zarah zaki mik'awa wayar idan kun shiga"ba tare da sun kawo komai a ransu ba ta ce "okay" suna shiga Lokacin Zarah na Danna waya "Gado Chuchu taje ta haye tana maida numfashi Dan kanta ke ciwo mik'awa Zarah k'aramar nokiar Asmy tayi ta ce " gashi Akace wai a baki"da mamaki Zarah ta ce "Nikuma" bata k'arasa maganar ba saka makon ringing d'in da wayar tayi Kallon number tayi taga An rubuta oga a jiki Kallon Asmy tayi itama ta Kalleta ta ce "Ki d'auka Inajin ko wayace zakiyi" da wa kuma"Zarah ta fad'a tana turo baki"ki amsa kiji ko meye cewar Asmy a sanyaye Zarah tayi picking call din"Jin shiru ya sanyata cewa Hello "Cikin sayayyar muryarta " Daga bangaren MD saida ya lumshe ido "Jin shiru ya k'ara sanya Zarah cewa " Hello ko ba aji"nan ma shiru Ba ansa dubawa tayi taga har lokacin ba a katse ba cike da jin Haushi ta ce "Zanfa kashe tunda baza ayi magana ba " Sai sannan MD yayi k'arfin halin cewa "Hey" saida gaban Zarah ya bada daram jin muryar da ta jima batajita ba saurin fusgewa tayi tare da hade rai tamau ta ce "waye" Mijinki ne"Ya bata amsa kai tsaye"Waro ido Zarah tayi kafin taturo baki kamar yana gabanta ta ce "Ni ai bani da miji budurwa ce" daga bangaren MD murmushi yayi ya ce "To Mijinki na Wata Tara" Hararar wayar tayi kafin ta maida kunnanta tana turo baki tayi shiru"Chan Bayan few seconds ya ce "na turo a daukeki kince bazakizo ba why?Ta tsinkayi muryarsa "Bana ra'ayi " Ra'ayin me?zuwan?Okay to ni ina ra'ayi "tsaki taja a ranta ta ce " Dan rainin wayau kawai to bazanzoba "a fili kuwa cewa tayi " saika hakura"bansan hakan ba "Hakurin?Eh" To sai kayi kuka"dukda baison yi Dariya saida ya danyi Wanda hartajiyo daga wayar ya ce "Kina son ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login